Ta ƙanƙame shi tana girgiza kai alamun ba zata iya ba. Ya sake kiran sunanta cikin sanyi,
“Yi haƙuri ki buɗe idanunki.”
A hankali ta buɗe idanun, sai dai tana kallonsa ta yi saurin rufe su tana sake jin hawaye suna kwaranya.
Yasa ɗan yatsarsa ya dinga ɗauke hawayen, kafin ya ci gaba da cewa,
“Ina sonki Suhaila. Na fara sonki a tun ranar da na fara cin girkinki a cikin gidanmu. Ranar da na fara ɗora idanuna akanki, sai na tabbatar da abin da ke cikin zuciyata. Sai dai a lokacin kin fi ƙarfina saboda abokina yana sonki, sannan zan auri ‘yar uwata kuma ‘yar uwarki. Na haƙura na miƙa komai ga Allah. Sai dai har ranar ɗaurin aure jikina ya kasa bani zan iya rasa ki, ba tare da na dogara da komai ba.”
Ya yi ajiyar zuciya, a lokacin da ya lura ta buɗe idanunta amma kuma bata kalle shi ba. Ya sake tallabo haɓarta ya ce,
“Yes! Da gaske nake yi maki. Ban taɓa sanin menene so ba sai akanki. Mahaifiyata ita ɗaya ce agun mahaifina, baya sha’awar mata biyu. Nima kuma bani da sha’awar mata biyu a cikin rayuwata. Kin isheni komai Suhaila. Idan kika ga na ƙara aure ki ɗauka Allah ya riga ya rubuta wannan ƙaddarar ce a cikin rayuwata. Ki kwantar da hankalinki kin ji? Na ƙara sonki na ƙara martabaki a ranar da kike jinyata, kike bani kulawa tsakaninki da Allah kamar jaririnki. Don Allah kada ki sauya daga irin tarbiyyarki. Allah ya yi maki albarka.”
Jikin Suhaila ya yi matuƙar sanyi, ji take yi kamar babu wanda ya taɓa gaya mata kalamai masu daɗin kalaman nan. Ta kasa furta komai sai cewa take yi,
“Ina sonka, bansan lokacin da na tsinci kaina a cikin sonka ba, tashi na yi kawai na tsinci kaina dumu-dumu.”
Sai kuma kunya ta kama ta, da sauri ta sake cusa kanta a ƙirjinsa tana jin hawayen farin ciki yana zuba. Za ta so ta kira wannan rana a matsayin rana mai matuƙar daraja da girma a idanunta. Za ta ajiye wannan ranar a cikin ƙundinta ta yadda ba zata taɓa mance shi ba.
*****
Sai dai kuma a cikin ƙauyen kalgo, wannan rana ta kasance rana mafi muni a cikin tarihin rayuwarta. Jawaheer ta ajiye wannan baƙar ranar a cikin ranakun da ba zata taɓa manceta ba. Kasancewar yau ta ƙi bin Ya’u wajen siyar da kayan miya, a cewarta zazzaɓi take yi. Shi kuwa ya yi mata shegen duka. Tunda take bayan Yayanta babu wanda ya taɓa sa hannu a jikinta. Irin dukan da ya yi mata sai da ya ji mata ciwo. Kuma abin mamaki mutanen gidan suna kallo babu wanda ya iya bashi haƙuri.
Da wahala wanda yasan Jawaheer idan ya ganta a yanzu ya ganeta. Tun bata iya cin abincinsu har ya zame mata dole cinsa, Idan ba haka ba sai dai ta mutu.
Duk ta lalace ta zama abar tausayi. Ga laulayin ciki da ya sanyata gaba, amma ko a jikinsa. Sosai yake jin tsanar Jawaheer sai dai yadda yake horata ya wuce yadda take hora talaka.
A wannan rana ita kanta Ummi ta amshi nata dukan a hannun Sadiq don hakane ita kanta take duban wannan rana a matsayin baƙar rana. Sai dai taimakonta Farouk ya iso gidan.
