Anti tana shiga ta sami Suhaila tana barcinta a natse. Ta daddage ta ɗaka mata duka a baya, hakan yasa Suhaila tashi a gigice. Tana huci ta dubi gefen gadon ruwa ne cike da glas Cup ta ɗauka ta sake sheƙa mata tana sake zazzaro idanu. Suhaila ta rintse idanu tana jin sanyin ruwan yana ratsata.
“Kin tashi kokuwa sai na sake samo ruwan zafi na antaya maki?”
Suhaila ta diro da sauri tana cewa,
“Na tashi Anti.”
Anti ta jawo kujera ta zauna tana karkaɗa ƙafafu,
“Ke! Jinya aka kawo ki kiyi kokuwa barci? Uban waye ya baki izinin yin barci a cikin ɗakin nan?”
Suhaila ta duƙar da kai, tuni hawayen ya fara sintiri a idanunta. Ta girgiza kai,
“Barcin ne ya kwasheni.”
Anti ta zaro idanu,
“Da kyau ‘yar matsiyata. Ba a iya samun wuri ba. Farouk yana can yana neman taimako, da ace ban ƙara so ba da tuni ɗana ya shiga mawuyacin hali, ke kina nan kin haye kin naɗe jiki wai kina barci.”
Suhaila ta ɗago a gigice, daga bisani ta miƙe jikinta yana kyarma ta yi hanyar waje. Anti ta yi saurin fizgota ta dawo da baya,
“Munafuka, ina zaki je?”
“Zan je induba shi ne.”
Wani irin kallo ta watsa mata,
“Dalla matsa can! Da baki duba shi ɗin ba kin ga wani abu ya ragu a jikinsa ne? Makira kawai.”
Anti ta fice abinta. Suhaila ta zauna ta yi tagumi kawai tana dogon tunani.
Anti tana fitowa Farouk ya dubeta duba ɗaya ya tabbatar da aikin gama ya gama. Musamman da ta yi masa sallama akan idan ankwana biyu za ta sake dawowa. Ji yake kamar ya tashi ya hau saman yaga halin da Suhaila take ciki. Dole sai dai ya yi dabara ya ƙwala mata kira. A gigice ta fito tana dudduba jikinsa tana tambayarsa ko wani abu ke masa ciwo. Ya kafeta da idanunsa ba tare da tasan yana kallonta ba, sai jin muryarsa ta yi cikin damuwa yana cewa,
“Suhaila me ya jiƙa maki riga? Me ya sa kika yi kuka? Anti ce ko?”
Dukkansu suka yi tsit kamar ruwa ya ci su. Da ƙyar ta ƙaƙalo murmushi tare da kauda maganar,
“Inkawo maka Madara?”
Tana ƙoƙarin ɗauke rigarsa da ke gefensa yasa hannu ya kamo hannunta. Kanta a ƙasa ta ɗan janye hannun, shi kuma ya ƙi saki. A haka akayi Sallama aka shigo ba tare da ya saki hannun nata ba. Ummi ce da Hajiya Asiya, duk suka dubi juna, a lokaci guda kishi ya nemi rufewa Ummi idanu ta yunƙura zata ƙarasa Hajiya Asiya ta yi saurin riƙo hannunta, ta yi mata alama da ido. Dole dai ta cije, sai dai batasan lokacin da ta sake antayo sallama da ƙarfin tsiya ba.
Sai a lokacin duk hankulansu ya dawo jikinsu da sauri Suhaila ta fizge hannunta jikinta babu inda baya rawa ta zube a ƙasa.
Duk suka yi ta mamakin yadda Farouk ko alamun rama babu a jikinsa, kamar ma bashi bane mare lafiyar.
Farouk ya gaida Momi, itama Suhaila ta gaidata amma sai ta yi kamar bata ji ba.
Ummi ta gaida Farouk ya amsa babu yabo babu fallasa. Momi ta dubi Suhaila ta haɗa rai ta ce,
“Ki ɗan bamu wuri zamu yi magana.”
Har ta tashi Farouk ya riƙo hannunta ya dawo da ita ta zauna kamar za ta yi masa kuka. Sannan ya dubi Momi ya ce,
“Suhaila ko ba dangi bace matata ce mun zama ɗaya, bare kuma cikakkiyar dangi ce, babu abin da za a ɓoye mata.”
Ummi ta fashe da kuka, irin wannan kulawan take mafarkin samu daga gun Farouk amma tsinanniyar nan ta yi mata sanadi. Cikin kuka take cewa,
“Yaya ka taimakeni ka taimaki rayuwata ka raba aurena da Yaya Sadiq, Ni kawai ka aureni duk da baka da lafiyar na amince ka aureni a hakan zan zauna.”
