Kauthar shiru kawai tayi tana kallonta cikin dan hasken daya ratso gidan. Tana so ta dafata, ta lallasheta, ta kuma nuna mata bata kullaceta ba kan abinda ta mata. Amma ta kasa. Ba zata iya ba.
Don kuwa a zance na gaskiya, Adidat bata mata adalci ba, bata kyauta ba.
Duk da cewa tana so ta tsaneta, taji haushin abinda ta mata ta wani bangaren, hakan kuma ya gagara. Domin kuwa uwa da da sai Allah. Sannan ita kanta Adidat din ai ta ga karshen zalunci da cin amana da butulci.
Gashi nan shekara da shekaru bayan abinda suka aikata din, amma basu samu farinciki da kwanciyar hankali ba, basu samu duniyar da suke son samu ba ido rufe.
Ta muskuta tana kallonta cikin sanyin murya, “Tabbas abinda kika yi ba dai-dai bane, kuma kin aikata min ba daidai ba inda kika yi wancakali da rayuwata, kika manta dani duk akan abin duniya. Amma ba zan kullaceki ba, saboda ko a haka dana ganki, nasan Allah Ya riga ya bi hakkina! Kika yar da ni akan titi bayan hatsarin da kika haddasa, kika tafi kika barni ni diyar cikinki, dalilin daya janyo min rasa ji ba tare da amfani da abin taimako ba. Kika tafi babu ko tunanin zan iya mutuwa ko in rayu, babu ko waiwaye….!”
Ta girgiza kai hawaye na kwararar mata.,
“… to yanzu ina dukiyar da kika gujeni saboda ita? Ina kudin suke? Me yasa yanzu kuke rayuwa cikin irin wannan kaskantacciyar rayuwar? Ta yaya kuma? Shi wanda kika yi hakan saboda son shi da kaunarshi, yana sonki har yanzu? Ina kaunar taku take? Me yake tsinana miki?”
Ganin irin kukan da Adidat din take yi na tashin hankali yasa ta dakata da fadan nata, ta juya mata baya tare da cire aid din kunnenta.
Kuka itama take yi na zuci, hawaye na zarya akan fuskarta. Wannan wace irin uwa ce haka?
Cikin sake-saken da take yi wani wahalallen barci ya dauketa.
Sama-sama take ji kamar ana tabata kamar ana janta, barci da gajiya sun cika mata idanu, bata ma san inda kanta yake ba. Jin alamun hannu a saman kirjinta ana lalube yasa ta bude ido cikin sauri, tana son ta tabbatar idan ba mafarki take yi ba. Ai bude idon nan da zata yi, sai ta ci karo da wani sangamemen matashi a saman ta, habawa, ta kware baki ta kwallara wani gigitaccen ihun da tasan sai ya tashi gabadaya mutanen unguwar.
Ai kuwa nan da nan mutanen gidan suka yi wur suka tashi, kamar dama barcin nasu rabi-da-rabi ne. Taga Adidat ta sa hannu gefenta sai gata da muciya, tayi caraf ta kama hannub barawon ta rike kam ta fara muka mishi a baya.
Nan da nan kuma sai ga su Yusuf shi da abokanshi sun fado gidan, kama-kama dai barawo ya samu ya sufce bayan suma su Yusuf din sun dan mummukeshi.
Hannu na masifar rawa ta lalubi aids dinta ta sanya. Adidat tana tambayarta lafiya, bai mata komi ba dai? Amma ta kasa yin magana.
Makota suka fara magana ta katanga ana jajantawa. Apparently su sun riga sun saba ma da barayi, abinda kawai suke fadi shine ayi barka tunda babu abinda ya dauka, kuma ma tunda su Yusuf sun san kowanene ai shikenan. Kuma da ya dauki wani abu ne ma koda an sanshi din ba lallai a sameshi ba tunda idan sun yayi kaya garin suke bari.
Daga wannan kuma sai kowa ya koma barcinshi, aka bar ta ita daya kuru a tsakar gida tana raba idanu. Motsi kadan idan taji sai ta zabura tana makyerkyeta.
