Skip to content
Part 4 of 4 in the Series Kangin Rayuwa by Fatima Rabiu

Mami ta idasa maganar tana sakin wani shegen tsaki, ta juya tana kwad’ama Tala kira.

Da rawar jiki Tala tazo tana zubewa k’asa ta ce “Hajiya gani”,

Sai da ta d’au mintina kamin ta ce “ina so kiyi mana kayan ciye-ciye please a soya mana harda kaji ayi mana miya ta soyu sosai, zamuyi tafiya ne, kin gane mi nake nufi?”

Da sauri Tala ta k’ara sadda kanta k’asa ta ce “eh Hajiya na fahimta insha Allahu yanzu za’a fara ma”

“Za ki iya tafiya”

Tashi Tala tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta nufi kitchen dan da nan suka fara aikin data sasu ita da Asabe.

A parlo Mami dake zaune duk zuciyarta babu dad’i, ta nisa cikin tunani, ringing d’in wayarta ne ya fargar da ita, Ifteesan ce ta mik’o mata wayar tana cewa,

“Lahh Mami Ya Khaleefa ne”

A yadda yaran suka shiga hankalin su suka nutsu dan da nan kamar Ya Khaleefan ne zai fito daga cikin wayar, sunyi shuru sun natsu.

Mami data yi picking d’in wayar tana kaiwa a k’unanta ta ce “Khaleefa ya karatun fatan dai kana lafiya?, wai yaushe ne ake muku hutu ne?, munyi kewarka gaskiya, ya kamata kad’au hutu ka dawo”

Daga cikin wayar wata sansanyar murya mai cike da kamala da zaki ya ce “Mami nima ina miss d’inku ai, ina yaran nan?, sun daina rashin ji ko?, I hope dai kuna lafiya?, Mima naji Daddy ya ce zakuyi tafiya ne, naso ina nan ina son yanayin garin su Daddy wallahi”,

Sakin baki Mami tayi tana sake cewa “wai mina ji kana cewa ne?, wannan banzan garin kake so?”

“Haba Mami wane irin banzan gari kuma garin su Daddy ne fa”

“Kai da’aAllah rufe min baki ni na rasa wane irin hali ne da kai nikam sai kace ba wadda ya fito daga cikina ba, wannan garin kake cewa kana wani so, ai garama da baka nan, haka kawai in kwashe yaran nawa mu nufi wannan gari dasu, aje a lashe min ku, kaga ka daina min irin haka kaji na gaya ma”

Shuru Khaleefa yayi yana lumshe idonsa cike da miskilancinsa da rashin son hayaniya cikin call voice nasa mai sanyin dad’i ya ce,

“Shikenan Mami am sorry Allah ya kaiku lafiya”

Wani tsaki ta saki tana cewa “nifa kaga My son ba’a san raina zamu ba, wallahi da nasan yadda zanyi wallahi saina ruguza tafiyar nan”

“Tohm Mami kayi hakuri mana ai ba wani dad’ewa zakuyi ba, yanzu dai bani su Ifteesan zanyi magana dasu”

Tashi Mami tayi tana mik’a ma masu wayar tayi cikin Bedroom tana faman mita, bama ta lura da halin dasu Khairat d’in suka shiga, cike da tsoro sukasa wayar a amsa kuwwa.

Can cikin wayar Ya Khaleefa ya fara magana ba wasa.

“Kunsan Allah kuka sake kuka je garin nan kuna nuna wannan halin naku na rashin son mutane, zan sani ne kuma kunsan mi zan muku”

Jin sunyi shuru yasa Ya Khaleefa a harzuk’e ya sake cewa “wai bakuji mi nake fad’a bane?”,

Har suna rige-rigen cewa “eh ehh Ya Khaleefa munji bazama muyi ba”

“Good kun cece kanku”

Yana fad’in haka ya tsinke kiran.

Wata irin ajiyar zuciya sukai suna aje wayar a hankali yadda kasan wayar ce Ya Khaleefan.

Khairat ce ta furzar da wata iska tana k’ara sauke ajiyar zuciya ta ce “na rantse Ya Khaleefa d’an rigima ne, karkiji yadda zuciyata ke harbawa, ita kuma Mami harda cewa wani munyi kewarshi, nidai wallahi bana so ya dawo, kwata-kwata komi kayi shi a wajansa kayi laifi”

Ifteesan ta amshe da cewa “hmm ai ni abinda yake ban tsoro ma a tare dashi idan ya fad’i magana koda baki ji ba, tofa kin kad’ai dan bazai maimaita miki ita ba, sai ya mula ya munmule tukun, gashi Mami tasa shi ya kusa dawowa”

Ifteesan ta kwab’e baki duk jikinsu yayi sanyi, ga zuwa K’auye da aka tilas tasu zuwa gobe.

