Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Kasaitar So by Nana Haleema

Amina ta gyara zama ta kalle su dukkanin su tace, “Batun aurawa Zaid Eman fa bai tashi ba, na rantse muku da Allah Zaid zai iya kashe Eman indai aka ce an aura masa ita, wannan zafin zuciyar tasa tsaf zai hallaka ta wallahi kunga kenan a garin neman gira zamu rasa ido, ya wuce duk inda kuke tunani gwara ku canja shawara amma kuma in kun shirya rabuwa da Eman d’in ne to bismillah” Amina ta fad’a tana d’age kafad’a alamun ko a jikin ta.

“Tabbas Maganar Amina gaskiya ce Yaya mu fara gabala akan sa da halayyar sa tukunna kafin mu kai ga aura masa ita d’in, yanzu mubar batu akan kawar dashi mu koma batu akan ta yadda za’ayi mu jawo shi jikin mu ya shak’u damu wannan zafin kan nasa ya ajjiye shi ta yadda muna bashi umarni zai bi kaga sai muyi amfani da damar mu aura masa Eman d’in.”  Amina tace, “Ina bayan maganar Yaya Bala nima abinda yace shi ya kamata ayi a yanzu.”

Ajiyar Zuciya Uncle Sani yayi yace, “Shikenan ayi hakan, zamu canja masa taku yanzu kowa ya b’oye tsanar da take ransa, ke kuma Eman ki san yadda zakiyi ki cusa kanki gare shi zan baki wasu turaruka ki dinga amafani dasu in zaki inda yake” ya fad’a yana nuna ta da tsaya.

Haka suka gana tattauanwar su kafin kowa ya watse ya kama gaban sa.

*****

Hankalin Umma ya tashi sosai na rashin dawowar Ibteesam gashi har magariba tayi, waya ta d’auko da take caji ta kira number mahaifiyar ta buga d’aya aka d’auka tare da sallama, bayan sun gaisa ne Umma take cewa, “Dada Ibteesam a nan zata kwana ne?”. Daga can b’angaren Dada tace, “Ibteesam kuma? Ai bata zo gidan nan ba.” Damm gaban Umma ya yanke ya fad’i murya na rawa tace, “Dada tun kafin azahar fa na aiko ta kawo miki dambun nama sai nace mata in dare yayi ta kwana a wajan ki to naga bata kira ni ba har yanzu na kira wayar ta kuma a kashe.” “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, ai kuwa Ibteesam bata zo gidan nan ba Halisa.”

“Dada to ina taje?” Umma ta fad’a a gigice tana shirin sakin kuka, “Kinga kwantar da hankalin ki Halisa, ki kira wayar k’awayen ta da kuma y’an uwan ta ko taje can.”

“Dada Ibteesam bata zuwa ko ina sai ta sanar dani da zata je da ta fad’a min.”  Ajiyar zuciya Dada tayi dan itama ta tsorata da lamarin amma sai ta danne dan gudun tashin hankalin Halisa yasa tace, “ba kin ce wayar ta a kashe ba? Wata kila rashin caji ya saka bata kira ki ba ki nutsu kiyi tunani” Dada fa tana kashe wayar dan ta fara jiyo sautin kukan Halisan.

Shigowar Abba b’angaren nata da sallama yasa ta nufe shi cikin kuka take fad’in, “Ibteey har yanzu bata dawo ba na kira Dada taje bata je can ba” ta fad’a a rud’e tana nuna masa hanyar k’ofa.  “Halisa nutsu kiyi kin bayani ina Ibteesam d’in? Zauna kiyi min bayani” ya fad’a yana rik’e hannun ta yana zaunar da ita akan kujera.

“Tun kafin azahar na aike ta gidan Dada har yanzu bata dawo ba na tambayi Dada tace min bata je bama gabad’aya” Umma ta fad’a a gigice cikin kuka.

Jimm Abba yayi kafin yace, “kuma bata je gidan y’an uwan ta ko k’awayen ta ba?”. “Inda zata je zata sanar dani bata zuwa ko ina ba tare da izini na ba.” “Shikenan kwantar da hankalin ki bara na kira y’an uwan ta muji ko taje ki daina kuka dan d’an.” Share hawayen tayi tana sauke ajiyar zuciya Abba ya kira yaran gidan kaf amma babu wanda yace yaga Ibteesam ma balle taje gidan sa, zuwa lokacin shi kansa Abba ya tsorata amma sai ya b’oye baya so ya nuna ya sake karyawa Halisa zuciya.

