Skip to content
Part 7 of 10 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

“Farouk ne.”

 Ta juyo suka zubawa juna idanu.

“Share hawayenki ki gaya min abin da ya faru.”

Tana kuka tana gaya masa ta ɗora da cewa,

“Ka taimakeni kada a ɗaura aurena da Yaya Sadiq, zai mutu da gaske, idan ya mutu zan kashe kaina nima. Don Allah ka dakatar da auren nan, bana son wani ya ƙara mutuwa.”

Bai ce komai ba, ya kaita har gidan kawai ya juya. Gabaɗaya kansa ya ɗau zafi, ya rasa gane abin da ke masa daɗi. Dole ya ɗaga waya ya kira Daddy. Sun jima akan waya Daddy yana bashi labarin rayuwar Suhaila, jikinsa ya yi matuƙar sanyi, bai iya cewa komai ba ya sauke wayar.

Ya jima yana jin abubuwa kala-kala bai taɓa jin labarin da ya tsaya masa a rai kamar wannan labarin ba. Ya kasa barci, ya rasa abin da yake yi masa daɗi.

A ranar bai iya rintsawa ba, dole ya yi Alwala ya gana da Mahaliccinmu, akaron farko ya tsinci bakinsa da yi mata addu’ar samun mafita akan matsalarta.

Da safe idanu jazir ya fito cikin shirin ɗaurin aure, kamar kullum fuskarsa babu fara’a ya fi jin zafin abin da iyayensa suka yi wa Suhaila. Ya kira Jawahir ya yi ta mata faɗa,

“Ki bi rayuwa a hankali domin ba ki san ƙarshenki ba.”

 Sai da ya je gun Alhaji suka zauna a falonsa anan yake gaya masa matsalar SUHAILA. Alhaji ya yi murmushi ya ce,

“Ni ina tunanin matsalar jinnu ne, kuma da yadda aka tsorata akayi amanna da abubuwan shiyasa suke ta faruwa. Yana da kyau musulmi idan abu ya same shi ya amincewa zuciyarsa daga Allah ne. Mutuwa kuma tana kan kowa, babu wanda ya isa ya gota ranar da Allah ya rubuto masa.”

Farouk irin zuciyarsa ɗaya da mahaifinsa, shiyasa tunaninsu ya zama iri ɗaya.

 Ƙarfe goma duk suka fito cikin shiri, suka isa babban Masallacin juma’ar wanda anan ne za a ɗaura aure. Suna isowa Farouk ya kira Sadiq ya tabbatar masa yana tafe.

Ƙarfe goma da rabi ya iso, kai tsaye ya jawo Farouk gefe idanunsa jazir,

“Farouk na fasa auren Suhaila. Wallahi ba zan aureta ba.”

Farouk ya zaro idanu cikin fargaba,

“Me ya sa haka Sadiq?”

Sadiq ya girgiza kai,

“Na yi mafarkin ana ta bina za a kasheni da wuƙa. Wallahi ina tashi naga wani gajeren mutum.  Ya yi min rantsuwa zai kasheni idan aka ɗaura min aure da Suhaila. Da safen nan kuma sai ga wayar Momi tana bani labarin komai akan rayuwar Suhaila. Anti ma ta kirani, ta tabbatar min duk yadda zan yi infasa aurenta. Wallahi ba zan aureta ba, agaban kowa zan faɗa.”

Farouk ya girgiza kai,

“Idan da gaske ne me ya sa bokan da ya ce ka aureta bai gaya maka rayuwarta ɗin ba? Ka yarda babu bokan da ya isa yasan me zai faru yanzu ko anjima? Don Allah kada ka fasa auren nan babu abin da zai…”

Ya kasa ƙarasawa ne, a lokacin da ya ga Sadiq ya yi gaba cikin Masallacin. Cikin gaggawa aka zo aka jawo hannun Farouk ana gaya masa yanzu za a ɗaura aure, kuma na Sadiq za a fara ɗaurawa. Ya yi mamakin ta yadda Sadiq ya kurkuɗa har ya shige gaban iyayensa, ya amshi abin magana ya ce,

“Iyayena ‘yan uwana abokaina ku gafarceni na fasa auren Suhaila. Da abani Suhaila gara anhaɗani da ko wacece a take anan zan karɓa ko da kuwa tana da muni. Saboda ita wannan amarya mutane tara suka zo neman aurenta suka mutu, ni ne na goman.”

