Skip to content
Part 14 of 18 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

*****

Sadiq ne zaune yana latsa remote Ummi ta ƙaraso cikin wani irin shiga na ƙananun kaya. Abin ya bashi mamaki, don haka ya zuba mata idanu kawai. Ta ƙaraso tana wani irin yauƙi, daga ƙarshe ta ce, “Dama miliyan uku nake nema ka ba ni zan ja jari.”

Sadiq ya yi murmushin mugunta,domin yasan za a rina. Wato tunda ta rasa Farouk bari su tatse shi kenan. Yana murmushi ya ce,

“Haba akan ɗan kuɗin nan kike noƙewa? To miliyan biyar zan baki ina fatan za su isheki?”

Farin ciki ya kama Ummi ta maƙalƙale shi. Babu shiri ya tashi ya je ya sha magungunansa ya dawo gareta. A ranar sai da ya yi mata kaca-kaca wanda yasa ta ji duk ta tsani kuɗin. Tana kuka tana roƙonsa akan ya ƙyaleta amma ko kallo bata ishe shi ba. Ga dukkan alamu ma da gangar yake aiwatar mata da komai. Ummi ta sha kuka kamar ranta zai fita, indai haka auren yake ta tsani auren gaba ɗaya.

Kwana biyu da ta cika matsa masa akan kuɗin, sai ya bata Cheque na miliyan biyar ya sake ƙosar da kansa. Haka ta lallaɓa tana jin ciwon jiki ta nufi banki. Anan aka tabbatar mata account ɗin ma ya daɗe ba a zuba masa kuɗi ba. Tana kuka wiwi ta nufi gidansu ta sanar da Momi komai. Ran Momi idan ya yi dubu to ya ɓaci, don haka ta ce ba zata koma ba, har sai Sadiq ɗin ya zo ya sameta. Shi kuwa Sadiq Yana dawowa ya sami bata nan ko a jikinsa ya gyara kwanciyarsa. Da ya ga shirun zai yi masa yawa kawai ya ɗaga waya ya kira budurwarsa. Ta shigo gidan suka ci-gaba da sheƙe ayarsu. A can gidan kuwa Daddy Yana dawowa ya ganta bai jira jin ba’asi ba ya fatattaketa, haka ta fito tana tafe tana kuka kamar ranta zai fita. Gani take yi rayuwa ta juya mata baya, abin da bata taɓa zato ba yau sai gashi ya dawo mata cikin rashin sanin mafita. A karo na farko da ta so ta je gurin Jawaheer tun faɗan da suka yi. Har ta kama hanya wata zuciyar ta gargaɗeta domin tana gudun ta haɗu da Suhaila. Ta tsani ta buɗa idanu ta ga Suhaila don za ta iya kasheta har lahira. Duk da irin abubuwan da suka faru har yanzu Farouk ya kasa zama tarihi a zuciyarta.

Da tarin tsaƙe-saƙe ta nufi gidanta. Ganin ƙofa a buɗe ta afka babu ko sallama. Mamaki ya kasheta ganin jakar mace a falon zuwa wayoyi. Wayoyi biyu ta shaida a wurin, su kansu dan sun kasance mallakin Sadiq ne. A falon ta zube tana ci-gaba da kukanta. Kamar an tsikareta ta miƙe ta kama hanyar ɗakin Sadiq. Sai dai babu kowa a ɗakin, hakan yasa ta nufi ɗakinta. Mutuwar tsaye ta yi, tana jin idanunta suna yi mata gizo. Mamakin ma yadda Sadiq yake sarrafa yarinyar ya fi kasheta. Sosai yake lallaɓata yana mata abubuwan da dole kowacce mace ce ma ta mutu akansa. Amma ita sai ya dinga yi mata irin abubuwan dabbobi? Ko dai dabba ya ɗauketa ne da har karuwa ta fita daraja? Sai yanzu ta an kare akan gadon da mahaifinta ya yi mata anan yake lalatarsa, wato gadonta ne ya dace da najasa ba tasa gadon ba kenan.

