Skip to content
Part 2 of 4 in the Series Kangin Rayuwa by Fatima Rabiu

DA SUNAN ALLAHU MAI RAHMA MAI JIN K’AI

Hajara ji tayi kamar ta saki shewa amma saita maze, tana sakin wani irin salati, tana fashewa da kukan k’arya, sosai fa hankalin su Inna Suwaiba ya tashi ganin A’i fa babu rai a jikinta.

Jikinsu ne yayi mugun sanyi Inna Khande ce ta amshi yarinyar da har yanzu bata yi koda tari bane.

Dan da nan Inna Khande ta had’a ruwan zafi ta wanke d’iyar tas, sai a lokacin tayi d’an kuka kad’an, ana gama mata wanka kuma bacci yayi awan gaba da ita.

Inna Khanden ce dai ta goyata saboda mutane da suka fara cika gidan, har an fara ma yarinyar surutu ganin irin kyan da Allah ya zuba mata.

A wajan Hajara ko sosai ta k’ara jin tsanar yarinyar da A’in ta haifa ganin irin baiwar da Allah ya zuba mata na kyau, da yadda taga mutane ke son daukarta yasa ta k’uduri aniyar saita sa kowa ya tsani yarinyar.

A sadda mazan suka dawo ba k’aramar girgiza Hamza yayi ba, dan har yaso ya fita daga tunaninsa dan Allah ya sani yana bala’in son matarsa, kuma uwar gidan sa.

Ganin haka yasa Hajara dake zaune kusa dashi ta banka mai hararara k’asa-k’asa, ganin yadda aka kawo mai yarinyar ya wani k’ak’k’ameta, yana kuka sai kace ba namiji ba, haushin su Inna Khande ta k’ara ji ganin yadda suke wani k’ara tausarsa, y’ar gwal ta mutu.

Wani murmushin mugunta ta saki, cike da makirci, ta kai hannunta zata amshi d’iyar tana sakin kukan munafurci tana cewa, “Allah sarki A’i wallahi yarinyar nan har taban tausayi zan rik’e ta, zan kula da ita kamar ni na haife ta”

Wani kallo su Inna Khande suka bi Hajara dashi can Hadiza ta banka mata harara a zuciyarta tana cewa “kaji makirar mata, wallahi wannan Hajarar y’ar san a sani ce”

Can ta bud’e baki ta ce “a’a Hajara keda kike cewa baza ki iya rik’e d’an wani ba, ina kuma gana kishiyar ki…..

Kamin ta idasa maganar Hajara ta tashi a zuciye tana nuna Hadiza da yatsa tana cewa,

“Hadiza ki kiyayeni ni ba sa’ar yinki bace karki bari na juyo ta kanki, mi kike nufi ne ina za’a kai yarinyar to nufinki kasheta zanyi?”,

Cike jin haushin Hajarar dan kwata-kwata gidan ba wani cika shiri sukai da junansu ba kowa burin sa yafi d’an uwansa ko kuma ya ga d’an uwansa cikin iftila’in rayuwa, ta ce “yo Ohho miki waya sani ma”,

“Mi kike nufi wai Hadiza?”

Cewar Hajara dake tsaye kanta kamar zata kai mata naushi a fuska.

Hamza ne ya tashi cike da b’acin rai ya ce “shin zaku barni da abunda nake ji ne ko kowa halin naku zaku nuna a gaban mutane?, kuma yarinya dai tawa ce sai inda naga dama ta zauna, dan haka bana son irin haka”,

Shuru wajan yayi Hadiza taja Na’ima cike da jin haushin su gaba d’aya suka shige d’aki.

Maryama ce ta tab’e baki tana jan Hajara gefe ta ce “wallahi karki yarda ki bari dangin A’i su amshi yarinyar nan dan ko idan kika bari hakan ta faru to tabbas wannan yarinyar sai ta zama abun kwatance”

Dafe k’irji Hajara tayi tana cewa “ke Mmn Bishira, maganar kifa abar dubawa ce, tabbas naci alwashin a cikin gidan nan zata girma, bauta ce saita yi mana saita koma kamar jaka a cikin gidan nan”

Tafawa sukai Maryama na cewa “da kyau ai nasan bakya wasa”.

Habiba ce ta jawo Maman nasu tana cewa “shin wai Mama miye ruwanki da shiga harkar adda Hajara ne?”,

“Ke nasan abunda nake yi kinji, wannan yarinyar da kuke gani kamar y’ar aljanu, kun fara tasowa a gidan nan duk wani aiki zai iya dawowa kanku, to ni kuma wallahi babu abunda ya isa ya takura muku, ita bakuga Hadiza yadda take nunawa ba, ita tsabar bak’in hali ne da hassadarta ta ta motsa, shi yasa ta amayar da abunda ke cikin ta tun yanzu, gara ta girma a cikin gidan nan ta zama jaka dan nasan wallahi ko sama da k’asa zasu had’e tofa Hajara bazata bari a matsa da ita ko ina ba”,

Haka ta gama masu karatun da kullum take yiwa yarin nata shi yasa suka raina kowa basa ganin mutumcin kowa.

