Skip to content
Part 3 of 10 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Suhaila ta fasa ƙaraaaa ta ƙwala masa kira,

“Surajjjjj!! Surajj!!”

 Ta gigice ta ruɗe ta ɗauki wayarsa hannunta yana kyarma ta danna lambar mahaifinta ta ce,

“Hello Abb… Abba.. Kamar Suraj ya mutu, Suraj shima ya mutu..”

 Ta datse wayar ta danna lambar Hajiyarsa,

 “Hajiya Ku zo ku ga Suraj! Na shiga uku na lalace..”

 Ta yi cilli da wayar a lokacin da ta ji alamun motsi a falon, ta sake ware manyan idanunta bata ga kowa ba, ta miƙe kawai kanta babu ɗankwali babu takalmi ta yi waje tana ihu. Mai gadi ya yi ƙoƙarin tsaidata amma ko kallonsa ba ta yi ba.. Tafiya kawai take a daren bata san inda ma take jefa ƙafafunta ba, saboda tsabar ruɗewa. Hannunta a tsakiyar kanta ta sake daddage ta fasa ihu mai ƙarfi, sai kuma ta yi shiru, sai yanzu hawaye suka dinga ɓulɓulowa kamar ruwa. Ta tashi zumbur! Ta ci gaba da tafiya babu ko waige.

Abba ya ja burkin motarsa da ƙarfi, bai tsaya kashe motar ba, ya biyo bayanta, a lokacin gudu kawai take yi da iya ƙarfinta, hakan yasa shima ya bita da gudun gaske, har Allah ya bashi ikon kamota. Gaba ɗaya ta zube a jikinsa a sume. Alhaji Sambo da tun fitar Abban daga mota, shima ya rufa masu baya, suka samu suka dawo da ita cikin mota, kai tsaye gidan suka nufa.

 A lokacin sun sha mamakin hatta Hajiyarsu tana gidan. Sumbatu kawai Hajiyar take yi tana faɗin sun kashe min ɗa.

A lokacin Alhaji Sambo ya samu ya watsawa Suhaila ruwa. Duk da ta farfaɗo ta kasa yin koda ƙwaƙƙwaran motsi. Tana jin irin mugayen kalaman da ke fita daga bakunan ‘yan uwan Suraj. Hawaye kawai ke bin gefen fuskarta.

“Ku zo ku bar magana gidan ɗan uwanmu. Matsiyata Mayu matsafa. Wallahi sai hukuma ta raba mu da ku.”

Wata ƙanwar Suraj Kenan take waɗannan kalaman cikin kuka. A lokaci guda ta yi kukan kura, ta cafki wuyar rigar Suhaila ta hau duka babu ji babu gani. Kafin wani lokaci Aljanunta sun bugeta, ta faɗi ƙasa tana numfarfashi.

Abba dai da Alhaji Sambo sun kasa ƙwaƙƙwaran motsi, sai idanu da suka zubawa Suraj da ke kwance kamar akira shi ya amsa. Suhaila ta fasa kuka, a lokaci guda ta faɗa jikinsa tana jijjigashi da iya ƙarfinta.

“Don Allah Suraj Ka tashi, don Allah ka taimakeni ka tashi, ka tashi ka ƙaryata su, ka gaya masu lafiyarka ƙalau.”

 Hajiya ta yi magana da kakkausar murya,

“Munafuka! Ki tashi ki bar gidan nan. Kin kashe min ‘ya’ya har biyu saboda baki da imani. Tsakanina da ke Allah ya isa!”

Sai a lokacin matar Suraj da ‘ya’yansa suka ƙaraso. Bata cewa Suhaila komai ba, sai dai itama ta durƙusa daidai fuskarsa.

“Abban Hanif.. Ka taimakeni ka tashi. Bani da kowa, ni marainiya ce, bansan kowa ba sai kai, ban buɗi idanuna da kowa ba. Kai kaɗai ka rage min a duniyata sai kuwa ‘ya’yanka. Don Allah ka tashi don Allah.”

Ta rushe da kuka, a lokacin ‘ya’yan suka matso kusa da mahaifinsu suna kuka suna roƙonsa ya tashi. Suhaila ta daina kukan, sai suya da zuciyarta ke yi. Tausayin matarsa da ‘ya’yansa suka taru suka gauraye ko ina na jikinta.

