Skip to content
Part 3 of 4 in the Series Kangin Rayuwa by Fatima Rabiu

Tunda Hajara ta shiga cikin gidan nasu, ganin har yanzu mutane keta shiga da fita, yasa ta saki wani shegen tsaki.

Dubanta ta kai gefe inda ta hangi mijinta Hamza da dangin A’i kamar suna cece kuce yasa ba shiri ta matsa kusa dasu cike da makirci ta tsoma musu baki.

“Ko kuwa in banda abunku ina Marmah za’a rik’e ta taji dad’i inba gidan ubanta ba, saura nan gaba a rink’a mata gori”,

Adda Khareema ce yayar A’i wadda suke uba d’aya da A’in saboda ita A’i bata da Wa ko K’anwa ko Yaya, a d’akinsu ita d’aya ce sai ko wadda suke uba d’aya da juna Mahaifiyarta ta rasu tun tana budurwa.

Ta ce “kee Hajara ki rufe ma mutane baki an sako ki a ciki ne?, makira al’gunguma, so kike abar miki Marmah ki azabtar da marainiyar Allah, waye bai san yadda A’i tasha wuya wajanki ba, sai yanzu kuma dan tsabar makirci zaki wani ce abar y’arta gidan nan naku mai kama da gidan Gandu”

Ta idasa maganar tana hararar Hajara.

Hajara dake tsaye tana jijjaga tsabar munafurcin dake cinta ta fashe da wani irin kuka tana cewa,

“Yanzu Abban Asma’u kana ji wa’innan maganganun da Khareema ke gaya min mi yasa zanki rik’e jinin A’i mita tsare min, kuma Marmah ce dai babu yadda kuka iya saita girma a gidan nan duk yadda zakuyi kuyi”

Kawu Baffa ne Yayan A’in yayi saurin tare lumfashin Kharima ganin tana niyar maida ma Hajara da magana dan yasan ko kwana za’ai ana zancan nan idan Hajara ta fad’i goma tofa sai Kharima ta maida mata da dubu.

Ya ce “ya isa haka nan”

Ya kai dubansa wajan Hamza dake tsaye ko ci kanku bai ce ba.

Ya sake cewa “shin kai muke sauraro d’iyar nan dai taka ce idan ka yanke hukunci a kanta ya yanku babu wadda ya isa tursasa ka, shin zaka bamu yarinyar nan mu tafi da ita ko kuwa?, tunda dai Allah ya sani babu abunda zata nema ta rasa a wajanmu”

Wani kallo Hajara dake bin Kawu Baffa dashi na raini tana sauraron mi Hamzan zai ce, ai koda zatayi yawo tsirara bazata tab’a bari su tafi da Marmah ba, bare ma sunyi kad’an suyi jayya da ita, yanzu kam tasan ko Hamza bai isa ya musa mata ba, tasan abunda ta taka.

Hamza daya nisa yana kallonsu d’aya bayan d’aya can yayi maganar da Baffa ya girgiza da jinta yana cewa,

“To Baffa mi kake nufi ne?, mu a wajan namu zata nemi wani abu ta rasa ne?, kuma a nan gidan nayi wayo a nan na girma dan haka itama a nan zatayi rayuwa na gama magana ta”

Yana idasa fad’ar haka yayi ficewar shi waje yana mik’a Marmah a hannun Hajara, Marmah ko kuka ta saki jin yadda aka mik’ata da k’arfi harta firgita.

Hajara data saki wani makirin murmushi tana matsawa kusa da Adda Kharima tana dubanta ta ce “ai duk wadda yaci tuwo dani miya yasha ni nan da kike gani kabaiwar kan kabari ce bak’in cikin mai taushe, ni d’uwawu ne dole a zauna dani”

Murmushi Kharima ta saki tana matsawa kusa da ita ido cikin ido ta ce “hmm indai yarinya ce har abada anbar muku ita, baza muyi jayya daku ba, kuma Marmah ce dai Allah yana tare da ita, babu abinda kika isa kiyi mata face Allah ya rubutasa, a k’undun k’addararta, daga yanzu idan kinga wani cikin danginmu yazo wai da sunan a bashi Marmah ko miye zaki iya yi an bar muku d’iyarku, ko kuma na ce d’iyarsa”

Wata shewa Hajara ta saki kamar ba gidan mutuwa ba, da yawan y’an gidan sun saki baki suna kallon ikon Allah masu murna nayi masu jin haushin Hajara nayi.

Ta sake cewa “yo kunma isa kuyi jayya da mai abu da abunsa, ai kunyi kad’an k’ana nan kwari”.

