Skip to content
Part 15 of 17 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Shi kuwa Farouk ji yake da mutum ne ya aikata masa hakan da babu abin da zai hana shi bai gaggauta wulakanta wannan mutumin ba, ko babu komai zai jawo masa matsala a mararsa. Haske sosai ya mamaye ɗakin kamar ba ɗakinsu ba, wata durƙusasshiyar mata ce tsaye da sanda a hannu kan nan babu komai sai walƙiya yake yi. Wata kakkausar murya ta fara magana, da murya irin ta yare.

“Kun raina mu, zamu ɗauki mataki akanku, duk hanyar da muka bi sai kun bi. Kai har ka isa ka sadu da matarka? Kunsa ana ta ƙona mu… Ni ce nan JAAAMUUU abin da ubanki ya yi min ba zan yafe mashi ba, za ayi min ƙarin girma ya jawo anhanani. Idan ka kusanceta ko da wasa sai na kashe gabanka ya daina aiki har abada… Hahahahaha… Sai ni nan JAAMUU… Mamana ta taimakeki ni kuma na kashetaaaaa…”

Suhaila ta sake shigewa jikin Farouk jikinta babu inda baya kyarma. Shi dai Farouk tunda ya saita fuskarsa kanta yake addu’a a zuciyarsa. A take suka ji ta saki razananniyar ƙara wuta ya nemi tashi a jikinta sai kuma ta ɓace. Farouk ya saki ajiyar zuciya, a take ya bi ƙusurwa-ƙusurwa ya tofe da Addu’a. Ita dai duk inda ya bi tana maƙale a jikinsa ta ƙi yarda su rabu. Can ta fashe da kuka mai cin rai. Ya shafi bayanta yana bubbugawa.

*****

Gabaɗaya Ummi ta rame ta lalace ta zama abar tausayi, amma duk da hakan zuciyarta tana nan akan Farouk babu canjin komai.

Dole Farouk ya sanar da Alhaji Sama’ila mahaifin Sadiq abinda ke faruwa. Cikin gaggawa Alhaji ya kira ɗansa ya rufe shi da faɗa ta inda ya shiga ba ta nan ya fita ba. Dole Sadiq ya ɗan sassauta mata ya barta ta ci-gaba da zuwa Makaranta da sharaɗin idan ta sake fita babu izininsa sai ya ɗauketa a ƙasar nan ya kaita inda sai ta gwammace kiɗa da karatu.

Shirye-shiryen biki ya kankama. A ranar Farouk ya ɗauki Suhaila ya kaita gidansu saboda za ayi Kamu. Suhaila bata shisshigewa kowa ba ta koma gefe abinta. A faffaɗan filin gidansu akayi taron, wanda aka haɗe shi da decoration abin sai wanda ya gani.

Har ango da amarya suka sami isowa Suhaila tana gefe bata sami daman ganin angon ba, sai da aka ce za ayi buɗan kai. A hankali ta taka ta je har wurin domin ganin yadda za ayi. Sosai Suhaila ta ware idanunta cike da fargaba, wa take gani kamar Ya’u? Tasan Ya’u a dalilin Momi da ke turasu da Ummi siyan kayan miya su jida su zuba a mota. Yana da barkwanci da son koɗa kyan mutum ko da kuwa bai kai hakan ba. Shi kansa yana kallonta ya tabbatar ta gane shi, ya jinjinawa ƙarfin idanunta. Domin hatta Ummi da ta daɗe ana aikota bata gane shi ba, ko don sajen da ya bari. Suhaila ta mitsittsike idanunta ta buɗe su tarr akan Ya’u. Yadda yake kauda kai ya sake tabbatar mata da shi ɗinne. Jiri ta ji yana son kwasarta ta ja da baya tana girgiza kai ta koma ta zauna tare da yin tagumi.

A gigice take tunanin abin yi, can ta hango Ummi kamar ta zauna tana hutawa ne, yanayinta kamar mai ɗauke da ƙaramin ciki. Da sassarfa ta miƙe ta iso gurin Ummi ta dafa kafaɗarta. Ummi tana ɗagowa ta ga Suhaila ce, aikuwa ta bige hannun tana zabga mata harara. Suhaila ta girgiza kai ta ce,

“Sis magana zan yi da ke don Allah. Kinsan…”

Da sauri Ummi ta miƙe ta bar wurin tana jin kamar ta shaƙota ta yi ta duka har sai ta daina numfashi.

