Skip to content
Part 17 of 17 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Da ƙarfi take bugawa tana ƙwala masa kira. Hakan yasa duk suka farka suna duban juna. Da kansa ya mayar mata da komai nata. Ya ɗauki ribom ɗin yana son mayar mata ta karɓa kawai jiki asanyaye ta mayar. Ya zauna bisa kekensa da kayansa duk ya cukurkuɗe. Kansa ya yamutse. Shi ya tura keken ya isa ƙofar ya buɗe. Suhaila kuwa tana maƙale babu inda jikinta baya rawa. Anti ta buɗe baki kawai tana kallonsa, shi kansa sai da kunya ta kama shi saboda irin kallon da Anti take yi masa. Ya sake ɗaga kai ya dubeta, a lokaci guda shima ya mayar da kallonsa inda take kallo. Bai taɓa tunanin haka kayan jikinsa suka hargitse ba. Ya ɗan gyara zaman kwalar rigarsa sannan ya yi gyaran murya ya ce,

“Wallahi Anti barci ne ya ɗan kwasheni shiyasa.”

 Anti ta kasa magana sai hanya da ta bashi ya ƙarasa fitowa. Sannan ta sa baki ta ce,

“Ke kuma fa? Zaki fito ko sai na zo na fizgoki?”

A hankali ta tako ta fito. Kamar a tsakiyar kunnenta ta ji muryar Anti tana cewa,

“Jarababbiya, duk sai ta bi ta ramar da shi saboda tsabar jaraba.”

Maganar ta daki Suhaila sosai, har sai da ta dafe ƙirji tana jin zuciyarta babu daɗi.

Farouk yana ji sai ya yi kamar bai ji ba. Babu abin da ta zo yi a gidan sai kame-kame ta dinga yi ta gama ta fice. Farouk ya kira mahaifin Sadiq ya Gaya masa komai, a daren Ummi bata kwana a gidansa ba ya damƙawa iyayensa. Sati guda ya ƙara a ƙasar ya ɗauke Suhaila suka bar garin…

Bayan sun isa sun natsa. Wani ƙuduri ne aransa a yau ya ci alwashin sai ya cika burinsa. Dare yana yi ya kintsa tsaf cikin kayan barcinsa wanda suka dace da fatarsa. A ƙudundune ya sameta har ta gama shiri ta bi lafiyar gado. Murmushi ya saki, sannan ya koma falo ya ɗauki ruwan zamzam ya yi doguwar addu’a, kai tsaye ya watsa a kowane ƙusurwa na gidan. Ya kunna Qira’a, daga nan ya sake bin kowane ƙusurwa ya tofa Ayatul Qursiyu. Jin kansa yake kamar bai da wata matsala. Ya tasheta ta buɗe idanu tana kallonsa, ya ce,

“Tashi ki je ki yi alwala. Bata kawo komai a ranta ba, ta je ta yi alwala ya shimfiɗa masu darduma suka fara gabatar da nafila. Bayan sun idar ya dafa kanta ya yi addu’a sosai, sannan ya ce su je su kwanta. Ji yake idan Jaaamuu ita ce Sarkin su na Mayu sai ta ɗaga masa ƙafafu yau.

A hankali ya jawota yana shafa bayanta kamar mai lallashi. Ta yi tsit tana jinsa, bata kawo komai a ranta ba dan tasan ba abu bane mai yiwuwa.

Cikin natsuwa ya amshi hakkinsa a wannan dare mai matuƙar girma da daraja a idanunsu. Rungumeta kawai ya yi yana sa mata albarka. A yayin da hawaye ke bin gefen idanunta, shikenan ta zama matar aure, ta zama cikakkiyar mace mai cikakkiyar kamala. Agun namijin da har gobe bata san matsayinta a zuciyarsa ba.

Jaaamuu kuwa tana ji tana gani, tana ihu tana hana su, amma ko alama tsawan da take yi da tsafinta babu abin da ya matso kusa da su, har sai da ta faɗi ƙasa tana burgima tana tsinewa Farouk akan ya rusa mata komai. Surutai kala-kala babu wanda bata yi ba, faɗi take yi,

“Sai na kasheka Farouk! Sai na kashekaaa!!”

 Bai bari sun kwanta ba ya raɗa mata a kunne,

 “Za ki iya tashi kiyi wanka?”

