Skip to content
Part 8 of 10 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Tuƙi kawai Abba yake yi, babu wanda ke cewa kowa uffan. Zuciyar Abba kawai azalzalarsa take yi. Suhaila kuwa kuka take yi babu ƙaƙƙautawa. Tana jin tabbas da ta kasance mayya kamar yadda ake faɗa da babu ko shakka Anti Laila da Momi za ta fara cinyewa. Kwantar da kanta kawai ta yi, tana jin tarin damuwa.

A can cikin gidan kuwa, Farouk ya lallaɓa ya kama hanya zai fice daga gidan, ya ji ansake riƙo ƙafafunsa ya waiwayo yana dubanta,

“Don Allah Yaya ka taimakeni ka aureni, kai kaɗai nake so, kai ne burina.”

 Farouk ya kasa furta komai sai dubanta yake yi. A hankali ya zare ƙafarsa ya ci-gaba da tafiya. Anti Laila ta zabura tasha gabansa tana jifansa da wani irin kallo,

“Za ka saketa ko sai na tsine maka nono na da ka sha?”

Ya ɗan dubeta, a karo na farko da fargaba mai Karfi ta shige shi, saboda bai taɓa jin baya shakkar mahaifiyarsa ba, sai yau. Bai san lokacin da ya yi magana ba,

“Anti wani irin saki kuma bayan yarinyar ma ta gudu? A gabanki ta ce da ta zauna da ni gara ta zauna da jaki. Ai aure tuni kun gama raba shi.”

 A lokacin Sadiq ya shigo kai tsaye gurin Ummi ya nufa ya ɗagota ya ce,

“Ummi kiyi haƙuri da irin wannan sauyin. Insha Allah zan riƙeki fiye da yadda Farouk zai iya riƙeki.”

 Ummi ta yi shiru tana jin baƙin ciki gami da tsanar Suhaila suna yawo a zuciyarta. Tana jin zata iya yin komai domin ganin Farouk ya dawo gareta.

  Farouk ya juya da sauri ya fice. A karo na farko ya buɗe sabon gidansa, ɓangaren da bai taɓa shiga ba ya shige ya rufe kansa.

 Alhajin Farouk da Daddy duk suka fice kawai daga gidan rai a ɓace. Jawaheer da Ummi suka shiga ɗakinsu kuka kawai suke yi.

Momi ta ce kowa ya bar mata gida antashi bikin. Kafin me? Duk anwatse. Momi da Anti Laila suka shiga ɗaki suka kulle kansu, su kaɗai suka san abubuwan da suke tattaunawa.

  A gajiye suka iso Maƙarfi, Salloli kawai suka yi kowa ya koma ya zauna jigum-jigum. Abba da tuni zazzaɓi ya rufe shi,duk suka taru akansa suna kuka.

 Haka suka kwana cikin tashin hankali. Ko karyawa sun kasa yi.

  Suhaila tana zaune da dogon hijabi suka ji tsayuwar mota. Tana gefen Abbanta, ta ji Sallamar Daddy. Kanta a sunkuye, sai da ta ji muryar Alhaji Marwan sannan ta ɗago tana dubansa, a lokaci guda ta durƙushe tana gaida su. Babu wanda ya amsa mata sai duban Abba da suke yi ya tashi zaune yana miƙa masu hannu. Suhaila za ta miƙe suka ce ta koma ta zauna. Sama-sama suka gaisa Daddy ya dubi Abba duba na tsanake ya ce,

“Sadiqu ka yarda da ƙaddara? Ka yarda kai Musulmi ne?”

 Bai iya magana ba, hawaye kawai yake zubarwa, ya ɗaga kansa kawai. Daddy ya ci-gaba da cewa,

“Idan magana kake akan ƙaddarar Suhaila, ba kai ya kamata kayi kuka da kanka ba, ni ya kamata inyi kuka, saboda gaba ɗaya nine silar faruwar komai. Duk abin da kayi kayi shi ne saboda ni. Kai kaɗai ka rage mini a duniyata, ba zan mance amanar da mahaifiyata ta bani akanka ba. Gani na zo tare da mahaifin Farouk ya ce yana neman taimako ka bashi Suhaila ta tare a ɗakin mijinta. Ni kuma a matsayina na uban Suhaila na yi mata izini ta tashi ta biyo ni, indai na isa da ita.”

  Suhaila ta fasa kuka. Abba ya dubi yayansa da yake so fiye da kowa ya ce,

“Yaya ka wuce komai aguna. Suhaila kuma ba ‘yata ba ce, ‘yarka ce ta halak! Duk yadda kayi da ita daidai ne. Suhaila ko bayan babu raina, idan kika yi wa Yayana musu Allah ya isa ban yafe maki ba. Ki bishi fiye da yadda zaki bini. Alhaji ga matar ɗanka ku tafi da ita.”