Hankalin Suhaila ya gaza kwanciya har aka tashi kowa ya kama gabansa. Sai da ta tabbatar Jawaheer tana ɗakinsu, sannan ta shigo anan ta same su da gogaggun ƙawayenta ana ta shewa. Ummi tana zaune a tsakiyar gadon, ita kuma Jawaheer tana sauya kaya. Suhaila ta dubi Jawaheer ta ce,

“Don Allah ina son magana da ke.”

Idan sun tanka dutse ya tanka. Har Jawaheer ta sauya kaya ta fice zuwa ɗakin Anti. Bata yi ƙasa a guiwa ba ta sake bin bayanta, a lokacin daga Anti sai ita Jawaheer ɗin su biyu tana bata wasu magunguna. Suhaila ta faɗo ɗakin kafin su yi wata magana ta ce,

“Kin kuwa san waye kike shirin aure? Kinsan wa za ki aura? Yadda kuka tsani talaka ta yaya zaki fara rayuwa da Ya…”

Kafin ta ƙarasa Anti ta sauke mata lafiyayyan mari. Jawaheer ta shaƙo wuyan rigarta tana haki,

“Idan kika sake aibata min miji narantse da Allah sai na zama ajalinki. Ba mu muka shafa maku talauci ba bare haukan ya ƙare akanmu. Wawuya kawai talaka ƙazama.”

Anti ta nuna mata hanya,

“Fice min a ɗaki tun kafin insa ƙartin maza su yi maki dukan tsiya. Idan kika sake aibata min suruki, zan kira shi ingaya masa masu gadinsa kaɗai sun isheki tashin hankali.”

Suhaila tana dafe da ƙuncinta ta fita jiki a sanyaye. Tunani ne kala-kala a zuciyarta dole ta gayawa mijinta gudun ayi auren danasani.

Tana fitowa a daren kawai ta kama hanya da ƙafa zata koma gidanta.

Gani ta yi ansha gabanta da mota, ta ja da baya tana duban waye? Ya’u ya fito yana murmushi. Suhaila ta dafe ƙirji tana kallonsa kaca-kaca sai kace ba shi bane ya zo wajen kamu ɗazu. Da yake unguwar akwai wadataccen haske.

“Kin yi mamakin ganina a matsayin surukin gidanku ko? Ko da yake kema na ji labarin abubuwan da suka faru da kuma suke kan faruwa na tausaya maki. Shawara ɗaya zan baki kada ki sake gigin gayawa wani wanene Ya’u dan babu wanda zai yarda da ke. Jawaheer ta kirani tana gaya min matar Yayanta bata sona ta ce wai ni talaka ne. Sai da na cire wayar da ga kunnena na yi ta dariya. Daga bisani na yi murmushin da take so irin na cikin littafan hausa, haka kawai wai ba zan yi dariya ba gudun mace ta rainani. Nace mata ita ta sani ko da gaske kike yi? Kinsan me ta ce min?”

Suhaila ta kasa amsawa saboda yadda jikinta ya yi sanyi, shima bai saurari amsar ta ba ya ci-gaba da cewa,

“Cewa ta yi inrabu da ke saboda kin ga ke ‘yar gidan matsiyata ne shiyasa kike yi mata hassada. Don Allah Suhaila Jawaheer matar aure ce? Mu talakawa shikenan mun zama marasa amfani a duniyar nan?”

Wannan karon Suhaila ta yi saurin dakatar da shi bayan ta samu ta daidaita natsuwarta,

“Ya’u ka gaya min me ya sa kake son kayi wa Jawaheer haka? Baka tunanin abinda zai je ya dawo?”

A gajarce ya gaya mata duk abubuwan da suka faru. A lokacin ne kuma Farouk ya faka tasa motar bayan ya samu ya hango Suhailar da yake nema. Idanunsa ƙyar akan Ya’u. Bai fito ba tasan ba zai fito ba, tunda suna zaton yana iya komai amma baya iya tashi tsaye. Tun kafin ya yi magana Ya’u ya ce,

“To mun gode bari mu ƙarasa mu kaiwa amarya saƙon.”

Har ta wuce ta shiga mota Farouk ya gaza magana sai da suka shigo gida bayan ta kawo masa ruwan lipton ya dubeta,

“Na yi ta nemanki ina kika shiga?”