Sai da suka yi kamar za su yi dambe da Sadiq, sannan suka sakko. Ya ce Ummi ta tattara kayanta su tafi. Ya dubi Sadiq ya ce,
“Zaka ji kira a kotu sai ka bata takardarta. Shashanshan namiji wanda bai san darajar kansa ba.”
Anan kuma sai jikin Sadiq ya yi sanyi, dan yasan halin mahaifiyarsa sarai. Dole ya saukar da kansa ya roƙi Farouk ya zauna su yi magana.
Da ƙyar Farouk ya amince da sasanci, ya Gaya masa dukkan abubuwan da take yi masa da baya so. Farouk ya yi mata faɗa shima kuma ya yi masa faɗa akan idan ya sake jin irin hakan Wallahi sai kotu ta raba su.
Sai mu ce muna taya Ummi murnar samun ‘yancin kai.
*****
Yau dai Anti da kanta ta sami Alhaji da shi kansa rashin ‘yarsa yake damunsa amma sai ya daure. Bayan ta zayyane masa damuwarta akan rashin samun Yaks, sai Alhaji ya gyara kwanciyarsa ya yi banza da ita ya ci gaba da sabgarsa.
Dole ta lallaɓa ta wuce gidan Hajiya Asiya ta gaya mata komai. Suka kwashi jiki suka bazama har gidan Jawaheer ɗin. Ga mamakinsu sai suka ga alamun da mutane a ciki. Suka tambayi Maigadi ko su waye a gidan? Maigadi ya tabbatar masu gidan yaron Alhaji Mamman Canji ne. Suka tambaye shi ko yasan Yaks ya ce a’a.
Dole suka fito suka shiga gidan. Bayan ‘yan gaishe-gaishe suka gaya masu Yaks Suka zo nema. Anan ma aka ce ba asan shi ba. Hakan ya ɗaga hankulansu, kuma tabbas ba kayan ɗakin Jawaheer ba ne a ciki. Dole suna fitowa kai tsaye gidan Farouk suka wuce. Da sallamarsu da shigowa falon a tare suka bayyana. Suhaila tana zaune Farouk yana kwance kansa a bisa cinyarta tana yi masa susa a tsakiyar kai, sai lumshe idanun yake yi. Tana ganinsu ta fara ƙoƙarin ture kansa amma fir yaƙi tashi. Ƙila daɗin ne ya rinjaye shi bai ji shigowarsu ba. Cikin daburcewa ta ce,
“Sannu da zuwa.”
Sai a lokacin ya buɗe idanu, yana ganin su Anti ya tashi zaune yana dubansu,
“Lafiya kuwa na ganku a haka?”
Anti ta yi ajiyar zuciya, sai kuma hawaye. Jikinta yana bata ‘yarta tana cikin mawuyacin hali. Amma shi Farouk da Babansa ko a jikinsu. Da ƙyar ta gaya masa komai, sai a sannan hankalinsa ya tashi ya ware idanunsa sosai yana Salati. Babu shiri ya miƙe kawai ya ce,
“Ina zuwa.”
Duk suka zauna jigum-jigum. Kai tsaye gidan Alhaji Mamman Canji ya nufa. Bayan anyi masa iso ne, suka sake gaisawa ya gaya masa komai. Alhajin ya kira ɗansa Kamal ya ce,
“Kai wai yaron nan da kasa muka karɓi aurensa ina ne gidansu? Ya tafi da ‘yar mutane shiru.”
Kamal da yasan komai ya yi fuska ya ce,
“Alhaji ƙanin wani abokina ne, ni abokin nawa kawai na sani shi ya ce suna neman gida na taimaka masu. To maganar da nake yi maka abokin nawa ya rasu. Kuma gaskiya bansan komai akansu ba. Taimako kawai na yi.”
Alhajin ya sauke wayar yana duban Farouk da gaba ɗaya ya yi suman zaune.
