Washegari suka tafi, Umaimah ta bar Kauthar cikin zuzzurfan tunanin maganganun da tayi mata.
Sai a lokacin da suka je wajen aiki ne ta fahimci lallai zancen Umaimah akwai kamshin gaskiya a tattare da shi. Matan ofishin tun daga kan musulmai da kiristoci, suna ta karakaina da zarya a sashen nasu duk akan dalilan da basu taka kara sun karya ba, sai su fake da sunan aiki.
Duk kuwa da yadda shi gogan ya nuna kamar ma hakan bai dameshi ba sam, kuma bai lura da manufarsu zuwa gareshi ba, hakan bai sanyaya ran Kauthar ba ko kadan.
Da ta daga computer dinta, taga sakonnin da wadda ya kamata ace mahaifiyarta ce ta dinga turawa mahaifinta, ta duba hotonsu ita da Anty Ummy a wayarta, sai taji ai AbdulMalik karamar matsalace a bayan matsalolin dake dabaibaye da ita.
Sai ta tattarashi da sauran shirgin yanmatan dake karakaina a kanshi, ta jefa su a can bayan ranta. Da zaryarsu ta isheta, musamman data hangi wata receptionist dinsu Ade, ta haya saman ta tsaya a gabanshi da dan mini skirt dinta daya tsaya mata a tsakiyar cinyoyi, ga wata yar latsitsiyar riga data sanya, rabin kirji a waje da dantsen hannu. Ta kuwa rukufa yadda zai hangi halittun kirjin nata sosai. Shi kuma kanshi a kasa yana nazarin abinda ta kai mishi rubuce a takarda, har ta gama bayaninta ta juya tana kara juya mishi kugunta bai daga kai ya kalla ba.
Kauthar tayi kokarin danne murmushin mugunta daya ziyarceta a lokacin data ga yadda Ade ta fita daga ofishin ranta a bace tana muzurai, amma hakan ya gagara.
Don haka ne ma ta rufe nata ofishin kawai don ma kada taje ta hangowa kanta abinda zai fi karfinta.
Kan kujera ta dan shingida saboda bata da aiki sosai ranar, hannunta dafe da mararta inda take ji tana mintsininta. Karshen watanta ya kama, ranta cike yake da taraddadin abinda watan zai je mata dashi.
Lokacin da aka tashi yin lunch break ma bata fita ba, tayi zamanta a cikin ofis dinta tana kokarin kammala ayyukan da take dasu.
Ganin haka sai yayi mata take away lokacin daya fita ya ci abinci, daya koma ofis din ya sameta tana sallah sai ya ajiye mata ya fita.
Da aka tashi haka suka koma gida kowa yana sake-sake a cikin ranshi. Tsaf ya kula da yadda take ta dafe fuska tana yatsina fuska, yasan wannan karon ma wata dambarwar ce za a sha amma ganin kamar bata son yin maganar, sai shima ya basar.
Ranar ko abinci bata iya ci ba, sai madara data sha itama sama-sama ta tafi ta kwanta.
Tun a lokacin take gwagwarmaya sai kace mai nakuda, tafi-tafiya ta kasa daurewa can cikin dare sai data kai ga ta tasoshi daga barci. Haka suka yi ta kaiwa da kawowa har goshin asubahi kafin wani azababben barci ya dauketa.
Ya gyara mata kwanciya a kan gado daga rub da cikin da tayi, ya dauki bargo ya ware ya lullube mata jiki dashi.
Komawa yayi ya zauna yana kallonta, tausayinta lullube da ranshi. Duk da cewa yasan lalurorin mata irin wannan tunda yana ganin su Na’imah da Umaimah suna yi, amma na Kauthar ya bambanta da nasu nesa ba kusa ba. Wahala take sha kwarai da gaske.
Wannan dalilin yasa yana sallame sallah ya lalubo Dr. Amanda a waya, da korafi da neman shawarar abinda ya kamata yayi. Ta zauna ta zana mishi dogon bayani akan lalurar, da abinda yake haddasata da wanda yake warkar da ita duk da cewa shima ba wai tana da tabbacin hakan bane dari bisa dari. Ya mata godiya ya kashe wayar kafin ya fada bandaki.
Wanka yayi a gurguje, jikinshi yayi tsami saboda rashin barci. Ya shirya cikin wani farin voile mai taushi, ranar bai dora hula a kanshi ba sai sumarshi daya taje ya shafa mata mai.