Daddagewa ta yi ta fasa ihu, wanda ya fargar da su. Yarinyar ce kaɗai ta firgita amma shi Sadiq ko a jikinsa. Ihu take yi tana burgima. Yarinyar ta lallaɓa ta sa kayanta ta yi hanyar ficewa. Allah ya ba Ummi sa’a ta fizgota ta hau duka. Sadiq ya tashi yasa ƙarfinsa ya ƙwaci yarinyar daga bisani ya ɗagata sama ya mayar kan gadon yana cewa,

“Ai babu yarinyar da ta isa ta sa inyi asarar abinda na yi ninya. Akanki zan fanshe.”

Tun Ummi tana ihu tana fizgewa har ta koma ta yi lankwaf. Hawaye kawai ke bin fuskarta. Tunda take jin labarin wulaƙanci da tozarci bata taɓa samun irin labarinta da Sadiq ba. Ta fashe da kuka tana cewa,

“Suhaila ba zan taɓa yafe maki ba, kin shigo rayuwata kin illata min ita. Kin auri mai tausayin kin bar min fasiƙi matsiyaci wanda bai san inda yake masa ciwo ba. Wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na sa kin ɗanɗani mafiyin azaban da na ɗanɗana a zamana da Sadiq. Kema sai rayuwarki ta zama abar kwantace.”

Tana ta surutanta har ta gaji ta yi shiru. Shi kuwa Sadiq ɗakinsa ya wuce ya watsa ruwa ya shirya fes! Ya dawo ɗakin suka haɗa idanu yana murmushi. Ta zabga masa harara. Ya ɗan ƙaraso yana cewa,

“In dawo kenan.”

Bata san lokacin da ta tashi zaune ba, wata azaɓa ta ziyarceta, ta fasa ƙara tana sake matse ƙafafunta.

“Don Allah kada ka kasheni.”

 Ya juya yana Murmushi ya bar mata gidan gaba ɗaya.

*****

Farouk ne zaune a bisa keken guragu, a saman kujera kuma Abba ne da Daddy sai Alhaji Marwan. Suhaila tana zaune daga bayan kujera ta yi shiru kanta a ƙasa.

Sannu a hankali Farouk ya zayyane masu komai. Momi tana laɓe tana saurarensu.

Abba ya yi shiru, ya kasa furta komai. Daddy ya yi gyaran murya,

“Amm.. Bamu taɓa tunanin Jaamuu ita ce take wannan aikin ba. Wato ba laifin Abbanki bane Suhaila. Lamarin ya faru da jimawa, na yi Makaranta ɗaya da Jaaamuu har muka shaƙu sosai. Kasancewarta inyamura bai hanamu zama abokai ba. Ashe a wancan lokacin Jaaamuu tana ɗaya daga cikin ‘ya’yan kungiyar matsafa. Kuma a lokacin ta riga ta bayar da ni. Yadda lamarin yake shi ne: Ta Zo min da maganar aure na nuna mata na amince saboda idanuna sun rufe sosai. Allah ya sakawa Abbanki da Alkhairi, shi ya jajirce ya tsamoni daga sharrin Jaaamuu.

“Ranar da Jaaamuu ta gama fahimtar Abbanki zai kawo mata cikas, saboda irin tsanar da yake nuna mata, yasa ta yanke shawarar Gara ta miƙawa dodon tsafinsu kawai tunda za a bata ƙarin girma irin wanda ba a taɓa baiwa wani a cikin ƙungiyar ba.

