Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah subahanahu wata’ala da ya bani ikon fara wannan littafi cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali, yadda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya amin, wannan labarin k’irk’irar sa akayi in yayi kama da naki ko naka ayi hak’uri rashin sani ne.
Ban aminta a canja min labari zuwa wata siga daban ba tare da izini ba!
Kafar Nasarawa, Kano State
Kasancewar yanayin damuna da ake ciki lokaci d’aya hadari ya had’o garin yayi bak’i yayi duhu sai iska me k’arfin gaske da take kad’awa, samari ne guda hud’u d’aya yana zaune a saman mota sauran ukun kuma suna tsaye a kusa dashi, kallo d’aya zakayi musu ka gano zallar rashin tarbiyya a tare dasu duba da yanayin shigar su da irin askin da yake kansu, wad’an suke k’asa a tsaye iska ta dame su sai rufe ido suke suna kare fuska da hannayen su suka kalli wanda yake kan motar yana danna waya kamar shi iskar bata dame shi ba.
“Mai gida iska tayi yawa fa gwara mu bar wajan nan kafin ruwa ya sakko” d’aya daga cikin wanda suke tsaye ya fad’a yana kallan wanda yake kan motar, bai d’ago ya kalle shi ba balle ya saka ran zai amsa masa sai ma cigaba da danna wayar sa da yayi yana d’an murmushi alamun abinda yake yi yana bashi nishad’i.
Ganin baiyi magana ba ya saka wani a cikin su ma zai masa magana d’ayan yayi saurin zaro masa ido yana girgiza masa kai alamun kada ya ce masa komai, dole suka kama bakin su sukayi shiru badan sun so ba dan sanin halin mai gidan nasu.
Bai d’ago ba bai kuma yi magana ba sai da ya gaji dan kansa sannan ya d’ago kai yana shak’ar iskar take kad’awa, saurayi ne matashi wanda bazai gaza shekara talatin zuwa talatin da biyu a duniya ba, kyakykyawa ne wanda ake kira kyau ajin farko, fari ne irin tas d’in nan me d’auke da doguwar fuska wacce take su6ul babu d’igon kurji ko tabo a jikin ta, manyan ido gare shi masu girman gaske da d’aukar hankali masu saka mutum ya shiga taitayin sa ko baiyi niya ba gasu farare tass, yana da hanci amma ba sosai ba dan baiyi wani tsaho can ba kuma bai bud’e sosai ba, bakin sa me kyau da d’aukar hankali kwantattcen gashin sa ya zagaye bakin nasa sai ya k’ara masa kyau da kwarjini.
Gashin kansa bak’i sosai duk da an aske ta anyi masa askin da ake kira low cut ita sumar ba’a aske ta duka ba kuma ba’a bar gashin ta, sai wata star guda uku da aka zana a kan nasa ta fito tarr kasancewar sa farin mutum, bud’e idon sa masu kyau yayi ya sauke su a kan wad’an da suke tsaye a kusa dashi fuskar sa babu alamun annuri ko kad’an yace, “Bana san yawan magana kun sani ku kyale ni.” ya fad’a cikin kakkausar muryar sa me firgita mutum.
Dole suka ja bakin su suka tsuke badan su so ba dan harga Allah iskar wajan ta dame su.
Sauri-sauri y’an matan suke yi duba da hadarin dake garin dole ya saka suke sauri kamar zasu tashi sama ko wacce burin ta taje gida lafiya, d’aliban makarantar yusuf mai tama sule dake unguwar k’ofar nassarawa dake garin Kano kenan da suka fito daga lecture a lokacin, y’an mata ne guda biyu da jakar goyo a bayan su suna ta sauri sunayi suna kallan sama.