Wata da Aljanunta suka tashi shaƙe Abba suka yi da iya ƙarfinsu har ya fara ƙaƙari.

Suhaila ta miƙe ta fizgo yarinyar daga jikin Abban, ta wanka mata mari. Sannan ta watsar da ita ƙasa.

“Duk wulakancin da zaku yi, ku yi min ne a matsayina wacce ta aure shi, amma mahaifina bai yi maku komai ba.”

Wata ta amshe da cewa, “Kuma Wallahi sai kun bar gidan nan, ba ki isa ki zauna a gidan nan ba. Ganinki zai iya sawa in zama ajalinki.”

Suhaila ta yi magana cikin rawar murya,

“Abba, Daddy ku zo mu tafi.”

Ita ta fara yin gaba. Sai a lokacin maza suka sami isowa. Abba ya juya kawai yana jin saukan hawaye bisa kuncinsa.

 Har suka kama hanya babu wanda ya iya furta komai. Suna isowa gida suka sami Inna ta kare ƙofa tana harara,

“Dakata! Ina za ta shiga? Wai gidan nan? Wallahi ba zan zauna gida ɗaya da mayya ba.”

Abba ya dubeta cike da mamaki.

“Idan ba za ki zauna gida ɗaya da ita ba, sai ki tattara ki bar min gidana, zan iya zama wuri guda da ita.”

  Alhaji Sambo ya ɗaure fuska yana huci,

 “Matsa ki bamu wuri tun kafin ɓacin raina ya sauka akanki.”

Kasancewar Inna tana shakkarsa yasa ta matsa kawai suka shige.

“Sadiqu gobe Suhaila ta shirya kayanta za ta koma gidana da zama. Ka tattara har takardunta na sakandire zan sama mata jami’ar da Ummi za ta shiga sai su zana Jamb tare.”

Duk da Abba baya ƙaunar rabuwa da Suhaila ya zama dole ya amincewa batun Yayansa.

Washegari da Asuba Alhaji Sambo da Suhaila suka kama hanyar Abuja.

ABUJA

Babu yabo babu fallasa Hajiya Asiya ta karɓeta, ita kuwa Ummi ta haukace da murnan ta sami ‘yar uwa, tunda ƙannenta duk maza ne Faisal, da Fa’iz. Unguwa ce irin ta masu kuɗi, ya wadatu da tituna masu ban sha’awa.

 A ɗakin Ummi ta sauka, kai tsaye banɗaki ta shiga da ninyar watsa ruwa, sai dai ta kasa amfani da inda za ta iya samun ruwan zafi ko na sanyi, don haka ta kira Ummi, ta nuna mata. A natse ta faɗa banɗakin, ta ci karo da mayukan wanka kala-kala. TSaf ta  karanta kowanne sannan ta fara wanke jikinta, da take jin datti yana sauka kamar wacce bata taɓa wanka ba a duniya.

  Ita kanta ta ji daɗin jikinta, ta fito ta sami Ummi ta ajiye mata riga da zani na atamfa ga dukkan alamu kayanta ne. Bayan ta kimtsa ta sakko ƙasa, anan ta sami  Momi da yaran suna zaune kowa da abin da yake yi. A lokacin Abba ya fito sanye da jallabiya ya dubi Hajiya Asiya ya ce,

“Momin yara ga Suhaila ta dawo nan da zama gaba ɗaya, insha Allahu za su fara karatu tare da Ummi. Sai ki haɗa su dukka ki riƙe ‘ya’yanki ne. Faisal Fa’iz Ummi, ga ‘yar uwarku ta dawo cikinku.”

Momi ta ce,

“Allah ya bani ikon riƙe su.”

 A ranar duk wanda ya dubi Ummi sai ya san tana cikin farin ciki.

  Washegari misalin ƙarfe goma sha biyu na rana, Ummi ta shigo ta ce,

“Sis ta shi mu je Momi ta aikemu nan ne babu nisa sai mu ɗan taka a ƙasa dan ki ga gari.”