Farouk ya girgiza kai yana ganin wannan laifin su ne, da ba haka ba Wallahi sai ya ɗaure shi kansa Alhaji Mamman ɗin. Duk da haka sai ya koyawa Kamal ɗin hankali.
Cikin tashin hankali ya dawo gidan,tun kafin ya iso har ya kira Mahaifinsa ya gaya masa komai. Idan banda Salati babu abinda Alhaji Marwan yake yi. Yana isowa gidansa bai kai ga yin magana ba Alhaji Marwan ya iso Shi da Daddy.
Farouk ya sake juye masu komai. Anti tasa hannu akai ta fasa kuka tana cewa,
“Shi kenan ya cuceni ya cuci rayuwar ‘yata.”
Alhaji Marwan ya daka mata tsawa,
“Kin cuci kanki dai! Kin kuma cuci rayuwar ‘yarki da kanki. Za ayi bincike kika nuna sam! Babu wanda ya isa. Duk wanda zai kawo maki wata magana akansa sai ki ce wai yana yi wa ‘yarki hassada. Yau gashi kin kashe rayuwar ‘yata.”
Farouk kuwa gumi kawai yake yi. Suhaila ta miƙe gaba ɗaya ta gigice ta nufi ƙofa hannu a bisa kai. Hawaye kawai ke zuba babu ƙaƙƙautawa.
Farouk ya yi ta maza ya dawo da ita tare da girgizata da ƙarfi,
“Me ke damunki?”
“Innalillahi… Yaya mun shiga uku. Ya’u ne ya saceta.”
Gaba ɗaya sai aka hau kallon-kallo. A lokaci guda duk suka haɗa baki,
“Ya’u?”
Ta gyaɗa kai, ta gaya masu yadda ta yi da Anti da marinta da ta yi, da yadda Ya’u ya sameta a hanya ya gaya mata ƙudirinsa. Ta dubi Farouk ta ce,
“Shi ne ka ganni tsaye da shi ana gobe bikin.”
Farouk ya koma ya zauna kawai. Anti ta shiga zazzare idanu tana cewa,
“Ayya ban fahimceki bane. Ki yafe min don Allah. Yanzu ina zan sami Ya’u?”
Alhaji Marwan ya dubi Daddy ya ce,
“Yanzu hankalina ya kwanta. Da na fahimci ba saceta ya yi ba, ya kaita ne domin ya gyara mata zama. Dama ina son Jawaheer ta fahimci rayuwar duniya. Tashi mu tafi.”
Daddy dai ya miƙe yabi bayansa ba dan ya gamsu da kalaman Alhaji Marwan ba.
Anti ta rushe da kuka ta kama ƙafafun Farouk tana roƙonsa ya taimaka mata. Shi dai ya kasa magana saboda tashin hankali. Dole aka kira Ummi duk suka kama hanya sai wurin siyar da kayan miya. Kowa cewa yake bai san ƙauyensu ba.
Farouk ya tafi har gidan Kamal yana fitowa ya dinga yi wa Farouk gani-gani. Don haka ya kira ‘yan sanda kafin su ƙaraso zuciya tasa Farouk ya yi masa mugun duka sannan aka kwashe shi. Rikici ya ɓalle tsakanin Farouk da Alhaji Mamman yana faɗin sai ya bi wa ɗansa hakkinsa, Farouk kuma yana faɗin idan duk duniya gatansa ne ba zai saki Kamal ba sai idan anga ƙanwarsa.
Ita kanta Suhaila kwana biyu ta rasa gane kan mijinta. Ko barcin kirki baya iya yi. Kullum addu’arsa Allah yasa ƙanwarsa tana cikin ƙoshin lafiya. Ganin halin da mijinta ya shiga ya sanya ta tafi gidan Anti Laila ta ce a bata direba zata je wajen ‘yan kayan miyan. Babu musu aka bata kawai ta kama hanya. Sai da ta kutsa har cikin kasuwar inda aka nuna mata wani aka tabbatar mata garinsu ɗaya. Da roƙo da alƙawarin kuɗi mai tsoka ya amince ya biyota. Don shi kansa ya ce yana daɗewa bai je gida ba, saboda wahalar hanyarsu. A gaban Anti Laila ta dire shi, wanda bata san ma Farouk yana falon ba. Anan aka shirya gobe da asubahi za su kama hanya. Ita Anti Laila ma taso tun yau su kama hanya.