“Mu biyu iyayenmu suka haifa, hakan yasa mana ƙaunar juna fiye da tunanin mutum. A lokacin da Jaaamuu ta kamani, sai aman jini kawai nake yi anyi maganin har anji babu daɗi angaji ma an fidda Rai da ni. Hakan yasa Abbanki ya bazama neman Jaaamuu domin bincike ya nuna ita ta kamani. Bayan wani lokaci ne ya sami labarin ta shigo Makaranta domin duba Jarabawarta, ina kiran Abbanki kada yaje, amma saboda zuciya ya wuce ya sameta tana tsakiyar mutane ya fizgota kawai ya kama duka babu ji babu gani. Abin da bamu sani ba, ashe a lokacin saura kwana biyu a ɓatar da ni daga doron duniyar. Anan ne Abbanki ya shaƙeta sosai har ta fara ƙaƙarin mutuwa. A lokacin bata zo da wani abu na kare kanta ba, kuma ko ta zo da shi tana tsoron jama’a su gane da gaske ne dan ta san sai sun kasheta. Ganin zata hallaka yasa ta fara roƙon Abbanki da ya ƙyaleta ya ce ba zai ƙyaleta ba. Ya jawota da ƙarfi da wasu mutane wanda suka kasance abokan mahaifinki suka kawota har inda nake. Abin mamaki tana zuwa ta shigo gidan ta ɗaga wani dutse sai gashi na tashi sarai. Abbanki ya yi mata shegen duka, ya miƙata ga ‘yan sanda. Tun a lokacin take cewa Sadiqu sai ta ɗau fansa, ba za ta taɓa barinsa ya yi farin ciki ba.

“Ta ci nasarar kashe abokansa, ni kuma da mahaifinki kakarmu ta bamu tsari wanda ya gagari Jaaamuu isowa garemu. Gaba ɗaya mun mance da ita, mun mance da maganar nan muna ta rayuwarmu, ashe ita kuma bata mance ba, ashe tana nan tana bibiyarmu. Shi ne ta dire laifin akanki. Tabbas ta ɗau hakkin jama’a kuma ta yi mana ramuwa mai ciwo da taɓa zuciya. Abin da yasa kuma ta kasa taɓa Farouk ina tunanin saboda ƙarfin addininsa ne. Farouk yana da addinin da bana jin aljani ma zai iya samun daman cutar da shi. Yanzu ina zamu ga Jaaamuu? Menene mafita? Idan muka ƙyaleta zata ci-gaba da bin mu ne har jikoki.”

Abba ya ɗago idanunsa jazir!

“Yaya Wallahi ban mance matar nan ba, duk abubuwan nan da suke faruwa na jima ina zarginta a zuciyata, ashe da gaske ita ɗin ce. Dama ance basa mantuwa. Babu wanda zai nemeta dan ya bata haƙuri, ta yi kaɗan. Muna da hanyoyin yin maganinta da ƙarfin ayar Allah. Mu musulmai ne, haka zalika Alqur’ani ba ƙarya bane. Ta riƙe takobin tsafi mu kuma zamu riƙe takobin muminai, sai mu ga da mu da ita waye ke da riba. Yadda ta cutar da mu, sai ta yi barin duniyar wulakanci.”

 Suhaila ta saki sassanyar ajiyar zuciya, jin cewar Abbanta bai aikata wani mugun abu ba, a zatonta wani abun Abba ya yi shiyasa ake hukuntata da shi. Alhaji Marwan ya yi gyaran murya,

“Gaskiya kun tsallake rijiya da baya. Shiyasa wato babu kyau ka yankewa mutum hukunci daga cikin irin zatonka. Addu’a zamu dage da yi, Jaaamuu take ko Jaaabuu? Ta yi kaɗan. Ita gaskiya tsaye take da ƙafafunta, ƙarya kuwa ƙafafun toka ke gareta kana taɓa ta zata ruguje. Suhaila ki kwantar da hankalinki ki sake dagewa da addu’a, mijinki bani da matsala da shi indai ta fuskar addininsa ne. Mu kuma sai mu nemi malamai a zauna da su a tattauna sai aji ta yadda za a ɓullowa lamarin.”

