Farouk ya gigice ya ruɗe, gaba ɗaya ya rasa me ke masa daɗi. Kai tsaye gidan Daddy ya nufa, yana gumi ya zayyane masa komai. Daddy ya dubi Farouk yana jin ƙarin ƙaunar yaron a zuciyarsa, ba zai taɓa mance halaccin da yaron ya yi masa ba.
“Farouk matarka bata zo nan ba.”
Ya sharce gumin ya ce,
“Daddy a taimaka a bani address ɗin gidan Abba.”
Daddy ya bashi tare da jaddada masa kada ya tafi yanzu ya bari sai gobe.
Farouk yana ficewa ya saita kan motarsa zuwa Maƙarfi. Ba karamin gudu ya yi ba, cikin lokaci ƙalilan ya bayyana a garin. Bai sha wahala ba wajen kai kansa gidan Abba.
A lokacin sun idar da Sallar Isha’i, suna zaman cin tuwo. Farouk ya yi Sallama, Abba ya leƙo yana mamaki,
“Farouk lafiya kuwa? Me ke faruwa?”
Ya ɗan sunkui da kai, hakan yasa Abba bashi hanya suka shiga ciki.
Babu wata doguwar gaisuwa ya zayyanewa Abba komai game da abin da ya faru. Abba ya yi shiru yana jin tausayin Farouk, tunani ne fal a cikinsa kamar ya gaya masa gaskiya, sai kuma ya girgiza kai,
“Umar ka natsu ka dawo hayyacinka, Suhaila ba za ta taɓa ɓacewa ba, duk inda take ba za ta iya yin kwanaki biyar ba tare da ta neme ni ba, banso ka taho ba, da ka sani ka kirani a waya sai mu yi magana.”
Farouk ya girgiza kai,
“Abba ina za ta je to? Na shiga damuwa ƙwarai. Don Allah Abba idan akwai wasu ‘yan uwa ni ka bani adireshinsu sai in nemo inda suke don Allah.”
Abba ya yi tunanin da farko Farouk taimakonsa ya yi ya auri Suhaila, sai yanzu Wata zuciyar take sanar da shi harda wani abu a ɓoye a cikin zuciyarsa.
Da ƙyar Abba ya lallaɓa shi, ya miƙe ya yi masu sallama. Kai tsaye Zaria ya nufa, ya yada zango a wani hotel.
Bayan ya idar da Sallolinsa ya nufi waje ya zauna yana kallon yadda kowa ke walwala da gani babu wata matsala da ke tattare da su. Nan da nan ya sake jin wani irin ƙunci, duk da babu wani abu da ya taɓa haɗa shi da ita, amma kuma kewarta yake ji.
Gabaɗaya sai ya ji ya ƙara tsanar komai da kowa, yana da tabbacin muddin bai ga Suhaila ba, babu wanda zai sake gane kansa.
Haka ya kwana ya kasa ko da rintsawa, sai rungumar Alqur’ani da ya yi, ya zame masa sanyin zuciya.
Washegari da asubahin fari ya bar garin zuwa Abuja. A natse ya shigo gidansu, daidai Alhaji yana zaune yana karyawa, ga dukkan alamu ba a gidan aka yi Break ɗin ba. Ya sunkuya har ƙasa ya gaida shi. Hannu kawai ya ɗaga masa ya miƙe ya bar wurin, fuskarsa ɗauke da murmushi. Farouk ya kasa motsawa har Anti ta ƙaraso tana dubansa,
“Farouk mahaifinka fa ya ɗau zafi. Baya cin komai da ya fito daga gidan nan, ya hana kowa taɓa motoci, yasa an rufe account ɗinmu. Yanzu abin da yake yi ya kamata kenan?”
Ya ɗago ya dubi Anti ido cikin ido, ita kanta ta faɗa. Ya ce
“Anti dole zamu nemo Suhaila mu dawo da ita gidan nan, idan ba haka ba Alhaji sai…”
Tsawa ta daka masa,
“Kai dalla dakata! Akan ɗan wannan fushin kake son karaya? Ka rabu da shi zai gaji ya sauka ne. Ni yanzu damuwata kasan yadda zaka yi Sadiq ya saki Ummi Ka aureta, kana yin hakan komai zai zama tarihi.”
Tunda Farouk yake bai taɓa ganin mace mai kafaffiyar zuciya kamar Anti ba, mamaki yasa ya dinga kallonta kallo mai cike da mamaki. Kawai ya girgiza kai ya miƙe ya fice gabaɗaya daga gidan. Ya yarda wanda ya yi nisa baya taɓa jin kira.