Washegari suka kama hanya da Anti da Farouk da kuma Yahuza sai Suhaila.
Tun suna tunanin za su iso har suka fara tunanin ko dai shi ma ya kawo su ne ya ci kansu? Sai yanzu suke ganin kuskurensu na rashin zuwa da ‘yan sanda. Dole suka tsaya a wani Out-Post suka sami ‘yan sanda da motarsu sannan suka ci-gaba da tafiya.
Da shigowarsu ƙauyen Suhaila ta hau dube-dube tana kallon wata da icce akanta ta kafeta da ido sai dai bata gane Jawaheer ba ce. A ƙofar gidansu Ya’u suka tsaya. Abinka da ƙauye anga motar ‘yan sanda, sai kowa ya firfito.
Suhaila ta nuna Ya’u da hannu ta ce,
“Ga Ya’un.”
Babu wanda ya gane shi sai ita. Aikuwa Farouk ya kama shi da duka. Ya shaƙe wuyar rigarsa ya ce,
“Ina ƙanwata?”
Anti ta daddage ta zabga masa mari,
“Dan ubanka ina ‘yata?”
Ya ce,
“Ni bansan inda take ba.”
Mutanen garin sun so su yi caaaa, ganin ‘yan sanda yasa duk suka dakata. Suhaila ta dubi Jawaheer sosai da iccen nan akai ta ƙaraso gabanta ta ture iccen ta ƙanƙameta tana jin ƙarin imani a zuciyarta. Jawaheer tana kuka tana cewa,
“Suhaila! Yaushe kuka zo?”
Suhaila ta waiwayo ta ce,
“Anti ga Jawaheer ɗin.”
Duk suka juyo. Lallai da ba dan ance Jini jini ne ba. Da babu wanda ya isa ya shaida Jawaheer. Ta ruga ta rungume Anti tana tsananta kuka. Farouk gaba ɗaya jikinsa ya mutu, kawai duban Jawaheer yake yi idanunsa sun kaɗa sun yi jazir. Ko me Jawaheer ta aikata a rayuwa bata cancanci hukunci irin na Ya’u ba.
Ta dawo ta rungume Farouk ta fasa kuka. Shi dai ya kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi. Ya nemi da ta shiga mota amma ta nuna masu ita ta fi son zaman nan garin. Farouk ya dubi ‘yan sanda ya ce,
“Ku yi masa duka har sai ya karya abin da ya yi mata.”
Basu kai ko ina a dukansa ba ya nufi bayan gidan da su ya cire abin da ya sanya. A lokacin ta ji kamar ankwance mata takunkumi. ‘Yan sanda suka kwashe shi a motarsu, su kuma suka juya ba tare da sun ƙara wasu lokuta ba. A wani gari dare ya yi masu dole suka nemi hotel. Babu kayan da Jawaheer zata sauya ko da kayan yafi son mahaifinta ya ganta a yadda suka ganta. Kwanciyar rashin kwanciyar hankali suka yi, da asussuba suka yi Sallah suka ci gaba da tafiya.
Kafin su iso gidan har ya kira Mahaifinsa ya gaya masa komai. Don haka da isarsu gidan suka sami gidan a cike. Alhaji Marwan Yana ganin Jawaheer kawai ya fashe da kuka. Hatta Daddy sai da ya dinga zubar da hawaye. Ya dubi Anti ya ce,
“Kin cuceni Laila kin cuceni kin cuci rayuwata.”
