Skip to content
Part 18 of 26 in the Series Kauthar by Hauwau Shafiu (Jeeddah)

Kowane bawa da irin kaddara da dalilin da yake samar dashi.

Tun daga ranar da aka daura auren Isma’il da Adidat kawo shekaru fiye da hudu da suka yi a matsayin ma’aurata, bai taba daga ido ya kalleta da sunan matar aurenshi ba. Haka bai taba kawo a ranshi cewa zai iya bata wani matsayi ko yayane a ranshi bayan na muguwar kaddara wadda ta kawar mishi da duk wani farinciki da buri nashi da walwala.

Wani karshen wata yaje gidan kamar yadda ya saba hutun karshen mako. Bai san yadda aka yi ba, a ranar da yaje da dare, ya tsinci kanshi da bin Adidat din da kallo wadda ta kwale cikin wasu yan iskan kayan shan iska da basu da maraba da babu.
Hutun data samu yasa fatarta ta kile, tayi wani irin taushi da kyau, hakan yasa halittun jikinta suka kara ginuwa kwarai da gaske. Tunda dama can tun asali macece mai diri da kira mai kyau. Ko baka sanyata a cikin masu kyawun fuska ba, to zaka jerata a sahun masu kyawun dirin jiki da sura.

Nan-nan take yi dashi cikin rashin gajiya da nuna tunzura akan kyamar da har a lokacin bai saddakar ya daina nuna mata ba. Ta dinga gicci tsakanin falo da kicin tana kokarin jera mishi kayan abinci data tanada. Shi kuma yana daga gefe yana dambarwa da zuciyarshi akan yanayin da take neman jefa shi a ciki, don kuwa da so samu ne, da zai so har ya kare rayuwarshi a haka bai ji bukatuwar Adidat a cikin ranshi ba.

Sai dai abinda ya manta shine, desire wata halitta ce da Allah Ya kirkira wadda idan ta so, ko makiyinka zaka iya bukata duk da dai tafi armashi a inda ake so da kaunar juna.

Kasa cin abincin yayi duk yadda yaso, don haka ya mike ya bar mata wajen kwata-kwata.

Bangaren mahaifiyarshi ya wuce kai tsaye, anan ya ci abinci suna hirarsu har dare yayi sosai. Yayi mata sallama ya koma sashenshi.

Shaf ya manta da batun matar daya baro sai daya shiga falonsu yayi tozali da ita. Ta kara cin kwalliya ta kwale cikin wasu shegun kayan barci masu kama da net, bai san lokacin daya fara binta da kallon kurillah ba cike da mayuntaka, ita kuwa ta kara gyarawa yadda zai ganta sosai da sosai.

Ai take abin baya ya taso har ma ya fi na bayan yawa.

Tsautsayi dai baya wuce ranarsa. A wannan rana, a kuma wannan lokaci, Isma’il ya karya alkawarin daya daukarwa kanshi shekara da shekaru.

Kamar wanda ake juyawa, haka ya ja Adidati a karon farko na rayuwarshi zuwa jikinshi cikin nuna affection.

Kauna ce aka barza saffa-saffa, don kuwa ya kasa sakar mata jiki. Ita kuwa ta nuna mishi barikanci da kwarewa har sai data sanya mishi shakkun anya bata dade da sanin harkar ba kuwa? Sai dai yana kokarin ture tunanin saboda shi dai zato zunubi ne.

Amma kuma abunda yafi daure mishi kai shine samunta a matsayin budurwa da yayi. Ya juya yana kallonta cike da alamun tambaya, ita kuwa sai ta haskeshi da murmushi, “ba gamo kayi ba, gaskiya ce. Wannan ranar babu abinda ya faru a tsakanina da kai, kawai dai an baka kwaya ne wadda ta gusar maka da hankali, ni kuma na kamaka da dambe sai aka dauki hotunan. Bayan nan kuma data bugar da kai kayi barci, shine aka samu jini aka zuba akan shimfidar. Amma babu abinda ya faru!”