Da safe tunda aka kai A’i makwacinta na gaskiya yarinyar data haifa take kuka mai ban tausayi, kamar tasan mike faruwa, har sai da aka mik’ata wajan Kakanta Sani yayi mata tofi sana ta sarara da kukan, inda ana dawowa aka rad’a ma yarinyar sunan Mahaifiyarta wato Aysha, Hamza yayi mata lak’ani da Marmah.

Babu wadda ya ce masa danmi ya maida sunan A’i dansu gansu muta nan sun ga abinda yayi dai-dai ne, koda a cikin gidan aka fad’i sunan yarinyar ba wadda ya tanka bare ayi cecekuce.

Hajara ko tunda sanyin safiyar ranar ta fice ta tafi wani mugun K’auye dake kusa dasu wajan Bokanta.

Wani irin daji ne mai duhun gaske tana tafiya ko d’igon tsoro babu a fuskata tana tafiya dajin na canzawa yana koma wani irin yadda kasan ba’a k’asar take tafiya kamar akan iska, ga wasu irin bishiyoyi masu ban tsoro, amma haka Hajara take k’ara danna kai cikin dokar dajin, har takai wata buka dake zagaye da wasu irin jajayan kyalle, ga wasu irin koke-koke dake tashi cikin dajin.

Zubewa Hajara tayi tana d’ukawa kanta har k’asa, kamar tana sujjada, ta mik’a hannunta gaba, tana wasu irin surutai, da wani irin yare, marar dad’in sauraro, wasu darussan tsafi ta k’ara dagewa da fad’i, da k’arfi, wata irin mahaukaciyar guguwa ce ta tashi, ta turnuk’e wajan, da wata irin mahaukaciyar dariya wacce take fitowa a rarrabe, yadda dariyar ke fitowa da amsa kuwwa, sai yasa mutum sumewa bai shirya ba, amma Hajara ko a jikinta, tana nan a duk’en da take.

Har sai taji wata murya mai kama da ta basamudan k’ato tana fitowa a rarrabe itafa da k’arfin gaske, har dajin na d’aukar maganar bishiyoyi na wata irin girgiza, tsabar k’atowar muryar dake tashi ana cewa.

“Ke la’ananniyar Allah wannan kira haka na gaggawa, wata muguntarce ta taso kike son ganinmu”

Da sauri Hajara ta tashi tana k’ara zubewa k’asa cike da girmamawa yadda kasan tana a gaban sarki ko shugaban k’asa, zata fara magana aka dakatar da ita da cewa,

“Hhhhhhh basai kince komai ba indai akan yarinyar da aka haifa ne tabbas za’a baki ita kuma sai yadda kikayi da ita, sai dai ki sani yarinyar nada wata irin baiwa, dan mu kanmu mun kasa ganin wacce irin baiwa ce, idan muka ce zamu matsanta da yi mata mugunta to tabbas, abun zai shafe mu, amma burinki zai ciki na rik’e yarinyar a hannunki, sai dai sai kinyi taka tsantsan”

Ana gama maganar Hajara ta nemi Bukar nan sama ko k’asa ta rasa guguwar nan ta b’ace babu ita.

Hajara da ba haka taso ba, ta so ta fad’i abunda ke ranta amma Boka bai bata dama ba, kuma ta sani ba’a kiran Boka Sank’are sau biyu, dan k’a’ida ne dashi, sai dai ta sake dawowa a irin wannan ranar a wani watan dai-dai kuma kwanan watan yazo d’aya, haka k’a’idarsa take, yatsanta ta d’an ciza tayi kwafa, ta juya ta fara komawa, tana tunani a ranta.

Koba komai ta cika burinta na bata Marmah a wajanta tabbas yarinyar saita gane shayi ruwa ne, indai, tana da rai Marmah bazata tab’a jin dad’i ba, tabbas yarinyar zata ga mugunta kala-kala, idan taji matsi ma ta mutu mana ina ruwan wani, ta tabbas Marmah kin shiga uku watan shiga K’angin rayuwarki ya kama.

Hajara ta fad’a da k’arfi, zuciyarta cike da tsanar yarinyar, a yanzu duk wata tsanar A’i da kishinta da take ji yasa dawo kan Marmah.

<< Kangin Rayuwa 1Kangin Rayuwa 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.