Skip to content
Part 13 of 17 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Ta yi murmushi kawai tana jujjuya kalamansa.

Bayan ya gama ne, ya ce ta je ta cewa Anti a kirawo Sadiq Shi zai iya taimaka masa ya yi wanka.

Da sauri ta fito domin isar da saƙon. Abin mamaki Anti ce ke zaune tana cin abincin da Suhaila ta girka. Har cikin zuciyar Suhaila ta ji daɗi sosai, tana wucewa ta haɗu da Sadiq ɗin, don haka kawai ta sanar masa.

Sadiq yana shiga ya rufe ƙofar duk suka yi murmushi. Farouk ya miƙe ya faɗa banɗaki ya yi wankansa fes! Ya yi alwala ya fito yana dubansa,

“Sadiq yarinyar nan ta iya jinya sosai.”

Sadiq ya yi murmushi yana ji a zuciyarsa dama shi ya yi sa’ar mace kamar Suhaila, sai yanzu yake ganin girman kuskuren da ya tafka.

“Kai dai yi ka shirya kafin ta kamaka.”

 Yana murmushi ya koma kekensa ya zauna yana cewa,

“Ɗaukata zaka yi mu fice, in shiga masallaci da ƙafafuna in gaida Ubangijina.”

 Sadiq ya turo shi yana dariya. Tare da Alhaji suka fice daga gidan. Suhaila ta nemi wuri ta zauna tare da tagumi a falon. Anti ta ƙaraso tana dubanta duba na ƙasƙanci, “Ke mayyar ina ce? Da muka koreki gidan uban wa kika je kika raɓe?”

 Suhaila ta sunkuyar da kanta tana jin kamar ta tashi ta fice kawai.

“Ba za ki yi min magana ba kike wani sumi-sumi da kai kamar tsohuwar ‘yar bori?”

 “Anti ƙaddara ce, ki yi haƙuri ki karɓeni a matsayin ƙadd…”

 Anti ta daka mata wata tsawa,

“Rufe min baki munafuka. Zan fasa shegen bakin nan. To bari kiji, Farouk yana samun lafiya zaki tattara ki bar min gidana tunda ba tare da ubanki aka gina gidan ba.”

 Suhaila ta goge hawayen fuskarta, sannan ta miƙe ta ce,

 “Allah ya kaimu.”

Ta shige ɗakinsa ta fashe da kuka da iya gaskiyarta. Zuciyarta kawai ke tafarfasa.

Ko kafin Farouk ya dawo har ta share hawayen ta sake gyara masa ɗakin, ta zauna kawai tana Karatun Alqur’ani.

Da sauri ta tashi ta ƙarasa shigowa da shi, ta faki idanunsa ta goge hawayen da suka zubo mata babu shiri. Yana zaune a keken yana dubanta. Da ƙyar ta iya mayar da shi gadonsa ta koma can gaban dressing Mirror ta zauna kanta a ƙasa. Sosai ya kafeta da idanunsa yana jin shima nasa ran yana ɓaci. Ta ɗago ta dube shi, muryarta can ƙasa ta ce,

“Ko dai kana da buƙatar wani abu ne?”

Girgiza kansa ya yi sannan yasa hannu ya kirawota. Sai da ta yi kamar ba zata je ba, sai kuma ta miƙe ta ƙaraso gabansa yasa hannu ya jawota ta faɗa ƙirjinsa,

“Ba ka da lafiya kada in ji maka ciwo.”

 Cikin damuwa ya yi mata magana,

“Suhaila me ke damunki? Waye ya ɓata maki rai bayan barinmu gidan nan?”

 Sai da ta yi kokawa da zuciyarta sannan ta ce,

“Haba yanzu yanzu wa zai ɓata min?”

 Shiru ya ɗan yi kamar ba zai yi magana ba, sannan ya ce,

“Kada kiyi min ƙarya, domin basu daga cikin siffofinki. Anti ce ko? Ki yi haƙuri watarana sai labari.”

Ta kasa daurewa, don haka ta fara kuka a hankali, hawayen suna zuba har cikin ƙirjinsa. Da tasan yadda kowane ɗiga na hawayenta yake fasa ƙirjinsa da bata yarda hakan ya faru ba. Ji ta yi ya yi shiru kamar baya motsi hakan ya firgitata ta ɗago tana goge hawayenta. Ta kai dubanta gareshi ya kafe saman ɗakin da kallo shi kaɗai yasan duniyar tunanin da ya faɗa. Tunani yake yi sai yaushe Anti za ta so Suhaila? Duk irin tashin hankalin da ta gani akan yadda aka guji ɗanta Suhaila ta zauna amma hakan bai isheta ishara ba? Me kuma take so? Yaushe Suhaila za ta sami ‘yanci kamar sauran mata?