Bai ji sanyin rai kamar yadda yayi tsammanin zai ji ba. Tunda aikin gama dai ai ya riga ya gama, karyar Adidat da tuggunsu sun gama wargaza mishi rayuwa.

Yace, “duk saboda me kika yi hakan kuma? Don kudina? Ko kyawuna? Ko kuma nasabata? Ko don ki rabani da Aisha? Don kuwa na tabbata ba don kina yi mun son gaskiya bane kika yi hakan. Mai sonka tsakani da Allah ai baya barinka ka shiga cikin garari da tashin hankali!”
Sai tayi tsit ta rasa amsar bashi, shi kuma ya tashi ya bar mata dakin.

Bai yi wani doki ba ko rawar kai akan yadda ya sameta, hasalima haushin kanshi ya dinga ji. Takaici goma da ashirin ya mishi yawa. Ya rasa inda zai tsoma ranshi yaji dadi, haka ya wanzu har gari ya waye cikin bacin rai. Sai bayan asubahi ya samu barci yayi gaba dashi.

Don haka bai baro dakinshi ba ranar sai da yayi sallar Azuhur, ya karya da girkin da Adidat tayi mishi, sai wani giringidishi take yi da rawar kai, bai kushe mata ba kamar yadda yake yi a yawancin lokuta, amma kuma dai bai sakar mata fuska ba.

Sai daya fara biyawa ta bangaren iyayenshi suka gaisa. Mahaifinshi baya nan, yana gidan gwamnati suna meeting da yan majalissu.

Hajiya Hadiza ta kalleshi cike da kulawa, lokacin yana zaune a gabanta da kwano shake da dubulan yana ci. Tace, “na lura da yanayinka kamar baka jin dadi Isma’il, lafiya dai ko?”

Ya kalleta a kaikaice yana girgiza kai, “babu komi Ummah, ciwon kai ne kawai na kwana dashi shi yasa nake jin jikin nawa babu kwari”

Ta juya kai cike da alhini, “ayya, fatan dai ka sha magani? Ciwon kai bashi da dadi sam, Allah dai Ya sawwaka!”

Ya amsa da “ameen”

Daga can bai yiwa ko’ina tsinke ba sai gidan Nuhu, wanda rufin asiri da ilhamar Allah ta dabaibaye ta kowane bangare.

Dansu, AbdulMalik ya wuce shekaru uku a lokacin. Saboda yawan zuwa gidansu da yake yi, har ya sanshi. Tun daga bakin kofar gida ya tareshi yana ‘oyoyo uncle’ har zuwa falon baki inda ya samu Nuhun. Nan ya shantake suna ta hira har duhu ya fara yi.

Yayi sallama dasu ya fita zuwa inda ya ajiye motarshi, Nuhu da AbdulMalik suna binshi a baya. A jikin motarshi ya jingina yana kallon Nuhu wanda shima yake kallonshi. Dariya ya saki a hankali, “wai kallon wannan na menene kam? Tun dazu na kula kake ta kallona, da alama bakin nan naka akwai magana!”

Nuhu yayi yar dariya shima, “eh to, don magana fa akwai ta, ban dai san ta yadda zaka dauketa bane”

Sai ya gyara tsayuwarshi yana kallonshi da kyau, “to ina saurarenka, Allah sa muji alkhairi”

Nuhu ya kara dariya, yace, “alkhairi ne mana! Naga dai yanzu girma ya fara kamaka, tunda ga da nan na fari kayi, ga kuma wani nan tafe akan hanya!”

Nan da nan yayi fara’a, yace “kai Masha Allah, a takaice dai kana fada min kana expecting baby kenan?”