 Kai kawai ta gyaɗa masa, kwata-kwata bata ƙaunar ma su haɗa idanu. A hankali ta jawo zani ta ɗaura ta lallaɓa za ta shiga banɗakin ya yi saurin cewa,

“Ki yi addu’a.”

Tabbas ya ankarar da ita da har ta mance. Bayan ta tsaftace kanta ne ta fito tana jin zafi kaɗan-kaɗan a ƙasarta.

Shima ya shiga ya watsa ruwa, yana fitowa ya zura jallabiyarsa ya haye gadon. Sai da ya lallaɓata har barci ya kwasheta sannan ya tofeta da Addu’a yana murmushi. Sakkowa ya yi ya buɗe Qur’ani yana bin karatun da ya sanya cikin natsuwa da walwala.

 *****

Bayan Jawaheer angama cin amarci, Ya’u ya ce ta shirya zai kaita gurin wani magani a wani ƙauye saboda baya jin daɗinta kuma yana da tabbacin wata budurwarsa ce ta yi mata asiri, saboda bai aureta ba. Ya sake ja mata kunne kada ta gayawa Anti gaskiya kawai ta ce mata za su ɗan bar ƙasar ne zuwa wani lokaci.

Jawaheer bata kawo komai a ranta ba, sai farin cikin irin yadda mijinta yake ji da ita yake kuma son lafiyarta.

Bayan sun yi Sallama da Anti ya ɗauketa suka kama hanya.

Tun suna wuce garuruwa har barci ya kwasheta ta saki jiki tana barci. Shi kuwa Ya’u ya dinga sharara gudu kawai yana kutsawa cikin ƙauyen. Buɗewa idanunta ta yi ta gansu a hanya suna ta keta dazuzzuka. Abin ya ɗan bata tsoro ta dube shi ta ce,

“Kai kuwa ya akayi kasan irin wuraren nan?”

Yana murmushi ya ce,

“Anan nake amso magani saboda kinsan jama’a idanunsu yana kan masu kuɗi.”

Ta jinjina kai kawai. Sai yamma likis suka sauka a wasu bukkoki garin babu wasu jama’a. Da ƙyar ta sauka, sai gani ta yi ana murna ana maraba ga Ya’u da matarsa. Mamaki ya sake kamata, amma tunda ta gaji wuri take nema tukuna. Ɗaya daga cikin bukkar suka shiga anshare shi fes, da wani gado irin na ciyayi.

Jawaheer ta zauna ta takure wuri guda tana ƙyanƙyani. A gabansu aka jere abubuwa harda su fura, amma sai ta ƙi ci. Dole ta nufi motarsu ta ɗauko abubuwan da suka siya a hanya ta buɗe tana ci.

Ya’u ya dubi yadda take kallon wurin kamar za ta yi kuka ya dubi tsohuwar mai ɗauke da ƙazanta a jikinta ya ce,

“Jawaheer nan ne asalina, wannan mahaifiyata ce. Da ni da ke anan garin zamu ci gaba da zama har zuwa ƙarshen rayuwarmu.”

Jawaheer tana murmushi a zatonta wasa yake yi. Ta ɗago ta zolaye shi taga fuskarsa babu annuri, ya sa kai ya fice can sai gashi ya dawo da kayansa masu datti, sai gaba ɗaya ya juye mata kamar wani mutum da ta taɓa gani. Ya ɗan yi murmushi ya ce,

“Da yake ƙwaƙwalwar kifi gareki nasan har yanzu ba ki gane ni ba. Ni ne Ya’u wanda kika wulakanta saboda ya ce yana sonki. Dukiyoyin nan da kika gani na yaron Alhaji Mamman Canji ne, na mayar masa da komai sai wannan motar, itama gobe za a mayar masa. Tare da ke zamu dinga zuwa siyar da kayan miya anan garinmu. Garin nan babu ntwrk bare har kiyi tunanin kiran wani. Kuma ban shigo da ke gidan nan ba sai da su Inna suka kafeki. Ko da kuɗi aka haɗa ki akan ki gujeni ba zaki iya ba Jawaheer. Ina son inkoyar da ke tarbiyyar da iyayenki suka kasa baki, ina son ki daina tantance mai kuɗi da talaka domin duk ɗaya suke agurin Allah. Sannan ki koyi daraja ɗan adam, baki isa Allah ya karrama ɗan adam ke ki ce zaki wulakanta shi ba. Kisha fura nan ne makwancinmu da ni da ke.”