Har lokacin Kauthar barci take yi, don haka ya balli takarda ya rubuta mata cewa ya tafi wajen aiki, yayi kari ya tafi.
Ita kam sai wajen karfe goma sha daya ta farka. Babu ciwon amma jikinta babu kwari, haka ta lallaba tayi wanka da ruwan dumi. Ta shafa lotion din aloe vera da Shea butter, ta gyara jikinta.
Riga da wando masu taushi ta sanya, ta dora hula ta rufe kanta kafin ta fita falo.
Karyawa tayi sosai, duk da cewa bakinta babu dadi amma yunwa sosai take kwarzabarta.
Tana gamawa ta koma daki, kamar kullum, layin Anty Aisha ta lalubo tana kira amma kamar kullum baya shiga. Wani abu ya makale mata a makoshi har taji kwalla tana cika mata idanu, sai tayi ta maza ta danneta.
Ta rasa wa zata tuntuba ta kira a cikin abokanta ko dangi. A lokaci irin wannan kwarai take kewar rashin abokai da dangi. Da ace tasan dangin mahaifiyarta da yan uwanta, ina zata zauna tana kame-kamen wanda zata kira? Da taga kadaicin zai mata yawa, sai ta kira Hajiya Hadiza, sun jima suna hira duk da cewa Hajiya Hadizan ce tafi janta da hira saboda ba wani sabawa suka yi da Kauthar din ba dama can.
Rashin abokin hira yasa Kauthar ta bare baki tana ta zuba mata hira, har ta gangara kan rashin lafiyar da take yi da yadda bata yi barci ba.
Hajiya Hadiza tayi shiru tana saurarenta har ta dasa aya, bata tari nunfashinta na sai data gama sannan ta tambayeta,
“naji kamar kina cewa ba daki daya kuke kwana dashi ba?”
Sai tayi kus tana rarraba idanu kamar wadda ruwa ya cinye.
Tace, “wato dama da kike cewa ba zaman aure zaki yi ba da gaske kike ko? Ke yanzu in banda hauka da shirme irin naki ma, wa yake sake da aure a wannan zamanin? To idan ma tunanin kashe aure kike yi, to ki san da sanin cewa daga ni har mahaifinki bamu maraba da hakan, kuma sai dai ki nemi wajen zama!”
Duk sai taji ta tsargu, amma sai ta dake, tayi narai-narai da murya, “to ni don Allah me ma ya kawo wannan zancen? Ni fa baki ji nace miki bana kwana a dakinshi ba.”
Tayi sauri ta katseta, “iyayenki nace Kauthar! Karamar yarinya kike so ki maidani kenan? To idan ba rashin kwana a daki daya ba me ya kawo miki ciwon da kike yi? Ko baki da labarin idan dai da har da gaske kuna kwana tare kuma da alakar aure, da ba zaki yi wannan ciwon ba? Kinga ma kenan hakan yana nufin kawai kallon-kallo kuke da juna!”
Kauthar dai ta rasa ina zata jefa kanta taji sanyin muzancin data shiga, tayi dana sanin kiranta yafi a kirga.
Cikin in-ina ta hau cewa “ni… fa ban ce miki… hhaka ba… kuma ma sai anjima.”
Tace, “ke dai kika sani, wanda ya gyara dai ya sani. Zaman aure ke kike yi, idan kin gyara kanki, idan ma kin bata kanki, ke kika jiyo. Allah ma ya taimakeki kika samu wanda kike rainawa wayau har ya kyaleki, wannan zamanin wa yake iya wannan aikin?!”
Ta dai samu ta mata sallama a diririce, ta kashe wayar tayi jifa da ita. Ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, Hajiya Hadiza ba dai iya kora bayani ba. Ko ina ruwanta da rayuwar aurenta? Ita dai ba tana can Saudiyya ba abinta tana hutawa ba?
Dan tsaki ta ja a karo na barkatai, ta daga drawer ta kusa da gado ta janyo wani album. Hoton data dauko a dakin Daddy ta bude tana kare mishi kallo, duk iya tunaninta da wasa kwakwalwa da take yi, ta kasa gano mu’amalar dake a tsakaninsu. Komi ya tsaya mata cak, ta rasa zaren kamawa.
