Skip to content
Part 9 of 18 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

*****

Jawaheer tana nan kwance a sume, tuni numfashin Ummi ya ɗauke itama ta zube anan. Hakan yasa wurin ya sake rikicewa da koke-koke. Alhaji ya ƙara so gaban Farouk ya taɓa shi, ya sake ja da baya yana jin gabansa yana tsananta faɗiwa. Shi kansa yasan idan babu Farouk rayuwarsa za ta ci gaba da yi masa barazana ne, har shi ma ya amsa kiran Mahalicci. A hankali ya zaro wayarsa ya danna lambar Likitansu ya sanar da shi komai. Cikin gaggawa likitan ya iso, cike da saƙe-saƙe.

Anti Laila har muryarta ta dashe tun bayan da Alhaji ya fizge kansa daga irin riƙon da ta yi masa, ya nunata da yatsa,

“Baki da iko da Farouk nike da iko da shi. Baki isa ki gaya min kinfi ni damuwa da rashin ɗa mafi soyuwa kamar Farouk ba.”

Shi kuwa Daddy sunkuyar da kansa ya yi, yana jin tabbas ya biyewa zuciyarsa wajen aikata kuskure da gangar.

Likitan yana shigowa, ya ƙarasa kusa da Farouk ya fara gwaje-gwajensa. A lokaci guda ya dawo da kallonsa bisa table ɗin falon, yasa hannu ya kwashi magungunan, yana dubawa.

“Alhaji wannan magungunan da kake gani, magungunan barci ne, suna da ƙarfi sosai. Farouk ya kirani ya tambayeni magungunan barcin da ya kamata ya yi amfani da su, kasancewar barci ya ƙaurace masa, ya ce min idanunsa zafi suke yi yana jin ɓacin rai a zuciyarsa yana buƙatar samun hutun azaban da yake sha. Na bashi shawarar kada yasha magani, ya zo mu fara duba shi. Shiru-shiru bai zo ba. Ashe ya siyo waɗannan ne, amma tabbas Farouk yana raye bai mutu ba, maganin barci yasha wanda yafi ƙarfin ƙwaƙwalwarsa. Amma yanzu a kawo min ruwa don Allah, akwai dabarar da zan yi insha Allahu yanzu zai farka.”

Anti Laila da Momi, harma da Abba duk suka ƙaraso gabansa jikinsu yana rawa. Anti Laila ta durƙushe agaban likitan ta rushe da kuka tana cewa,

“Don Allah ka dawo min da rayuwar ɗana, ko nawa ne zan baka. Na yarda in zama talaka in baka dukka dukiyata, muddin rayuwar ɗana zata dawo.”

 Likitan ya yi murmushi ganin har Alhajin a ruɗe yake ya ce,

“Ki kwantar da hankalinki Hajiya, babu ko sisi ɗanki zai tashi ya ci-gaba da rayuwa kamar kowa.

Sadiq ya je ya kawo ruwan, ya miƙa masa. Shi kuma ya koma kan Jawaheer ya watsa mata ruwa, ya koma kan Ummi.

Farouk ya buɗe idanunsa a hankali da suka yi jawur saboda barci. Ba zai iya tuna iya lokacin da ya kwashe yana irin wannan barcin mai kama da mutuwa ba. A hankali ya tashi ya zauna da ƙyar, sannu a hankali ya ɗaga kansa yana duban iyayensa.

A lokacin Jawaheer da Ummi suka farfaɗo. Jawaheer ta ware idanunta sosai ta gigice tana kuka ta kama hanyar ficewa waje, Sadiq ya riƙeta. Fizgewa kawai take yi tana cewa,

“Ku taimakeni kada in rasa Yayana, don Allah ku ƙyaleni.”

Dole Sadiq ya sadata da Farouk, wanda Anti ta riƙe hannunsa ɗaya tam tana jin kamar za a ƙwace mata shi ne.

“Jawaheer ki natsu, Yayanki yana nan da rai, buɗe idanunki ki ganshi.”

 Cewar Sadiq.

 Farouk ya kafeta da idanunsa yana son sanin abin da ya firgita su haka.

 Jawaheer ta rungumeshi tsam tana kuka da iya ƙarfinta, haka ma Ummi jikinta babu inda baya kyarma. Da ƙyar ya ɗaga hannunsa ya shafi kawunansu. Alamun lallashi. Abba ya saki ajiyar zuciya da ƙarfi.

Farouk ya ɗago ya ce,

“Alhaji me ke faruwa ne haka?”

Alhaji ya nemi wuri ya zauna, wanda tun zuwansa yake a tsaye,

“Cewa suka yi ka rasu, wai Suhaila ta kashe ka.”