Gaban Suhaila ya faɗi da ƙarfi, ta duƙar da kai tana jin zuciyarta babu daɗi. Momi ta gyara zama ta ce,
“Rayuwar Sadiq tana Bani tsoro, da yaron ba haka halayyarsa take ba. Idan ya gaji da ita ya saketa kawai. Duk Suhaila ta jawo mana wannan masifar. Wallahi ba zan yafe maki ba Suhaila tunda kika sa rayuwar ‘yata a cikin garari.”
Suhaila ta sake saukar da kai sai hawaye sharr! Farouk ya ɗan musƙuta ya ce,
“Zan yi magana da Sadiq ɗin. Abin da nake so da ku Momi ku yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinsa.”
Momi ta harare shi,
“Da ace baka aureta ba ka auri ‘yar uwarka da duk hakan zai faru ne?”
Farouk ya girgiza kai, yasan ba za su taɓa fahimtarsa ba, don haka ya yi shiru. Sai da suka gaji suka yi masa sallama. Kai tsaye gidan Anti suka wuce. Sai da suka yi da ƙyar sannan Anti ta dube su. Bayan ta gama sauraren maganganun Ummin ta ce,
“Duk wa ya ja? A lokacin da baki guji ɗan uwanki saboda lalura ba, da tuni nasan yadda na yi Sadiq ya sakeki. Amma yanzu tunda kin dawo hanya babu laifi, zamu san abun yi.”
Anan suka yi ta ƙullawa suna kwancewa. Daga ƙarshe suka bar maganar akan za su je gidan wani boka a samu Sadiq ya saketa, sannan a kora Suhaila. Sai dare Ummi ta koma gida cike da farin ciki.
A bakin ƙofa ta sami Sadiq fuskarsa a ɗaure, ta samu ta raɓa shi ta wuce. Tana shiga ya biyota yana mazurai,
“Uban wa ya baki izinin fita gidan nan?”
Ta dube shi sheƙeƙe
“Ubana ya bani izini.”
“Ai ba ubanki yake aurenki ba.”
Ummi ta miƙe ta dube shi,
“Ka zageni na ƙarshe Wallahi ka sake zagar min uba sai na rama, dan uba bai fi uba ba.”
Har zai mareta, sai kuma ya janye ya juya kawai yana cewa,
“Zan yi maganinki.”
****
Farouk ya ɗaga waya ya kira Sadiq ransa a ɓace ya ce masa ya zo ya same shi. Sadiq yana ƙarasowa ya fahimci babu lafiya, amma sai ya yi fuska. Farouk ya gama gaya masa duk abinda zai gaya masa daga ƙarshe ya ce,
“Ka fara jawowa Ummi tana ganin Gara ta bar aurenka, kai kana ganin hakan ya dace? Idan Alhajinka ya ji maganar nan me kake tunanin zai faru? Don Allah Sadiq Ka gyara, ka koma sak! Irin Sadiq ɗin da na sani mai tausayi.”
Sadiq ya nuna masa babu komai.
Sai dai yana komawa gida abin ya ƙara ƙazanta, ta yadda ya koma rufe ƙofarsa idan zai fita, hakan yasa hatta Makarantar ma ta daina zuwa. Hajiya Asiya ta yi zuwa ya fi a ƙirga akan taga Ummi, sai dai su yi magana ta window. Daga baya kuma ya koma cewa mai gadi ya gaya mata ya yi tafiya da Ummin, ya ƙwace wayar hannunta.
Wannan lamari yasa Hajiya Asiya shiga tashin hankali. Gashi Daddy ya ƙi bata fuska bare ta tunkare shi da maganar. Dole ta sake wankar ƙafa ta je gurin Farouk ta gaya masa. Hankalinsa idan ya yi dubu to ya tashi. Ya kira lambar Sadiq ya fi a ƙirga baya ɗauka.
Duk hanyar da yasan za a ganshi ya datse hanyar.
Ana hakane shirye-shiryen auren Jawaheer ya kankama, da wani mashahurin mai kuɗi. Sai dai kuskuren da Jawaheer take shirin tafkawa ya fi na Ummi, domin kuwa mutumin da ke sonta ɗin ya fara zuwa wurinta a talakarsa ta wulakanta shi ta tara masa jama’a tana cewa wannan almajirin ne wai ke son aurenta, bai ga irin motar da take hawa bane? Mutane da yawa suka yi ta tsine mata.