“Kaji bata je, innalillahi wa’inna ilaihir raji’un ina Ibteesam take? Ina ta shiga? Ya Allah ka bayyana min wannan baiwa taka cikin k’oshin lafiya” ta fad’a tana kuka mai tsuma zuciya.

Jiddah da Jafar ma kuka suke sosai ganin Umman su na kuka gashi kuma ana cewa ba’a ga Ibteesam ba, “ku daina kuka yanzu zanje na duba ko Allah ya saka mu ganta” Abba ya fad’a yana mik’ewa ya fice daga falon nata.

A cikin daren nan duk inda ake tunanin za’a ga Ibteesam ba’a ganta ba hankali ya tashi sosai kawai sai aka k’addara anyi kidnapping d’in tane.

K’arfe goma na dare Abba ya dawo gidan ya tarar dasu a babban falo sunyi jugum-jugum, sai da ya samu waje ya zauna kafin yace, “duk inda muke tunanin zamu ga Maryam bamu ganta gashi dare yayi balle muje gadaje radio mu bada cigiyar ta sai dai gobe in Allah ya kaimu” Abba ya fad’a a sanyaye. Shiru falon yayi babu abinda ake ji sai sautin kukan Umma da Jidda, “Ki daina Kuka Halisa za’a ganta insha Allah” Mama ta fad’a tana kallan Umma da tausayawa, duk da bata san Ibteesam amma taji babu dad’i tana kuma tausayawa Umma.

Yaran Abba ya kalla yace, “Ku tashi kuje ku kwanta dare yayi, Jidda ki bar wannan kukan haka addu’a zaki taya ta da ita”. Dukkan su suka mik’e kowa ya shiga b’angaren mahaifiyar sa.

Mama da Abba suka dinga rarrashin Umma suna bata baki har ta tsaida kuka ta mik’e ta shiga b’angaren ta.

Washe gari.

Kaduna

Ibteey ce a kwance a cikin wani k’aton bedroom mai kyau tana bacci a hankali, har lokacin hodar da aka watsa mata bata sake ta ba bacci kawai take yi, Wizzy yana zaune a falo yana canja cannel d’in tv yaji k’arar bud’e gate, da sauri ya mik’e ya lek’a ganin wanda ya shigo ya saka ya bud’e k’ofar ya fita da sauri. Sai da Zaid yayi parking d’in motar kana ya fito ya kalli Wizzy yace, “I hope komai normal?”. “Mai gida ina fa normal yarinya tun jiya take bacci har yanzu bata farka ba” Wizzy ya fad’a a d’an tsorace yana kallan Zaid, Gaba yayi Wizzy ya bishi a baya kafin yace, “ba wani abu bane ba jinin ta bashi da k’arfi sosai” ya fad’a yana nufar saman dake steps d’in sa suke mak’ale a falon.  

Wizzy yana bayan sa suna hawa saman hannun sa rik’e da jakar Zaid d’in suka k’arasa k’ofar d’akin da yake mallakin Zaid, har ya rik’e handle d’in k’ofar zai shiga ya juyo ya kalli Wizzy yace, “A wanne d’aki take?”. Da hannu ya nuna masa wanda yake d’an nesa da nasa kad’an, baice komai ba kawai ya shiga d’akin Wizzy ya take masa baya.

Jakar ya ajjiye kafin ya juya ya fita shi kuma ya fad’a band’aki. 

A hankali take bud’e idon ta da suka yi mata wani irin nauyin gaske, biyu-biyu take hakan ya saka ta kasa tantance a inda take tayi saurin runtse idon ta bud’e s hankali ta fara gani sosai har idon ya bud’e tarrr, da sauri ta mik’e zaune tare da dafe kanta sabida nauyin da yayi mata, wani irin ciwo dukkanin jikin ta yake mata wuyan ta ya sage sosai kamar wacce ta d’auki buhun gero a kai.

A hankali take tuna abinda ya faru ai da sauri ta diro daga kan gadon tana mik’ewa tsaye ta saki wata irin k’ara sabida yadda k’afar ta tayi wani irin tsami take ji kamar ana soka mata kibiyoyi a ciki, da sauri ta koma ta zauna tana runtse ido sabida zafin da k’afar ta take mata.

Zaid da ya fito daga wanka ya jiyo k’arar baiyi wani gaggawar zuwa ba sai da ya shirya tsaff sannan ya fito daga d’akin ya leko k’asa ta wata taga yace, “Wizzy”. Wizzy najin haka ya mik’e ya hau saman da sauri yana amsawa, “waccan yarinyar ta tashi naji ihun ta, ina matar da take abinci a nan?”. “Tana k’asa mai gida.” “Okay ina kayan nan?”. “Suna d’akin ka”. Baice komai ba ya juya kawai ta koma d’akin shi kuma Wizzy ya koma k’asa. 