Anan suka Sallami kowa suka kama gabansu. Suhaila da Farouk suka koma gidan Farouk ba tare da sun koma can gidan iyayensa ba. Ya dubeta a tsakiyar falon ya ce,

“Idan mun gama da ɓangaren Jaaamuu sai mu dawo ɓangaren Anti. Domin damuwata akan Anti ta fi ƙarfin damuwar wata Jaaamuu…”

Suhaila ta riƙe kanta ita kaɗai tasan tarin damuwar da take ciki. Ta dube shi a sanyaye ta ce,

“Me za mu ɗauka a nan?”

Ya kauda kansa,

“Zama zamu yi, na gaji da abubuwan cikin gidanmu. Kada watarana in faɗi in mutu saboda baƙin ciki.”

Neman wuri ta yi ta zauna kawai. Sallamar Sadiq ya sa duk suka dubi ƙofa. Suhaila ta miƙe ta yi saurin shigewa ciki. Ta tsani ko haɗa idanu ta yi da Sadiq. Abun yana damun Farouk. Ya so ta kawo masa ruwa, amma ganin ta shige ta ɓame ƙofa yasa ya miƙe da kansa ya kawo masu ruwa mai sanyi yana dubansa.

 “Naga kamar kana cikin nishaɗi ne.”

 Farouk ya buƙata yana sake zura idanunsa a cikin na Sadiq.

Ya sake sakin murmushi yana shafar kasumbar fuskarsa. A natse ya warwarewa Farouk duk abubuwan da suka faru a tsakaninsa da Ummi.

Farouk kawai ya zura masa ido, yana mamaki. Suhaila kuwa tana jikin ƙofa ta ji dukkan tattaunawarsu, ta durƙushe a jikin ƙofar tana jin hawayen tausayin Ummi suna zubo mata. Yanzu da ita ce take cikin irin wannan masifar? Zina akan gadon sunna? Suhaila ta rushe da kuka tana jin ɗaci a bisa harshenta. Yau duniya ta zo ƙarshe ta yadda har bawa zai aikata kuskure ya fito yana faɗin ya aikata abinda Allah ya hana? Toshe bakinta ta yi, tana son sauraren maganar Farouk.

Shi kuwa Farouk ji ya yi ransa ya yi mugun ɓaci, ko babu komai Ummi ‘yar uwarsa ce ta jini, dole zai ji babu daɗi idan aka wulaƙanta masa ita.

“Sadiq!! Ka dawo hayyacinka. Wani irin shaiɗani ne yake yi maka yawo a ƙwaƙwalwa yana watsa maka fitsarinsa? Yaushe kayi nisa har haka? Ka gane da wanda kake maganar nan kuwa? Da Yayan Ummi kake magana! Zalunci ne wannan ni kuma bana goyon bayan zalunci. Har kake iya gaya min ka lallaɓa karuwa! Amma matarka ta sunna kana binta kamar dabba? Anya kana tsoron Allah kuwa? Zina kake faɗin ka aikata a bisa gadon Sunnah! Gadon da kake raya Sunnah da matarka.”

Farouk ya sassauta murya yana jin zuciyarsa tana ƙuna,

“Kuma saboda cin fuska da wulakanci a cikin dattinka na zina, ka sake kwanciya da matarka ta ƙarfin tsiya? Me Ummi ta yi maka haka da zafi? Wa ya gaya maka ana rama zalunci da zalunci? Sadiq baka taɓa ɓata min rai irin na yau ba. Da ka sani da baka gaya min maganar da za ta iya hanani barci ba. Ka sake rura wutar gaba a tsakanin Suhaila da Ummi. Ummi bata da fahimta, za ta ce saboda zaɓin da akayi mata ne yasa yake yi mata hakan. Za ta dinga tunanin Suhaila tana can tana jin daɗinta a wurina. Haba Sadiq! Haba Sadiq!!”