Ta ce masa ta kama hanyar gida ne ta haɗu da waɗannan masu tambayar. Bai sake cewa komai ba, sai bayan ya kammala shan tea yana satan kallonta Bakinta yana motsi amma ta gaza furta abin da ke ranta. Ya danganta hakan da abin da Anti ta Kira shi ta gaya masa Suhaila ta yi masu. Sosai Farouk yake zargin wasu abubuwa, amma ko menene ya barwa Allah.

A rungume a jikinsa ta yi barci. Sai dai a barcin ta dinga mafarki ta tashi a zaburai da sunan Ya’u a baki, har ga Allah bata son Jawaheer ta auri Ya’u ko talakanne ma ta fi son ta auri wanda yasan mutuncin kansa. Farouk ya dinga nanata sunan Farouk yana mamaki.

Yau dubban jama’a suka shaida ɗaurin auren Ya’u da Jawaheer. Sai dai tun agun ɗaurin aure aka fara waswasi kasancewar ba sunan Alhaji Mamman Canji bane Ya’u ya yi amfani da shi wurin ɗaurin aure. Sai dai Alhaji Marwan ko a jikinsa bai ma tsaya bin ta kan maganar ba, ya sa kai ya bar wurin.

Farouk ya dawo gida cike da saƙe-saƙen sunan Yakubu Muhammad saɓanin Canji da ya saba shigowa cikin laƙabin kowanne ɗansa.

Suhaila ta tunkare shi hankali a tashe,

“An ɗaura auren?”

Ya yi mamakin maganarta, sai da ya cire hular ya goge gumin goshinsa sannan ya gyaɗa kai,

“Jawaheer ta zama matar aure sai fatan Allah ya basu zaman lafiya.”

Daɓas ta nemi wuri ta zauna. Su Anti kuwa tuni antura tanfatsetsen gidan anshiryawa Jawaheer kayanta, duk da Anti tana ta mitan Gidan bai yi mata ba, bai kamata da arziƙinsa ya zauna anan gidan ba. Ya tabbatar masu akwai ginin da ake yi masa ba a gama ba acan yake son sanya Jawaheer. Kuma da yake ba za su wuce wata ɗaya ba, zai ɗauketa su bar ƙasar. Wannan magana babu wanda Anti bata gayawa ba, har tana samun Farouk tana cewa idan ya je Egypt ɗin Jawaheer za ta kawo masa ziyara ita da mijinta. Shi dai sai kallonta kawai yake yi.

Haka aka tattara Jawaheer aka kaita gidan mijinta, aka kuma watse aka bar amarya ita ɗaya.

A ranar ango ya tare a ɗakin amaryarsa.

A can ɓangaren kuwa Suhaila ta kasa barci sai kuka take yi, shi kansa ya rasa me ke yi masa daɗi. Tambayar duniyar nan ya yi mata amma ta kasa bashi amsa. Daga ƙarshe ta ce sai dai ya mayar da ita gida wurin Abbanta. Babu wata damuwa suka shirya suka kama hanyar Kaduna.

Abba ya yi mamakin zuwansu babu sanarwa, amma sai Farouk ya nuna masa kawai sun zo su gaishe su ne.

Suhaila ce zaune a ɗakinsu shiru ta rasa me ke yi mata daɗi, sai ga Inna ta ƙaraso tana dubanta,

“Ke kuwa ko dai baki jin daɗin auren nan ne?”

Suhaila ta zuba mata idanu kamar mai son tuna wani abu,

“Inna me ya sa kika ce haka?”

Inna ta taɓe baki ta ce,

“Naga duk kin rame kin lalace ne.”

Suhaila ta sake duban Inna, tana son tambayarta zoben nan na Adnan, wanda babu ko shakka Zoben zai taimaka mata daga masifar JAAMUU. Matar da ta iya kashe mahaifiyarta waye ba za ta kashe ba?

“Inna ni kuwa ina zoben nan na Adnan?”

Inna ta yi duru-duru ta riga da ta yi rantsuwa ba zata baiwa Suhaila zoben nan ba, saboda tasan amfanin zoben. So take Hafsat ta ɗan ƙara girma ta ɗauka ta bata.

“A ina kika bani ajiyar zobe? Ban gani ba bansan inda yake ba.”

Daga nan ta kakkaɓe jikinta ta bar wurin. Ƙamshin turarensa ya sanar da ita yana kusa da ita, don haka ta ɗago asanyaye. Shi ɗinne yake ƙare mata kallo kamar yau ya fara ganinta. Dole ta mayar da kanta ƙasa. Sunkuyawa ya yi kusa da ita, ta yadda take iya jin hucinsa,

“Za mu fara shiri saboda za mu bar ƙasar.”