Ibteesam kuwa dak’yar ta samu ta mik’e taci sa’a k’afar tata ta daina mata zafi ta bud’e kofar da take tunanin band’aki ne dan a matse ta farka, ta jima sosai a band’akin kafin ta fito kamar yadda ta shiga sai dai ta wanke bakin ta da sabob brush d’in da ta gani. Dawowa tayi ta zauna ta buga uban tagumi tana tunani a ina take? Sai kawai ta mik’e ta bud’e k’ofar ta fito daga d’akin, falo ta gani mai kyau madaidaici wanda aka zuba masa kaya masu kyau da d’aukar hankali, kalla take sosai tana so taga ko tasan gidan amma babu alamun hakan, “a ina nake? Su waye suka kawo ni nan? Dan Allah kuyi hak’uri kuzo ku mayar dani gidan mu?” Ta fad’a tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

Wizzy da ta jiyu ta ya hauro saman fuskar sa a tamke ya kalle ta itama shi take kallo dan ta gane shine wanda ya zuba mata powder d’in, “Dan Allah ina ne nan? Me nayi maka ka d’auko ni?” Ta tambaye shi tana kuka sosai.  “Dalla malama rufewa mutane baki ba’a yi mana ihu a gidan nan kin ji ko?” Ya fad’a a fusace yana zaro mata jajayen idanun sa.

Shiru tayi jikin ta na rawa dan ta tsorata dashi sosai a tunanin ta masu garkuwa da mutane ne, “in kina da dama ki tashi kije kiyi sallah dan yau ba Juma’a bace asabar ce, asabar d’in ma azahar tayi kinga kenan ana binki salloli da yawa” yana gama fad’a mata haka ya juya ya sauka da bai sake kallan inda take ba. Da sauri ta mik’e ta koma d’akin tana salati, sai da tayi wanka sannan tayi alwala ta fito ta tayar da sallar azahar din jiya, tana yi tana kuka har ta idar duka tayi addu’a sosai kafin ta koma jikin gadon ta takure kanta na mata ciwo.

Bud’e k’ofar da akayi ya saka ta zabura ta kalli k’ofar da jik’akkun idanun ta, Wizzy ne ya shigo hannun sa d’auke da tray na abinci ya ajjiye mata yace, “Ga abinci nan” ya fad’a yana niyar juyawa. 

Duk da tana jin yunwa amma hakan bai hana tace, “Bana ci tunda baza ka fad’a min kai waye ba, ba kuma zaka fad’a min abinda nayi maka har ka kawo ni nan ba, ka kwashe abincin ka bana ci” ta k’arashe fad’a a tsawace tana cike da rashin kunya, Juyowa yayi ya kalle ta ya tab’e baki yace, “oho yunwa ai ba k’anwar uwa bace haka ba  k’anwar uba ba balle ta tausaya miki” yana gama fad’ar hakan ya bud’e k’ofar yayi ficewar sa.

Komawa tayi ta jingina da Gadon cikin ta na wani irin murd’awa sabida yunwar da take ji, sake Bud’e k’ofar akayi ya sake shigowa ya cilla mata wata leda yace, “Ga riga nan ki canja” yana fad’ar hakan nan ma ya rufe d’akin. Hannu ta saka ta bud’e plate d’in da yake gaban ta, doya kwai ne da da soup a kan plate d’in, wani ta Bud’e shi kuma chip’s ne da ketchup, sai wani d’an k’aramin flasks d’in tea da kuma kayan shayin.

Tea d’in kawai ta had’a tasha shima black babu komai ta ture kayan ta cigaba da kukan ta.

Tana zaune a wajan har akayi la’asar zuwa lokacin ciwon kan nata ya k’aru ga jikin ta d yake mata ciwo kamar duk ya sage kamar wacce tayi wani aiki mai yawa, a zaune tayi sallar la’asar bayan ta idar ta kwanta a wajan tana sauke nufamshi ga wani zazza6i da yake neman kama ta.

Wizzy ne ya lek’o ya ganta kafin ya koma ya tarar da Zaid ya zaune yana danna waya yace, “Mai gida yarinyar can fa bata da lafiya”. Shiru yayi bai amsa ba sai daga baya yace, “Ciwon jiki daman zai dame ta da kuma ciwon kai, a kai mata magani” ya fad’a ba tare da ya d’ago ba.