Sai can wajen gabannin asubahi sannan ta lallaba ta koma bayan Adidat da take ta faman sakin minshari baki a bude saleba na kwarara, ta kwantar da kanta akan filo. Barci sama-sama ya dauketa wanda tayi shi cikin rashin sukuni, ko yaya taji motsi sai ta zabura ta farka.
Hayaniya mai karfi ta tasheta. Ta bude idanu, kanta taji yayi wani irin gingirim kamar an dora dutse saboda rashin barci, ga gajiya data dirar mata kamar ma a lokacin ta kwanta.
Aids dinta ta kara gyarawa zama, ta maida kallonta ga dakin Babansu Zainab inda nan ne hayaniyar ke fita. Adidat ce ke magana cikin bacin rai da fada sosai.,
“Sati fiye da daya kenan AbdulFatah, sai dai ka tashi ka kakkabe riga ka fita. Kwabo wannan bata hadani da kai ta abincin gida, amma haka zaka dawo ka tarar da abinci ka kuma zauna ka cinye babu ko tambayar ta ina kudin suka zo mana. Wai alhakin ciyarwar wannan a kaina yake ne ko kuwa kanka? Na fa gaji in fada maka gaskiya wallahi. In yin, yin. In bari, bari. Amma ba zai yiwu ba ina auren mutum kuma ina ciyar da kaina ba da yara. To me amfanin auren kenan?”
Bata ji me yake fada ba saboda a hankali yake tashi maganar, amma daga jin yadda muryar Adidat din take kara hauhawa kasan ba magana mai dadi ya fada ba.
“…To ni ina ruwana da rashin aikin yinka? Ni na hanaka aikin? Ko kuma ni na matseka a gida na hanaka ka fita neman na kanka? Kai in fada maka gaskiya fa yau babu inda zaka motsa ba tare da ka bani kudin cefane ba wallahi! Idan kuma ba haka ba, zan cire kwanonka daga gidan nan! Don ba zai yiwu ina mace in zauna ina ciyar da kato ba!!”
Wata maganar ya sake yi wadda da alama ta kara tunzurata. Cikin karaji da daga murya taji tana cewa, “wasu yaran? Sata kake so Yusuf din yaje yayi ko me? Ita Kauthar din da kake fada diyarka ce ko dolenta ne kai? Jiya tana gaisheka ma da kyar ka dinga amsawa kamar kaga mala’ikan daukar rai. Amma da yake zuciyarka a mace take irin ta yan bani na iya shine har zaka iya daga baki kace wai….!”
Ta ma kasa karasa abinda take son fada sai wani mummunan tsaki data ja,
“…kai, Allah wadaran naka ya lalace wallahi! Wannan hali naka bai hadu ba…!”
Ta karasa sauran maganar tata cikin yare.
Tana ji suka cigaba da fafatawarsu. Ta maida kanta kan filo ta rufe idanunta cike da tsananin takaici da gajiya. Abu goma da ashirin ya dabaibayeta.
Tana jin lokacin da AbdulFatah din ya fita, Adidat ta bishi har kofar gida tana zazzaga fada wanda yawanci cikin yarensu ne amma Kauthar din tana tsintar wani abu.
Ta lalubi wayarta ta duba lokaci taga har karfe shida ta gota, ko sallar asubahi bata samu sukunin yi ba.
Ta hau barar-rabi da tunanin ta yaya zata tashi tayi alwala. Zata so ace ta samu ruwa mai dumi sosai ta fara yin wanka ko zata warware gajiyar jikinta. Amma tasan idan tace zata yi hakan a bayin gidan, ba ma zata samu nutsuwar da take bukata ba.
Tana nan sai ga Zainab da Yusuf sun fara shigowa da jarkokin ruwa da suka dauko a famfo.
Ta yunkura ta tashi zaune da kyar. Suka ajiye ruwan su duka suka duka suna gaidata, ta amsa musu da fara’arta.
Adidat ta karasa wajenta da rawar jiki tana murmushi, “a’ah, babyna kin tashi?”
Ta gyada kai tana dan murmushin yake, “ehh. Ina kwana?”
Ta amsa da sauri, bakin nan nata har kunne, “lafiya lau babyna. Ya gajiya?”