HAJARA POV

Shigewa d’akinta tayi da Marmah a hannunta tana zuwa ta dungure ta waje guda, yarinyar ta saki kuka domin yinwa take ji, kallonta Hajara tayi cike da tsana tasa d’an yatsa ta dungure mata kai, tana cewa “kee jarababbiya kin ishemu da kuka, Allah ji nake kamar na shak’eki ki mutu kibi uwarki kowa ma ya huta, shegiyar yariya da kyau kamar y’ar aljanu”

Ta idasa maganar tana sakin tsaki tashi tayi tana harkar gabanta duk kukan da Marmah keyi hakan baisa ta aje abunda take yiba, baiwar Allah tun tana kukan har wani wahalallan bacci ya d’auke ta, jin shuru Hajara ta saki tsaki tana k’ara cewa “da karda ma kiyi shurun ko mutuwa zakiyi da yinwa sai ubanki ya kawo abinda za’a baki, nidai ba nono zan baki ba, a’ato”.

Bishira ce ta fito daga d’akinsu ita da y’ar uwarta Habiba ance wata shegiyar kwalliya za’a fice talla, daga yin mutuwa amma su ko a jikinsu daga su har uwarsu, Maryama dake masu kirari tana kod’asu har suka shiga zaurar gidan suna faman washe baki.

Hamisu ne ya taho bai lura dasu ba kawai yaji an bangaje, tsayawa yayi yana nuna Bishira da yatsa cike da jin haushin yaran ya ce “keee dabbar ina ce bakya gani ne?, kuna tafiya sai kace mahaukata”,

Wata uwar hararara Habiba ta banka mai tana murgud’a mai baki, Bishira dake mai wani kallo na raini ta rik’e k’ugu ta ce “to sannu mai hankali kai akwai ma wadda ya kaika rashin hankali, ai cikin mahaukatan garin nan kaine lanba d’aya, mai shaye-shaye har an gaya mai rashin hankali”.

Batai aune ba ya matso kusa da ita yana d’auke ta da wani kyakkyawan mari tasssss tassss, wata irin mahaukaciyar chafka ta mai ta chakumo wuyan rigarsa, itama kamin ya sauke hannun nasa itama ta wanke shi da nata marin, tana sakin shi ta hankad’eshi gefe, kamar wani kayan wanki.

Wata shewa Habiba ta saki tana cewa “kai amma y’ar uwata na rantse kinmin dai-dai, shashasha kawai marar hankali”,

Tasowa yayi a zuciye yana nuna kanshi da cewa “kaiii ni ne marar hankalin?”.

Wata shewar suka sake saki suna cewa a tare “yo kaine mana akwai wani ne dake tsaye a nan bayan kai?, hankalin ne da kai?, ai kowa yasan mai shaye-shaye da neman mata basu cika hankali ba, ni wallahi kama cucuni dana had’a jiki da kai Allah ya isa na kuma wallahi bari ma ka gani”.

Bishara ce ta idasa maganar ta k’arshe tana sakin wani uban kuka tayi cikin gidan nasu da gudu, tana kururuwa, yadda kasan ana yankan naman jikinta.

Dukansu mutanan gidan ba shiri suka fito, Maryama ko har tuntub’e take wajan fitowa, tana tayi saurin isa kusa da Bishira tana jijjaga tana dudduba jikinta sai faman tabbayarta take miye ya same ta.

Habiba dake shigowa tare da Hamisu daya saki baki yaga wane irin shirri, Bishira ke son k’ulla mai.

Itama Habiba kukan munafurci ta saki tana nuna Hamisu.

Ba shiri Maryama ta matso kusa da Hamisu taci kwalar rigarsa tana cewa “to tanbad’and’e ubanmi kayiwa yara na?, na rantse da sarkin dake busan lumfashi zan sharara maka mari idan baka gaya min abunda kayi musu ba, haka nan dai baza su shigo gidan nan a haka ba, zaka yi magana ko kowa d’an iskan yaro kawai”

Sa’ade ce tazo ta bangaje Maryama tana cewa “keee Malama dagata na ce abun ya isa haka, ban haifi d’an iska ba, na gaji da irin abubuwan da ake ma yaro na a cikin gidan nan gaskiya, mi yasa ba zaki iya tabbayar yaran naki ba sai shi?”.

Hajara dake tsaye ta rik’e k’ugu tana murmushin jin dad’i tana so taga ya za’a k’are.

Bishira ce ta k’ara sakin kuka tana cewa “Mama wallahi Hamisu d’an iska ne, munzo fa fita zaure shine na d’an bigeshi ban gani ba, na basa hakuri, amma kawai ya mare ni yana rungume ni yasa hannunsa cikin rigata yana matsa min nono Na…

“Innalillhi”,

Gaba d’aya suka d’auka da cewa.

Wani kukan kura Maryama tayi tana zanfga ma Hamisu wani gigitaccan mari, ba shiri yayi baya-baya zai fad’i, da mugun sauri Sa’ade ta taro shi, tana taroshi ta matsa kusa da Habiba itama tana zafga mata mari tasssss tassss kake ji…

<< Kangin Rayuwa 3

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×