A lokacin babu yadda abokansa basu hana shi tasowa daga gurin da yake saida kayan miyarsa ba, dan ya furta abinda ke zuciyarsa amma ya ƙi saurarensu. Wasu kuwa daga wurin jinjina ƙarfin hali irin na Ya’u kawai suke yi.
A lokacin wani kwastomansa yana tsaye yana kallon komai, ya kira shi gefe ya ce masa yana sonta zai iya aurenta? Ya’u ya girgiza kai cike da baƙin ciki ya ce ya tsaneta baya ko son ganinta. Mutunin ya ƙarfafa masa guiwa akan zai bashi komai da zai nuna shi mai kuɗi ne ya je ya aureta dan ya koya mata darasi. Ya ce zai yi wa mahaifinsa magana tunda shi ɗin ya yi suna, yana da tabbacin mahaifinsa zai karɓe shi a matsayin ɗa har ya ɗaura masa aure. Wannan lamari yasa Ya’u jin daɗi, tun daga nan ya sauya rumfar da yake saida kayan miya saboda kunyar jama’ar wurin. A cikin Makarantar su Jawaheer ya samu sake ganinta bayan yasha ado da kayan alfarma. Dama kuma da kyansa babu laifi zafin talauci ne yasanya shi ya sauya. Yadda yake magana da jan aji yasa Jawaheer ta fara tunanin za aje da Yaks kamar yadda ya gaya mata haka sunansa yake. Babu ɓata lokaci ya bayyana kansa gaban iyaye, su Anti sai rawar ƙafa akeyi tana jin kaf dangi babu wanda ya ciri tuta kamarta. Hatta Hajiya Asiya sai da ta ga canji agun Anti. Farouk yaso a bashi dama ya zurfafa bincike amma sai Anti ta rufe idanunta ta kama yi masa masifa akan waye baisan Alhaji Mamman Canji ba kaf Abuja. Dole ya kawo idanu ya zuba masu.
***
Farouk ya kammala shirinsa tsaf yana fesa turare Suhaila ta shigo ɗakin tana riƙe da flask wanda yake ɗauke da ruwan zafi a cikinsa. Kawai ta ga mutum a tsaye cikin shigarsa mai kyau. Saboda tsananin ruɗewa batasan lokacin da ta saki Flask ɗin ba. A razane ya juyo saboda jin ƙarar fashewar abu. Suka kafe juna da idanu. Murmushi ya sakar mata ya fara taku har ya iso gareta. Bakinta yana rawa ta ce,
“Yaushe ka fara tafiya?”
Ya sake jifanta da lallausan murmushi sannan ya kamo hannunta ta zauna kusa da shi.
“Dama lafiyata ƙalau, kuma ban taɓa ciwo ba.”
Baki ta buɗe kawai, farin ciki ya tsirga mata, a lokaci ɗaya ta fara dariya hawaye na bin fuskarta. Daga bisani ta juya masa baya alamun ta yi fushi. Ashe sakin jikinsa da yake yi idan ta zo kwantar da shi yana gogan jikinta duk da gangar yake yi. Farouk ya miƙe ya durƙusa kusa da ita ya sa hannayensa a kunne,
“Sorry Wife..”
Tsigan jikinta ya tashi yarr! Ta juyo tana murmushi ta cire hannunsa a kunnen ta ce,
“Kada ka ƙara aure babu kyau.”
Yana ɗan murmushi ya ce,
“Promise.”
Ta ma rasa me za ta yi ne kawai sai farin ciki take yi, tana dariya. A lokacin suka ji Sallamar Anti, gaba ɗaya sai farin cikin su ya koma ciki. Abin da ya sake ɗaure mata kai yadda ya ɗauko keken ya zauna akai, sannan ya kashe mata ido alamun ta zo ta gungura shi. Za ta yi magana yasa hannu a laɓɓansa, dole ta haɗiye maganar ta gunguro shi tana jin zuciyarta fes! Dan kullum da tausayinsa take kwana a cikin rai take tashi…
A falon suka tsaya cirko-cirko, daga bisani Suhaila ta durƙusa ta gaidata. Bata amsa ba sai ma duban fuskar Farouk da ta yi ta ce,
“Ki bamu wuri zan tattauna da ɗana.”
Jikinta har yana rawa ta fice. Anan ta zauna tana zazzare idanu,
“Wato Farouk ƙiri-ƙiri kake hassada da mijin da Allah ya baiwa Jawaheer ko? Ana ta shiri ban ji inda ka buɗa baki kace ta zaɓi ƙasar da take son zuwa zaɓo kayan ɗaki ba. Ban ji kana ɗokin bikin ba. Haba Farouk.”