Farouk ya ware idanunsa, kansa yana sara masa sosai. Ya dafe kan, a lokaci guda ya ce

“Innalillahi Wa innaaa ilaihi raji un. Alhaji ina Suhaila take? Ba su dai cutar da ita ba ko?”

 Alhaji ya rintse ido, sai yanzu ya ji ƙwalla a idanunsa, ya yi saurin gogewa yana girgiza kai,

“Ba zan iya sani ba sai na ga Suhailar. Amma ina tabbatar maki Laila, muddin wani abu ya sami Suhaila sai na yi mugun ɓata maki. Bai kamata ki kirawo kanki a musulma ba, tunda baki yarda da ƙaddara, ba ki da tauhidi ko kaɗan. Sannan har yanzu kin kasa kaɗaita Allah, da ace kin kasance mai kaɗaita Allah da zuciyarki bata gaya maki mutum yana iya kashe mutum ɗan uwansa ba, sai dai sanadi.”

Farouk ya miƙe jikinsa yana rawa, sai dai jiri ya ɗibe shi ya koma ya zauna. Har yanzu barcin yake ji sosai.

Likitan ya dakatar da shi yana masa sannu. Jawaheer kuwa ta kasa matsawa ko nan da can.

Alhaji ya dubi Sadiq ya ce,

“Duk inda aka kai Suhaila a fito da ita yanzun nan.”

 Jikin Sadiq yana karkarwa ya danna lambar ‘yan sandan da suka yi mata lilis suna tambayarta yadda aka yi ta kashe Farouk. Ita gabaɗaya tunaninta da tashin hankalinta suna kan Farouk, ta damu sosai, ta shiga tashin hankali, ta yi kuka ta yi kuka, ta yi danasanin biyayyar da ta yi wa iyayenta har ta ji babu daɗi.

Ɗan sandan jikinsa ya yi sanyi da bayanin Sadiq, dole suka fito da ita ba dan tasan inda za akaita ba, faɗi kawai take yi,

“Ku kasheni don Allah ku kasheni. Idan baku kasheni ba, zan kashe kaina.”

Babu wanda ya tanka mata har suka iso gidan Farouk. Da ƙyar take taka ƙafafunta, tana riƙe a hannun wata Police, har cikin falon. Gaba ɗaya suka zuba mata idanu, halittar fuskarta ta sauya saboda azaban duka. Rarraba idanu take yi har ta hango Daddy ta zabura, har ta mance ciwon jikinta ta yi wajensa tana zazzare idanu,

“Wallahi Daddy ba ni na kashe shi ba, tun bayan da ya ajiye min abinci ban sake ganinsa ba. Me Farouk ya yi min da zan kashe shi? Daddy ka fahimceni duk mazajen da suke mutuwa kai shaida ne Daddy ba ni nake kashe su ba.”

Ta rushe da matsananciyar kuka. Muryar Alhaji ta ji yana magana da kakkausar murya,

“Yanzu illar da kuka yi wa Suhaila kenan?”

Sai a lokacin ta kula da yana cikin ɗakin, don haka ta rarrafa tasa kanta a bisa guiwowinsa jikinta yana rawa bakinta yana rawa ta ce,

“Alhaji ba ni ba ce, ban taɓa yin kisa ba, ka yarda dani ban kashe maka ɗanka ba.”

Ta maƙalƙale shi tana ci gaba da yin kuka. Hatta Momi da ta yankewa rashin mutunci cibiya, sai da tausayin Suhaila ya taɓa ta. Gabaɗaya ta gigice. Alhaji ya ɗago fuskarta ya ce,

“Suhaila ki kwantar da hankalinki kin ji? Dubi can mijinki ne ke zaune lafiyarsa ƙalau, maganin barci yasha.”

Suhaila ta ɗago agigice ta dube shi, tun shigowarta yake binta da kallo zuciyarsa tana wani irin suya. Suhaila ta ƙaraso kusa da shi, bata san lokacin da ta ƙanƙame shi ba tana magana cikin kuka,

“Don Allah don Allah ka sakeni kada ka mutu muna tare, nima kasheni za a yi. Ka taimakeni don Allah.”

 Ya ɗaga hannunsa ya rufe mata baki, duk suka zurawa juna idanu. A lokaci guda ta rungumeshi tana jin kamar tunda Allah ya halicceta bata taɓa shiga farin ciki irin na yau ba. A hankali kuma ta tuna agaban sirikai take don haka ta zame kawai tana jin zafin irin bugun da akayi mata.

Daddy ya miƙe yana yiwa Anti Laila mugun kallo,

“Kin ci sa’a zan ɗaga maki ƙafa saboda darajar mijinki, da kuma ɗanki. Ke kuma Asiya ki kwashe kayanki ki bar min gidana, ba ni da dalilin zama da ke.”