Ya gyada kai yana murmushi, “Alhamdulillah kam! To kaga dai kullum girma kara hawanka yake yi abokina. Ina ga yakamata a manta baya, a rungumi yanzu da kuma abinda gaba zata haifar. Shi zaman a haka, kana da iyali amma kamar baka dasu, bashi da dadi mutumin. Kayi hakuri ka rungumi matarka hakanan, ba’a san inda alkhairin Allah yake ba”

Isma’il yayi jim yana saurarenshi har ya dasa aya, ranshi ya sosu da maganganun Nuhu, amma idan ya duba su, yasan tabbas maganarshi haka take. Amma yaya zai yi ne? Bai iya ce mishi komi ba a lokacin sai, “ina yin kokarin hakan!”

A gurguje suka yi sallama.

Ya dauki hanya ya koma gida cike da tunani a ranshi. Ya rasa me yasa, duk yadda yaso ya manta, ya kasa. Abinda Adidat din ta mishi is unforgivable and unforgettable, amma zai yi kokarin yi.

Wannan dalili yasa kwanakin ya dan sake mata, duk abinda ta nema da ma wanda bata nema ba tana samu a wajenshi. Nan da nan kuwa ta kara yin clean da clear har ma ta ninka da.

A haka yake zuwa wajen aiki, ya dawo gida ya musu hutu ya koma. Hajiya Hadiza dai har zuwa lokacin bata kaunar Adidat, tana kuma nunawa kiri-kiri ba tare data saya ba. Don kuwa in maye ya manta ai uwar da ba zata manta ba.

Tun sau daya dinnan, bai kara nemanta da sunan wata mu’amalar aure ba. Duk yadda taso ta canja akalar rayuwar auren nasu abin ya gagara. Don zama su dan taba hirar yau da gobe shi da ita, zai zauna suyi. Zai daga waya ya kirata idan baya gari haka itama idan ta kirashi zai daga. Amma kowa da wajen kwananshi, ya kuma ki bata fuskar komawa dakinshi da kwana kamar yadda ta so.

Shi yasa ba karamin mamaki yayi ba bayan watanni masu yawa kawai ya dawo ya ga mata da ciki gingirim a gabanta. Ya ma rasa me zai ce. Da yake irin mutanen nan ne masu munafukin jiki, cikin nata bai bayyana da wuri ba sai daya girma. Kuma Allah Ya taimaketa bata yi wani laulayi mai zafi ba.

Tsakanin farinciki da bakin ciki ya rasa wanne zai yi a ciki. Daga karshe dai Ya fawwalawa Allah al’amuranshi. Sai dai bai wani zauna yana nuna mata giringidishi ba.

A haka dai har Allah Ya sauketa lafiya, ta haifi yar ta mace.

Zuwan wannan yarinya yaje musu da wani irin canji wanda basu tsammata ba. Hausawa suka ce wai albarkacin kaza kadangare kan sha ruwan kasko. Kuma ko a lahira wani yana cin albarkacin wani. Sai kuwa hakan ya zama gaskiya. Daga lokacin da Isma’il ya daga wannan diya ya rungume a kirjinshi, sai yaji ita kanta Adidat din ya yafe mata ta dalilin wannan jinjira.

Kakanninta ma da duk wani dan uwa nasu da abokin arziki, ba karamin murna suka sha ba.

Aka sha bidirin suna irin wanda ba a taba yi ba, yarinya taci suna Kauthar.
Sai dai har aka yi shagalin wannan aka gama, babu wani dan uwa na Adidat daya taka kafa ya lekasu, sai abokai da suke ta kara-kaina da shigi-da-fici kamar gidan iyayensu.

Ba karamin gata yarinyar nan take samu ba daga wajen mahaifanta da kakanninta. Wani wawakeken fili da Allah kadai Yasan iyakarshi na Alhaji Abdullahi dake Abaji, shi ya damkawa Isma’il a matsayin nata, Hajiya Hadiza ma manyan hannun jari a wani kamfanin atamfa ta damka musu. Yarinya fa taje da goshi Masha Allah.

Adidat sai ta kara mike kafa tana cin duniyarta da tsinke. Kadarori, tsabar kudi, gwala-gwalai, ta tara su kamar babu gobe. Tatsar Isma’il kawai take yi kamar wata saniya. Shi kuwa da yake mutum ne mai ihsani kuma baya da bin diddigi, sai ya barta tana abinda taga dama.