 Inna da take laɓe ta faɗo ɗakin tana kumfar baki,

“Gaskiya wannan zalunci ne, kunsan yarinyar nan tana da matsalar maita, me zai sa ku ɗauketa ku kaiwa gidan mutunci irin gidan nan? Mazaje tara ta kashe a duniya, Farouk shi ne na goma. Kuyi wa kanku faɗa ku daina son zuciya.”

Daddy ya dubeta ya girgiza kai,

“Har abada mata sunanku ɗaya! Na tabbata da ɗiyarki ce ba zaki taɓa jifanta da kalaman nan ba. Idan mun tafi da ita sai ki zo ki ɗaukota.”  Inna ta fice fuuu tana faman kumfar baki.

 Suhaila tana kuka kamar ranta zai fita, a ganinta Inna ta faɗi gaskiya ne.

A gaba ta zauna ta ƙudundune kanta, Daddy da Alhaji suna baya. Abba ya ƙara so har gaban motar ya ce,

“Ban yarda musu ya haɗa ki da mijinki ba, ki yi wa uwar mijinki biyayya kamar yadda zaki yi min. Ki riƙe addu’o’i. Allah ya yi maki albarka, na yafe maki Suhaila.”

Hafsat tana kuka Suhaila tana kuka Driver ya ja motar. Inna kuwa ko leƙau bata yi ba, hakan bai yi wa Suhaila daɗi ba, ta so ta yi Sallama da ita, duk da dai tana da tabbacin gobe za ta dawo bayan Farouk ya rasu. Ta sake rushewa da kuka. Babu wanda ya ce mata uffan, sai ma suka ci gaba da tattaunawa akan yadda za su biyowa matansu dan gudun fitina.

  Gudu Driver ɗin yake yi kamar zai tashi sama, hakan yasa suka iso cikin Abuja da wuri. Kai tsaye sabon gidan Farouk suka shiga.

  Yana zaune a falonsa yana sanye da doguwar jallabiya fara sol! Yana riƙe da Alqur’aninsa ga dukkan alamu karatu yake yi. Ƙofar a buɗe take kasancewar bai jima  da fitowa farfajiyar gidan ba.

  Bai ɗago kansa ba, har su Abba suka nemi wuri suka zauna Suhaila kuwa a can wani ƙusurwa ta zauna ta maƙale jikinta.

  Sai da ya kai ƙarshe cikin Qira’arsa mai daɗin saurare, a cikin Suratul Rahman. Ya rufe Qur’anin. Cike da mamakin wanda ya gayawa mahaifinsa inda yake ya dube su, a lokaci guda ya ƙasƙantar da kansa ya gaishe su. Kwata-kwata bai kula da Suhaila a ɗakin ba.

  Alhaji ya musƙuta ya fara doguwar nasiha, shi dai yana mamakin dalilin da zai sa shi yi masa nasihar aure, kuma yana haɗa wa su biyu. Daga ƙarshe ya ji Alhaji ya ce,

 “Farouk ga matarka Suhaila. Ka riƙeta amana, amanata ce ni naje har gidansu na roƙi mahaifinta kuma ya bani. Ga ubanta agabanka bani da haufi akanka, na tabbata ba zaka taɓa cutar da Suhaila ba. Allah ya yi maka albarka. Suhaila mu zamu tafi, daga baya za a kawo maki akwatinan da Sadiq ya yi maki, ita kuma Ummi za akai mata wanda Farouk ya yi mata, tunda duk da sunanku akayi.”

 Suhaila da sanyin AC ɗin ɗakin ya sake rikita mata jiki, ta sake maƙale kanta tana tuna kalaman mahaifinta. Ko kaɗan bata ƙaunar zamanta inuwa guda da Farouk ta tsane shi a tun lokacin da ya amince aka ɗaura masu aure, ta tsane shi tun lokacin da mahaifiyarsa take aunowa mahaifinta munanan kalaman, da har ta mutu ba zata mance su ba.

 Farouk ya ɗan dubi saitin da take, ya kauda kansa. Ya sake ƙasƙantar da kansu kamar zai kwanta masu,

“Insha Allahu zaka sameni mai biyayya ga umarninka.”

 Suka sa masa albarka Duk suka miƙe. Alhaji ya ƙaraso kusa da ita ya kama hannunta ta tashi ya maidota bisa kujera,

“Ki daina baƙunta gidanki ne. Anan gaba insha Allahu zaki yi rayuwarki da ‘ya’yanki a cikin gidan nan. Ki ɗaukeni tamƙar mahaifinki, duk abin da kike buƙata zan aiko maki da waya ki gaya min ko menene. Zaki yi alfahari da auren Farouk anan gaba kaɗan.”

 Duk suka yi murmushi Farouk ya rakasu har gurin motarsu suka yi Sallama. Ya dawo ko dubanta bai yi ba ya ce,

“Mu je ki ga ɗakinki.”