*****
Tun Farouk yana ɗaukar abun wasa har ya koma rama a tsaye, abin da ke sake ɗaure masa kai babu wanda yake tambayarsa halin da Suhaila take ciki, duk sun kawo idanu sun zuba masa.
Gabaɗaya ya daina shiga aji bare ya haɗu da Ummi. Yau kamar an jeho shi ya shiga gidan Mama Karima. Suhaila tana ciki ita da Suwaiba tana koya mata karatu, ta ji sassanyar muryarsa ya yi Sallama. Cak! Ta dakata tana jujjuya muryar, gabanta yana tsananta faɗuwa. Duk da bata nemi komai ta rasa ba, amma kullum zuciyarta ta gaza daina tausayin Farouk. Ko ba komai ya yi mata halacci. Kullum sai ta karanta takardar da ya bata, tana jin wani abu yana tsirga mata.
Da sauri ta miƙe har ta kai bakin ƙofa ta ji muryar Mama Karima,
“Koma ki zauna zan je in duba.”
Jikinta a sanyaye ta juya ta zauna, tare da rafka tagumi. Suwaiba ta ƙaraso kusa da ita ta cire mata tagumin ta ce,
“Anti kin ce tagumi babu kyau yau kuma naga kinyi.”
Suhaila ta yi murmushi ta kauda idanunta da suka kawo ruwa. Ko sai yaushe zata yi bankwana da matsala?
Mama Karima ta shigo tana dubanta,
“Ki ɗauki niƙaf kisa ki je ki kai masa abinci da ruwa. Ban ce ko magana ki yi masa ba bare ya gane ki.”
Jiki babu ƙwari ta yi yadda Mama ta ce mata, sai dai tana sunkuyawa gabansa ta buɗe robar ruwa ya kafeta da idanu gabansa yana tsananta faɗiwa. Zuciyarsa take gaya masa yasa hannu ya buɗe niƙaf ɗin. A hankali ya kai hannu zai buɗe, a lokacin kuma ya ji Sallamar Mama a tsakiyar falon, dole ya kaucewa abin da ya yi niyya, har ta tashi ta shige. Ya dubi Mama ya ce,
“Mama wacece wannan kuma?”
Sai da ta zauna kamar ba zata bashi amsa ba, sai kuma ta ce,
“Mijinta ya kawota ajiya. Ya su Alhaji?”
Ta kauda maganar. Bai amsa ba, bai kuma ce komai ba, haka yaƙi tashi a dole sai ya sake ganinta.
“Mama a kirawota ta kwashi kayan abincin.”
Mama Karima ta karkace ta kirawo Suwaiba ta ce ta kwashi kayan. Ba haka yaso ba, dole ya yi mata sallama ya tafi. Sai dai abin mamaki washegari sai gashi ya dawo, tunda Mama ta fahimci ya fara ganowa sai ta hana Suhaila fitowa kwata-kwata. Haka ya gaji da sintiri, ya fara shirye-shirye babu ɓata lokaci ya yi Sallama da Alhaji akan zai je wani Course ya wuce abinsa ya bar ƙasar zuwa London.
*****
Yau Ummi tana kwance ta yi ɗaiɗai a ɗakinta tana barci, yau ta mance bata kulle ƙofarta ba, kamar yadda ta saba, hakan yasa Sadiq ya shige ɗakin yasa key. Kamar ance ta buɗe ido, ta hangoshi tsaye daga shi sai gajeren wando. Ta daddage ta fasa ihu, amma ko gezau bai yi ba. Da Allah ya bashi sa’a ya haye kanta, babu maganar wasa ko lallashi ya fizge duk kayayyakin jikinta. Ihu take yi, tana yakushinsa, tana roƙonsa kada ya taɓa wa Farouk kayansa. Yasa bayan hannu ya buge mata baki,
“Farouk ya fi ƙarfinki, yanzu ni ne daidai da ke.”
Tana ji tana gani ya kauda budurcin da ta jima da yi wa Farouk tana ji. Bai ƙyaleta ba, sai da ya yi mata kaca-kaca. Yana tashi yaga bata motsi, ko a jikinsa ya yayyafa mata ruwa tana buɗe idanun cikin azaba ya jefeta da zafafan kalamansa,
“Ban iya lallashi ba, sai ki lallaɓa ki gyara kanki. Duk nasan shirinku shiyasa nayi maganinki. Allah ya ga zuciyar Suhaila shiyasa ya hanani mallakarta, ya baiwa abokina mai sanyin hali kamarta. Maimunatu ni Sadiq ni ne daidai da ke.”