Kafin ta bata amsa ta maida dubanta ga Zainab, tace mata,
“Taso maza ki rakata gidan Uncle Aminu sai taje ta kintsa acan. Kafin ku dawo nan nasan mun hada abin kari sai ta karya bayan nan sai ki rakata ta gaida Uncles da Aunties dinta.”
Babu musu Zainab din ta tashi. Itama kuma taji dadin jin hakan, don haka ta mike tana lalubar gyalen kayanta da wayarta.
Adidat ta cewa Zainab, “idan kunje sai ki cewa Sikirat tunda nasan zata yi sa’arta, ta bata aron kayan da zata canza ko?”
Zainab din tace “to.”
Ita kuma karamar jakarta data ba Adidat din ajiya ta amsa. Ta kira Yusuf suka fita waje dashi.
ATM card dinta ta bashi da pin, ta fada mishi yaje ya cira kudi. Ya samo mata kayan sanyawa dana amfani, ta kuma fada mishi ya sayo kayan abinci masu yawa da duk wani abu da ake bukata a gidan ya kai.
Kallonta suka tsaya suna yi sararo! Kamar basu taba ganinta ba. Kafin Yusuf din ya hau zuba mata godiya ya juya da sauri ya tafi aiken data mishi. Su kuma suka tafi.
Gidan Uncle Aminun bashi da nisa da nan cikin sa’a. Matan da ‘ya’yan suka tareta da murnarsu. Nan da nan kuma aka hada mata ruwan wanka a baho. Ta shiga bandakin, wanda bai kamo kafar rabin wanda take amfani dashi ba, amma ya ninka na su Adidat sau dari.
Tayi wankanta ta dauro alwala. Tana fita aka kaita dakin Aunty Grace, matar Uncle Aminun. Ta kula ita Christian ce shi kuma musulmi. Ta shirya anan kafin Zainab ta rakata dakin ya’yan gidan, wadanda suke ta shirin tafiya makaranta. Riga da siket aka bata na atamfa, ta sanya. Sun dan kamata amma ba can ba. Ta sanya ta fara biyan sallar Asubahi da bata yi ba.
Tana kan sallayar tana yin Azkar, Sikirat ta shigar mata da flask din shayi da biredi da wainar kwai. Sai data gama azkar din, ta daga wayarta da ta dinga kara taga AbdulMalik ne, da bata daga ba ya tura mata sako yana tambayar ta tashi lafiya? Da taga yace meeting zai shiga, sai itama ta mayar mishi da amsar tana lafiya. Ganin wayar ta kusa mutuwa yasa ta kalli Sikirat tana tambayarta ko ya za ayi ta samu inda za a kai mata cajin waya? Tace mata bari ta amso mata power bank din babansu sai ta sanya. Ta mata godiya.
Sai data sanya cajin kafin suka zauna ita da Zainab suka fara kari. Yaran tuni duk sun wuce makaranta.
Suna karin take tambayarta, wani matakin karatu take a makaranta?
Zainab data cika baki da wainar kwai ta amsa mata, “na gama ssce tun last year, Yusuf kuma yana ss2 going to 3”
Tace, “to amma me yasa naga bai tafi makarantar ba? Ke kuma me yasa baki jona wata makarantar ba har yanzu?”
Kafada ta daga sama, “babu kudin makaranta, dama can Mama ce take biya. Yanzu kuwa abubuwan sun fi karfinta. Ssce dinma da kyar na samu na gama da taimakon Uncle Aminu.”
Ta jinjina kai cike da jimami.
Tana ganin tayi rayuwa cikin kunci da maraici da takaici, ashe ita a bilis take rayuwar ma. Tunda ko babu komi dai ta samu ilimi a manyan makarantu a garin Abuja, ta kuma tashi cikin samun ci da sha da sutura, wadanda bata taba rasawa ba tun tashinta.