  Daddy ya fusata da irin wannan cin mutunci. Abba kuwa kuka yasa wiwi kaman ƙaramin yaro. Wuri ya hargitse da surutai, da ƙyar aka samu wurin ya rage hargowa. Farouk ya ƙaraso gaban Sadiq idanunsa sun kaɗa sun yi jazir! Har gara ya kira iyayen gefe ya gaya masu, fiye da irin wannan cin mutuncin.

  Farouk ya rintse idanu yana tausayin Suhaila, ya tabbata za ta iya kashe kanta muddin ta ji wannan mummunan labarin.

Alhajin Farouk ya dinga girgiza kai yana jin ɓacin ran abin da Sadiq ya aikata masu. Ayayin da mahaifin Sadiq yake jin lallai yana bayan ɗansa.

Farouk ya ƙaraso ya durƙusa a gaban mahaifinsa, wanda shi yake faman ba Abba baki akan ya yi haƙuri. Ya sunkuyar da kansa ya ce,

“Alhaji ka amince min zan auri Suhaila, amaimakon Ummi. Idan aka ɗaura auren na mutu, kayi min addu’a ka sa min albarka, ka kuma amince Allah ne ya kawo lokacin mutuwana.”

Sai wuri ya yi tsit. Daddy da Abba suka yi ta kallon Farouk cike da mamaki da tsoro.

Alhaji ya dubi Sadiq ya ce,

“Kana son Ummi a matsayin matar aure?”

Da sauri ya gyaɗa kai,

“Wallahi ina sonta, zan riƙeta tsakani da Allah.”

Ya dawo da dubansa ga Liman,

“Ɗaurin aure ya sauya. Farouk ɗana, zai auri Suhaila, Sadiq zai auri Ummi. Ni zan bayar da sadakin auren Suhaila. Idan Farouk ya rasu gobe mu yi masa addu’ar dacewa da rabo mai girma.”

Mutane da yawa suka ce

“Allahu Akbar!”

Abba ya yi ta kallon mutanen ya rasa me zai ce. Haka Daddy. A take aka sauya ɗaurin auren mai dumbin tarihi, ɗaurin aure mai abin mamaki.

 Wani ƙanin Anti Laila ya zagaya ya kirata ya gaya mata komai.

Anti Laila ta fasa ihu, wanda ya jawo hankulan jama’a da dama. Kafin wani lokaci jininta ya yi mugun hawa, tuni ta zube a sume.

*****

Daga Masallacin kowa ya dinga yi wa Farouk kallon mamaki, ayayin da mutane da yawa daga cikin ‘yan uwansa, suke yi masa kukan gawa. Alhajin Farouk yana riƙe da hannun ɗansa, yana jin tamkar yaron ya yi wata shahada ce, da zai fi kowa alfahari da hakan. Daddy kuwa, ko ajikinsa da wannan sauyi, sai ma farin ciki da yake ji, ba a kunyata ƙaninsa ba. Shi kansa Sadiq sai ajiyar zuciya yake saukewa babu ƙaƙƙautawa.

A lokaci guda suka dugunzuma zuwa gida.

  Hajiya Asiya tana cikin taron jama’a, bata san wainar da ake toyawa ba. Kamar a tsakiyar kunnuwansu suke jin maroƙi yana cewa,

“Anɗaura auren Alhaji Farouk da Suhaila. An ɗaura auren Alhaji Sadiq da Maimuna (Ummie)

 Hajiya Asiya ta ɗago a firgice ta dubi ‘yan uwanta. Inna ta zaro idanu ta dafe ƙirji. A lokaci guda duk suka shashantar a ganinsu ya yi kuskure ne. Wata ta ɗaga murya ta ce

“Ku koma ku gayawa mai kirarin nan, ya gyara batunsa.”

 A lokacin Daddy ya ratso tsakiyan jama’a ya dubi Hajiya Asiya ya ce,

“Ki zo falo ina son magana da ke.”

  A lokacin Ummi ta ratso da gudun gaske, kanta babu ɗankwali, ƙafafunta babu takalmi, da gani tun daga gidan da suke zaune, har izuwa gidan iyayenta a ƙafa ta ƙaraso kuma da gudu.

Tana zuwa gaban Hajiya Asiya ta fasa ihu. Sai a lokacin Suhaila ta ja tunga daga irin gudun da itama take yi tana binta, tana tambayarta lafiya? Me ya faru? Tunda suna shiryawa ne aka kira Ummin a waya aka gaya mata maganar da batasan ko mecece ba. Suna shigowa Ummi ta sake tabbatar da maganar ta hanyar kirarin da maroƙin yake yi, wanda kwata-kwata Suhaila ba ta ji ba.

Hajiya Asiya ta riƙe ƙafaɗunta gabanta yana tsananta bugawa,

“Ke! Lafiyarki ƙalau kuwa?”

