Yawan fitar da Isma’il yake yi bayan yaci kwalliya ta kece raini yana matukar addabar ran Adidat, ga waya daya kirkiri yi a kowane lokaci, babu dare ba rana, kuma baya boye mata yana yi a yawancin lokuta, wannan dalili yasa ta fahimci cewa da mace yake wayar. Fadar hankalinta ya tashi ma bata baki ne.
Sai kuma wani karin tashin hankalin shine a cikin satin, yayan Hajiya Hadiza wanda suke kira da kawu Sa’idu yaje gidan shi da babban abokin marigayi Alhaji Abdullahi. Yini guda suna ta tattaunawa wadda ta rasa ta mecece.
Aikuwa kasa daurewa tayi, suna barin gidan ta garzaya wajen Hajiya Hadiza tana tambayarta cikin hikima da son bugun cikinta. Don kuwa tasan idan zata kwana tana tambayar Isma’il ko kallonta ba zai yi ba balle ya bata amsa.
Itama Hajiya Hadizar bata samu wata gamsasshiyar amsa a wajenta ba. Don kuwa ce mata tayi kawai “babu abinda ke faruwa sai alkhairi!’
Ta koma bangarenta cikin sanyin jiki.
A ranta dai ta riga ta gama yankewa a ranta, matukar abinda take tunanine zai faru, to lallai zasu ga tashin hankali irin wanda basu taba gani ba. Ita ai bata ga namijin daya isa yayi mata kishiya ba. Ta rantse, ta maya, idan har ya kuskura ya dauko mata maganar aure, musamman da Aisha wadda tafi kyautata zato, to wallahi ta gwammace ko shi ko ita ko su duka su mutu kawai, kowa ma ya huta. Gani take mutuwar tafi mata sauki akan wannan guggubeben al’amari da Isma’il din yake kokarin dauko musu.
Ila kuwa, ba a dauki wani lokaci ba ya zaunar da ita a falo yana bata labarin aure zai kara, kuma ba da kowa ba sai Aisha. Amma ta kwantar da hankalinta, saboda ya mata alkawarin ba a gida daya zasu zauna ba kowa gidanta daban, kuma zai canza mata kayan daki gabadaya, zai mata sabon lefe har da galleliyar mota wadda ta jima tana rokon ya bata, alkawarurruka da dama dai masu tarin abin arziki.
Kallonshi kawai take yi yana ta kora mata wannan bayanai har ya kammala.
Ta gyara zama tana wani irin murmushi mai dauke da zallan tashin hankali da dibar albarka. Tace, “Isma’il kenan! Kana tunanin wannan sakarkarun abubuwan daka zano sune zasu sanyani in kai kaina ga halaka ina ji ina gani? To ba mota ba, Allah sa kamfanin motar ne gabadaya zaka siya min, bana so! Idan kuma kana son kanka da arziki, to ka ma janye wani maganar aure don wallahi babu kishiya a tsarin rayuwata, kuma baka isa ka kakabo min ita ina zaman-zamana ba!”
Isma’il ya kalleta da mamaki, yace, “saboda ke kike aurena bani nake aurenki ba ko? To bari kiji, idan ma zaki dorawa ranki hakuri to ki dora don kuwa aurena da Aisha babu fashi, kamar anyi ne an gama!”
Ya suri makullan motarshi ya tashi yana kallon yadda take raba idanu, “dama da kika ga nazo na sameki a nutse, nayi zaton zamu iya maganar ne cikin fahimtar juna, amma tunda kin nuna haka, babu matsala. Ni dai alkawarin dana miki yana nan ba zan janye ba!”
Fita yake kokarin yi, bai san ta yadda aka yi ta tashi ba, sai ganinta yayi a gabanshi. Kwalar rigarshi ta ciwo da dukkan karfinta, idanu a rufe ta fara zazzaga mishi ruwan alkaba’i da masifa. Rantsuwa take tana kari, babu shi ba wani aure, don kuwa ta haramta mishi shi.