Kawai yasa kai ya fice.
Ummi ta fasa ihu wanda baya fita saboda azabar kuka.
Da ƙyar ta rarrafa ta shiga banɗaki, tana shiga ruwan zafi ta fasa ƙara. Ta yi kuka, ta tsine masa yafi a ƙirga, daga ƙarshe ta lallaɓa ta kirawo Momi ta gaya mata tana kuka. Momi ta an tayo uban ashar ta aunawa Sadiq. Ji take yi kamar zuciyarta zata fito waje saboda ɓacin rai.
******
Farouk ya zama abin tausayi, ko acan ɗin bai cika shiga hulɗar kowa ba. Sai yau da ya sami kira daga abokinsa, ya dinga roƙonsa ya zo su shiga gari. Dole ya amince masa ko don neman sassauci a cikin zuciyarsa.
Sun yi nisa da gida, Alhaji ya kira shi. Mamaki ya kama shi da ya ga lambarsa, alamun mahaifinsa ya shigo ƙasar kenan. Kamar ba zai ɗauka ba, saboda ya yi tunanin mahaifinsa zai fi kowa fahimtarsa sai ya ga saɓanin hakan.
“Alhaji Barka da warhaka.”
“Kana ina? Ina hanyar gidanka.”
Sai da ya ɗan yi jim, kafin ya ce,
“Alhaji mun fita ne.”
Ya gyaɗa kai,
“Ok zan ajiye maka saƙo a gidan, saboda zan bar ƙasar zuwa wata ƙasa nan kusa, akwai wani aikin da zan yi.”
Kawai ya amsa masa, yana mamakin saƙon menene haka? Bai tsaya tsawaita tunani ba, suka nausa wani wurin da abokinsa Sulaiman.
Farouk bai sake waiwayar gida ba, sai cikin dare, ya dawo. Mamaki ya kama shi, ganin gidan an gyare ko ina, sai ƙamshi kawai ke tashi. Dining table an jere shi da abinci. Mmakinsa ya ƙaru, babu shiri ya nufi table duk ya bubbuɗe komai. Hakan nan ya tsinci kansa da son cin abincin, kasancewa ya ɗibo yunwa. Sosai ya ci abincin ya dawo falo yana tunanin aikin mahaifinsa ne. Sai dai kuma ina ya samo girki irin na gida? Girkin ma kamar ya taɓa cin shigensa. Yana nan zaune a falon, ta fito sanye da doguwar riga mai ɗaukar idanu. Ta yi kyau sosai, ta gyara gashin kanta. Kafeta ya yi da idanu babu ko ƙyaftawa, yafi tunanin gizo take yi masa. Ita kanta sai yanzu kunya ta kamata ta rufe idanunta da tafukan hannunta da suka zanu da ƙunshi. A gigice ya miƙe ya ce,
“Suhaila! Ke ce? Wa wa ya kawoki nan?”
Ta rasa dalilin da take jin farin ciki tsantsa, bata san lokacin da ta rugo ta rungume shi tsam, tuni hawaye masu ɗumi suka wanke mata fuska,
“Farouk ka yafe min, ka yafe mini kuskurena Ka yafe mini sanyaka a cikin tashin hankalin da nayi ba da ninya…”
Cak! Ta dakata da kalaman da take gaya masa a lokacin da ta dawo hayyacinta, ta fahimci girman wautar da ta yi. Tana ƙoƙarin raba kanta da jikinsa, ya sa hannu cikin mutuwar jiki ya mayar da kanta ƙirjinsa yana jin wani sanyi yana tsirga masa. A hankali ya kai hannu yana shafa tsakiyar kanta zuwa gadon bayanta. Yana jin wani irin sanyi yana ratsa shi.
Sun jima tsaye a haka, kafin ya saki ajiyar zuciya tare da janyeta daga jikinsa. Kowanne ya nemi wurin zama ya zauna, ba tare da ɗaya ya furtawa ɗan uwansa wata magana ba.
Suhaila ta miƙe ta shige ɗakinta, tana nazarin irin miskilancin Farouk, da alamun za ta sha wahalarsa.
Barci ke fizgarta, kamar daga sama ta ji mutum a bayanta. Ta so ta tashi, sai dai ya hana faruwar hakan ta hanyar yi mata rumfa da jikinsa.
“Duk tsawon lokacin da nake ta nemanki a ina kika ɓoye?”