Ta girgiza kai cikin matsananciyar kuka,

“Momi ki taimakeni ki ƙaryata abin da nake ji. Wai Yaya Farouk Suhaila ya aura ba ni Maimunatu ba.”

Momi ta zare idanunta, a lokaci guda ta mayar da kallonta ga Daddy da ke tsaye yana kallonsu jikinsa a sanyaye.

“Ka ji wani zance. Ka ƙaryata abin da Ummi take faɗa kada ‘yata ta sami matsala a ƙwaƙwalwarta.”

Daddy ya girgiza kai, a lokacin da ita kanta Suhaila ta mayar da kallonta kan Daddy tana fatan aƙaryata zancen nan. Ganin Daddy ya yi shiru ya sa Suhaila gigicewa. Da ta auri Farouk gara ta mutu babu aure, domin ta sani sarai, Anti Laila za ta iya kasheta, muddin ɗanta da ta fi so fiye da kowa ya halaka. Ba ma wannan ba, ta fi kowa sanin Anti Laila bata ƙaunarta. Daddy ya share guminsa ya ce,

“Mu ɗauki hakan a matsayin ƙaddara. Sadiq Shi ya zama angon Ummi, Suhaila kuma Allah ya rubuta Farouk ne angonta. Kada ku ga laifin kowa, zan yi maku baya…”

Bai kai ga ƙarasawa ba Ummi ta zube a sume. Suhaila kuma ta fasa ƙara ta yi hanyar waje da gudun gaske. Gaba ɗaya ta zama mahaukaciya. Kafin ta kai ga fita gate ɗin, Anti Laila da farfaɗowanta kenan, ta fizgi mota ita da Jawaheer suka zo gidan, a bakin Gate ta fice daga motar ko kasheta bata yi ba. Kawai Suhaila ta ji anfizgota, anhaɗa kanta da bango. Ta saki rikitacciyar ƙara, ta dafe wurin. Jawaheer ta fizgota jikinta yana kyarma,

“Mayya! Idan ba ki saki kurwar Yayana ba, sai na hallakaki. Ki sake shi nace maki! WALLAHI muddin ina numfashi ke baki isa ki shigo gidanmu da sunan aure ba, haka muddin wani abu ya sami Yayana ko ciwon kai ne, sai nasa hukuma sun sabauta maki kamanni.”

 Dukanta kawai suke yi ko ta ko ina. Anti Laila ji take yi sai ta kashe Suhaila tun kafin ta kashe mata ɗa. Jawaheer ta ji anfizgota, ko kafin ta san waye ya ɗauketa da mahaukacin mari. Ya finciketa daga jikin Suhaila da kanta ke fidda jini. Ya sake raba Anti Laila da jikinta, a lokacin itama Anti Lailan ta ji anriƙeta, tana ta hauka, hakan yasa wanda ya riƙe ta ya ɗauketa da mari. Sai a lokacin hankali ya shigeta. Farouk ne yake huci riƙe da Suhaila. Da sauri Anti Laila ta waiwayo taga waye yayi mata wannan aikin? Idanunta fes akan mijinta, shima fuskarsa kamar bai taɓa Dariya ba. Suhaila ta nuna Farouk da hannu tana son ta yi magana, amma ta kasa, sai ajiyar numfashi kawai take yi.

 Abba da idanunsa suka kaɗa saboda azaban ɓacin rai, ya ƙaraso har gaban Anti Laila Yana jin kamar ya mutu.

 “Muddin wani abu ya sami ‘yata sai na yi Shari’a da ke, ki bar ganina a matsayin talaka, Allah yana tare da irinmu masu tawakkali da irin matsayin da muka tsinci kanmu. Kuma ina tabbatar maki sai kinyi danasanin wannan abun da kika aikatawa Suhaila.”

 Anti Laila ta yi kururuwa ta ce,

“Ubanka ya ci ubansa! Shege maye! Talakan banza! Kai baka isa ka bani tsoro da kalamanka ba! Ni zan ɗaureka dan ubanka idan baka sa anraba auren nan ba. Allah ya tsinewa maitan da ya fasa zuwa yau ya kasheni.”