Ranar haka ta wuni tana kame-kame da kiraye-kiraye. Bata kara cin komi ba sai tangerine data yini sha har zuwa lokacin da AbdulMalik din ya dawo.
Kamar ko yaushe sai daya fara lekawa ta dakinta, ya sameta zaune a tsakiyar gado, ta mike kafafu yayinda ta saka laptop dinta a tsakanin kafafun nata da glass a idanunta fari tana ta danne-danne cikin sauri kamar tashin duniya.
Ta daga ido a nutse tana kallonshi ba tare data dakata da abinda take yi ba, yace, “jiki yayi sauki sosai tunda har kina aiki?”
Tace, “da sauki sosai Alhamdulillah”
Ya gyada kai, “Masha Allah, haka ake so ai!”
Daga haka ya maida kofar ya rufe ya wuce dakinshi.
Da dare suna falo bayan sun gama cin abinci, yana zaune kan kujera yana kallon labaran talbijin, ita kuma tana kasan carpet a zaune tana ta latse-latsen kwamfutar dai.
Gabanta plate din gullisuwa ne data sa aka mata. Ta ki cin komi sai cin abubuwan kwadayi kawai take yi.
Ya dauki remote yana rage volume din TV.
Ce mata yayi, “munyi waya da Amanda dazu game da wannan yawan ciwon da kike yi, kin san me tace?”
Bata amsa ba sai daga kai da tayi tana kallonshi alamun tana saurarenshi.
Ya rausayar da kai gefe, “cewa fa tayi saboda ni dake we are not equal har yanzu ne shi yasa kike yawan ciwon nan…”
Ya zame daga kan kujerar da yake kai ya zauna a gabanta zaman rakumi, ya kamo hannunta cikin nashi yana shafawa a tausashe,
“…Shine nace, me zai hana ba zaki hakura haka nan ba Kauthar, ki daure muyi zamanmu na aure kamar sauran ma’aurata? Wannan kadai na roki kiyi mun, ni kuma in Allah Ya yarda nayi miki alkawarin zama duk wani abu da zaki bukata da ma wanda baki bukata ba a rayuwarki. Zan so ki, zan kaunaceki, zan tattaleki Kauthar fiye da tunaninki!”
Tayi maza ta cune fuska jin irin kalaman da yake. mata, duk da cewa maganganun nashi sun tsumata kwarai da gaske.
Hannunta ta fara kokarin janyewa, “a’ah! Ni da ban ce maka ina son zaman aure da kai ba meye na kawo min wasu maganganun kabli da ba’adi kuma? Ai na fada maka ba zaman aure nazo yi ba, kace mun kaji ka gani a hakan, to kuma me kake so inyi maka?”
Cikin karaya da ita ya daga baki yana mai ambatar saunanta, “Kauthar…!”
Sai tayi gaggawar katseshi, “don Allah mu bar wannan maganar haka nan, kaima kasan cewa abinda kake fada ba zai taba yiwuwa ba!”
Ta warci waya da laptop dinta ta tashi fuu ta shige daki. Wurgi tayi da kayan hannunta kan gado. Ji take kamar ta dora hannu aka ta kwala ihu saboda yadda take jin ranta yana tunzura da tafarfasa.
Kafin ta fara kokarin hucewa ma taji an banko kofar dakin, kofar ta hadu da bango ji kake gararammmm! kamar zata fita.
Ta juya tana kallonshi. A fusace yake kwarai, ranshi a matukar bace yake, ya fara gajiya da abubuwan nan.
Yadda ta ganshi yasa ta fara shan jinin jikinta, kafin ta yi kokarin guduwa ko neman magana ya fara zubda maganganu,
“Kauthar, believe me when I say na gaji da abubuwan da kike yi mun! Wannan wulakancin har ina? Ina aurenki, da aurena a kanki ki dinga tsaga tsakiyar idanuna kina ce min wai ke ba zaman aure zaki yi dani ba? To idan ba zaman auren ba, zaman me zamu yi iye? Ki fada min nace!”
Maimakon ta saduda sai itama ta fara hawa, “ehh, nace ni ba zaman aure nazo yi ba, uwata kawai nake nema wallahi, ina samo inda take shikenan sai dai ka sallameni in kara gaba. Ni ai na fada maka ba zanyi wannan zaman cin amanar ba!”
Ya hau gyada kai kamar wani tsohon kadangare, “ok! Dama abinda kike nufi kenan? Abinda kike yi kenan? Saboda ke kike da ikon sauwakewa kanki auren nufinki ko me?”