Ta dalilin Kauthar yasa suka shirya da Isma’il, duk da cewa dai shirin sama-sama ne ba can ba.

Tana da shekaru biyu da yan watanni aka aika mishi da rasuwar mahaifinshi a Lagos. Yana shirye-shiryen fara neman takarar shugaban kasa kuwa a lokacin.

Mutuwar ta girgiza Isma’il da Hajiya Hadiza fiye da tsammani. A matukar rikice ya dawo gida. Rashin lafiya ce yayi ta yan kwanaki, ashe ta ajali ce.

Aka yi jana’iza da zaman makoki, aka watse aka barsu sai su kadai, sai kuwa tarin dukiya da gado daya bari kamar me. Shi da mahaifiyarshi kadai suka gajeta saboda ba wasu yan uwa shakikai ke gareshi ba.

Irin dukiyar da Adidat taga ya gada ya sanyata kara tsinkewa da lamarinsu. Taga ashe ita ba komi ta ci ba a cikin dukiyarshi.

Ta mike tsaye tun karfinta ta fara neman haihuwa idanu a rufe, namiji take so ta haifa da zai mata gadon dukiyar Isma’il.

Suna cikin wannan hali sai ga Adidat da ciki, aka kuma tabbatar mata da cewa namiji ne. Zo kuwa kaga murna da farinciki da dagawa, musamman da Isma’il ya tattara ya dawo nan Abuja kacokam saboda mahaifiyarshi.

Cikin ikon Allah kuma sai Allah Ya kaddara dan bai zo da rai ba. Adidat ta shiga damuwa kwarai, kullum cikin kuka take da tunani kamar bata ma taba haihuwa ba. Har sai da Isma’il ya dinga mata fada akan rashin tawakkali da yarda da kaddara, sannan ta dan dinga boye wasu abubuwan.

Rayuwa ta cigaba da tafiya, har aka kara daukar wasu shekaru Adidat bata kara samun wani cikin ba. Ta ziyarci likitoci da kashashe da dama akan rashin haihuwarta, amma kullum amsarsu daya ce, mahaifarta lafiya lau, kawai dai lokacine bai yi ba.

Shi kuma ta bangaren Isma’il hakan bai dameshi ba sam. A kodayaushe cikin tunanin kada taje tana zaune bata haihu ba Isma’il ya kara aure ya samu wadda zata cika mishi gida da magada. Da ita ya zata yi kenan? Don tana kula da take-taken Hajiya Hadiza, wadda ta fara fakewa da rashin haihuwar tata tana kokarin cusawa Isma’il din akidar kara aure wadda shi baya da ita.

Ana cikin haka ranar nan sai yaje gidan Nuhu kamar yadda yake yi a yawancin lokuta. Lokacin yaranshi uku, shi da Nuhu din nan suka dauki yaran har Kauthar da yaje da ita, suka tafi yawan shakatawa wajaje da dama. Sai yammaci likis suka koma gida.

A masallacin unguwar su Nuhu suka yi sallar magriba. Daga nan ya koma ya dauki Kauthar wadda har tayi barci, yayi sallama da iyalanshi zai koma.
A inda ya ajiye motarshi suka tsaya shi da Nuhun suna kara yin sallama bayan ya bude motar ya kwantar da ita.

Nuhu ya kalleshi fuska dauke da murmushi, yace, “baka ji wani abu ba!”
Ya gyara tsayuwa yana kallonshi cikin alamun tambaya, “me fa?!”