  Suhaila ita kanta za ta so hakan, duk da tunanin halin da dangin Suraj suke ciki ya hanata sukuni. Dukkansu sanye suke da Hijabai har ƙasa, ita kuma Suhaila ta sanya niƙabi ta yadda ba a iya ganin ko da ƙwayar idanunta, amma ita tana iya kallon kowa. Suna tafe Ummi tana yi mata bayani, har idanun Suhaila suka hasko wani gida, wanda kaf unguwar babu gida mai kyau da tsaruwarsa. Kalan ginin gidan ya tafi da hankalinta wanda ke ɗauke da lemon green, da kuma ratsin fari. Tun kafin ta kai ga tambaya Ummi ta fara magana,

  “Kin ga gidan nan ko? Yadda ya haɗu haka mamallakin gidanma ya haɗu. Yaron Yayan Momi ne, gidan iyayensa zamu je yanzu. Kinsan me sis? Allah ya jarabceni da sonsa kamar me. Kuma fa _Lecturer_ ne  a babban Makarantar nan ta NOUN. Ana ji da shi sosai, yanzu haka baya ƙasar.”

  Suhaila ta yi murmushi, surutun Ummi yana burgeta, babu ruwanta bata da ɓoye-ɓoye.

 “Ya akayi lakcara yake da irin wannan gida na ban mamaki? Kuma yasan kina sonsa? Kada ki jawowa kanki wulakanci.”

  Sai da Ummi ta yi dariya cikin fara’arta sannan ta ce,

“Babansa Yayan Momi mai kuɗine, yana ɗaya daga cikin masu kuɗin da ake ji da su a garin Abuja. Zamu je za ki ga Alhaji, yadda zai jawoki a jiki. Shi ba irin Momi bane yana da son jama’a. Amma Anti Laila ita ce masifar. Bata son wargi, da Momi kaɗai take shiri kaf danginsu. Ta tsani talaka. Shi kuma Yaya Faruq sai ya ɗauko halin Alhaji, wajen taimakon talakawa da rashin ɗaukar kansa shi wanine. Amma fa bai da kirki, baya dariya, ban taɓa ganinsa ko murmushi ya yi ba. Mutum kullum fuska a ɗaure kamar an aiko masa da saƙon mutuwa. Lokacin da ya karɓi aikin koyarwa Anti Laila kamar za ta yi hauka. Amma shi ko a jikinsa ya ce ya fi sabawa da koyarwa. Amma duk da haka yana business sosai, yanzu haka ma business ɗin ya fitar da shi ƙasar.”

 Suhaila ta yi murmushi ta ce,

 “Ummi abin da na tambayeki amsar da kike bani daban. Cewa na yi yasan kina sonsa?”

 Ta ɗaga kanta,

“Ya san ina sonsa kamar inmutu. Kuma da Daddy, suka zauna da Alhaji, aka ajiye shi a tsakiyar su Anti Laila aka ce masa za a haɗa mu aure, babu wata damuwa a fuskarsa ya ce ya amince. Yanzu insha Allahu ina da tabbacin ina fara karatuna za asa ranar biki. Amma fa baya kirana a waya, sai inkira shi sau dubu bai ɗauka ba sai ya gadama zai kirani ya ce Ummi ya kike? Shikenan sai ya ce zai kira, baya sake kirana.”

 Suhaila ta jinjina kai tana ganin ƙarfin halin Ummi.

“Ki dai bi a hankali. Wallahi ni labarinsa kawai da kika bani har kin sanya min mugun tsoronsa. Allah yasa kada ya hango wata. Kuma ki rage cusa kanki agunsa.”

 Ummi ta yi dariya ta ce,

“Kin kuwa ga haka Momi ta ce min. Ita kanta Anti Laila cewa ta yi inkula da darajata ta ɗiya mace kada ya rainani. Yauwa wannan gidan zamu shiga.”

 Suhaila ta ja da baya tana zare idanu. Tunda take bata taɓa ganin gida mai girman wannan gidan ba, bama wannan ne ya fi firgitata ba, a’a yadda wasu gardawa suke mazurai a gaban Gare ɗin gidan ya fi ɗaga mata hankali. Kafin ta dawo hayyacinta ta ji ƙarar mota daf da su, hakan yasa duk suka koma gefe. Wata rantsattsiyar mota ce ta sawo kai, hakan yasa Ummi faɗaɗa fara’arta ta jawo hannun Suhaila, kawai suka buɗe suka shiga. Ita dai Suhaila ta yi tsuru-tsuru, a lokacin da take hango ƙeyar yarinyar da take jan motar ba za ta wuce sa’arsu ba.