Suhaila ta shiga da ita ciki ta haɗa mata ruwan wanka mai zafi ta fara shiga ta warware gajiya, daga bisani ta zuba mata dettol. A ƙalla sai da ta yi wanka da ruwa ya kai biyar sannan ta fito. Doguwar riga kawai ta sanya Doctor ya zo ya duddubata ya sa mata ƙarin ruwa da allurar barci.
Duk suka dawo falo suka yi jigum-jigum.
Sai da Jawaheer ta yi kwanaki ana kula da lafiyarta kafin ta fara dawowa daidai. Doctor ne tsaye akan Anti ya tabbatar masu Jawaheer tana ɗauke da juna biyu. Kamar daga sama suka ji muryar Farouk yana magana cike da takaici,
“Doctor a zubar da cikin nan.”
Kowa ya zuba masa ido. Lallai ya ɗau zafi da yawa. Doctor ɗin yaso yayi masa ƙarin bayani amma fir Farouk ya ƙi tsayawa ya saurare shi.
Ita kuwa Jawaheer sai tasa kuka ta ce,
“Yaya kayi haƙuri ina son cikina…”
Juyowa ya yi ya watsa mata kallo sannan ya ce,
“Sai dai ki koma gidan uban ɗan ki haife shi.”
Ya juya kawai ya fice. Sun yi zaton lamarin da sauƙi, sai suka ga Farouk ya fi kowa ɗaukan zafi. Da ƙyar ya amince aka saki Kamal, Shi kuwa Ya’u ya yi rantsuwa sai ya yi gidan yari.
*****
Yana zaune ya haɗa kansa da hannun kujera ya yi shiru. Shi kaɗai yasan yadda zuciyarsa ke tuƙuƙi, kullum idan ya kalli Jawaheer sai ya ji idanunsa sun cicciko da hawaye. Yanayin da ya ganta a garin Kalgo ya ƙi ɓace masa a zuciya. Suhaila ce ta shigo cike da damuwa ta ɗago kansa suka dubi juna, sai kawai ta sa masa kuka. Tuni ya yi watsi da damuwarsa ya shiga tambayar abin da akayi mata.
“Yaya Farouk me ya sa ba zaka daina sa damuwar nan a zuciyarka ba? Rabon da insami kulawarka har na fara mancewa. Tunda anganta kuma tana gabanmu sai ka sassauta wannan damuwar don Allah.” Tabbas ta fi shi gaskiya, dole ya jawota jikinsa yana lallashi. Cikin salonta ta fara mantar da shi damuwa, babu shiri suka yi ciki domin sauke nauyin da suka ɗaukarwa kansu.
Da yamma Suhaila ta shigo ta kaiwa Jawaheer ruwan zafi a kofi, ta ganta da Anti kamar suna tattaunawa. Don haka ta juya zata fita, Anti ta kirawota ta dawo. Ta shafi bayanta ta ce,
“Suhaila mun zama ɗaya. Haƙiƙa da ba dan ke ba da ba zamu ga Jawaheer cikin sauƙi ba. Ki yi haƙuri ki yafe mana don Allah.”
Suhaila ta duƙar da kanta ta ce,
“A kullum a matsayin uwa nake ɗaukarki baki yi min komai ba.”
Jawaheer ma ta roƙeta har tana hawaye.
*****
Rayuwa ta miƙa. Ummi ta sami ‘yancin kanta, sun kuma nemi afuwar Suhaila. Gaba ɗaya idan ka gansu abin sha’awa. Jawaheer da ƙaton cikinta, ita kuma Suhaila a lokacin cikin ke shiga wata shida. Ya’u kuma yana can gidan yari.
Anti ta nemi afuwan mijinta sun sasanta. Haka Inna ta zo har gida ta dinga roƙar Suhaila afuwa, ta nuna mata babu komai.
*****
Farouk ya fito zai tafi aiki hannunsa ɗauke da cup Yana kurɓar abinda ke ciki a natse. Ita kuma Suhaila tana tafe da jakarsa a hannu hularsa ce akanta suna ‘yar hirar su cikin nishaɗi.