Da tayi fadan taga bai ma nuna yaji ba, sai ta dauki rigar hauka ta yafa. Duk wani abun amfani na falon wannan, sai data lalata. Yana fita waje, nan ma ta bishi ta sunkuci karfe ta buga mishi a gaban mota sai data kashe duka gilasan motar. Da kyar da jibin goshi ya warceta ya kai daki ya rufe bayan ya falla mata marika a kumatu.
Cikin kwanakin sam zaman lafiya sai da yayi musu karanci. Adidat hauka take yi tuburan, kuma ga dukkan alamu hakanta ba zai cimma ruwa ba, don kuwa shi dai Isma’il ko a jikinshi, sai shirye-shiryen bikinshi ma daya cigaba da yi.
Ta koma ga kashedi da gargadi da barazana, akan zata watsa wadancan hotuna data dauka idan har bai janye zancen aurenshi ba.
Yayi dariya sosai a lokacin, don kuwa dama yasan za a rina. Yace mata, “kalleni da kyau ki gani Adidat, ni ba wannan matashin da kika sani bane a da wanda bashi da katabus. Ko a wancan lokacin ma kin fi kowa sanin fin karfi kawai aka min na aureki, kuma darajar iyayena ce tasa har na iya cigaba da zama dake. Ba wai so ba, ba kuma tsoro ba. Martabawa ce. A yanzu kuma kina cin darajar Kauthar ne, saboda ko babu komi ina so ta tashi tasan mahaifiyarta, shi yasa nake daga miki kafa. Amma idan kina ganin watsa wadannan hotuna sune daidai a gareki, to bismillah, ki watsa din ki gani wa zaki zubarawa da mutunci da kima? Kirarine zaki yi kawai ki lumawa cikinki wuka!!”
Ya tafi ya barta tana kwallara ihu tana yamutsa kanta kamar dai mahaukaciyar da gaske. Shi kuwa zuwa lokacin abin na Adidat ya daina bashi haushi ma da takaici sai dariya. Ya girgiza kai yana mai nema mata fatan shiriya a cikin ranshi.
Ga biki yana ta matsowa, ga duk wani abu data ke yi a banza, babu mai jinta. Ita kanta Hajiya Hadiza ta kula ba karamin ji da bikin nan take yi ba. Itama tun tana tausar Adidat tana nusar da ita da bata hakuri, har ta hakura ta daina, don kuwa Adidat bata ji sai ma kara tuburewa da take yi.
Babu ma ya ranar da aka kai mata kayan lefe, sak iri daya dana amaryar haka aka hadasu wadanda suka ci dubunnan daruruwan kudade. Ta hadesu duka ta malala musu fetur ta bi da ashana. Duk sai lamarin nata ya fita akan Hajiya Hadizar.
A daren ranar ta taka zuwa bangaren nata da niyar yi mata fada akan irin abinda ta aikata da kuma kara yi mata nasiha, sai ta tsaya a kofar dakinta tana sauraron wayar da take yi cike da tu’ajjibi da mamaki. Ji tayi tana cewa..
“…yauwa! Amma kafinnan ku tabbatar da cewa ya sanya hannu a duka takardun, mallakinsu ya dawo nawa… eh… kawai kayi abinda nace maka…. ehh, idan ma mutuwar ce yayi! Ni ba gwara min ya mutun bama!! Akan ya dauko min wata can da zamu raba dukiyar da ita ba!!”
Hajiya Hadiza ta dafe kirji cikin tsananin kaduwa tana kara sauraron maganganun data ke yi. Shiri ta shirya tsaf ita da wanda suke waya, zasu shiga gidan kamar masu fashi ne, ta fada musu duk wani waje da yake ajiyar kudi da manyan kadarori da takardunsu. Idan suka tursasa shi yayi signing din komi nashi ya koma na Adidat, sai kuma su kasheshi ko su mishi lahani su kara gaba.