Girgiza kai Kawu Baffa yayi yana jan Kharima gaba yana kallon Marmah dake kallon sama tana tsotsar hannu baiwar Allah, yana matuk’ar tausayin yarinyar, akwai babban K’angin rayuwa da zata shiga nan gaba, koma ya ce a yanzu zata fara gani, zama a wajan matar uba wacce koda uwarta nada rai ba raga mata take ba, bare yanzu da ba idon Mahaifiyarta, ai sai abunda Allah yayi, yana mata addu’ar kariya daga Ubangiji.

Bayan fitar su Kharima Sa’ade dake tsaye cikin matan gidan ta tab’e baki ta ce “ni ko Hajara banga anfanin amsar wannan yarinya da kika dage sai kinyi ba, dan nasan tabbas babu abunda zaki iyayi mata sai tsabar mugunta da makirci da kike shirin aiwatarwa, da kinbar yarinya taje inda za’a kula da ita, am…. Cike da jin haushin ta Hajara ta fara mai da mata magana tana cewa,

“Kinga Malama babu ruwanki a ciki, da kike maganar bazan iya kula da ita ba, ai naga ke kin kula da d’an naki, kin kasa basa tarbiyar data dace yaro ya fitsare ya gagari uban kowa, ke har kina da bakin magana wajan cewa ba’a iya ba yara tarbiyar ba”

Zage-zage suka farayi suna faman tunama junan asiri.

Su Inna Suwaiba sunyi-sunyi amma yadda kasan k’ara tura su sukeyi kamar zasuyi danbe da juna.

Hamisu ne ya shigo gidan a buge yasha yayi mak’is yana tangad’i, ganin abunda ke faruwa yasa ya matsa zai d’auke Hajara da mari ba shiri Hajara tayi kukan kura ta hankad’e shi, tana ba Inna Khande Marmah dake hannunta tana nuna Hamisu da yatsa.

Ta ce “wallahi kul d’inki ahir d’inki nafi k’arfin kasa k’azamin hannunka ka tab’a lafiyar jikina, banyi sanadiyar nakasa rayuwarka ba, yaron banza kawai wadda uwarsa ta kasa basa tarbiyar data dace”

Wata irin hargowa Sa’ade ta saki tana kunfan baki wajan cewa “eh ban basa tarbiyar ba, ai ke naga kinba yarinyar taki tarbiyar, Asma’u, waye take ganin mutumcinsa a gida nan, idan kika d’ora mata talla dan da nan take kawo miki ciniki, idan yarinya ba iskanci take da mazan banza a waje ba, ubanmi take da zata rink’a kawo miki kud’i haka, saboda tsabar son kud’inki, kike amshewa ki lamushe, garani na godewa Allah namiji ne dani, koda yayi iskancin nasa ado yayi kefa duk randa ta kwaso miki abu….. Maganar Sa’ade ce ta mak’ale jin saukar mari a kumatunta.

D’ago kanta tayi tana duban Hajara dake ihuce gaf da ita ta zafga mata mari ko a jikinta, tana nunata da yatsa ta ce “insha Allahu abun kunya da kike min fata a kanki zai k’are nafi k’arfin ki wallahi, Sa’ade ki bini a hankali idan ba to tabbas zakiga mi zan miki”

Hamisu daya taso a zuciye shima yana shirin sake kaima Hajara mari yaji an rik’e hannunsa, ana d’auke sa da wani mari tasssss tassss kake jinsa.

Ba shiri mutanan gidan suka kai dubansu ga wadda yayi wannan mari ganin Hamza dake tsaye rik’e da hannun Hamisu ya nuna sa ya ce “kaiiii rashin mutumcin naka har ya kai haka rashin kunyar taka akan matata zaka sauke ta, kaje kayo shaye-shayen banzarka zako zo ka tada ma mutane hankali, to tabbas ka kusa daina shigowa cikin gidan nan”.

Wani bak’in ciki ne ya hana Sa’ade tankawa sai bin Hajara take da kallo da Hamza.

Can suka tsinkayi muryar Iron yana cewa “kamar ya Hamza mi kake nufi ne?, na cewa Hamisu ya daina shigowa gidan nan, ai bata yiwuwa yadda kake da gado a cikin gidan nan shima haka yake da shi, dan haka bana son maganar banza”

Hamza zai sake magana suka ji gyaran muryar Mahaifinsu wadda suke kira da Malam yana kallonsu cike da takaicin abunda ke yawan faruwa da ahalin gidan a yanzu, tunda mata sukai ma gidan yawa munafurci ya sake k’aruwa.

Cike da kakkausar muryar ya ce “saboda matanku da yaranku kuke shirin yin fad’a da sa’insa, matanku suna so su raba kawunan ku, wannan ai rashin tunani ne, daga yau bana son na sake jin irin haka, bana son ganin kowa a nan bare naji tashin wata maganar, anyi mutuwa ma bazata zama izina a gareku ba?, dan haka gaba d’ayanku ku b’ace min da gani, karna sake jin tashin maganar wani, idan ba haka ba, ran mutum zaiyi mummunan b’aci”.

