Skip to content
Part 2 of 5 in the Series Kasaitar So by Nana Haleema

Ibteesam kuwa basu koma gida ba sai bayan magariba duk da daga makarantar zuwa gidan su babu nisa kasancewar ruwa da akeyi ga matsalar abin hawa da suka samu dole suka yi dare.

Suna zaune a babban falon gidan nasu ana cin abincin dare kamar yadda aka saba koda yaushe kowa yana cin abincin sa hankali kwance, “ke Ibteey d’azu uban wa kika yiwa tsaki?” Wata budurwa wacce bazata wuce sa’ar ta ba ta fad’a tana tsaye a kanta rik’e da k’ugu.

Banza tayi mata bata d’ago ba sai abincin ta da take ci hankalin ta a kwance,  “Ba magana nake miki bane ba?”. “Kinga Asiya ki shiga hankalin ki kar ki hasala ni daman raina a b’ace yake wallahi zan sauke miki b’acin ran nawa yanzu” ta fad’a cikin masifa tana tuna ta da yatsa.

“To sarakan fad’a za’a fara ne?” Wata mata da ta shigo falon ta fad’a tana kallan su, “Umma ina ruwan ta dani kawai ina zaune zata zo tace wai d’azu nayi mata tsaki? Ban shiga sabgar ta ba haka kawai zata ja na fasa mata baki” Ibteey ta fad’a tana kallan wacce ta kira Umma. “Asiya kiyi hak’uri mana Ibteesam ai k’anwar kice ki dinga jan girman ki gudun raini.” “Bazan ja d’in ba daman ai kece kike goya mata baya kuma wallahi…..” bata k’arasa maganar ba taji saukar mari a kuncin ta wanda ya saka ta rud’ewa lokaci d’aya, “wacece ke da zaki d’agawa uwata murya eyeee?? Rashin kunya zaki mata.”

“Kut Ibteey ni kika mara?” Asiya ta tambaya hannun ta na kan kuncin ta, sai kuwa tayi kukan kura ta fad’a kan Ibteey suka fara kokawa da iya k’arfin su, “to iyalan fad’a an fara fad’an ne?” Wani babban mutum ya shigo falon fuskar sa a had’e yana kallan Ibteesam da Asiya.

Ganin Abba ya saka suka saki junan su kowa na hararar d’an uwan sa, “yo daman indai k’arami bazai bawa babba girman sa ba ai dole aita fad’a kullum kamar karnuka” wata mata ta fad’a taba fitowa daga wata k’ofa tana jifan Ibteesam da wani irin kallo me kama da na tsana.

“Kee Asiya me ya had’a ku?” Abba ya tambaya yana kallam Asiya yana zama akan d’aya daga cikin kujerun falon, kuka ta saki kafin ta fara cewa, “Abba kawai daga nazo na same ta nace akan me d’azu ta bar makaranta bata jira mun tawo tare kamar yadda kace ba shikenan ta fara min ihu tana cewa baza ta tsaya d’in ba sai dai na fad’a maka d’in ko me zakayi kayi, dan nayi mata fad’a shine kawai ta mare ni” ta k’arashe maganar tana goge idon ta. Baki bud’e Ibteey take kallan ta duk da tasan halin Asiya ta iya makirci abinda yafi haka ma tsaf zata aikata.

“Ke Ibteesam haka akayi?” Abba ya tambaya yana kallan Ibteesam, “Abba kawai ina zaune tazo tace min d’azu nayi mata tsaki ban kula ta ba sabida bana son ina yi mata rashin kunya matsayin ta na yaya ta shiyasa na k’yale ta ban kula ta ba sai da Umma ta fito tana mata magana sai take fad’awa Umma magana mara dad’i, ni kuma harga Allah bazan jure akan fad’awa Umma magana a gaba ba ban san lokacin dana mare ta ba” ta k’arashe fad’a muryar ta a sanyaye.

“Da bamu san asalin ungulu ba sai tace daga masar take, yo ita wacce kike tada jijiyoyin wuyan a kanta ce miki akayi itace…..” “Zubaida!” Abba yayi saurin dakatar da ita yana zare mata ido kafin ya mayar da kallan sa ga yaran yace, “Kee Asiya kece babba amma bakya jan girman ki banda abinki ina ke ina fad’a da Ibteesam? K’anwar kice fa ai abun kunya ne ki dinga fad’a da ita, ke kuma Ibteesam baki da kunya bakya girmama Asiya a matsayin yayar ki dan haka bana so na sake ji ko ganin wani abu makamcin wannan kunji ko?”. D’aga kai sukayi dukkan su kafin ya kalli Ibteesam yace, “Bata hak’uri.” “Yi hak’uri” ta fad’a rai a b’ace zuciyar ta na wani irin tiriri sabida b’acin rai.