Jawaheer za ta fi son koma waye a kusa da ita da ya wanke mata mari domin ta farka daga barcin da take yi.

Suhaila dai tunda wannan lamari ya auku a tsakaninta da Farouk gabaɗaya ta daina sakin jiki da shi, tana tsoron kada a sake maimaita irin hakan. Sai dai tuni Farouk ya fita wayo da gogewa, don haka ya nuna mata ba abin da ke gabansa ba kenan. Sai da suka kwashe sati guda cur! Bai nemi wani abu ba, hakan yasa ta fara sakin jiki da shi, sannu a hankali ya yi amfani da damarsa ya cusa mata shaƙuwa da shi.

Abin har mamaki yake bata, idan babu shi a kusa sai ta ji duk duniyar ta yi mata zafi. Tana jin wani sabon al’amari akansa wanda bata taɓa ji akan wani ɗa namiji ba.

Yau ma kamar kullum tana zaune gaban tv tana sauya tasha, ta ji alamun mutum a bayanta. Farin ciki ya tsirga mata ta tashi da sauri ta maƙale shi tana shafa goshinsa. A hankali ta zame hannunta cikin rauni kamar za ta yi kuka ta ce,

“Yaya Farouk baka da lafiya ko?”

Idanunsa da suka kaɗa suka yi jaaa ya ɗan saci kallonta, a lokaci guda ta jawo hannunsa zuwa kujera ta amshe duk wasu abubuwan da ke hannunsa. Babu ɓata lokaci ta nufi kitchen sai gata ta dawo da ‘yar roba da ruwa da ƙaramin tawul. Ta dinga tsoma tawul ɗin idan ta cire sai ta matse sannan ta manna masa a goshi.

Maɓallin rigarsa ta sa hannu tana ɓallewa hakan yasa ya tsura mata idanu, yana jin tsigar jikinsa yana tashi. Rintse idanunsa ya sake yi yana sauraren duk irin abubuwan da take yi. Tashi ta yi ta ɗauko magani ta ɓare ta bashi. Sannan ta jawo hannunsa zuwa ɗaki.

A zatonta barci zai yi shiyasa ta jawo masa bargo, amma sai ta ji ya riƙe hannunta sosai. Ta waiwayo a sanyaye, tana son yin magana amma yanayinsa ya haddasa mata mutuwar jiki. Dole ta dawo gadon gaba ɗaya ya rufe su, jikinsa babu inda baya kyarma. ‘JAAAMUU’

Zuciyarsa ta ambata da ƙarfi. Da sauri ya tashi ya yi addu’a ya tofa a kowacce ƙusurwa, sannan ya dawo ya ja masu bargo.

*****

Sannu a hankali Suhaila tana sake tantance menene auren? Sai dai abin da ke damunta wai shin sai yaushe Farouk zai furta mata da bakinsa yana sonta ne? Wannan abu yana damunta.

Yau ma kamar kullum tana gyara gado ta ji shigowarsa, bata waiwayo ba ta ci-gaba da abin da take yi. Yana ƙarasowa ya zauna a gefen gadon ya jawo hannunta ta zauna kusa da shi, ya ciro wani abun hannu mai kyau da sheƙi ya kama tsintsiyar hannunta yana sanya mata.

Bayan ya gama ya sumbaci hannun yana murmushi,

“Komai naki mai kyau ne. Mun kusa komawa gida Nigeria.”

Dam! Gabanta ya faɗi ita har ta fara mance wata aba wai matsala. Dole ta ƙirƙiro yaƙe ta gyaɗa masa kai kawai tare da gode masa.

*****

A can gida Nigeria kuwa cikin ikon Allah su Daddy sun sami nasara akan Jaaamuu bayan wahalhalun da ta baiwa kowa. Sanadiyyar hakan gaba ɗaya matsafan ta tarwatse.

A irin lokacin ne kuma su Farouk suka sami isowa gida.

Kai tsaye gidansu suka sauka, sai dai a yanayin da ya ga Anti abin ya ɗaga masa hankali. Bayan ya gaisheta ya sake dubanta, “Anti wani abu yana damunki ne?”