Yanayin da suke ciki ya shagalar da Suhaila, don haka ta yi magana ƙasa-ƙasa,
“Ina gidan Mama Karima.”
Bai nuna mamakinsa ba a fili, amma tabbas abin ya bashi mamaki. Ya saki ajiyar zuciya yana ƙoƙarin rabata da kayan jikinta, zai so kafin ya dawo ƙasar ya yi wa Suhaila ciki, ta yadda dole Anti ta haƙura ta kuma yi fatali da tsattsauran ra’ayinta.
Gabaɗaya sun afka wata duniya, babu abin da Farouk yake hange sai ya cimma burinsa akan Suhaila. Ya gama sakankancewa ya nemi gabanta sama ko ƙasa babu komai, kamar an shafe da siminti. A gigice duk suka tashi zaune, ya lalubi haske ya kunna. A tare suka kaiwa wurin kallo babu komai. Ya sake dubanta a tsorace. Sai yanzu tunani ya zo masa ko dai ba Suhaila ba ce aljana ce? Tunda yake bai taɓa ganin irin tashin hankalin da yake gani a yanzu ba. Dama an taɓa halittar bawa a haka? Bai san lokacin da ya ce,
“Dama ke ba mutum ba ce? Ta ina fitsari ke fita a jikinki? Ta ina kike yin al’ada?”
Suhaila ta yi matuƙar kaɗuwa, don haka ta maƙale jikinta babu abin da take yi sai kuka. Ran Farouk ya sake ɓaci, gashi ya riga ya kai maƙura, dole ya miƙe ya je ya yi wa kansa ‘yan dabaru.
Suhaila ta miƙe ta shiga banɗaki abin mamaki sai ta ga ya dawo lafiya lau kamar yadda yake da. Ta zaro idanu, a lokaci guda tsoron kanta ya shigeta.
Hankalin Farouk bai kwanta ba, har sai da ya kira Alhaji a waya, yake tambayarsa shi ya kawo Suhaila? Alhaji ya tabbatar masa da haka abun yake. Ya tambaye shi ko lafiya? Farouk ya gaza furta komai, sai sauke wayar da ya yi. A natse ya shiga ya watsa ruwa ya yo alwala, anan falon ya shimfiɗa Sallaya ya fara gabatar da nafilfili. Suhaila kuwa duk ta muzanta, kuka kawai take yi.
*****
Momi ce zaune tana ƙarewa Ummi kallo a lokaci ɗaya ta kai hannu ta ciro wani magani, ta miƙa mata,
“Karɓi wannan ki tafasa ki dinga shiga ciki, zaki haɗe ki koma tamkar budurwa, ta yadda shi Farouk ɗin ba zai taɓa ganewa abokinsa ya sanki a ‘ya mace ba. Ki daina koke-koken nan, saboda idan kika lalace ba lallai ki burge Farouk ba. Mun yi magana da Laila Insha Allah yana dawowa za a ɗaura maku aure. Yanzu mun sa wani boka ya yi aiki, kafin Farouk ɗin ya dawo Sadiq zai sakeki, sai ki dawo gida in sake gyareki.”
Ummi ta dubi maganin tana jin wani irin sanyi yana ratsata.
“Na gode Momi.”
Haka suka ci gaba da tattaunawa har ta yi mata sallama ta fice.
Kwana uku Ummi ta yi amfani da maganin nan ta ji garau, a ranar kuma da daddare Sadiq ya sake komawa ya yi mata kaca-kaca kusan ma abinda ya yi mata na yau ya fi na farkon. Yana murmushi ya miƙe ya barta anan kwance ko ɗan yatsanta bata iya ɗagawa.
*****
Abin duniya ya fara isar Laila, yau ta yanke shawarar zata je ta baiwa Alhaji haƙuri, domin ta wahala da irin matakin da ya ɗauka akansu.
Yana zaune yana latsa wayarsa ta ƙara so ta zube a ƙasa,
“Don Allah Alhaji ka…”
“Dakata don Allah! Tashi ki bar min ɗaki ko kuma ki ga mafi munin wulakanci. Ki tashi!”
Jiki babu ƙwari ta miƙe tana waiwayarsa. Babban damuwarta kullum ta kira wayar Farouk bata samu, komai ya tsaya mata cak! Sai dai har yanzu babu danasani a cikin zuciyarta.
*****
Sannu a hankali tsanar SUHAILA yana cin nasarar huda zuciyarsa, sau tari yakan zauna ya yi tunanin laifin me ta yi masa haka? Tana bashi tausayi matuƙa, amma da zarar ya yi ninyar yi mata magana sai wata zuciya ta hana shi.