Sunzo gab da wad’an nan samarin d’aya daga cikin samarin ya kalli y’an matan yace, “Kai kaga wata cika had’ad’dar gaske” ya fad’a yana kallan ta gefen haggu wacce tafi d’ayar sauri, yarinya ce dan baza ta gaza shekara sha takwas ba, sanye take da doguwar riga tayi rolling kanta da mayafin rigar, fara ce ita sosai doguwa siririyar gaske, dai-dai lokacin suka k’araso wajan motar wanda yake kallan ta yasha gaban ta yana k’are mata kallo.
Ja baya tayi sauri tana dafe k’irji dan harga Allah ta tsorata tace, “Malam lafiya?”. K’are mata kallo yake tun daga sama har k’asa yana yi mata wani irin kallo yace, “Lafiyar kenan malama.” Dirowar Zaid daga kan motar ya saka Gaye ya juyo yana kallan sa, k’arasowa yayi inda yarinyar take yana k’are mata kallo tun daga sama har k’asa, tab’e baki yayi ganin ta y’ar cili da ita kamar taliya shi bai san meyasa sam siririyar mace bata burge sa ba, yarinyar da ta gama tsorata da Gaye da Zaid ta zaro idon ta waje tana girgiza kai ganin Gaye yana nufo ta.
Juyawa tayi ganin wacce take son gani ta tawo da sauri ya saka ta da sauri ta k’arasa wajan ta tana fad’in, “Anty Ibteey kin ganshi yau ma suna biyo ni” ta fad’a a tsorace tana nuna mata Gaye da yake wani irin munafukin murmushi, wacce aka kira da IBTEESAM ta mayar da yarinyar bayan ta ta kalli Gaye tace, “Malam Lafiya?” Ta fad’a fuskar ta a tamke tana bin sa da wani irin banzan kallo.
D’ago kai da Zaid zaiyi suka had’a ido da Ibteey kafin ya d’auke kansa yana can tsaki, da confidence dinta ta nufo shi tana zuwa ta kalle shi tun daga sama har k’asa kamar yadda shima yayi mata, “mtsww meye dalilin ku na tare min k’anwa?” Ta tambaya tana binsu da kallo. Wizzy ya kalli Zaid tare da sauran abokan su kana suka dawo da kallan su ga Ibteey Gaye yace, “An tare ta d’in ko akwai uwar abinda zakiyi?” Ya tamabaya cikin muryar marasa d’a’a.
“Wallahi akuyar ku ta kiyayi rama ta in kuma tare sauran yara ku zauna lafiya wallahi baku isa ku tab’a min k’anwa ku zauna lafiya ba” ta fad’a tana nuna su da yatsa gabad’ayan su. Dukkanin su tsoro ya bayyana a fuskar su ganin tana nuna Zaid da yatsa har tana hararar sa tare da tsaki, “Ke! Dan uwar ki kin san su waye mu!?” Wanda yake amsa sunan Mugu ya fad’a yana zaro mata jajayen idon sa.
“Su waye ku banda y’an iska y’an shaye-shaye? Su waye ku banda y’an zaman banza masu tare yaran mutane kuna lalata musu rayuwa? Su waye ku in ba abinda na lissafa ba?”. A fusace Zaid ya zaro manyan idon sa masu kama da madara yace, “Kee!! Su waye y’an iskan?.” “Suku, kaine ma babban d’an iskan ma dan na lura kaine shugaban cikin su, to ba shugaba ba ko jagaba ne kai baka isa ba balle su, ku fita hanyar k’anwa ta ba yau ne na farko da waccan yake tare mata hanya ba na rantse da Allah aka sake sai na nuna muki baku da wayo, banzaye y’an iska y’an shaye-shaye, masu lalata yaran mutane” tana gama fad’ar taja wani dogon tsaki tana bin su da wani kallo taja hannun Jidda suka bar wajan.
Wizzy ne ya yunk’ura zai bita Zaid yayi saurin d’aga masa hannu alamun kar yaje, “Mai gida kana ji tana jifan ka da wad’an nan kalamai kace a kyale ta? Ka barmu da ita mu canja mata kamanni dan Allah”. Dai-dai lokacin aka fara ruwan sama a lokacin Ibteey da Jidda suka shiga keke napep bayan ta juyo ta sake sakar musu harara.