Alhaji Marwan yana ƙwalawa Daddy kira, amma ko waiwaye bai yi ba ya fice kawai yana jin tarin damuwa akan yanayin da ya ga Suhaila a ciki. Ya ji baƙin ciki da har Suhaila take cikin damuwa ya kasa magance mata, sai ma ƙarshe ya ɗaukota ya kawota cikin rikici da tashin hankali.

 Alhaji Marwan ya miƙe yana dubansu idanunsa jazir,

“Dukkanku ku fice a gidan nan. Ke kuma Laila hukuncin da zanyi maki sai kin gwammace da irin hukuncin Asiya kika samu.”

A rikice suka lallaɓa dukka suka fice, harda Sadiq. Doctor ya rage don haka ya ce ta lallaɓa ta je ta yi wanka zai zo ya dubata.

Babu ɓata lokaci ta shiga wanka ta tsaftace kanta, shi dai Farouk yana nan zaune baya fahimtar wasu abubuwan saboda barci. Dole Doctor ya kira ‘yar uwarsa ma’aikaciyar jinya mace, ta zo cikin gaggawa. Ita ta taimakawa Suhaila harda wata doguwar riga, saboda gidan babu kaya. Da ƙyar ta amince tasha tea ɗin, sannan ta yi mata allurai barci ya kwasheta.

Cikin dare ya ware idanunsa, a lokaci guda wata yunwa ta yunƙuro masa, babu ɓata lokaci ya tashi zaune yana mitsittsike idanunsa. Abinci ya gani an ajiye abisa table. A natse ya buɗe ya fara ci. Sai da ya ji ya ƙoshi sannan yasha ruwa. A lokacin kuma komai ya dawo masa cikin kai. Zumbur ya miƙe da nufin dosar ɗakin Suhaila, sai dai kuma wani tunani da ya dawo masa bai yi Salloli ba. Hankalinsa ya kai matuƙa a tashi, kasancewar tunda yake bai taɓa yin hakan ba. A take ya shige banɗakin falon da ninyar yin alwala. A lokacin banɗakin ya dinga juyawa da shi. Da ƙyar ya iya yin addu’a kasancewar babu addu’a ya shiga banɗakin. Da ƙyar ya yi alwala ya fito ya shimfiɗa dardumarsa. Bayan ya idar ne ya buɗe Alqur’aninsa, duk yadda yaso ya yi karatun ya kasa. Yana nan zaune ya rasa meke yi masa daɗi. A lokacin labulen falon ya fara kaɗawa kamar ana iskar ruwa. Shi dai yana nan zaune yana bin ko ina da kallo.

Idanunsa fes akan inuwar mutum daga can saman bangon falon. Ya kamata ya ji tsoro, sai dai hakan ya guji zuciyarsa. A hankali inuwar ta sakko, tana takowa har zuwa gare shi. A lokacin kamar an buɗe masa baki, Allah ya bashi ikon zura idanunsa akan Alqur’anin ya fara da kore shaiɗan sannan ya ci-gaba da rero karatun Alqur’aninsa cikin zazzaƙar Qira’a.

A wannan lokaci inuwar nan ta yi ƙoƙarin watsa masa farar fauda da ke linke a hannunta, sai dai hakan ya gagareta. Wannan ne karo na biyu da ta taɓa kai farmaki tana kasa aiwatar da hakan. Karatun da yake yi ya yi mata zafi, hakan ya tilastata ficewa daga ɗakin cikin tashin hankali, kafin wani lokaci gefen fuskarta ta ƙone, hakan ya sake fusatata, ta ci alwashi akan sai ta je har gidan Alhaji Marwan ta ɗau fansar abinda ɗansa ya yi mata, daga bisani ta koma ta hallaka shi.

Bayan ya idar da Karatun, ya rufe ya yi addu’a ya shafa. Kai tsaye ɗakin Suhaila ya nufa cikin damuwar halin da take ciki.

Barci take yi sosai, hakan ya tilasta masa hayewa gadon yana ɗan bubbugata. Cikin magagi ta jawo hannunsa tana kuka,

“Ba ni na kashe shi ba, kuyi min uzuri.”

Tausayinta ya tsirga masa, ya jawota gabaɗaya ya rungumeta tsam a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Tasa hannunta ta rungume shi. Yadda yake shinshinarta yasa ta buɗe idanunta. Ya ɗago fuskarta suna fuskantar juna sosai, yadda har tana iya jiyo hucinsa. Ta riga ta sadaukar kissing ɗinta zai yi, don haka ta rintse idanu gabanta yana tsananta faɗiwa. A hankali ya yi magana kamar mai raɗa,

“Tashi ki je ki yi Sallah, dare ya yi.”