Sadiq ya kauda idanunsa yana jin ko a jikinsa.

“Ni ka ganni nan? Ba zuwa nayi kayi min wa’azi ba. Ƙanwarka bata da tarbiyya shiyasa ni kuma naga dacewar in gyara mata zama.”

 arouk da yake jin kalaman Sadiq kamar ya mutu, ya damƙi wuyar rigarsa yana huci,

“Babu babban mara tarbiyya kamarka Sadiq! Tarbiyyar ce ta koyar da kai aikata zina akan gadon matarka? Ko kuwa tarbiyya ce tasa kake afkawa matarka ta yadda ka gadama?”

Sadiq da ya ji shaƙar ta yi yawa ya fara ƙoƙarin ƙwace kansa. Sai da ya kusa fita daga falon sannan ya waiwayo ya ce,

“Ni aka fi cuta fa da aka ba ni Ummi a matsayin mata. Idan da gaske ka damu da halin da ƙanwarka take ciki ka bani Suhaila ka karɓi Ummin mana. Kai dai ka kwashi banza a sama kawai.”

Farouk ya yi banza da shi ya koma ya zauna a kujera yana huci. Sai da Sadiq ya jima da ficewa kafin Suhaila ta fito da gudu ta rungume Farouk ta saki kuka.

Damuwarsa ta sake ninkuwa saboda baƙin cikin Suhaila ta ji tattaunawarsu. Baya son kukan yarinyar, kukanta yana taɓa masa zuciya.

Shafa bayanta yake yi da hannunsa ɗaya alamun lallashi, baya jin zai iya furta ko da kalma ɗaya a yanzu. Ita kanta gajiya ta yi da kukan ta fara sakin ajiyar zuciya, shi dai bai daina bubbuga bayanta ba. Kafin wani lokaci barci ya yi awon gaba da ita…

Alhaji Marwan da su Daddy su tashi tsaye da addu’a, sun sanya malamai su yi addu’ar haka zalika su da kansu ba abar su a baya ba.

Yau ma kamar kullum Farouk yana zaune a ɗaya daga cikin kujerun falonsa Anti ta yaye labulai ta afko. Huci kawai take yi, shi kuma ya kafeta da idanu bayan ya tabbatar da ya saita zamansa irin na marasa lafiya.

“Farouk Ni zaka watsar akan wata mace?”

Ta furta tana mai sake zuro kanta cikin falon.

“Ko ɗaya Anti. Likita dai ya bani shawarar in koma inda zan fi sakewa sosai, sai naga gidan nan zai fi.”

Anti ta ƙaraso kusa da shi tana dubansa,

“Ina matar gidan ta barka kai ɗaya?”

Sai da ya ɗan dubi sama sannan ya ce,

“Tana ciki tana barci.”

Anti ta zaro idanu,

“Au kana nan kana fama da kanka ita barci ma take yi kenan ko? Sannan idan anyi magana ace wai tana taimaka maka. Idan ɗiyar ƙwarai ce ai kamata ya yi ace yanzu haka tana zaune tana jiran ko za ka nemi wani abu.”

Farouk ya ɗan kauda kansa kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce,

“Anti kenan. Yarinyar nan duk girman gidan nan ita ta gyare shi, ta kuma yi abinci. Ni nace ta je ta kwanta ta huta dan bana buƙatar komai.”

Anti ta haɗiye wani ƙaton abu ta miƙe tana cewa,

“Bari ni inje mu gaisa da ita.”

Yana zaune ya kafeta da idanunsa har ta ɓace masa. Bai isa ya hanata isowa ga Suhaila ba, bare har ya ci nasarar hanata sanya Suhaila kuka, kamar yadda da ƙyar ya tsaida hawayen idanunta akan damuwar halin da Ummi take ciki.

<< Kaddarata Ce 13Kaddarata Ce 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×