Skip to content
Part 2 of 10 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Tana murmushi ta gyaɗa masa kai. Har wajen mota yau ta raka shi. Kallon da yake mata ya yi yawa, dan haka ta ce,

“Wai me ya sa kake ta kallona ne bana so fa.”

Ya ɗaga mata gira,

“Ina so fa.”

 Gaba ɗaya suka yi murmushi.

 Yana tafiya ya kira wayar Inna kasancewar wayar da ya bata babu caji.

 Cikin wata murya yake magana,

“Suhaila zoben nan Kakata ta bani, babu wani mugun abu da ya isa ya zo kusa da ke muddin da zoben nan a hannunki. Yanzu duk tsarin da ta bani yana kan zoben nan, ni kuma na sadaukar maki.”

Suhaila ta ruɗe, ta gigice ta ce,

“Don Allah ka dawo ka karɓi zoben, ban sani bane, me ya sa zaka bani? Ni ka dawo don Allah.”

Abin ya bashi dariya, kawai ya katse wayar gaba ɗaya.

Ta rasa dalilin da yasa ta kasa barci jikinta babu inda baya rawa. Barci ya kwasheta, ta farka cikin dare da wata ƙara jikinta yana kyarma.

Abba da Inna suka shigo suna jijjigata. Ta rungume Abba tana kuka,

 “Abba! Sun kashe min Adnan! Abba don Allah ka kira Adnan ka ji.”

 Abba ya gigice don haka ya ɗaga waya ya kira Adnan, amma wayar a kashe. Ya kwantar mata da hankali akan gobe zai je gidan.

 Cire zoben ta yi tana jin ta tsani dalilin raba shi da wannan zoben. Da sassafe ta zura hijabinta, Abba yana ƙwala mata kira amma ko dubansa ba ta yi ba, ta nufi hanya domin neman abin hawa. Dole Abba ya ɗauko motarsa ya ce ta shiga.

Tun daga shan kwanan gidan take ganin mutane. Motar Abba bata gama tsayawa ba, ta buɗe ƙofar sai gata a ƙasa. Ba ta damu da azaban da ya ziyarceta ba, ta miƙe a gigice tuni ta watsar da takalmanta. Ba ta tsaya tambayar kowa ba ta kutsa kanta falon mahaifiyarsa.

Cak! Ta ja ta tsaya tana duban yadda ƙannensa da yayyensa suke kuka. Ga gawan nan shimfiɗe a falon.

“Adnan!” Ta ƙwala masa kira, a lokaci guda ta sunkuya a gaban gawan tana shessheƙa kamar mai suma. Hannunta yana wani irin rawa ta sa hannu ta kwaye rufan da aka yi masa. Yana kwance kamar ka kira shi ya amsa, fuskarsa ɗauke da murmushi.

Da ƙarfi ta jijjiga shi,

“Adnan! Wallahi ba ka isa ka tafi ka barni ba, Walh baka isa ba! Me ka ce min jiya? Me ya sa? Me ya sa? Waye ya kashe ka Adnan?”

Ta fasa kuka, wanda yasa ɗakin aka sake gocewa da sabon kuka. Babansa kuka yake da iya ƙarfinsa. A lokacin Abbanta ya sa kansa cikin falon shima idanunsa hawaye ne kaca-kaca. Ji yake kamar shi aka yi wa mutuwar nan.

Suhaila tana ganin mahaifinta ta rungume shi tana cewa, “Abba shi ma ya mutu! Adnan ya mutu Abba!! Bani da rabo a duniya! Sun kashe min Adnan.”

Abba ya sake gocewa da sabon kuka. Ya kasa magana sai bubbuga bayanta yake yi alamun lallashi. Suhaila ta ƙwace kanta da ƙarfi ta nufi waje da gudu. Wani Yayan Adnan ya kamota, suka kama kokawa. Gabaɗaya ta haukace faɗi take,

“Ku barni zanje wurin Adnan ne, ba shi bane a kwance yana asibitinsa yana duba marasa lafiya.”

 A tsakiyar kunnenta ta ji wani yana cewa,

“Allah ya jiƙanka Adnan halinka na gari ya bika.”

 Suhailat ta sake gigicewa ta fasa ƙara, wanda ya tafi gaba ɗaya da numfashinta.

 Farfaɗowa ta yi tana jin hayaniyar jama’a. Ta kasa miƙewa. A lokacin kuma ta ji ana cewa,

“Allahu Akbar! Allah ya baka sa’ar tafiya.”