Maganin ya d’auka ya bud’e d’akin da Ibteesam d’in take yace, “Ke tashi ga magani nan kisha” ya fad’a yana cillo mata inda take ya koma inda ya fito, Jikin ta na rawa ta b’alla maganin tasha ta koma ta kwanta.

A hankali take jin ciwon kan yana raguwa har ta samu ya sauka sai jikin ta da babu dad’i kawai, yunwa take ji sosai amma tayi alqawarin baza taci abinci ba sai taji dalilin sato ta da akayi, a haka ta daure har i’sha bata ci komai ba sai dai ta mik’e tayi sallah ta koma ta kwanta.

Tana kwancen Zaid ya shigo d’akin hannun sa rik’e da leda mai d’an girma, da sauri ta mik’e zaune tana zaro ido waje tana kallan Zaid da fuskar nan take kamar hadari babu alamun d’igon fara’a a tare da ita ya ajjiye kayan ya kalli abincin da aka shigo mata dashi na rana dana dare duka suna nan bata tab’a ba, d’ago ido yayi suka had’a ido tayi saurin kawar da kanta jikin ta ya fara wani irin rawa kamar an jona mata wutar lantarki, tsoro da fargaba ds tashin hankali suka tarar mata a lokaci guda.

Dariya ta bawa Zaid ganin yadda ta tsorata kamar ba itace tayi masa rashin kunya ba amma sai ya sake tamke fuska ya zaro mata ido yace, “Welcome, yau gaki a hannun d’an iska d’an shaye-shaye mai lalata yaran mutane” ya fad’a a hankali yana kallan ta tare da nufo inda take cikin d’aurewar fuska, duk taku d’aya da yake yi zuwa inda take ji yake kamar saukar masa da tsanar ta ake yi a zuciyar sa.

Jikin Ibteesam ya fara rawa ta zaro ido waje sai yanzu ta gano inda ta sanshi hankalin ta ya tashi ta mak’ale a jikin gado tace, “dan Allah kayi hak’uri ka yafe min ban san kai da gaske d’an iskan bane da ban fad’a ba.” Sake ware manyan idon sa yayi jin abinda tace ya kalle ta yayi k’wafa yana sake matsowa inda take a hankali, “me zakayi min to?” Ta tambaya tana kuka tare da toshe bakin ta, banza yayi mata bai amsa ba sai tsayawa cak da yayi kawai yana kallan ta cikin tsana da jin haushi, “wayyo Allah dan Allah kar ka min komai na rok’e ka!” Ta fad’a cikin ihu tana sake mak’alewa a bango.

Hannu biyu ya saka ya dafe kunnen sa yace, “shiiiiii” ya fad’a da k’arfi yana runtse idon sa, Hannu ta saka ta toshe bakin ta tana girgiza kai tana cigaba da zubar da hawaye, “ban d’auka zaki bada hak’uri haka da wuri ba ai na d’auka baza kiji tsoron d’an iska d’an shaye-shaye ba” ya fad’a muryar sa a ciki yana cigaba da nufo ta, “Kayi hak’uri dan Allah kar ka min komai kaji?”. D’an lumshe ido yayi ya bud’e yace, “Babu abinda zan miki kawai kema zan mayar dake y’ar iska ne kamat.” Hannu ta d’ora a ka ta zaro ido waje tace, “Na matsayin Annabi kayi hak’uri wallahi ni ba y’ar iska bace.”

“Ni kuma kinga d’an iska ne dan haka daga yau ki fara lissafa kanki a matsayin karuwa dan baza ki bar gidan nan ba sai na mayar dake karuwa mai lasisi” ya fad’a da tsawa b’acin ran sa yana k’ara k’aruwa tsanar ta kuwa kamar zuba masa ita ake yi a zuciyar sa, ji yake kamar ya shak’e ta ta bar duniya.

Cikin tsoro da tashin hankali da fargaba tace, “Kayi hak’uri dan Allah, kuma wallahi ina da ciwon HIV kar na goga maka” ta fad’a tana masa wani irin kallo mai nuni da zaka yiwa kanka, duk da b’acin ran da yake ciki sai da yayi murmushin gefen baki ya kalle ta ganin wai shi zata yiwa wayo, d’age gira d’aya sama yana kallan ta tare da tab’e baki yace, ” kar ki damu ke kina da HIV ni kuma ina da condom so ba wani abun d’aga hankali bane” ya fad’a yana nufar ta gadan-gadan ganin yadda ya nufo ta ya saka ta saki wata gigitacciyar k’ara. 

Comments and fisabinillah ❤️🙏🥰

<< Kasaitar So 4

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×