 Abban Farouk yasa hannunsa ya ɗauketa da mari a baki, tuni bakin ya fashe. Suhaila ta fasa kuka mai tsananin ƙara. Ta fizge kanta daga jikin Farouk da hatta maƙogoronsa a bushe yake. Tunda yake bai taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba. Ga mutane sun taru sun cika wurin. Suhaila ta dubi Farouk a ƙoƙarinta na nemo dauriya ta ce,

“Idan kai ne autan maza a duniya wallahi ba zan zauna da kai zaman aure ba. Da ka zama mijina gara in zama mazinaciya, ‘yar iska! Karuwa. Daga ƙarshe in kafa siyar da goro da sigari. Idan ni ‘yar halas ce kuma Saddiqu shi ne mahaifina, ba za ka taɓa zama mijin mareniya ba. Ba ka isa ba! Uban waye ya baka shawara ka aure ni? Bacin kun kasance daga ƙasƙantattun bayi, mutanan da suke fariya da dukiyar da za ku bari a duniya.”

 Ta taka ta ƙaraso gaban Anti Laila tana dubanta ido cikin ido,

“Ubana ya fi ki daraja! Ya fi ƙarfin ki zauna kina yi masa zagin maguzawa. Na rantse da Allah, wannan shi ne karo na ƙarshe da bakinki zai sake antayowa mahaifina irin wannan zagi masu tsananin ɗaci. Idan ɗanki shi ne autan maza, idan kun kasance daga tsatson fir’auna a dukiya da rashin sanin Allah, sai ɗanki ya sakeni. Ko bai sake ni ba, zanje infaɗa rayuwar karuwanci, da dai inzauna kusa da matar da ta dubi mahaifina a gabana ta yi masa irin wannan mummunan zagin. Ko Yayansa, bai isa ya zagi mahaifina haka inzuba masa idanu ba, bare ke haɗuwar bariki.”

 Abba ya sharara mata mari, wanda yasa ta riƙe kuncinta. Tana hawaye ta riƙe fuskarta tana magana cikin kuka,

“Abba ka gafarceni, da in zauna da Farouk a matsayin miji, gara ka nema min jaki, na zauna da shi, ko banza nasan shi dabba ne bai da idanun da zai iya yi maka kallon banza, bare kuma har ya buɗa baki ya zagi halittar da na fi so fiye da kowa.”

 A hankali ta juya tana tafiya jiri na ɗibarta, don haka tafiyar ta kasance a hankali take yinta. Gaba ɗaya Suhaila ta juye masu tamkar wacce basu taɓa sani ba a duniya. Babu wanda ya iya dakatar da ita. A lokacin Ummi ta farfaɗo ta fito zuwa gaban Farouk tana matsananciyar kuka, wanda muryarta ta daki Suhaila hakan yasa ta ɗan dakata da tafiyar ba tare da ta juyo ba, tana jin tsantsar tausayin Ummi a zuciyarta.

“Don Allah ka taimakeni kada ka rabani da kanka, kai kaɗai ne rayuwata, zan iya mutuwa muddin na rasaka. Ban san so ba sai akanka, kada kayi min haka. Idan laifi na yi maka ka gaya min ingyara kuskurena.”

Ta sake rushewa da kuka. Farouk ya zura mata idanu yana jin tausayinta yana ratsa shi. Jawaheer kuwa tana nan kwance a gefe kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa. Tunda take ba a taɓa marinta ba, sai yau, yau ɗin ma Yayanta da ke bala’in ji da ita. Amma ta fi jin zafin auren fiye da zafin marin.  Anti Laila ta ƙaraso ta ɗagota tana goge mata hawaye,

“Ki kwantar da hankalinki, aurenki da Farouk babu fashi muddin  ina numfashi a duniya.

  Abban Farouk ya dubeta sosai,

“Auren Farouk da Suhaila babu fashi ya ɗauru, muddin Farouk ke da ikon sakinta. Ki bi a hankali Laila kin kai ni ƙarshe igiyoyinki suna lilo a hannuna.”

 Ta zabura tana dubansa,

“Dama a tunaninka ina tsoron rabuwarmu ne? Akan wannan auren, ina tabbatar maka komai na shiryawa faruwarsa.”

Hajiya Asiya ta ƙaraso gaban Abba tana shirin marinsa, kamar anjuyo da Suhaila da ke shirin fita gate ɗin, sai dai kafin ta ƙaraso Daddy ya riƙe hannunta yana huci.

Hajiya Asiya ta dubi Suhaila da itama hucin take yi, ta ce

“Da me za ki yi?”

Suhaila ta yi murmushi,

“Wannan ne kuskure na ƙarshe da za ki aikata har ki mutu kina da na sanin aikata shi. Ta dawo ta kamo hannun Abba suka fice daga gidan. Inna da Hafsat suka bi bayansu. Duk yadda Daddy ya so ya dakatar da su babu wanda ya dube shi, saboda kowa ya hassala.

<< Kaddarata Ce 6Kaddarata Ce 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×