“Ku tashi ku bani waje” suka mik’e ko wacce ta nufi b’angaren babbar ta, Umma da take zaune a wajan tunda ya fara musu fad’a bata ce uffan ba hankalin ta yana kan tv, “Kee Zubaida ki shiga hankalin ki wallahi ki kuma iya bakin ki in ba so kike kiga b’acin raina ba” ya fad’a yana nuna wacce take amsa sunan Zubaida, Kawar da kai gefe tayi tana kad’a k’afa tana wani d’aga kai, tsam Umma ta mik’e ta kalle shi tace, “Sai da safen ku” bata kuma cewa komai ba ta bar wajan cikin nutsuwa, Da kallo ya bita har ta shiga b’angaren ta kafin ya d’auke ido daga kanta ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi, dogon tsakin da Mama tayi ya saka ya kalle ta da mamakin me take yiwa wannan tsakin har haka, “Aikin banza haka kawai yarinya tazo gidan uban wasu ta hana su sakewa ba dangin iya babu na baba waye ya sani ko zina iyayen ta sukayi suka haife ta an d’auko ta an k’ak’aba mana ita har tana neman tafi y’an gida matsayi” ta fad’a cikin masifa amma a hankali take maganar.

Sosai Abba ya had’e rai ya kalle ta yace, “Zubaida! Zubaida!! Zubaida!!! Sau nawa na kira sunan ki?”. D’auke kanta tayi tana wani d’aga kai tace, “uku”. “To wallahi tallahi ki kiyaye ni akan maganar Ibteesam in ba so kike igiyar auren ki tayi rawa ba”. Zaro ido waje tayi tace, “igiyar aure na fa kace? Akan wannan yarinyar?”. “Kwarai kuwa, in kina mamaki ma gwara ki daina tun kafin ki kaini ga furta abinda ban furta ba da, wallahi Zubaida wani a cikin gidan nan ko a wajan gidan nan yasan maganar nan na rantse da Allah da ya halicce ni sai na yi miki abinda baki tab’a tunani ba, shashasha mara hankali da tunani” yana gama fad’ar haka ya mik’e ransa a b’ace ya fita daga falon.

Baki bud’e ta bishi da kallo tana girgiza kai tana aiyana irin matakin da zata d’auka akan Ibteesam, a fusace ta bar falon ta shiga b’angaren ta.

Alhaji Yusuf Umar haifaffan garin Kano ne mazaunin garin Kano kuma, tsohon ma’aikacin gwammati ne yayi aiki a k’ark’ashin First bank kafin yayi ritaya, matan sa biyu Zubaida itace uwar gidan sa tun auren saurayi da budurwa ta haifa masa yara biyar, babban d’an sa shine Umar, Sadik, Rukayya, Asiya sai d’an autan ta Kamal, Zubaida mace ce wacce take shiga abinda babu ruwan ta irin matan nan ne da ko fad’a ake a maqota tsaf zata shiga ayi da ita, matar sa ta biyu itace Halisa mace ce me sanyin hali babu ruwan ta da abinda nai shafe ta ba koda yaushe tana k’okarin ganin ta k’are mutuncin ta, sau da dama Zubaida na yawan yar mata da magana amma sam bata kula ta sabida ita daman can bata saba da fad’a ba kasancewar ita kad’ai iyayen ta suka haifa ta taso gidan su shiru babu mutane, yaran ta biyu kacal a duniya daga Jidda sai k’anin Jafar, Halisa ta jima bata samu ciki ba lokacin auren su har mutane suka dinga cewa daman ita ba jinin haihuwa bace musamman y’an uwan sa tun bata damuwa har ta damu, kwatsam Allah ya kaita gidan marayu ziyara taga Ibteesam yarinyar ta kwanta mata a rai sosai ta kuma bata tausayi sai tayi shawara da mijin ta ta d’auka ta rik’e ta kamar y’ar ta a lokacin shekarar ta biyu a duniya, dangin sa suka dinga magana da yake mutum ne tsayayye tunda yayi musu jan ido akan hakan kowa ya shiga hankalin sa akan ta tunda sun san mutum ne mai zafi indai ya fad’a zai aikata, shekara biyu da d’aukar Ibteesam Allah ya bata cikin Jidda bayan ta haifi Jidda Zubaida taita zuga akan a mayar da Ibteesam tunda sun sami nasu amma ya nuna sam shi bai aminta ba.