Hajiya Hadiza ta kara sakewa da al’amarin Adidat kwarai da gaske, rashin imani irin nata ya bata mamaki kwarai da gaske. Dama dan musulmi zai iya aikata wannan mummunan abu, balle kuma ace mata ta aikata hakan ga mijinta!!
Allah Ya sa Isma’il din bai yi nisa ba, yana can bangarenta ta baroshi da Kauthar da take yin barci. Ta koma ta kirashi, yana binta a baya har dakin Adidat, yana tambayarta meke faruwa ma bata iya cewa komi ba sai hawaye da take faman sharewa.
Adidat din har tayi kwanciyarta cikin jindadi da tunanin ta gama kashe matsalar dake gabanta. Sai taji bugun kofa, ta tashi ta bude kofa tana shan kamshi da hura hanci, duk ga tunaninta tausarta aka je ayi.
Hajiya Hadiza ta watsa mata harara, tace, “muguwa, munafuka!”
Sai duk su biyun suka bita da kallon mamaki, don babu wanda yayi zaton abinda zata ce kenan. Don rashin kauna fa bata kaunar Adidat, amma hakan bai taba haddasa musu matsala ba, tunda bata taba fitowa baro-baro ta nuna musu ba.
Isma’il yayi karfin halin tambayarta, “Umma lafiya? Me ya faru kuma?” Saboda duk a zatonshi rigimar dazu ce ba a gama kashewa ba.
Hajiya Hadiza ta kalli Adidat kafin ta maida kallonta ga Isma’il, babu bata lokaci ta zayyane mishi abinda kenan tun daga farko har karshe.
Ta watsawa Adidat wani sakaran kallo bayan ta gama koro bayanin, wadda tayi firi-firi tana rarraba ido cikin tsananin dimuwa da dimauta, ashe ita duk abinda take yi shuka take a idon makarwa! Wannan fa shine an yanka ta tashi din!
Hajiya Hadiza tace, “don haka ba a gidan nan ba, kuma ba a gaba na ba! Don haka Isma’il yau dai na maka umarnin ka saki wannan yar iskar mata. Dama tun farko abinda yasa ban yi hakan ba, tunanin watakila rabo da kaddarane ya hada ku. Ashe rabon bana komi bane face na ranka data ke son dauka tun lokaci bai yi ba, don haka sallamarta, taje can ta nemi dai wanda zata kashe amma wallahi ba dana ba!”
Adidat tayi fiki-fiki tana kokarin nade tabarmar kunya da bori, “ke kiji tsohuwar banza, ta nan zaki bullo min saboda kinga kin buga dani kin kasa cin galaba? To a yanzun ma wallahi ahir dinki, don kuwa ni nan naci dubu sai ceto, babu yadda zaki iya dani sai kallo sai harara ehhe!! Makiya, mamugunta wadanda ke raba albarkar aure!! To Allah dai Ya tsinewa ire-irenku!”
Isma’il yayi kanta a fusace, yace, “kul! Nace kada ki kuskura ki zagar min mahaifiyata a gaban idona don kuwa hakan ba zai haifar miki da d’a mai ido ba.”
Hajiya Hadiza tace, “barta mana, tayi min dibar albarkar data dade tana neman dalilin yi bata samu ba sai yanzu. Kuma kome zata yi, sai dai tayi, don kuwa maganata babu dagi, yanzu anan zaka rubuta min takardarta ka bani in damka mata!”
Duk da abinda take kokarin aikatawa a gareshi, haka ya juya ga mahaifiyarshi da niyar tayi hakuri ta janye kudirinta. Yasan bacin rai dana zuciya ne kawai ya haddasa hakan.
Kafin ya kai ga furta wani abu, Adidat tayi kukan kura tayi kan Hajiya Hadiza a sukwane kamar wata kububuwa tana ihu da karaji,
“Dama can nasan ba sona kike yi da danki ba kuma ba a son ranki nake zaune anan gidan ba! Tsinanniyar tsohuwar najadu, munafuka….!”