  Sai da ta ɗan yi shiru, daga bisani ta miƙe ta bi bayansa. Ɗakinta yana kusa da nasa ne, anan ya buɗe mata ta shiga kawai ya sa kai ya fice. Suhaila ta sake rushewa da sabon kuka, tana da tabbacin yau ɗinnan Farouk zai bar gidan duniya.

 A daddafe ta shiga banɗakin ta yi wanka tare da alwala ta fito. Bayan idar da Sallah ta ƙarewa ɗakin kallo tana mamakin irin kuɗin da aka kashe a ɗakin. Tunawa ta yi da Ummi ta ji wani sabon hawaye, ta gama cin burin shiga gidan nan ashe ba ita ce za ta fara shiga ba.

  Shi ya samo mata abinci ya ƙwanƙwasa, tana buɗewa taga abinci anjere mata kuma bata ga wanda ya kawo abincin ba. Ta ɗauka ta ci kaɗan, tasha ruwa, kawai ta mayar da kanta tana tsiyayar hawaye.

  Washegari da asubahi, Alhaji Marwan ya haɗa Anti Laila da Jawaheer ya zaunar da su ya yi masu nasiha, daga bisani ya gaya masu lallai Suhaila ta tare a ɗakinta. Anti Laila ta ji kamar zata mutu, don haka Alhaji yana shigewa ɗakinsa jikinsu yana kyarma suka ɗauki mota sai gidan Farouk.

 Da yake itama Ummi ankaita ɗakinta, don haka daddy ya yi wa Momi nasiha shima, ya kuma tabbatar mata Suhaila a ɗakinta ta kwana. Don haka tana tashi ta kira Anti, suka ce su haɗu a gidan.

 Momi ta riga su ƙarasowa ta tsaya jiransu, gaba ɗaya suka shiga gidan. A babban falon Farouk ne kwance kamar mai barci, a lokacin ita kuma SUHAILA tana ɗakinta tana jan carbi idanun nan sun kumbura sun yi suntum.

 Anti Laila ta bubbuge shi, amma shiru. Jawaheer ta taɓa shi a tsorace nan ma shiru. Gaba ɗaya suka zaro idanu. Anti Laila ta jijjiga shi, shiru. Ta fasa ihu tana ƙwala masa kira. Jikinta yana rawa ta kira Sadiq, cikin mintuna ƙalilan ya bayyana tare da Ummi kasancewar tana ta yi masa kuka. Yana zuwa ya tattaɓa shi ya zube ƙasa ya sa hannu akai hawaye kawai ke zuba daga idanunsa,

“Shikenan mun rasa Farouk. Sun kashe shi.”

 Wata ƙara da Jawaheer tasa shi ya ci nasarar isowa tsakiyar kunnuwan Suhaila, ta fito a gujen gaske. Tuni Jawaheer ta sume. Anti kuwa gaba ɗaya ta zama mahaukaciya cewa take yi,

“Sadiq kirawo min ‘yan sanda tun kafin inkashe yarinyar nan.”

 Momi da Ummi da Anti suka fizgo Suhaila. Irin dukan da suke yi mata abin ba acewa komai. Ganin za a sami ƙarin gawa yasa Sadiq kiran ‘yan sanda. Ko kafin su iso sun yi wa Suhaila dukan fitar rai. Sun farfasa mata kai, hatta jikinta fitar da jini yake yi.

  ‘Yan sandan suna isowa, da ƙyar suka ƙwaceta suka fita da ita, a lokacin kuma Sadiq ya sake kiran Alhaji yana kuka yana faɗa masa Farouk ya rasu. Duk dauriya irin ta Alhaji sai da gabansa ya yi mugun faɗiwa, agigice ya ƙara so gidan. A lokacin shima Daddy ya sami kiran waya ya ƙara so jikinsa yana kyarma.

 Ga dai Farouk a kwance kamar zai yi magana. Gaba ɗaya suka sa shi a gaba ba tare da sun san abin yi ba. Anti ta sa hannu akai ta sake fasa ihu tana cewa,

“Walh sai nayi ƙararku, ku kuka je har gida kuka kawo min mayya cikin gidan ɗana, bayan kuna sane.”

Gidan fa ya rikice koke-koke kawai akeyi. Alhaji da abin ya cake Shi kasa ƙwaƙƙwarar motsi ya yi. Da ƙyar ya iya buɗe baki ya ce,

“Ina Suhaila?”

 Sadiq ya ce,

“Sun farfasa mata jiki,yanzu haka tana wurin ‘yan sanda.”

 Alhaji ya zabura yana dubansu,

“Me ya sa zaku yi haka? Ku barta ta ji da mutuwar mijinta mana.”

Anti ta sake haukacewa, kawai ta ci kwalar rigar Alhaji tana sumbatu, tana faɗin sai ya biya mata ɗanta.

<< Kaddarata Ce 7Kaddarata Ce 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×