“Ummi kina da kan gado kuwa? Me zai kai ki fitowa a ƙasa tun daga gida har zuwa nan?”

Ummi ta zari Choculet ɗin da ta gani zube a gaban motar, ta miƙawa Suhaila ɗaya tana cewa,

“Ke ni na fi jin daɗin tafiyar ƙafar. Momi ce ta aikoni gurin Anti, kuma Suhaila da nake baki labarin yarinyar Baba Sadiqu ita ce ta dawo gidanmu da zama.”

  Bata ce komai ba, ta jinjina kai kawai. Nisan Gate ɗin kafin akai gidan ya sa ta sake cika da al’ajabi. Bayan sun fito ne Suhaila ta sami daman ƙarewa budurwar kallo. Duk iya kushe da hassadarka baka isa ka samo makusarta ba. Tsantsar bafullatana ce mai kama da larabawa. Ummi ta jawo hannunta a lokacin da take ƙoƙarin shiga ciki,

“Watarana ba kirki gareki ba. Sunanta Suhaila. Suhaila ga sisterna, kuma ƙanwar Yaya Faruq, sunanta Jawahir.”

 Jawahir ta ɗan yi murmushi ta miƙa mata hannu suka gaisa, sannan ta ce,

“‘Yar uwarmu Barka da zuwa. Sai dai irin wannan rufe fuskar? Anti ba za ta so ba, idan kika shigo mata a haka.”

 Suhaila ta yi murmushi ta cire niƙaf ɗin tana mai sake yi mata murmushi.

“Suhaila me ya sa kike rufe baiwar da Allah ya yi maki? Kina da kyau sosai, har kin zarta duk wata mace mai tunanin ita mai kyau ce.”

 Duk suka yi murmushi. Gaba ɗaya suka cusa kansu ciki.

 Gaba ɗaya sai Suhaila ta ruɗe ta gigice. Duk yadda za ta fasalta haɗuwar  gidan abin ya wuce tunaninta. A ƙasa ta duƙa ta gaida bafullatanan matar, mai cike da kwarjini. Ko alamar fara’a fuskarta babu ta amsa tana sake kallonta.

  “Ummi wannan ce Suhailar da Asiya ta ce ankawota?”

 Ummi ta amsa da “Eh Anti.”

Ta ɗan murmusa ta ce,

“Masha Allah. Kyakkyawa da ita.”

 Suhaila tana ta mamakin mutane irin su har hango kyan wata suke yi? Ummi ta jawo hannunta suka faɗa ɗakin Jawahir. Anan ma sai ta sake raina kanta. Jawahir ta firfito da kayayyakin da ta siyo ta ɗibarwa Ummi da Suhaila. Anan kuma sai hira ta ɓarke a tsakanin ‘yan uwan biyu.

“Don Allah kirawo Yaya nasan idan yaga kiranki ne zai ɗauka.”

Jawaheer ta jawo rantsattsiyar wayarta ta danna lambobi ta danna kira sai ga sunan BROMIE ya bayyana. Ta latsa Speaker.

“Assalamu alaikum.”

Jawahir ta ɗan kauda wayar, ta ce “Bari mu koma ustazai kafin yanzu injawowa kaina.”

“Wa alaikassalam. Babban Yaya Barka da warhaka.”

Qira’a ce kawai ke tashi a inda yake, hakan ya burge Suhaila har ta tsinci kanta da kwantar da kai jikin filo tana lumshe idanu,

“Barkanmu da juna. Ina Karatu yanzu zamu yi magana anjima.”

Kafin ta amsa ya katse wayar. Ummi ta fasa ƙara ta yi tsalle ta dira akan gadon, sannan suka kashe da Jawahir.

“Wayyo Jawahir ina son Ya Faruq kamar inmutu. Komai nasa dabanne. Shiyasa na koyi da dogayen hijabai domin mijin nawa ustaz ne.”

 Duk suka sake yin dariya.

 Suhaila ta sake jawo filo, tana jin mamallakin Muryar yana mata yawo akai. Idan har ‘yar uwarta ta aure shi, babu ko shakka za ta fi kowa farin ciki da hakan.

<< Kaddarata Ce 2Kaddarata Ce 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×