Da hannu yayi musu alama da su shiga mota, ba musu suka shiga Wizzy ya ja motar suka bar wajan, _banzaye, y’an iska, y’an shaye-shaye masu lalata yaran mutane_ kalmomin da suke yiwa Zaid amsa kuwa a cikin kunnen sa kenan, tunda Allah ya kawo shi duniya ya tsani a kira shi da d’an iska baya so ba kuma ya k’auna koda wasa, ko waye kai ka kira shi da wannan suna zai ya ci mutuncin ka sabida sunan yana k’ona masa zuciya.
“A nemo min address d’in ta da sunan ta daga nan zuwa gobe, duk wannan yayi k’okarin samowa a cikin ku yana da 200 thousands” Zaid ya fad’a muryar sa a d’an shak’e sabida b’acin ran da yake ciki, dukkan su suka amsa da an gama me gida a dai-dai lokacin da suka iso titin race course, ba wanda ya sake magana a cikin su har suka k’arasa gate d’in wani gida me bala’in kyau tun daga waje, horn Wizzy me gadin ya bud’e suka shiga cikin gidan.
Tun daga wajen zaka san mallakin gidan ba k’aramin hamshakin me kud’i bane ba duba da girman gidan da kuma motocin da suke zube a parking space d’in gidan kamar wajan saida motoci, neman waje Wizzy yayi ya faka ya kashe motar Wizzy yana niyar bud’e motar Zaid yace, “Noo kuje da ita kawai we will communicated” ya fad’a yana b’alle murfin motar yana ficewa da sauri sabida ruwan da yayi k’arfi ga magariba tayi, baban falon gidan ya bud’e ya shiga ba tare da yayi sallama ba, farin dattijo ne me kama da Zaid sak kana ganin sa kaga mahaifin sa a tsaye yana saka hula da alama masallaci zaije sabida kiran sallar da akayi yaga shigowar Zaid da sauri.
“Hii Dad” ya fad’a yana niyar wucewa sama, “Abdallah!” Daddy ya kira shi cikin taushin murya, cak ya tsaya tare da juyowa yace, “Yes Dad.” “Tawo mu tafi masallaci anyi kiran sallah.” Baiyi musu ba ya dawo da baya yana gab da zuwa inda yake Daddy ya kalle shi sosai kafin yace, “Abdallah koma sama kaje ka canja wannan d’agaggiyar rigar da wannan guntun wandon ka dawo mu tafi.” Marairaicewa yayi yana kallan kansa amma dake yana cikin yanayin b’acin rai sai Kawai ya haura saman da gudu.
Baifi 3mint ba ya sakko cikin jallabiya bak’a mai dogon hannu Daddy na ganin sa suka nufi hanyar fita tare.
Dake ana ruwa sosai dole masallacin k’ofar gidan aka had’e magariba da i’sha lokaci d’aya, bayan sun idar da i’sha ne Daddy da Zaid suka fito suka nufi cikin gidan, a falo Daddy ya yada zango ya kalli Zaid da yake niyar wucewa yace, “abinci fa?”. Yatsine fuska yayi tare da sake tamke ta yace, “noo I’m okay”. “Okay, dawo ka zauna muyi hira”. “Dad plss” ya fad’a cikin k’osawa yana had’e hannun sa waje guda.