Yace, “wallahi shekaranjiya kwatsam sai muka yi arangama da mutuniyarka Aisha a sabuwar mall din da aka bude a wuse 2”

Isma’il ya wangale baki, “don Allah fa?!!”
Yace, “wallahi kuwa! Ashe mall din tata ce, cikin watan nan aka budeta”

Isma’il yayi shiru yana saurarenshi, cikin sanyin jiki da sagewar gwiwa yace, “nayi cigiyarta a gidansu har na gaji, Aisha ta kini. Daga baya ma sai naji ance aure zata yi, shi yasa na hakura da nemanta ba wai don na daina sonta ba. Watakila we are not meant to be together”

Nuhu ya kalleshi cike da tausayawa, don kuwa shi din shaida ne akan irin kaunar da yake yi mata, wadda har a lokacin bata ragu ba.
Yace, “wane aure? Ai in fada maka bata yi aure ba, fasawa aka yi. Sai ta tafi USA tayi digirinta na biyu har da masters, bata jima da dawowa ba”

Yaji wani hope yana shigarshi, dama ance bawa baya yanke kauna da rahamar Ubangiji.
Dadi ya kai mishi har ya rasa inda zai sa ranshi, yace, “da gaske?”
Nuhun yace, “da gaske fa! Ita take ma fada min da bakinta. Kuma sai data ma tambayeka da iyali”
Ya dafe kirji yana jin kamar ana mishi tafiyar tsutsa a ciki, “kai kuma kace mata me?!”

“Nace kuna nan lafiya mana! Har na kara da cewa ita data ki mu? Sai tayi dariya tace ‘ai dokin zuciya ne ta hau.’ Dana kara tambayarta nace, ‘yanzu ta sauko daga kan dokin ko?’ Sai tace ‘wannan kuma, amma dai ai nasan da tsohuwar zuma ake magani ko?’ Kaga kenan dai har yanzu ana yinka mutumina!”

Isma’il ya bashi hannu suka tafa, ruwan fara’a kawai yake zubdawa kamar wani sabon ango. Bai tsaya doguwar magana ba yayi sallama da Nuhu, ya ja mota a sukwane ya koma gida.

Wanka ya tsalla, ya fito da wata dakakkiyar shadda sabuwa dal ta sha guga sai daukar ido, har da kafa hula abinda bai cika yi ba, ya fita daga dakinshi yana watsa kamshi kala-kala.
Cike da mamaki Adidat take bin shi da kallo. Yana yawan fita babu laifi, musamman da dare ko da yamma din, amma baya cin wannan uwar kwalliya kamar wani ango.

Tana so ta tambayeshi inda zai je amma bata ga fuskar hakan ba. Tana ji tana gani haka ya sanya kafa ya bar gidan.
Ko bangaren Hajiya Hadiza bai leka ba, ya tada mota ya fita. Masallaci ya fara tsayawa yayi Isha’i, daga nan yayi zarce sabon gidansu Aisha wanda suka canza. Lokaci zuwa lokaci yana zuwa su gaisa duk da dai yanzu yayi kwana biyu bai je ba.
Aka mishi iso suka gaisa da Hajja Babba, Fahima yar shekaru takwas a lokacin, ita ta zauna tana tayashi da hira da labari a inda aka yi mishi masauki, anan farfajiyar gidan waje na musamman da aka tanada saboda shan iska da kuma baki.

Hankalinshi rabi-da-rabi, yana saurarenta da kuma kallon kofar fitowa cikin tsumayin tsohuwar zumar tashi.

Bayan kamar mintuna ashirin, ta fito cikin atamfa riga da zane, ta yafa gyale mai fadi, cikin tafiya mai daukar hankali da jan aji.

Yayi sagara yana binta da kallo kamar wani sakarai. Idan da ba don ya mata farin sani ba, kuma yasan ko a halin mutuwa da rayuwa zai iya ganeta, to da cewa zai yi wata ce amma ba Aishar daya sani ba.

Tayi wani irin kyau da girma da cika mai burgewa, aji da alamun sanin ciwon kai sun dabaibayeta ta kowane bangare.

Tashi tsaye yayi hannu a jimke yana jefa mata ruwan kirari, “ranki shi dade uwargijiyata, kaga Hajiya Aishatu manyan mata, gaba salamun baya salamun giwa, takawarki lafiya giwar mata, ina miko gaisuwata da fatan za a karbeta da hannu bibbiyu!”