Ibteesam na samun kulawa sosai a wajan Umman ta kasancewar ta yarinya kyakykyawar gaske hakan ya saka ta shiga ran kowa, in aka cire Umar da yake babba a gidan da mai bin sa babu wanda yasan Ibteesam ba y’ar su bace kuma ya hana a fad’a kasancewar su maza kuma koda wasa basu tab’a tunanin fad’awa wani ba dan har mantawa ma su suke.

Maryam wato Ibteesam yarinya ce fara tas kyakykyawa sosai, tana da manyan kyau dan lokaci d’aya kana kallan ta zaka gano kyauwun da Allah yayi mata, ba doguwa bace can dan tana da qiba sai qibar tata ta shanye tsahon nata sai tayi y’ar dai-dai da ita, Allah yayi mata baiwa da yawa a tare da ita wannan ya saka mahaifiyar Halisa wacce take amsa sunan kaka a wajan Ibteesam take mata lak’abi da matar manya, wannan kyauwun nata sai ya ja Asiya take bak’in ciki da hakan kasancewar ta sa’ar ta.

Ibteesam bata da kunya ko kad’an in kana so kaga b’acin ranta lokaci d’aya ka tab’a mata Umman ta da kuma Jidda kasancewar Jidda tana da stickler hakan ya saka take tausayawa mata sosai sometimes har haushin Umma take ji akan me basu yi genotype ba kafin suyi aure, bata jin magana tana da zafin zuciya yanzu zata mata abu yanzu zata rama hakan ya saka bata saurara kowa a gidan indai za’a tab’a mata uwa, Kasancewar Umma fara ce sosai sai Ibteesam ta saje da yaran ta baza ka taɓa cewa ba ita ta haife ta ba.

Alhaji Yusuf ya isa da gidan sa sosai kowa shakkar sa yake ko kara ya saka babu wanda ya isa ya tsallaka hatta matan nasa, wannan dalilin ya sanya babu wanda ya tab’a gigin fad’awa Ibteey maganar da zata nuna cewa ita ba y’ar gidan bace duk da  daman ba kowa na gidan bane ya sani.

Ibteey tana level 300 a Yusuf mai tama sule tana karanta microbiology, a islamiyya kuma ta sauke alkur’ani mai girma tare da littafai da dama, yawan ci in zata lecture yamma in ta kama ranar babu islamiyya tare suke tafiya da Jidda in ta fito dai su tawo tare, Jidda suna yawan had’uwa da Gayr in ta riga Ibteey fitowa hakan ya saka take yawan yi mata complain a kansa basu had’u ba sai a lokacin da ta yi musu rashin kunya.

*****

Washe gari da wuri Ibteey ta tashi ta gama aikace-aikacen b’angaren Umma, kasancewar ko wacce b’angaren ta falo d’aya ne da kitchen da dak’una uku ko wanne da band’aki, sai kuma main falo me d’auke da kayan kallo da kujeru saiti biyu da k’aton dining table mai d’auke da kujeru guda goma sha biyu da kitchen wanda yake ko wacce zata iya amfani dashi.

Da wuri ta gama da ciki ta dawo main falon ta gyara shi tsaf ta d’ora breakfast, bata jima ba ta gama ta jera a akan babban dining d’in, b’angaren Umma ta koma ta shiga d’akin su tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atampa d’inkin rafa yayi mata kyau sosai a jikin ta ta fito ta shiga d’akin Umma.

“Umma na kammala breakfast d’in fa” ta fad’a lokacin da take shiga cikin d’akin, da murmushi Umma ta kalle ta tace, “to y’ar albarka sannu Allah ya baki miji na gari”. Murmushi Ibteey tayi kunya ta saka ta kasa cewa amin, “yau ba makarantar ne?”. “Hmmm Umma karatu a Nigeria ko wahala an kuma tafiya yajin aikin da ba’a san ranar komawa ba.” “Tohh Allah ya kyauta, to maza ki karya anjima na aike ku gidan Dada”. Murmushi Ibteey tayi tace, “To Umma” ta fad’a tana mik’ewa ta fice daga d’akin Umma ta bita da kallo.

*****

Sanye yake cikin wando three quarter wanda ake jira da crazy irin wanda yake a tsagen nan blue colour, rigar jikin sa k’arama mara nauyi sosai itama kamar ta blue ta d’ame shi ta fito masa da duk wani cikar zatin da Allah yayi masa, kansa yasha gwara sai kyalli yake zanen kan nasa ya fito tarr.