A bakin ƙofar ya manneta da bangon da sunan karɓar hularsa bayan ya ajiye cup ɗin da ke hannunsa. Ya ɗan bata fake a wuya hakan yasa ta tsinci kanta cikin wani yanayi. Gyaran muryar da suka ji ne yasa duk suka waiwayo. Ummi ce da Sadiq, duk suka dubi juna. Ummi ta riƙe haɓa,
“Ohhh Yaya Farouk duk inda kuka samu soyayya kuke yi abinku.”
Suhaila ta sunkuyar da kai. Sadiq da Farouk suka yi murmushi tare da tafawa. Suka fice Ummi kuma da Suhaila suka shige ciki.
BAYAN WASU SHEKARU.
Farouk yana sauka a mota yaran suka yi masa caaaa ana oyoyo Daddy. Adnan ne a gaba babban ɗansa, sai Anisa da ke biye da shi a baya ita ce ta biyu. Ya ware idanu ganin ɗan gidan Jawaheer Haidar shima aguje. Yana murmushi duk ya tare su da murnarsa. Anisa kawai ya ɗauka yana faɗin ta yi nauyi da yawa.
A falo ya basu tsaraba suka fice aguje. Ya bi su da kallo yana cewa yara kenan. Suhaila ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa yana lumshe idanu. Sai da ta tabbatar ya kintsa sannan ta ce masa,
“Abban Adnan yanzu dai nasan ka amince Jawaheer ta koma wurin Ya’u ko? Tunda komai ya daidaita Alhaji da kansa ya amince da hakan, ita kanta ta amince. Ka dubi irin zaryar da yake yi mana. Don Allah ko dan darajar Haidar.”
Sai da ya jawota jikinsa ya shafi bayanta,
“Na amince shugaban ‘yan naci. Allah ya yi maki albarka.”
Ta rungume shi tsam a jikinta tana dariya. A lokacin wayarta ta yi ƙara tana ɗauka ta fara tsalle. Ya kamota yana dubanta,
“Ke kin mance? ‘Ya’yanki uku. Kin ga Adnan, Anisa, Haidar. Haba kin wuce tsalle.”
Tana dariya ta ce,
“Daina rage min matsayi. ‘Ya’yana haka.”
Ta ware ‘yan yatsu huɗu. Shima ware idanun ya yi, idan ya fahimceta Ummi ta haihu kenan.
“Ummi ta haihu?”
Ta miƙa masa hannu suka tafa,
“Yes! Sarkin zurfin tunani. Yanzu Momi ke gaya min wai suna asibiti ta sami ‘ya mace.”
Yana murmushi ya ce,
“Iyye… Lallai su Ummi an girma. Zo mu je ciki ki ji wata magana.”
Ta maƙale kafaɗa,
“An ƙi wayon.”
Ya ɗan marairaice,
“Don Allah mu je a ƙarawa Anisa ƙani.”
Anisa da ke bayansu ta ƙara so da gudu ta ce,
“Daddy yanzu zaka ƙara min ƙani?”
Gabaɗaya Farouk ya daburce. Suhaila kuwa ta sami mugunta sai dariya. Ya ɗaure fuska ya ce,
“No Anisa. Ina nufin Anti Ummi ta haifa maki ƙanwa mai kyau. Maza je ki ki gayawa ‘yan uwanki.”
Ta ruga da gudu ta yi waje. Shi kuma ya jawo hannunta suka shige.
Yaran suna shigowa falon suka tabbatar da iyayensu suna ciki, suka juya. Wannan ce tarbiyyarsu, indai mahaifinsu yana nan ba su zuwa ko da ƙofar ɗakinsa.
Alhmdllh Alhmdllh Alhmdllh
Mun kammala. Fatimarku ce ‘Yar gidan Ibrahim, jika agun Garba ‘yar mutan Borno.