Kamar jira take kawai ta fara kuka,

“Farouk yanzu ko bayan babu raina irin riƙon da zaka yi wa ƙanwarka kenan? Kullum ina neman lambarta bata shiga haka lambar mijin. Hankalina ya tashi, kai kuma ka tafi ka yi zamanka, wannan baƙar munafukar tana neman ta raba ni da kai.”

Farouk ya duƙar da kai shiru, sannan ya ce,

“Anti kina nuna mana bambanci a tsakanina da Jawaheer. Na dawo kin ganni da ƙafafuna na sami lafiya banga wata murna a idanunki ba. Sai ma zagin wacce ta taimaka min kike yi? Maganar Jawaheer ke kika gaya min mijin ya ɗauketa sun tafi yawon shaƙatawa, me ya sa zaki damu? Matarsa ce yana da iko ya kaita duk inda ya gadama. Tsakaninmu da su addu’a ce.”

Anti ta ɗan sami natsuwa a zuciyarta, don haka ta ɗan yi murmushi ta ce,

“Ai tun kana can na dinga murna ko? Ina ce addu’a ta ce ta sa har ka sami lafiya? Yanzu ya maganar aurenka da Rumaisa? Gaskiya ina son ka ƙara aure.”

Gabaɗaya Suhaila sai ta tsure ta kama gumi a wurin. Bata taɓa sanin tana da kishi haka ba. Ji ta yi gaba ɗaya ta gundura da zaman. Shi kuwa tashi kawai ya yi ya nufi ɗakinsa, Anti ta bi bayansa. Suhaila ta miƙe har tana karo da kujera, ta nufi hanyar fita daga gidan.

Bata san yadda akayi ba ta kawo kanta gida tana shiga ta shige ɗakinta kawai ta fasa kuka. Tana mamakin Anti Wacce iri ce? Duk matsalolin nan da suke shirin tunkararta har yanzu bata san ta dawo hayyacinta ba?

Tana nan kwance inbanda kuka babu abin da take yi, ji take duniyar ta yi mata baƙinƙirin.

Shi kuwa yana shiga ya waiwayo ya dubi Anti ya ce,

“Anti ba zan iya ƙara mace a gidan nan ba. Ra’ayina iri ɗaya ne da mahaifina, yadda bai ƙara aure ba nima mace ɗaya nake buƙata a rayuwata. Duk wanda zai ce yana son ɗanki a yanzu ƙarya yake yi maki, dole akwai wani abu da yake so agun ɗanki ne amma ba zuciyarsa ba. Suhaila bata da matsala ko kaɗan, idan kika zauna da ita zaki fahimci halin yarinyar.”

Anti ta dube shi sama da ƙasa ta ja tsaki, kafin ta ɗora da cewa,

“Ko ma menene bai dameni ba, tunda nace bana sonta ai kasan bana sonta ɗin. Na baka sati biyu kaje kayi tunani akan abin da na gaya maka. Baka taɓa yi min jayayya ba, ban taɓa sa doka ka kauce min ba. Amma tunda ka auri yarinyar nan shikenan nake ganin ba daidai ba. Ta yaya kake tunanin zan sota? Ba zan taɓa sonta ba.”

Girgiza kansa kawai ya yi ya sake ficewa. Sai dai kuma neman duniya ya yi mata bai ganta ba, dole ya fito yana tambayar masu gadi, suka tabbatar masa ta kama hanyar gida.

Da sauri ya ɗauki motarsa ya bi bayanta.

Shessheƙan kukanta ya tabbatar masa da ɗakin da take. Sai da ya saki ajiyar zuciya sannan ya cusa kansa.

A hankali ya ɗagota, kawai ta rungume shi ta cusa kanta cikin ƙirjinsa tana maganganu cikin ruɗewa. Gaba ɗaya ta mance irin kunyarsa da take ji, da kuma yadda take yi masa rowar kalamai,

“Ni…Ni… Ba na son kishiya, yaushe muka yi auren? Don Allah don Allah kada ka auro wata ka haɗa ta da kanka.”

Tana maganar tana ajiyar zuciya. Shiru ya yi ya kafeta da idanunsa yana jin ƙarin sonta a cikin zuciyarsa,

“Suhaila… Buɗe idanunki ki kalleni.”

<< Kaddarata Ce 15

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×