Idanunta suka rufe, ta dinga zage-zage da tsinuwa.
Mamaki ya kusa kashe Hajiya Hadiza, da dan yatsa ta nuna kanta tana tambayar Adidat, “ni ce tsohuwar najadu din?”
Babu ko dar a cikin ranta tace, “ehh! An fada din, idan kuma da abinda zaki iya yi akai kiyi, masharranciya kawai!”
Kafin ma ta rufa baki Hajiya Hadiza ta daga hannu ta falla mata mari. Aikuwa bata yi wata-wata ba ta rama, hakan bai yi mata bama sai data kara. Tayi tsaye a kanta tana kurma ihu da daga murya, jikinta har rawa yake, “ramawa zanyi tunda ke din ba komi bace face tsohuwar banza! Ai ba a halicci dan iskan da zai bugeni yace yaci banza ba wallahi, ke din banza…!”
Isma’il yayi kukan kura ya hankadeta daga kusa da mahaifiyarshi. Hannu ya daga zai rama marin, ya ga idan yace ma zai tsaya bugunta kasheta kawai zai yi saboda yadda ranshi ke tafarfasa.
Yace, “ke wata irin sakarya ce, dakikiya wadda bata san Annabi Ya faku ba? To bari in fada miki, baki mari banza ba wallahi, kin mari igiyar aurenki!!”
Aikuwa ta kara karfin ihu da kururuwar da take yi, rantsuwa take tana kari, akan babu wani mahaluki daya isa ya raba wannan auren, zai ma mayar da ita ne ko bai yi niyya ba. Abinda ya kara bata ranshi kenan, ya juya yana watsa mata wani mummunan kallo, yace, “to bari kiji, ba saki daya ba, na kara miki biyu ma akan wanda nayi yanzu. Na sakeki daya, biyu, uku. Ki kuma tabbatar da kafin gari ya gama yin haske kin bar min gidana ba tare da kin taba min ko allura ba, tunda nawa ne, haka zikal dinki kika zo, kuma haka nake so ki koma!”
Hannun mahaifiyarshi ya kama zasu fita. Da tayi wani tsallen kura ta dira a gabanshi, hannuwanta biyu tasa ta kamo wuyan rigarshi, tace, “karyarka ta sha karya Isma’il! Ai in ka ga na bar gidannan to wallahi sai dai in gawata ce za a fitar. Kuma saki kayi a banza, don kuwa ban saku ba! Abubuwa nawa na sadaukar a kanka? Na sadaukar da karatuna, na sadaukar da iyayena, da yan uwana, da abokaina, duk akan aurenka! Yanzu kuma kazo kace min mu rabu? Wallahi karya kake yi!”
Idanuwanshi sun kada jawur da bacin rai, duk wani karfin halin duniya ya tattaro yana tausar kanshi akan kada ya daga hannu da niyar bugun wannan mahaukaciya dake gabanshi, don kuwa yasan zai iya kasheta murus har lahira.
Yace, “wannan kuma kinyi a banza! Ki kuma yi kuskuren bari in ganki a gidannan gobe da safe, na rantse da wanda raina yake a hannunshi sai dai a fitar da gawarki din kamar yadda kike ikirari!”
Ganin balbalin fadan dake ranshi yasa jikinta ya dan rusuna, har ta iya bari suka fita suka bar mata falon.
Bayan fitarsu, tsayawa tayi tana safa da marwa cikin zuzzurfan tunani har dare ya kusa rabawa.
Isma’il bai gama saninta ba, yana underestimating dinta. Watakila shi yasa ya bar dakinshi a bude bayan tasan duk wata ma’ajiyarshi ta kudade.
Ta dauki jaka ta shiga dakinshi, duk wani waje data san yana ajiyar muhimman abubuwa ta kwashe tun daga kan kudade da agogunanshi masu tsada da sauran abubuwa. Itama ta samu duka gwala-gwalanta da katinan banki, ta warci makullin mota ta fita.