A hankali yake sakkowa daga saman sa hannun sa rik’e da waya yana dannawa har ya sakko bai d’aga kai ba abinda yake gaban sa kawai yake yi, “Zaid an sakko?” Anty ta fad’a tana kallan sa da murmushi a fuskar sa. D’an lumshe ido yayi ya bud’e ya d’ago idon sa ya watsa shi a fuskar ta ya tab’e baki yace, “A’a ban sakko ba ina sama” yana gama fad’ar hakan ya rab’a ta zai wuce tayi saurin tare hanyar tace, “Wai Zaid me na maka ne baka sona?”

Bai magana ba sai zuba mata ido da yayi yana mata wani irin kallo me firgitawa bai magana ba ya sake rab’a ta zai wuce ta sake tare hanyar, “Daddy ka fad’awa matar ka ta daina shiga sabga ta bana san irin wannan rayuwar in ban kula ta ba ta daina cewa zata kula ni” ya fad’a cikin harshen turanci yana kallan Daddy da ya sakko daga saman sa a lokacin.

“Amina bashi hanya, kai kuma zo nan” ya fad’a yana kallan su dukkanin su, wata banzar harara ya sakar mata tare da jan tsaki ya matso kusa da Dady ya tsaya har lokacin bai daina danna wayar ba bai kuma yi magana ba, “Wai Zaid meyasa kake haka ne? Amina fa matsayin uwa take a wajan ka meyasa ka raina ta uhumm?.”  “U said matsayin uwa not My mother, Daddy i totally hate her wallahi, bana san ganin ta sam” ya fad’a yana kulle idon sa cikin b’acin rai da takaici.

“Zaid me yake damun ka haka? A gaba na kake cewa ka tsane ta?” Daddy ya fad’a cikin fad’a yana kallan sa, runtse ido yayi ya saka hannu ya d’an toshe kunnen sa yace, “Daddy why shouted me?” Ya fad’a da wata irin murya yana juya kansa. Ganin halin da ya shiga ya saka Daddy ya gigice ya rik’o shi ya zaunar dashi yace, “ayya sorry son i don’t want to hurt you, but abinda kake yiwa Amina baka kyautawa Uwa ce a wajan ka tunda matata ce ko gaishe ta baka yi fa.” “Daddy kasan bana k’arya in na fad’a maka akasin abinda na fad’a a kanta k’arya nayi maka, na tsane ta kawai bana so na ganta bana tunanin kuma zan so ta har na d’auketa matsayin uwa ta” yana fad’ar hakan ya mik’e zai bar falon Daddy yace, “Zaid!” Da sauri ya juyo yace, “please Daddy” yana fad’ar hakan ya saka kai ya fice daga falon.

Kallan Amina Daddy yayi da take tsaye tayi tagumi tana kallan su, duk sai yaji wani iri a gaban ta d’an da take da iko dashi yake cewa ya tsane ta duk sai jikin sa yayi sanyi ta bashi tausayi sosai, zaiyi magana aka bud’e k’ofar falon aka shigo.

Mayar da kansa yayi ga k’ofar ganin masu shigowa ya saka gaban sa ya fad’i ya kalle su yana fad’in, “A’a Yaya kune tafe?” Ya fad’a yana k’arasowa kusa dasu. “Eh mune Abubakar tunda kai baka zuwa inda muke ai mu gashi munzo” ya fad’a yana sab’a babbar rigar sa yana zama akan kujera.

Zama shima Daddy yayi ya kalli yayyen nasa da k’anin sa yace, “Ina kwanan ku.” “Lafiya, kai mu ba wannan ba a kawo mana abinci muma muci arzuki ko ba haka ba?” Wanda ya fad’a ya tambayi na zaunen, “gaskiya kuwa Yaya”.

Kallan Amina yayi da take tsaye yace, “Amina kawo musu abin breakfast”. Ba musu ta juya ta koma kitchen. Bata jima sosai ba ta dawo bayan ta sako hijjabi d’auke da k’aton tray ta ajjiye ta koma ta sake kawo wasu kayan ta kuma ajjiyewa kafin ta koma falon ta, bajewa sukayi suna shan tea da madara dan wanda suke zuba madarar kana gani kasan harda mugunta a ciki.

K’ofar aka bud’e Zaid ya shigo hankalin sa na kan wayar sa kunnen sa kuma ya manna Bluetooth yana sauraran waka, har ya wuce Daddy yace, “Zaid baku gaisa da uncles d’in ka ba” ya fad’a yana kallan Zaid d’in.  Juyowa yayi ya kalle su ya tab’e baki yace, “Heyyy Uncles” yana gama fad’ar hakan ya d’aga k’afa da niyar tafiya.