Yana gama maganar ya juya ya shige turakarsa cike da damuwa a ransa, yasan tabbas baza su tab’a dainawa ba, koda yayi gargad’i kuma yasan ba laifin yaransa bane laifin matansu ne, duk su ke had’a wannan husumar.

Kowa na tsakar gidan watsewa yayi suna nufar d’akonansu wasu na jin haushin Mlm daya katse musu kallon fad’a wasu na dariyar mugunta.

A wajan Kawu Sule bai tashi jin mutuwar matar d’an uwansa ba sai washe garin da akai mutuwar Mlm yasa Abubakar kiransa ya shaida masa, sosai fa mutuwar ta shigesa inda ya ce insha Allahu gobe goben nan suna nan tahowa tare da iyalansa.

Bilkisu dake zaune akan wata kujera mai kyan gaske tasha gayu ga y’an aiki dake ta mafan hidima dasu, da yaranta dake zaune wadda basu wace shekara shidda ko biyar ba, Khairat da Ifteesan.

Fuskarta da walwala amma jin yana waya da dinginsa na K’auye, har take jin wai gobe yake shirin su tafi yasa fuskarta ta canza.

Yana aje wayar ya juyo wajan Bilki dake kallonsa ya ce “kinji mutuwa akai mana matar d’an uwana Hamza ce ta raso uwar gidansa, dan haka ku shiri gobe gaba d’ayanmu nake so muje zamu kwana biyu a can”

Wata irin zabura Bilki tayi tana cewa “Allah ya jik’an musulmi, amma maganar muje mu kwana Daddyn Khairat ai nake ganin bata taso ba, tunda kaga yara suna zuwa school nake…… Dakatar da ita yayi da hannunsa, ba tun yau ba ya fuskanci Matar tasa bata son y’an uwansa bata son tushansa a inda ya taso.

Ya ce “babu ruwa na da school d’insu gaisuwa ce saifa sunje kinji na gaya miki”

Tashi ta k’ara yi a kansa tana cewa “haba Daddyn Khairat ya zaka ce haka yaran nanfa basu saba kwanan K’auye ba, mi zai hana mu dawo ranar, ko abincin can baza su iya ci ba wallahi bare mutanan can da basu saba dasu ba”.

Ran Daddy idan yayi duba ya b’ace tashi yayi shima yana cewa “lallai Bilki kinban mamaki, ni ba’a can na taso ba?, ko kowa ni na rasa raina da nayi rayuwa a can, can d’in da kika raina kika tusama yaranki tsanar y’an K’auye, karki manta nima d’an K’auyen ne, mi yasa baki gaya masu uban nasu wadda suke tak’ama dashi shima d’an can bane?, Bilki na riga na yanke hukunci saifa sunje, kinma sa na k’ara kwanaki akan wadda nayi niyar muyi, wallahi sai munyi sati d’aya kinji na rantse kuwa”.

Yana idasa maganar ya haura sama yana jan dogon tsaki yana ayyana wani abu a ransa tabbas sai yayi maganin Bilki.

Su Ifteesan da tun d’azo suka bar parlon suka koma Babbn parlon gidan, dan k’a’idar gidan ce haka indai iyayan nasu na magana basu isa tsaya masu a kai ba, sunma sani dasun fara, ko basu ce su fita su basu waje ba, sun sani zasu fice.

Y’an aikin dake aiki a parlon Asabe da Tala sukai saurin barin parlon, dankar ta dawo kansu, suna addu’ar yasa ma ya ce sai sunyi fin sati d’ayan ma, suna matukar hakuri zaman gidan domin kuwa Bilki ta sani duk wani Talaka ko d’an K’auye, shi yasa suka shige suna murmushin abunda Daddyn yayi mata, yayi dai-dai wallahi.

Su Ifteesan ne Suka k’araso kusa da uwar tasu suna faman tab’e baki saboda sunji Daddynsu na cewa sai sunje K’auye.

Ifteesan ce ta ce “Mami wai da gaske Daddy yake K’auye zamu wai?, nidai gaskiya bana son zuwa K’auye”,

Ta idasa maganar tana tab’e baki kamar zata fashe da kuka.

Da sauri Mami ta ce “kuyi hakuri ai ba dad’ewa zamuyi ba, kuma koda munje da abunda zamu ce zan tafar mana dashi, kuma babu ruwanku da duk wadda kuka gani, zan d’au mataki a kansu ne gaba d’aya dangin nasa, sunga shine mai abun duniya abu kad’an an bugo mai ana neman maula y’an wahala kawai…

<< Kangin Rayuwa 2Kangin Rayuwa 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×