Mamaki ya kasa barin Farouk ya yi ƙwaƙƙwaran motsi, sai kallon mahaifiyarsa yake yana tunanin anya kuwa ita ce wacce ta kawo shi duniya? Anya ita ce mai ƙaunarsa?
Anti ni ne zan yi baƙin ciki da ƙanwata? Nace ku bani dama inyi bincike kun hanani, yanzu kuma na kawo idanu kin ce ina baƙin ciki da ita. Sam ban taɓa jin hakan a wurin maƙiyina ba, bare ƙanwata wacce duk duniyar nan bani da kamarta. Anti ki Gaya min me kike son inyi ya nuna maki ƙanwata har abada ƙanwata ce? Idan duk arziƙina kike son inbata zan bata.”
Ya ƙarashe cikin wata kasalalliyar murya. A lokaci guda imani ya karyowa Anti, ta ɗan sunkui da kai ta ce,
“Yanzu na ji batu. Ai da na zata kaima irin dangin ubanka ne. Yanzu rashin lafiyar nan taka ita kaɗai ce damuwata. Wai har yanzu babu wani ci gaba ne?”
“Akwai ci gaba, bikin Jawaheer kaɗai zai dakatar da ni, daga zuwa Egypt akwai aikin da za ayi min da yiwuwar insha Allahu insami lafiya gaba ɗaya, sai ki tayani da addu’a. Ita kuma Jawaheer duk abinda take buƙata a sanar min ko Cheque ne sai inrubuta mata.”
Zuciyar Anti fara tas! Ji take kamar bai taɓa kwantar mata da hankali kamar yau ba. A can ƙasar zuciyarsa kuwa rantsuwa ta yi kafin Farouk ya dawo Nigeria za ta aura masa Rumaisa, dan hankalinta ya fi kwanciya da Rumaisa fiye da Ummi, kasancewar ta gane tuni aikin gama ya gama a tsakanin Ummi da Sadiq, don haka babu wacce ta isa ta baiwa ɗanta rabin mace.
Har ta kusa fita ta sake dawowa, “Amma dai ba tare da Suhaila zaka bar ƙasar ba ko?”
Shiru ya yi kamar bai ji ba, hakan yasa ta dawo sosai ta dafa keken ta sake nanata masa. Murmushi ya ƙwace masa,
“To Anti ni da wa zanje idan ba da ita ba? Kin dai ga yadda Sadiq ya zama sai addu’a.”
Sai da ta haɗiye wani ƙaton abu da ya tsaya mata a tsakanin maƙoshi sannan ta saki yaƙe ta wuce kawai ba tare da ta furta uffan ba.
Suhaila bata fito ba, don haka ya miƙe yasa key a ƙofar falon sannan ya haura sama. Tana kwance ta lafe, ita kaɗai tasan tunanin da take yi. Irin kwanciyar da ta yi shima irinta ya yi duk suka ƙurawa juna ido. Yana murmushi yasa hannu ya ɗauke ƙwallan gefen idanunta,
“Me kike buƙata na bikin Jawaheer?”
Sai da ta yi shiru kamar mai nazarin abinda za ta gaya masa sannan ta girgiza kai,
“Ba na tunanin ko bikin zan iya leƙawa. Allah ya basu zaman lafiya.”
Ɓata ransa ya yi sosai,
“Bikin ‘yar uwata kike gayawa haka?”
Mamaki ya kama ta, ta yaya wasu mazan suke da tsananin son kansu ne? Yanzu da za ta je ayi mata wulakanci kawai haƙuri zai bata, ko kuma wata rigimar ta taso. Bata jin yin doguwar magana, tana da buƙatar hutu musamman ta fannin ƙwaƙwalwa, don haka ta rufe idanunta kamar mai barci. Ba ta san hawaye sun gangaro a lokacin da ta rufe idanun ba, hannunsa kawai ta ji yana ɗauke mata su. Daga nan salon ya sauya, ya fara aika mata da zafafan saƙon da suka gigita tunaninta. Wasu kalamai yake gaya mata wanda suka sake rikitata. Za ta so tana zaune ne a gabansa yake yi mata kalaman nan ba tare da rowarsu ba, da ta fi kowa murna da farin ciki, sai dai kash! Ta sani fita hayyaci ne ya jawo masa irin kalaman nan. Burinsa yana gaf da cika suka ji wani irin tsawa mai hargitsa ‘ya’yan hanji. Suhaila ta miƙe tana kare jikinta da bargo. Gaba ɗaya ilahirin jikinta babu inda baya kyarma.