Yana da buƙatar zuwa ya yi magana da mahaifiyarsa. Ƙoƙarin tashi yake yi, hakan yasa ta taimaka masa ba tare da tasan inda zai je ba.

 “Yanzu ka dawo ya kamata ka huta. Ina za ka je kuma?”

 Bai yi magana ba, ya fara murza keken da hannu guda. Ta yi ƙoƙarin taimaka masa ya girgiza kai, ya fice da kansa.

Tana zaune ita da wata doguwar mace mai kyau da ita. Abin da bai sani ba yarinyar ce suke son haɗa shi da ita, akan zata jira shi idan ya samu lafiya sai a yi bikin.

“Anti ina son magana da ke.”

Ta dubi Rumaisa ta dawo da dubanta gare shi,

“Ka yi maganarka Rumaisa ‘yar gida ce, ‘yar aminiyata ce Hajiya Safiya, baku haɗuwa saboda dukkanku ba mazauna bane. Rumaisa ga Yayanki Farouk ku gaisa.”

Rumaisar cikin ƙwalisa da iyayi ta gaida shi. Ya kauda kansa ya ƙi amsawa yana sake duban Anti.

“Anti, ya kamata ki fahimta a yanzu ki gane mai sonki tsakani ga Allah. Suhaila ita kaɗai ce bata gujeni ba a halin da nake ciki, ta tausaya min a matsayinta na matata. Me ya sa ba zaki rangwanta mata ba? Me ya sa ba zaki gode mata da irin ɗawainiyar da take yi da gidan jininki ba? Duk duniya wacece zaki samu wacce za ta yi sadaukarwa dan Allah kamar yadda Suhaila ta yi? Idan har duk abubuwan nan da suka faru ba za su sanya ki sota ba, sai inɗauketa mu koma gidanmu. Ina jin tsoron itama ta juya min baya kamar sauran.”

 Anti ta zaro idanu,

“Yanzu ni me na yi mata da zaka zo ka tasani a gaba kamar wata ‘yarka? Kasan Allah ni ban zauna wuri guda da Suhaila ba bare ma har inyi mata mugun kallo. Na shiga uku! Ba dai har yarinyar nan ta fara haɗa mu faɗa ba?”

Girgiza kai ya yi yana mamakin dalilin da zai sa Suhaila kuka haka.

“Ko ɗaya ba ita ta gaya min ba. Na fita na dawo na sami idanunta sun yi ja saboda kuka, kuma nasan ke kaɗai ce sai Jawaheer a gidan nan kuma ina sane da duk baku sonta.”

 Anti ta zura masa ido tana mamakin tunda take Farouk bai taɓa tsareta kamar yadda yayi yau ba. Lallai idan hakane ya zama dole ta ƙara shiri. Tana kallonsa ya juya kan kekensa ya fice. Rumaisa ta dubi Anti ta zaro idanu,

“Anya zan iya? Haka ta shanye shi baya ji baya gani? Gaskiya Anti Akwai matsala.”

 Anti ta yi yaƙe,

“Wannan ba matsala ba ce Rumaisa, ni zan shawo kan komai.”

Rumaisa ta yi shiru tana sake siffanta Surar Farouk a zuciyarta. Indai haka Guy ɗin yake babu ko shakka zata jira ya warke ta aure shi domin nunawa ƙawaye irin nata zarran da ta yi masu. Ta tabbata irin wannan ba ƙaramin ƙara mata daraja zai yi a idon duniya ba. Abin da yasa ma a yanzu ba za ta iya aurensa ba saboda gudun ƙawaye suyi mata dariya, za su iya zuwa su yi ta gulmarta akan mai zama a keken guragu ta aura, daga nan shikenan Class ɗinta ya ragu.

“Anti ki kwantar da hankalinki, insha Allahu sai na ƙwato maki Farouk a hannun tsinanniyar can. Ke dai kiyi addu’ar Allah ya bashi lafiya cikin gaggawa.”

Anti ta jinjina kai alamun ta gamsu da wannan bayani.

Farouk ya koma ɗaki ya sake samunta ta yi tagumi, ya sa hannu ya cire mata tagumin duk suka dubi juna.

“Anti ta ce min baku haɗu ba, ki gaya min abinda ya ɓata maki rai.”