Tayi murmushi a tausashe yayinda take jan kujera tana zama, “kaji Isma’il da wani zance, giwa kuma? Hajiya ai tana inda take, kirani da Aishata zalla kawai”

Shima ya koma ya zauna yana murmushi bakinshi cike da fara’a, yace, “ai kinfi kowa sanin cewa kece Hajiyata kuma Giwata! Idan kuma baki yarda ba, to nasan lokacine zai nuna mana hakan!”

Tace, “yanzu dai duk ba wannan ba, ya kake, ya bayan rabuwa?!”

Bayan gaishe-gaishe da tambayar juna bayan rabuwa, Isma’il bai bata lokaci ba wajen sanar mata dalilin daya kaishi gareta. Tatsuniyar gizo dai bata wuce ta koki, so yake yi su koma da soyayyarsu, kuma so yake yi su kai ga aure nan ba da jimawa ba.

Ta gyara zama tana kallonshi a hankali. Rayuwar ta mika da yawa, tayi karatun, ta kama kasuwancin, settling kawai take so tayi a yanzu. Ta kuma riga data gama sanin babu wanda zata iya zaman aure dashi wanda ya wuce Isma’il din.

Tun bayan rabuwarsu, ta kasa samun nutsuwar zama tayi wata soyayyar. Sau biyu ana sanya ranar aurenta, na farko shi ya janye da kanshi, na biyun kuma ita ta janye saboda tasan idan ta auri wani namiji ba lallai ta iya daurewa ta iya bashi hakkinshi na aure dake kanta ba. Shi yasa ma ta kirkirarwa kanta karatu saboda ma kada iyayenta su takura mata. To da yake yan boko ne, kuma suna tausayawa halin data shiga ga kuma bugu da kari dauri gindi data samu daga wajen yayyenta biyu dake aure, sai abin yafi je mata da sauki. Yayarta da take bi wa, Anty Azimah, ita ta samar mata gurbin karatu a US da yake acan take aure, tayi tafiyarta abinta ba tare data kara bi ta kan Nigeria ba.

Bata ja maganar da tsayi ba ta nuna mishi kuskurenta na rashin tsayawa ta saurareshi a wancan lokacin, ta kuma bashi hakuri. Shima hakurin ya bata. Bai tsaya tono da abinda ya riga ya faru ba, tunda dai mai afkuwa ta riga ta afku, sai dai a koki gaba.

A take suka yafi juna, aka kuma dasa hirar yaushe gamo kuma ta soyayya har sai da dare yayi. Sai da aka tura kiranta daga cikin gida, sannan suka yi sallama da kyar. Su dukansu jinsu suke yi kamar wasu sabun shiga a fannin soyayya.

Yana komawa gida ya samu Hajiya Hadiza yayi mata bayanin yadda suka kare da Aisha. Ta tayashi murna kwarai da gaske, ta kuma ji dadi har cikin ranta musamman yadda taga yana ta farinciki da fara’a. A haka dai yayi mata sallama ya koma sashenshi.

A falo ya samu Adidat, ko motsawa daga inda ya barta bata yi ba da alama. Ta kalli agogo taga har karfe sha daya ta wuce, ta duba yadda yake ta murmushi da farinciki, sai ta tsargu.

Haka nan dai ta daure bata yi mishi maganar inda yaje ba, ta cije ta mishi sannu da zuwa. Nan ma ya amsa a sake cike da murna.

Ta mishi tayin abinci yace mata a koshe yake, don kuwa snacks suka yi ta ci da shan lemuka, cikinshi a cike yake. Bai kara ce mata komi ba ya wuce dakinshi.

Tasan karshen zancen kenan sai kuma da safe, tunda da yana da bukatarta zai gayyaceta zuwa dakinshi ne.

Ta ciza yatsa tana jinjina kai cike da takaici. Lallai koma menene zata kamo bakin zaren tun da wurwuri kafin a mata sakiyar da ba ruwa.

<< Kauthar 17Kauthar 19 >>

1 thought on “Kauthar 18”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×