Wani ƙarfi ya zo mata, ta fizge daga jikin matar da ba za ta iya gane ko wacece ba. Gabaɗaya zuciyarta ta bushe. Tsam! Ta riƙe makaran tana zazzare idanu,

“Wallahi ba za ku tafin min da shi ba, sai dai ku haɗa har da ni.”

Ta fasa kuka tana jan Makaran. Da ƙyar wasu maza suka cire hannunta daga jikin Makaran, suka rirriƙeta, tana ji tana gani aka tafi da Adnan inda za a yi masa Sallah.

Ta durƙushe ƙasa ta fasa kuka. Bakinta kawai ke motsi, babu magana. Ta tabbata daga kan Adnan ta gama soyayya. Zuciyarta kawai gaya mata take yi, ta je ta faɗa titi itama ta mutu ko za ta huta da irin raɗaɗin da take ji.

A lokacin Hafsah da Inna suka shigo. Hafsa ta ruga da gudu ta rungume Suhaila tana cewa,

“Anti wai wai wai Yaya ya mutu.”

Yarinyar ta fasa kuka. Suhaila ta rungumeta tsam a ƙirjinta tana cewa,

“Eh Yaya ya tafi, ya barmu a duniyar. Shikenan babu wanda zai sake raɓarmu, shi kenan mun rasa babban wa namiji, mun rasa Adnan Hafsa ba mu san ya zamu yi ba.”

A hankali ta ji wani hannu ya dafa kafaɗarta. Ta ɗago jajayen idanunta, ta dube shi. Ta gane shi Yayan Adnan ne, wanda Adnan yake matuƙar so kamar ya kashe kansa. Kamanninsu ɗaya. Suhaila ta yi saurin janye idanunta da suka ƙankance saboda kuka,

“Ku daina kuka Suhaila. Har yanzu ba ku rasa ɗan uwanku ba, nima ku ɗaukeni a matsayin yayanku.”

Hajiyarsa ta rarrafa ta rungume Suhaila tana cewa,

“Kullum sai ya bar min wasiyya akan ki, ashe ba zai ga lokacin aurenku ba.”

Suhaila kawai ta koma tana ajiyar numfashi cikin sarƙewa ta kwantar da kanta a jikin Hajiyar tana ji dama ace mafarki take yi ba gaske ba.

Sai da aka yi bakwai, sannan Hajiyarsa ta yarda ta bar gidan.

 Abba ya zaunar da ita ya yi mata nasiha mai ratsa jiki, daga bisani ya ɗora da cewa,

“Bansan irin lalurar nan taki ba. Don Allah daga yau ki daina fita, bare ki haɗu da samarin. Har zuwa lokacin da zan sama maki magani.”

Inna ta ce,

“Ai dama ya zama dole ta daina fita kuwa.”

Haka Suhailat ta koma zaman gida. Karatun da Adnan ya ci burin ta ci-gaba da yi, ya sha ruwa. Ganin islamiyyarta za ta gurgunce ya sa, ya kira wani malami yana biyansa. A lokacin ne kuma Yayan Adnan ya bayyana a gidan a matsayin zai dinga kula da komai na Suhaila har ta sami mijin aure.

*****

Suhaila ta koma shiru-shiru bata um bare um-um. Abin da bata sani ba, tuni Suraj da malamin Islamiyyarta da yake zuwa koyar da ita sun kamu dumu-dumu da ƙaunarta.

Yau ya zo ƙara mata karatu ya dubeta yana murmushi,

“Suhaila na jima a cikin ƙaunarki wanda ya mamayeni. Don Allah ki bani dama aurenki zan yi.”

Ta dube shi kawai ta kasa magana, sai girgiza kanta da take yi. Bata iya bashi amsa ba sai kuka dole ya Sallami kansa yana mai jaddada mata gobe zai dawo.

A daren Suraj ya bayyana da tasa ƙoƙon baran, ya tabbatar masu baya son aja wasu kwanaki a sati guda yake son ayi komai. Duk irin bayanin da Abba ya yi masa yasa ƙafafu ya take.

Washegari tana kwance bata aikin komai sai kuka. Ta ji Muryar Inna tana Salati da ƙarfi. Hakan ya jawo hankalinta ta fito tana duban Inna.

“Suhaila ko dai Malam Umar ya ce yana sonki ne?”

Gabanta ya yi wani irin faɗuwa, ta gyaɗa kai cikin damuwa.

Inna ta sake doka Salati,

“Yanzu aka aiko min wai ya rasu.”

Suhaila ta zauna dirshan a ƙasa hawaye suna sake kwaranya daga idanunta. A lokacin ne kuma suka ji hayaniyar jama’a a ƙofar gidansu suna cewa sai sun kashe Suhaila mayya ce. Tana nan zaune ta yi tagumi, sai mutuwar Adnan ya dawo mata sabuwa.