 Suhaila ta ɗan yi jim kafin ta ce,

“Wai zuwa kayi ka sameta? Ni kawai Abbana na tuna babu wanda ya ɓata min.”

Farouk ya kasa gamsuwa da bayananta, don haka ya yi alƙawarin zura idanu sosai domin ya tabbatar da abinda yake zargi. 

Za ku yi hakuri da ni, akwai wani rubutu da nake yi ana buƙatansa da gaggawa, don haka yasa kuke jina shiru. Amma insha Allahu zan dinga ƙoƙari duk da ba na son in cika matsawa kaina.

Ya lumshe idanu yana jin ko ta ina zafi. Ya yi tunanin zai sami sukuni ta wannan hanyar sai dai kuma kamar abin sake ta azzara yake yi. Ya rasa a cikin irin mutanen da ya kamata ya sanya Anti a ciki. Ta hana kanta sukuni da zama cikin kwanciyar hankali, ta hana mijinta ta hana ɗanta da take tutiyar tana sonsa fiye da komai.

Suhaila ta yi saurin ficewa daga ɗakin, hakan ya bashi daman miƙewa tsaye yana kaiwa da komowa cikin damuwa. A natse ya haye gadonsa ya yi rigingine yana tunani.

Suhaila ta dawo kawai ta yi turus tana dubansa ido cikin ido. Bai damu da kallon mamakin da take yi masa ba, ya kauda kansa kawai. Da sauri ta ƙaraso ta haye gadon, tare da tallafo kansa,

“Ya aka yi ka iya hawa gadon kai kaɗai?”

 Dubanta kawai yake yi, tana bashi tausayi sosai,

“Allah ya ba mu baiwa kala-kala. Har banɗaki zan iya kai kaina. Kawo min tea.”

Babu musu ta mayar da kansa ta je kitchen ta jona ruwan zafi, sai ga Anti da Jawaheer sun biyota,

“Uban me kike yi min a kitchen kamar gidan tsohonki?”

Cewar Anti da ke tsaye tana zazzare idanu. Suhaila bata ce komai ba ta duƙar da kanta kawai tana jujjuya lamarin.

“Kina jina ko? Ki tattara kayanki ki bar min gidana, jinyar ce bana so ni zan kula da shi, tunda a lokacin da yake jariri babu wacce ta tayani kulawa da shi bare ace ai na gaza ne.”

Suhaila ta juya da nufin barin kitchen ɗin, Jawaheer ta fizgota ta watsa mata ruwa a kofi mai sanyi, wanda yasa ta yi firgigit tana jin saukar ruwan har cikin jikinta. A razane ta ɗago tana duban Jawaheer fuskarta cike da hawaye,

 “Jawaheer me na yi maki?”

 Sai da ta dubeta Sama da ƙasa sannan ta ce,

“Kin shigar mana rayuwa, shi ne abinda kika yi mana. Da ace zaki yi wa kanki faɗa ki rabu da mu, ai da kin huta.”

 Girgiza kanta ta yi hawayen suna sake zuba,

 “Insha Allah daga ranar da Yaya Farouk ya sami lafiya zan bar maku gidanku in kama gabana.”

 Ta wuce da sauri ta wuce can baya ta sunkuya tana shessheƙar kuka. Abin da bata sani ba wurin da ta sunkuya daidai saitin window ɗin Farouk ne. Kamar a mafarki yake jin shessheƙa hakan yasa ya tashi ya buɗe labulen ya zura mata idanu. Kuka take yi da iya gaskiyarta, dole duk wanda ya ci nasarar ganinta a irin wannan yanayin ya ji tausayinta ya kama shi. Komawa ya yi gado ya kwanta shiru, idan ya sanar da Alhaji komai zai sake lalacewa ne a maimakon ya gyaru.

Sai da ta gama kukanta sannan ta share hawayen ta koma ta juye masa ruwan zafin ta shigo da sallama. Ya yi saurin rufe idanunsa kamar mai barci, hakan yasa ta ƙaraso ta zauna a bakin gadon shiru..

“Suhaila ina kika je nake ta jiranki?”

Ta tsinkayi muryarsa a tsakiyar kanta. Firgigit ta yi ta fara kame-kame. Bai ce komai ba ya nemi da ta dinga bashi tea ɗin a baki. Babu musu ta aiwatar da abinda ya gaya mata cike da saƙe-saƙe.