Kamar mahaukaciya haka ta dinga komi. Masu gadi biyu suna ta kwasar barci da munshari ta daga gate din ta tura motar a silale ta fita. Har tayi nisa, wata dabara ta fado mata. Ta sake maida akalar motarta baya. Daga can gefen gidan tayi fakin, ta sake fita.
Sai data ji iska yana kadata sannan ta tuna ashe fa kayan barci ne a jikinta.
Ta sake komawa dakinta ta dauki burmemiyar hijabi ta sanya.
Bangaren Hajiya Hadiza ta wuce kai tsaye, tasan Isma’il baya gidan tunda bata ga motarshi ba, shi yasa take komi kanta a tsaye.
A dakin Hajiya Hadiza din ta samu Kauthar kwance akan gadonta tana barci, ta daddabeta a hankali har sai data farka.
Cikin murnar ganinta ta fada jikinta tana mai ambatar sunanta, yini guda bata ganta ba saboda tunda ta fara fada da aka kai mata kayan lefen nan kafin ta kai ga konasu, Hajiya Hadiza ta tafi da ita can sashenta ta hanata fita.
Adidat ta sungumeta tayi waje da ita. Ta sake bi ta gaban masu gadi, ta sanyata a mota ta tayar tayi gaba cikin wani irin gudu.
Kuskuren da tayi shine data turawa Isma’il sako ta waya, cewa tunda ya ki sauka daga kan bakarshi, ta dauke Kauthar ta tafi. Duk ranar daya shirya sai yaje ya sameta. A gurgun tunaninta, tasan irin son da yake yiwa Kauthar, ba zai iya zama babu ita ba. Don haka duk inda take ma zai je ya nemeta, ita kuma zata yi amfani da Kauthar har ya mayar da ita dakinta.
Cikin talatainin daren, motar kirar 406 ta yanki kan titin da gudu kamar zata tashi sama. Adidat kara karfin gudu kawai take yi, hankalinta sam baya kan Kauthar dake gefenta, ta kankame belt din motar da aka zagayeta dashi da dukkan karfinta. Tsoronta a bayyane yake, hawaye ne babu adadi suke mata zarya a fuska.
Murya na rawa ta juya ta kalli Mamanta, “mommy, ina zamu je? Ina Daddy?!”.
A kaikaice ta juya ta kalleta, hankalinta once again, yana komawa kan titi, “guduwa zamu yi mu bar garinnan Kauthar, Daddynki baya sonmu, don haka muma mun daina sonshi!”.
A shekarunta a lokacin, bata fuskanci tsantsar tsanar dake fita daga cikin kalaman Mamanta ba, don haka ta turje kafarta ta fara kukan kiran Daddynta. Tun Mamanta tana aikin lallashi da ban hakuri, har ta kai hannu ta bugi bakinta, cikin zare ido da karaji take cewa, “ki mini shiru nace stupid!! Baki san komi ba sai kuka. Ba za a kaiki wajen Daddyn ba nace, don haka ki min shiru. Idan kuma kika kuskura naji sauti ya kara fita daga bakinki, sai na babballaki, kina jina?!”.
A matukar tsorace ta daga mata kai. hakan bai hana idanunta cigaba da tsiyayar da ruwan hawaye ba.
Na dan lokaci baka jin komi a cikin motar sai karan shesshekar kukanta. A haka bata san lokacin da barci ya dauketa ba.
Mamanta ta cigaba da sharara gudun da take yi babu kakkautawa.
Bata san yadda aka yi ba, sai jin kakkarfan salatin Mamanta tayi, kafin komi ya gama buduwa a gareta, taji motarsu tayi sama tana katantanwa, ta dire a tsakiyar titin. Kanta ya bugu sosai, wata irin azaba da bata taba dandanawa ba ta ji tana ratsata ta cikin kunnuwanta. Ta saki wani kakkarfan ihu kafin komi ya daukewa ganinta, duhu ya mamayeta…
I am so simple but difficult to understand