 Cikin mutuwar jiki ta janye jikinta, sai dai tana ɗora ƙafarta a ƙasa ta fasa ƙara, cikin gaggawa ya ce,

“Tsaya kada ki jiwa kanki ciwo.”

Tsayawa kawai ta yi tana kallonsa. Bata taɓa tunanin yana da muryar lallashi ba, kamar a yanzu ɗin nan da take kallonsa. Shi kansa irin kallon da take yi masa yasa duk ya tsargu.

Tana tunanin abin da zai yi mata, ta ji ya ɗauketa cak! Sai banɗaki. Ta kasa amincewa kanta wai Farouk ne a kusa da ita, ta fi amincewa zuciyarta mafarki kawai take yi.

Yana shiga banɗakin ya ajiyeta ya fice, domin yana da tabbacin zata iya yin komai. Bayan ta gama ne yaga ta buɗe ƙofar tana ɗingisa kafafun, domin ta ci alwashin ba zata sake barinsa ya ɗauketa ba.

Yana kallonta har ta shige ɗakinta ya koma falo kawai ya zauna shiru, yana tunanin makomar wannan aure, a lokaci guda muryarta ta dinga yi masa kuuwa,

‘Da in zauna da shi gara na zauna da jaki.’

 Ya rintse idanu yana jin ɗacin kalamanta. Sai yanzu Istakharan da ya yi ya dawo masa kai. Gashi a hankali komai yana ƙara lalacewa. Ko a tunani bai taɓa sanin Suhaila zata zama mallakinsa ba.

Miƙewa ya yi ya ɗauki abinci ya kai mata. A lokacin tana zaune tana jan carbi. Bayan ya ajiye mata ya fice kawai zuwa ɗakinsa. Wanka ya fara gabatarwa, sannan ya yi alwala. Wannan ƙa’idarsa ce kwanciya da alwala. Bayan ya fito ne ya zauna akan gado ya jawo ƙaramin Ƙur’ani yana karantawa a cikin zuciyarsa. Inuwar da ya gani ya dinga tunawa a zuciyarsa, sai dai ya kasa gazgatawa.

Washegari da sassafe Alhaji ya zo gidan da kansa yasa aka kawo mata akwatunanta, da kuma sabuwar waya. Bai jira ya gaisa da kowa ba ya fice. Farouk ya fara sakkowa yaga kayayyakin, kawai ya ɗan yi murmushi, ya fice daga gidan gaba ɗaya, kasancewar yana da shiga Class ƙarfe tara, kuma zai yi masu test.

Bayan ta farka taga komai, kai tsaye ta buɗe wayar tasa lambar wata ‘yar Class ɗinsu tana ɗauka ta ce mata duk abin da take yi ta bari ta zo Makaranta yau Malam Farouk zai yi masu test. Gabanta ya faɗi dole ta lallaɓa ta buɗe akwatin ta ciro doguwar riga da hijabi ɗan madaidaici, tasa. Sai dai kuma gaba ɗaya takardunta suna gidan Momi, dole ta kira lambar Daddy take gaya masa. Babu ɓata lokaci ya turo mata Driver don haka ta fito tana ɗingisawa ta shiga motar tare da jawo jakarta, tana duba hand out ɗinsa.

A lokacin da ta shigo har tara ta gota, ya rigata shiga. Dole ta yi ƙundumbala ta faɗo Class ɗin kanta a ƙasa.

Idanunsa fes! Akanta, yana mamakin yadda akayi har ta zo Makarantar, amma sai ya kirne ya ɗaure fuska. Daga cikin ɗaliban akwai waɗanda suka san abubuwan da suka faru don haka duk suka zuba masu idanu.

“Sorry Sir ba ni da lafiya ne shiyasa na yi latti.”

Ummi ta zuba masu idanu cikin wani irin kishi ji take kamar ta kama Suhaila da duka saboda tsabar tsana.

Bai ce komai ba ya kaɗa mata kai, har za ta wuce ta nemi turguɗewa ya yi kamar zai kamota ya ce,

“Ki kula.”

Sai kuma ya yi saurin janye hannunsa. Kusa da Ummi ta nemi ta zauna,yana kallonsu yadda ta yi bake-bake da wurin ta hanata zama. Har ta juya zata koma ta can baya kusa da wasu maza, Farouk ya ce,

“Ke Ummi matsa ta zauna anan kusa da ke.”

Ya faɗa cikin tsare gira. Ummi ta turo baki kamar zata yi kuka ta matsa. Suhaila ta koma ta zauna cike da damuwa.

<< Kaddarata Ce 8Kaddarata Ce 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×