“Da kai da heyyy d’in kunci uwar ku” Babban yayan Dady Uncle Sani wanda ake kira da wanda su Daddy suke kira Yaya Babba ya fad’a yana kallan Zaid rai a b’ace.  Da sauri Zaid ya juyo ya cire Bluetooth d’in kunnen sa ya kalli Uncle d’in nasa cike da tsana da tsantsar jin haushin sa yace, “You said what?”. “I said kunci uwar ku kai da heeyy d’in” ya sake fad’a bayan ya cika bakin sa da wainar kwai.

“Wato Abdullahi shaye-shayen naka haka ya mayar da kai? Dan tsabar iskanci mu zaka kalla kace mana wani heyy? Uwar kace heyy d’in? Nace uwar kace hiii d’in dan uban ka Abubakar, dan ka raina mu da wannan kayan jikin naka zaka zo kace mana wani Heey, to da uban ka Abubakar kame” wanda yake bin Babban Yaya ya fad’a yana yiwa Zaid dak’uwa. Cize baki Zaid yayi ya zaro manyan ido sa da suka fara canja launi sabida b’acin rai yace, “Don’t insulting me again” ya fad’a yana zaro musu manyan idon sa.

“In an kuma zagin naka uban me zakayi? Tsigagge mara kunya mara tarbiyya,? Kaga d’an iskan yaro giya da kwaya ta tab’a masa kwakwalwa yana zagin mu” k’anin Daddy ya fad’a shima a fusace yana kallan Zaid.

Zaid ya kai matakin k’arshe a b’acin rai zuciyar sa sai k’ara harzuk’a take jikin sa ya soma rawa idon sa ya fara fitar da wani irin ruwa na b’acin rai, a fusace yayo kan su yana neman kaiwa k’anin Daddy duka. Daddy ya mike da sauri yace, “Zaid!” Ya fad’a a fusace yana kallan sa.

“Are u in sense Zaid? Y’an uwan nawa kake fad’awa wannan maganar? Da ka tawo a fusace dukan su zakayi? Daddy ya fad’a a fusace cikin fad’a da k’araji.

“Daddy meyasa baka hana su zagin na ba? Kana ji suna cemin d’an iska d’an shaye-shaye and suna kuma zagin Mama duka baka hana su ba sai ni zaka hana d’auka hukunci? in ban sab’a musu kamanni ba hankali na bazai kwanta ba” ya fad’a yana yo kansu gadan-gadan.   “An fad’a maka d’an shaye-shaye in ka isa kazo ka dake mu dan uwar ka Maryam!” Uncle sani ya fad’a yana kallan sa da b’acin rai.

Ai bai san lokacin da ya d’auki glass cup da yake kan center table d’in ba ya cillawa Uncle Sani a kansa, sunkuyawa yayi kofin ya bugi bango ya tarwatse a wajan, tasss Daddy ya d’auke Zaid da mari shima ransa a b’ace, baki kawai Zaid ya bud’e yana kallan Daddyn nasa idon sa a waje jikin sa na wani irin rawa yace, “Da…ddy…. you…slapped me…?” Ya fad’a a rarrabe bakin sa na wani irin rawa, bai jira amsar Daddy ba ya juya a fusace ya haura sama da gudu.

Jikin sa har rawa yake wani irin zafi yake ji duk da a.c da take falon nasa amma tsiyaya yake kamar an fito dashi daga oven, hannun sa har rawa yake ya d’auko waya ya danna kira, daga can b’angaren Wizzy ya d’auka yace,”Hello mai gida”. “Wizzy where are you?” Ya fad’a muryar sa na wani irin shaking, “ina kan aikin da ka sani, mai gida lafiya naji maganar ka haka?” Ya tambaya a rud’e.

“Duk wanu thugs da ka sani ka tattaro su yanzu kuzo kusa da gidan mu, akwai wanda zasu fito yanzu daga gidan mu tare su ku jasu inda babu mutane ku wahalar dasu kar ku tausaya musu” ya k’arashe fad’a cikin k’araji tare da zubewa akan kujera.

“An gama mai gida” yana gama fad’ar hakan ya kashe wayar ya fara lalubo number y’an daban da ya san sun kware a fannin dabanci da rashin imani dan yadda yaji muryar mai gidan nasa yasan sun b’ata masa rai da yawa dole suma a b’ata musu.

Comments and share fisabinillah!

<< Kasaitar So 1Kasaitar so 3 >>

1 thought on “Kasaitar So 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.