“A’a Zaid baza ka ci abincin bane?” Wata mata ta fad’a tana fitowa daga kitchen da jug a hannun ta tana kallan Zaid, wani banzan kallo ya jefa mata bata samu matsayin ya kula ta bama yayi sama abin sa, jikin tane yayi sanyi cikin kissa ta kalli Daddy tace, “Zaid Dad wai me nayiwa Zaid ne baya sona har haka?”. Daddy ya mik’e ta tawo wajan ta da tausayawa ya karb’i Jug d’in hannun ta ya ajjiye a dining yace, “Bawai baya sanki bane Amina in kika duba Zaid yaro ne kwata-kwata nawa yake? Kuma har yanzu bai saba dake ba na fad’a miki yana da wuyar sabo sabida shi baya shiga cikin mutane yafi son rayuwar kad’aici tunda da ita ya saba.”
“Ko yaushe nayi maka magana sai kace yaro ne Zaid da ko yanzu zai iya rik’e mata hud’u kace min yaro ne? Rashin sabo kuma yau shekara ta nawa tare dakai ace har yanzu bai saba dani ba? Kawai ya tsane ni ne baya kauna ta ban san abinda nayi masa ba” ta fad’a hawaye na cikowa a idon ta. Hugging d’in ta yayi yana bubbuga bayan ta yace, “Ohhh kada kiyi kuka mana Minali na, haka yanayin Zaid yake kin sani amma zan masa fad’a kiyi hak’uri kinji?” Ya fad’a cikin sigar lallashi dan shi kansa yasan abinda Zaid yake mata baya kyautawa ko kad’an, baya kallan ta a matsayin matar mahaifin sa duk abinda yaga dama yi mata yake yi, Shiru tayi bata amsa ba tana tunanin hanyar da zata bi tayi maganin Zaid.
Zaid kuwa had’ad’dan part d’in sa da yake sama ya shiga wanda zaka iya shigo shi ta waje ba tare da mutanen falo sun san da kai ba, falon ya ratsa ya wuce kafin ya bud’e bedroom d’in ya shiga, d’aki ne babba me kyaun gaske a gyare yake tsaff sai khamshi da yake tashi a d’akin, wajan wani k’aton hoto da yake manne a bango ya k’arasa ya saka hannu ya shafi hoton yace, “Allah ya jikan ki Mama na.” Jikin sane ya kuma yin sanyi ya jima a wajan hoton kafin ya bar jikin hoton ya dawo ya zauna akan gado yana wani irin wuci sabida yadda ransa yake a b’ace.
Ya kwashe kusan mintina talatin a zaune haka babu fuskar wacce take masa yawo a ido sai Ibteesam da kalaman ta da suke barazanar tarwatsa masa jin sa, wayar sace tayi k’ara yayi banza da ita har ta katse bai d’auka ba, wani kiran ne ya sake shigowa ya d’auki wayar a fusace ganin sunan Wizzy ya saka ya d’auki wayar cikin fad’a yace, “Dallah malam lafiya ka dame ni da kira? Ka bani ajiya ne?”. Shiru yayi alamun yana sauraran me yake cewa kafin yace, “Okay ina sama” yana gama fad’ar hakan ya datse kiran ya fito falo ya zauna yana jiran Wizzy.
Bai jima ba ya shigo ya zauna idanun Zaid da suka koma ja yace, “Lafiya?”. “Mai gida na samo details d’in yarinyar nan ne shiyasa nazo na fad’a maka.” Da ido yayi masa alamun ina ji ka, “Sunan ta Ibteesam shekarar ta 22 a duniya suna zaune a cikin gari a unguwar Yakasai, mahaifin ta tsohon ma’aikacin gwammati ne basu da kud’i sosai amma suna da rufin asiri dan gidan su ma yana da girma, wacce take karewa a d’azu k’anwar tace wacce suke ciki d’aya itace k’aramaa d’akin maman su tana ji da ita sosai kasancewar tana da cutar sickler, tana karanta microbiology a Yusuf mai tama tana level 300 a yanzu, bata da kunya ko kad’an a yadda na samu labari ma a gidan su tafi kowa zafi da fad’a shiyasa bata ragawa kowa” ya k’arashe maganar yana kallan Zaid da yake danna waya kamar baya jin me yake cewa.