Yau abokinsa Sulaiman ya kawo masa ziyara shi da matarsa Salma. Sun karɓe su hannu bibbiyu, har suka ɗan taɓa hira, kafin Sulaiman ya buƙaci su zo a ɗan fita yawan buɗe ido. Suhaila ta ji daɗin hakan kasancewar kaɗaici ya isheta.
Farouk ya lalubo hannunta ya riƙe, hakan yasa ta kaiwa hannun duba, sannan ta ɗago ta dube shi, itama ita yake kallo ido cikin ido. Sosai tausayinta ke addabarsa, ya rasa me ke shirin faruwa da su.
Suna isa wurin kowa ya ja matarsa gefen wani ruwai mai sanyi da daɗi. Suna nan zaune ta yi magana a hakanli,
“Ko sai yaushe matsalata za ta zama tarihi?”
Ya dubeta duba na tsanaƙe ya ce,
“Idan kika ji matsalar wata sai kin fahimci taki ba komai ba ce.”
Ta kafe Sulaiman da matarsa da ido yadda take kwance a ƙirjinsa, a lokacin da suke sumbatar juna idanunta suka haɗu da na Farouk, wanda shima ya ci nasarar ganinsu. Duƙar da kai ta yi tana wasa da yatsu, babu zato ya jawota jikinsa ya haɗa fuskokinsu wuri guda yana magana dab da bakinta, hakan yasa ta lumshe idanu tana jiran abinda yake da ninyar yi ya faru,
“Me ya sa kike kallonsu?”
Abin da ya buƙata kenan a lokacin da hucin bakinsa yake dukan nata, wanda saboda tsananin kasala bata san lokacin da ta sake kai bakinta gab da nasa ba. A hankali ya ɗora laɓɓansa a bisa nata, yana jin wani irin feelings yana taso masa. Ita kanta bata san lokacin da ta cusa hannunta cikin gashin kansa ba, tana sosawa a hankali.
A lokaci guda tunani ya dawo masa, ya tuna kawai zai tayar da hankalinsa ne a banza, don haka ya zare kansa yana jin zuciyarsa tana tafarfasa.
Gaba ɗaya ta rasa abinda ke yi mata daɗi, ta rasa dalilin irin wannan matsalar. Jikinta babu ƙwari ta miƙe ta sauya wurin zama gaba ɗaya ta yi tagumi, ta nausa duniyar tunanin marigayi Adnan.
Abubuwan da suka faru da ita kamar almara take ganinsu, yanzu babu abinda take da burin sani a duniyarta da ya wuce dalilin waɗannan matsalolin. A lokaci ɗaya tunaninta ya tsaya akan aljanu ne a jikinta da basu son ta yi aure.
‘Amma me ya sa ba su kashe Farouk ba?’
Wani ɓangare na zuciyarta ta an tayo mata wannan tambayar. Ta lumshe idanu tana da tabbacin ƙarfin addinin Farouk ba zai taɓa barin wani abu ya cutar da shi ba. Akwai kyakkyawar mu’amala a tsakaninsa da addininsa. Ta jima bata ga mutum mai yawaita kusantar kansa ga Mahaliccinmu ba, kamar Farouk. Duk da hakan ba yana nufin Allah ba zai jarabceshi bane, kawai jarabawar za ta zo masa ne da sauƙi.
Ji ta yi an dafa kafaɗarta, ta ɗago asanyaye suka zubawa juna idanu, daga bisani ya ce,
“Tashi mu tafi gida.”
Babu musu ta yi ƙoƙarin tashi, ya miƙa mata hannu kamar ba za ta kama ba, sai kuma ta kama ya ɗagota.
Bayan sun koma gida sun natsa, ya sake kai kansa a karo na biyu, babu labari. Dole ya saɓule kansa ya barta anan. Cikin ikon Allah barcin wahala ya kwashe shi ba tare da ya yi addu’a ba.
‘Hahahaha!! Kana tunanin ka fi mu wayo ne? Kai ne mutum na farko da ka taɓa wahalar da mu, mun je gun mahaifinka shi ma ya ƙona mu. Mun gaya maka ka rabu da Suhaila ka zauna lafiya. Kada kuma kayi tunanin mu aljanu ne, Wallahi mu mutane ne kamar kowa. Yau sai ka baƙunci lahira…
‘Farouk ya fara ƙaƙari sakamakon wani irin shaƙa da ta yi masa, gabaɗaya idanunsa sun firfito waje, kumfa kawai ke fitowa daga bakinsa.