Bata ce masa komai ba, sai jinjina kanta da ta yi.

Kwana ɗaya suka yi suka juya zuwa Abuja.

*****

Tunda Sadiq ya fahimci ciki ne a jikin Ummi ya haukace mata, shi bai shirya haihuwa ba sai an zubar da cikin. Ita kuwa Ummi ta ce babu wanda ya isa yasa ta zubar da ciki. Suka yi ta tashin hankali daga ƙarshe ta zubar da ciki ta tafi wurin Farouk da kuka ta ce Sadiq ya zubar mata da ciki. Farouk ya rasa me zai yi wa Sadiq, sai kawai ya ce Ummi ta zauna a gidansa na kwana biyu shi zai yi maganin abun.

Tsakanin Ummi da Suhaila sai zaman ya zama tamkar kishiyoyi ko haɗa hanya suka yi sai habaici da baƙaƙen magana. Hakan ya ƙara tashin hankalin Suhaila ta sami Farouk yana zaune a kekensa a falo ta sunkuyar da kai.

Hannunsa yasa ya jawota gaba ɗaya rabin jikinta yana nasa, yasa hannu ya ɗago kanta yasa baki ya hure mata idanun da suke a rufe. A hankali ya ce,

“Madam akwai matsala ko? Gaya min menene?”

 Kauda kanta ta yi sannan ta yi magana cikin taushi,

 “Ya kamata ka kira Sadiq akan matsalar Ummi.”

Haka kawai bakinta ya dinga burge shi, ya sake kai hannu ya ɗago kanta yasa yatsu biyu bisa laɓɓanta yana zagaye su. Ummi da ke tsaye daga hanyar kitchen sai ta ji duk duniyar ta yi mata zafi. Tunda take da Sadiq Baka taɓa sanin irin wannan soyayyar ba. Ganin suna shirin wuce gona da iri, yasa Ummi ta koma kitchen ɗin ta fasa ihu. Hakan yasa duk suka dawo hayyacinsu. Farouk kuwa ko a jikinsa sai ma kwantar da kansa da ya yi, yana nazarin da gaskiyar Suhaila gara ya mayar da Ummi. Wani irin nishaɗi yake ji, irin wanda ya saba tsintar kansa a duk lokacin da irin yanayin nan ya riske shi.

Suhaila tana shiga kitchen ɗin ta sami Ummi tana kuka tsakaninta da Allah. Ta yi saurin ƙarasowa tana cewa,

“Sannu ƙonewa kika yi?”

Ummi ta daddage iya ƙarfinta ta hankaɗa Suhaila har sai da ta ƙume kanta, wata azaba ce ta ziyarci kwanyarta. A lokacin kuma Ummin ta fice daga kitchen ɗin da sauri ta shige ɗaki tasa key. Jikin Farouk bai bashi ba, yadda ya ga Ummi ta fito a fusace, hakan yasa ya tashi da ƙafafunsa ya iso har kitchen ɗin. Da sauri ya ƙarasa shigowa ya jawota gaba ɗaya jikinsa tare da cire hannunta a inda take liliyawa.

“Me ya same ki? Bugewa kika yi? Ko Ummi ce?”

Ya jejjero mata tambayoyin a jejjere Yana jin tamkar ciwon a jikinsa yake.

Girgiza kanta ta yi tana son ƙwace jikinta,

“A’a bugewa nayi.”

Jawo hannunta ya yi zuwa ɗakinsa, har zai kulle ya tuna kekensa ya koma ya ɗauko ya rufe ƙofar gaba ɗaya. Sai da ya gamsar da kansa ba tare da ya tunkari neman hakkinsa ba, dan yasan abinda zai iya zuwa ya dawo don haka bai wahalar da kansa wajen aiwatar da abinda ba zai yiwu ba.

Daga nan kuma barci ya kwashe su gabaɗaya.

Ummi ta dinga kaiwa tana komowa dan dai ta ga sun fito amma abin ya gagara. Tana cikin tashin hankalin nan ne sai ga Anti ta shigo. Ummi ta ruga ta faɗa jikinta tana shessheƙa. Ta ɗagota tana tambayar ko lafiya?

“Anti tun ɗazu suka rufe ƙofar sun ƙi buɗewa.”

Anti ta zaro idanu. Daga bisani ta tunkari ƙofar jikinta har yana kyarma.

<< Kaddarata Ce 14Kaddarata Ce 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×