*****

Tafiya kawai take yi bata san inda zata je ba, dogon layin ta miƙa samɓal babu ko waige. Wata dattijuwa ce take tafiya da sandarta a hannu. Ko kafin Suhaila ta ankare har matar nan ta tuntsura ta zube a ƙasa. Jikinta har kyarma yake yi saboda tausayin tsohuwar. Da sauri ta ɗagota ta dawo da ita inuwa sannan ta je ta samo mata ruwa ta kawo mata.

Tsohuwar ta dubeta sosai ta ce,

‘Na gode. Allah ya yi maki albarka.’

Suhaila ta gyaɗa kanta,

“Babu komai. Ina za ki je ne in kai ki? Kin ga zaki sha wahala kafin ki isa.”

Tsohuwar nan ta sake kafe Suhaila da idanu, can ta ce

‘Kisa hannu a gefen wuyarki zaki ji kin taɓa wani abu ki ciro ki bani abun.’

Suhaila ta dubeta da mamaki, sai kuma ta aiwatar da abinda tsohuwar nan ta sanyata. Tana cirowa bata tsaya duba ko menene ba ta damƙa mata a hannu, sai a lokacin ta dubi hannun tsohuwar ashe kunama ce. Za ta yi ihu, ta ji kamar an sanya cingam a liƙe bakin.

 ‘Ki kwantar da hankalinki. Cuta ce a jikinki wanda aka saka maki tun kafin ki zo duniyar nan. Ba kowa bane ya sa maki face ‘ya ta. Zata ɗauki fansa akan mahaifinki ne. Idan kina son ki ji gaskiyar lamari, ki sami mahaifinki da Yayansa da mijinki ku zauna sannan ki basu labarina, ki ce masu wacece JAAAMUU… Menene alaƙarsu da ita? Me mahaifinki ya yi mata har ta fusata take ɗaukar fansa akanki? Ni yanzu cuta ɗaya kawai na cire maki, wato cutar da ke ɗauke a cikin idanunki, wanda shi ke kashe mutane. Domin kuwa Jaamuu tana can tana gagarumin shiri akanki wanda zata tarwatsa duk wani jin daɗinki da na danginki. A yanzu haka mijinki ya fara tsanarki. Amma ki bi komai a hankali zaku sami nasara akanta. Tashi ki tafi na gode da wannan tausayawa.’

Suhaila ta miƙe kawai tana tafe tana waiwayenta har suka daina ganin juna.

A lokacin ta yi firgigit ta tashi jikinta duk zufa. Farouk ta gani a kishingiɗe yana karatun Alqur’ani cikin natsuwarsa. Bata san lokacin da ta ƙanƙame shi ba, gaba ɗaya ta mance da wai bai da lafiya jikinta sai kyarma yake yi.

“Me ya faru? Mafarki kika yi ko?”

Cikin rawar murya ta gaya masa komai. Ɗakin ya yi tsit kamar babu kowa. Tabbas shima mafarkin ya tashe shi daga barci, sai dai nasa da bambanci da irin nata. Shi kuma JAAAMUU ce ta zo masa cikin fushi da son ɗaukar fansa akansa.

Ya zama dole malamai su shigo cikin lamarin nan.

Da asubahin fari Farouk ya lallaɓa lokacin Alhaji ne kaɗai ya farka, baya son aga fitarsa kai tsaye ya tafi har gidan Daddy ya zayyane masa komai, Daddy ya yi shiru kafin ya nisa ya ce,

“Ikon Allah kenan. Wannan lamarin akwai ɗaure kai. Amma zan aika Ƙanina ya zo nan sai mu haɗu har ma da malamai a zauna a warware komai.”

Yana dawowa gidan ya fahimci ma’aikata suna iya ganinsa don haka ya fitar da kekensa a inda ya ɓoye ya hau ya ci gaba da tura kansa.

Suhaila ce ta tarbe shi da murmushinta sannan ta kama keken ta maido shi ciki. Ga mamakinsa daga fitarsa yaje ya dawo har ta tsaftace komai nasa ta adana su. Ɗakin idan banda ƙamshi babu abinda yake yi. Kai tsaye ta wuce kitchen bayan ta ajiye masa kayan da zai sanya. Ko kafin ta gama haɗa Break har ya yi wanka ya kimtsa. Ta dube shi da mamaki. Ko irin ramar nan ta marasa lafiya babu a jikinsa, sai ma wata alama ta hutu da jin daɗi.  

Yana ɗan murmushi ya ce,

“Ki shirya zuwa anjima da yamma zamu je gidan Daddy.”

 Bata kawo komai a ranta ba ta gyaɗa kai kawai.

<< Kaddarata Ce 12Kaddarata Ce 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×