Sai da ya kwashe mintina sama sa biyar kana yace, “Kai a ina ka samu labarin ta lokaci d’aya haka?”. “Mai gida lokacin da na sauke su Gaye na koma na ganta a hanya napep d’in su ya lalace kasancewar ana ruwa sai suka zauna a ciki sai da ya d’an tsaya ruwan sauka suka samu wani shine nayi tracking d’in ta.”
“Good, you know what? Banda yau kada a bari ta sake kwana a gidan su i mean gobe da safe koma da yaushe ne kasan yadda kayi kayi ka d’auke ta ka kaita Naital quarters Kaduna.”
“An gama mai gida” ya fad’a yana niyar mik’ewa, dakatar dashi yayi ta hanyar fad’in, “Butt make sure to do it correctly bana so a samu wani problems.” “Insha Allah baza’a samu ba mai gida”. “U can go, and drop your account details on my inbox” yana fad’in haka ya mik’e ya koma d’aki shi kuma yayi godiya ya sauka.
D’aki ya koma ya zare jallabiyar jikin sa ya zauna akan gadon yana kallan mudubin jikin wardrobe d’in sa da yake kallan sa yace, “I will teach her lessons, I’m sure baza ta sake yiwa wani rashin kunya ba balle ta kiran shi d’an iska, zan nuna mata ni d’an iskan ne number 1 yadda ta kira ni me lalata yaran mutune tabbas itama zan lalata ta.” yana fad’ar hakan ya mik’e ya fad’a toilet.
Bai jima sosai ba ya fito d’aure da towel a k’ugun ta d’aya kuma yana rataye a kansa yana goge ruwan jikin sa, shape-shape ya shirya cikin blue colour d’in boxer me d’auke da tambarin kungiyar real madrid ya saka farar vest ya fesa turaruka masu khamshi a jikin sa, jikin dorowa ya k’arasa ya d’auki kwalin sigarin sa da leter ya fita falo, wata k’atuwar k’ofa me kyau dake can k’arshen falon ya k’arasa ya bud’e, k’atuwar varader ce wacce kana hangon gate d’in gidan duk wanda ya shigo gidan ko zai fita zaka ganshi, lilo babba wanda zai d’auki mutum biyu a ajjiye a wata y’ar rumfa da akayi a wajan sai d’an k’aramin table a ajjiye a gaban lilon, kasancewar ruwan ya d’auke sai iska da ake me sanyi da shiga jiki Zaid ya lumshe ido sanyin na ratsa shi.
Kara d’aya ya d’auki na sigarin ya kunna yana zuk’ar ta cikin k’warewa yana fesar da hayakin, dogon tsaki yaja da ya kalli k’asan gidan ganin matar mahaifin sa ta fita tana yiwa mai gadin gidan magana, zuba mata ido yayi yana kallan ta har ya gama da mai gadin ta dawo cikin gida, ya tsani ta baya san ganin ta ko kad’an, duk wani abu indai akace nata ne baya qaunar sa shiyasa yake fatan Allah yasa kada ta haihu da Daddy dan in ta haihu da mahaifin sa wacce ta haifa ta zama k’anwar sa shi kuma baya san hakan, bai tab’a jin tsanar wata a duniya ba kamar yadda yake jin tsanar ta.
“That girl” ya furta a hankali yana cize leb’en sa yana kuma zugar hayakin sa, bayan matar mahaifin sa babu wacce yake jin ya tsana kamar Ibteesama yanzu kalaman ta sun ki barin zuciyar sa gashi shi kuma mutum ne mai zafin gaske baya barin ta kwana ko waye kai kayi masa sai yayi maka,cillar da k’aran sigarin yayi ya saka k’afa ya take ya jingina da bango ya lumshe ido a hankali ya furta, “She will know the real meaning of d’an iska” yana gama furta hakan ya fita a fusace ya rife k’ofar da k’arfin gaske.
Share fisabinillah