“Allah na roƙeka ka sa nice gawa ta ƙarshe da zan biyo bayan waɗannan mutanen.”

Ta fashe da kuka. A lokacin Abba ya shigo a gigice goshinsa duk jini. Suhaila ta miƙe jikinta babu inda baya kyarma. Tana ganin jini ta sa hannu ta toshe bakinta ta fasa kuka.

Suna cikin wannan halin ne Suraj ya shigo. Shi ya samu ya kora jama’ar unguwar tare da yi masu barazanar kiran ‘yan sanda.

Da kansa ya taimakawa Abba har jinin ya tsaya, a lokacin kuma Abba ya goce da kuka mai ban tausayi. Suraj bai da yawan magana, matarsa ɗaya, da ‘ya’ya biyu. Ya dubi Abba sosai ya ce,

“Abba ka bani izini gobe a ɗaura min aure da Suhaila. Don Allah kada kayi musu, indai ka yarda da Allah shi ne mai kashewa mai kuma rayawa.”

Suhaila ta dinga girgiza kai, bata son a sake yin kuskuren da akayi akan Adnan. Tuni Suraj ya yi wa Abba zaƙin baki har ya amince. Yana komawa ya sanar da Hajiya, itama bata ja ba, ta yi fatan alkhairi.

Abba ya kira Yayansa daga Abuja wanda shi kaɗai ya rage masa ya ce,

“Yaya Sambo idan babu damuwa gobe da sassafe ka zo gidana.”

 Alhaji Sambo ya dage yana tambayarsa ko lafiya, Abba bai ce masa ga dalili ba ya dai sake jaddada masa.

 Da asubahin fari Alhaji Sambo ya kamo hanya, cikin ikon Allah sai ga shi a Maƙarfi. Abba ya jawo ɗan uwansa gefe ya zayyane masa komai, har lokacin mutuwar Mahmud wanda shi kaɗai ya sani, har zuwa kan Adnan da abin da Suraj ya ce. Alhaji Sambo ya damu soaai ya ce babu damuwa Allah ya shige masu gaba.

  Abin ya dami Alhaji Sambo matuƙa, yana mamakin yadda ɗan uwansa ya ɓoye masa bai gaya masa ba. Ya ji tausayin Suhaila sosai.

Bayan iyayen Suraj sun iso aka ɗaura auren Suhaila da Suraj.

Suhaila ta ci kuka sosai kamar ranta zai fita.

Alhaji Sambo ya ce yana buƙatar ya tsaya ya yi kwana biyu tukun domin jin yadda zamansu zai kaya.

Suraj ya ce baya buƙatar komai sai Suhaila, Alhaji Sambo ya ce a’a ai tana da gata, shi zai yi komai nan da sati guda. Kasancewar Mai kuɗi ne sosai, Abban ne ma ya ƙi yarda ya shige masa tun lokacin da matarsa Hauwa ta yi masa wulakanci ya riƙe talaucinsa.

Suhaila tana kuka aka wanketa bayan Sallar Isha’i Alhaji Sambo da kansa ya ɗauketa a mota da Driver ɗinsa motar Suraj tana gaba ya kaita ƙaton gidanta mai ban sha’awa.

 Alhaji Sambo ya ji daɗin ganin inda Suhaila za ta zauna har ma ya yi wa Ummi ‘yarsa fatan ganin ranar aurenta. ‘Yar nasiha ya yi masu sannan ya fice daga gidan ya bar Suhaila tana kuka. Ta so ace wannan ranar ta kasance ita da Adnan ne ba Yayansa ba.

 Ya dubeta kamar baya jin daɗi ya ce,

 “Ki tashi ki je ki yi alwala.”

Ta ware lulluɓinta ta dube shi sosai. Sai yau ta ƙare masa kallo. Shima ita ya kafe da idanu. Jikinta bai bata ba, don haka ta girgiza kai tana share hawaye,

“Ka zo mu je ka rakani ina jin tsoron inbarka kai kaɗai wani abu ya sameka.”

Ya yi murmushi ya miƙe yabi bayanta. Har ta shiga banɗakin ya ji wayarsa tana ƙara ya ce zai je ya ɗauki wayar. A lokacin ta yi alwala ta fito tana nemansa.

 A falo ta same shi kwance a doguwar kujera kamar mai barci. Gabanta ya faɗi da ƙarfi ta ƙaraso ta girgiza shi, sai kawai ya biyota ya zube ƙasa.

<< Kaddarata Ce 1Kaddarata Ce 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×