Ta murguda baki, “oho! Tunda dai nace bana yi ba sai a kyaleni ba? Ana zaman aure dolene?!”
Wani irin murmushi yake na takaici, yace, “ko ba a zaman aure zaki yi dole Kauthar, saboda wallahi idan kinga rabuwar aurennan namu to sai dai idan dayanmu ne ya rasu. Kuma ko a lahira ba zai rabu ba. Ai abinda Allah Ya hada babu wanda ya isa ya rabashi, har ke kanki kuwa! Hakkina na aure dake kanki kuma, ki shirya yau sai kin bani shi ko kin ki Allah! Ko kina tunanin tsoronki ne yasa har yanzu naki amsa?”
Ta zabura tayi baya a sukwane, ya kuma sa hannu ya damkota rikon da ba zata iya kwacewa ba, “na rantse da Allah baka isa ba! Kaje can dai inda ka saba amsar hakkinka naka wajen wadanda kake amsa, amma wannan hakkin ya zama haramiyarka”
Jin maganganun da take fada yasa shi sakinta babu shiri, ya tsaya yana kallonta puzzled, “ban gane ba, me kike nufi? A wajen wa nake amsar hakkin da ba nawa ba? Wace magana ce wai kike yi haka Kauthar?!”
Baki ta murguda, “ai ka fini sani! Ko kuwa kana tunanin ban san abinda kake ciki bane? Ko ba bin mata kake yi ba?”
Sai ya ma rasa abinda zai ce mata tsabar kaduwa, yayi sararo a tsaye kamar wanda ruwa ya cinye yana kallonta.
Ita kuma sai tayi tunanin tsabar mamakin ramfoshi da tayi ne yasa yayi hakan.
Sai ta cigaba, “ai na san komi. Ko kana tunanin ban sani bane? Da idanuwan wannan nawa na ganka rungume da mace, macen da ba taka ba a bainar jama’a bayan ko cikakken wata daya matarka bata rufe da rasuwa ba. To na ga hakan da idanuna, kana ganin me zan yi da kai? Mutumin da bai girmama marigayi ba ina ga rayayye? Sai dai ka sani, baka yiwa Anty Ummy adalci ba ko kadan. Saboda na tabbata da ace ita ce a matsayinka, to ba zata taba aikata haka ba. Sam Anty Ummy bata cancanci abinda kayi mata ba!”
Hankalinta a gushe take sakin maganganun da duk suka je bakinta. Watakila shi yasa bata kula da yadda ya tsaya yana kallonta bane, yana karance duk wani abu da yake fita a fuskarta, sai data dasa aya sannan.
Yadda taga yana kallonta ne yasa ta shiga taitayinta babu shiri. Sosai ya dumfareta gadan-gadan, kamar wanda yake shirin cinyeta danyarta. Duk dauriyarta kasawa tayi, ta fara ja da baya a rikice, idanunta sun fito waje kuru-kuru, hular dake hannunta ta sanya tana kare fuskarta kamar ita zata kwaceta daga hannunshi.
Sai daya danganata da bango, ta jita ta lafe a jiki kamar zata shige ciki.,
Ya duka yana kallon tsakiyar idanunta da wani irin murmushi na gefen baki kwance akan fuskarshi, taji wasu abubuwa masu kama da jan wutar lantarki na yawo a sassan jikinta….
Murmushi ya sake saki, “kina ta babatu da daga murya akan Anty Ummynki Kauthar, sai dai, me yasa dana kalleki nake ji a jikina kamar ba ita kike tayawa kishi ba? Me yasa nake ji kamar…. kishina ne yake cinki? Me yasa nake hango tsabar kishina kwance a cikin idanunki, iye Kauthar? Me yasa?”
Ganin yadda take faman zare idanu kamar kazar da aka lakume za a yanka, yasa ya ja da baya, wannan murmushi nashi dake matukar bata mata rai yana kara fadada akan fuskarshi, sai ya juya ya fita daga dakin. Ta sani, kamar yadda ya sani, bashi da sauran ta cewa, don kuwa ya riga ya gama daureta kam da jijiyoyin jikinta!
Ta silale a jikin bangon, zuciya na bugu kamar zata fasa kirjinta, ta samu kanta da maimaita tambayarshi a gareta, ‘Me yasa? Kuma me yake nufi?’