Idan tayi duba da irin rayuwarta da wadda su Adidat da iyalanta suke ciki, idan tayi comparing sai taga ashe ita a matsayin sarauniya ma ta rayu. Amma duk wannan tsayin lokaci cikin mita take da rashin godiya da korafi. Mitar mahaifinta baya nuna mata soyayya, amma duk da rashin nuna soyayyar da me ya rageta? Babu. Korafi na rashin rayuwa da mahaifiyarta, but then again, me hakan ya rageta? Samun soyayya da kulawar Anty Aisha da ta Anty Ummy wadda tana da tabbacin ta ma yi tsararon data linka wadda Adidat zata taba nuna mata? Data kara dubawa sai taga ashe ita tama kasance butulu, wadda ta kasa godewa baiwa da ni’imar da Allah Yayi mata, ta rayu cikin mutunci da rufin asirin Allah, amma ta kasa gode mishi. Allah Yayi mata baiwa da miji nagari kuma na kere sa’a, nan ma taki godewa Allah sai ma butulce mishi data dinga yi da kuma kokarin kaucewa umarnin mahaifinta. Tana da tabbacin lallai data bijirewa Daddy, hakika Allah ba zai kyaleta ba. Watakila sai Ya jefata cikin ukuba wadda tafi wadda Adidat take a ciki.
Ukuba mana! Tunda hausawa fa cewa suka yi kowa ya kwana lafiya shi yaso. To hakika kuwa Adidat dai bata so zaman lafiyar ba, bata bi hanyar da zata zauna din ba kuma. Kauthar tana da tabbacin hakkinta ne dana su Daddy yake bibiyarsu kawai ba wani abu ba.
Makoshinta ya toshe, taji abincin ma ya fita a kanta. Ture kwanon tayi gefe guda ta lumshe idanu tana mai jan istigfari a cikin ranta.
Zainab da bata kula da halin data shiga ba, tayi zaton koshi tayi da abincin, ta kuwa hada har nata ta tada shi cikin kankanin lokaci.
Bayan sun gama Zainab din ta rakata suka gaisa da Uncle Aminu, mutum mai matukar girma da cika fuska. Cike yake da wata irin kamala da haiba wadda kanwarshi Adidat kam ta rasata.
Zainab din ta barta tare da Uncle din yana kara yi wata wa’azi da kara bata hakurin irin abinda mahaifiyarta ta aikata mata.
Zuwa lokacin da suka yi sallama dashi ya tafi, tuni taji jikinta ya kara sagewa yayi sanyi.
Ta kuma kudiri niyar matukar ta koma gida, abu na farko da zata yi shine ta kira Daddy ta mishi godiyar rainonta kawai da yayi, shi da Anty Aisha.
Dakin da suka fara sauka nan ta koma, ta zauna a gefen katifa tana kallon Zainab data ajiye mata wayarta a inda take caji fuskarta dauke da murmushi.
Itama da dan murmushin take kallonta, “ke da waye haka kike ta dariya?”
Ta girgiza mata kai, “babu komi Anty, wani abu ne na tuna kawai shine yake bani dariya”
Baki ta dan tabe, tace, “to tashi mu koma gidan ko?”
Suka tashi suka yiwa Aunty Grace sallama kafin suka wuce.
Akan hanyarsu ta komawa din tana yi tana duba wayarta cikin dakon wayar AbdulMalik, amma shiru kake ji. Bai kira ba, kuma bai mayar mata da amsar sakon data tura mishi ba. Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye, wani irin yanayi take ji a tattare da ita. Ji take idan bata ji muryarshi ba ko ta ganshi ba, numfashinta zai iya daukewa. Wani irin sabon al’amarine ya sameta kuma wanda bata taba fuskanta ba tunda take. Cikin saddakarwa ta sake tura mishi wani sakon kafin ta rufe wayar ta jefata a jaka.
Suna komawa ta samu Yusuf ya sayo duk wani abu da za a bukata. Ta samu Adidat a gigice ta sanya tarin kayan abincin da aka sayo a gaba tana ta zabga sambatu rabi hausa da turanci har da fulatanci, har baka fahimtar abinda take cewa.
Duk wani abu na ci da za a bukata an ajiye musu har ma da sabon camping gas wanda aka cika shi tsaf, ga kayan shafa dana sawa. Gefe guda kuma bulo ne tari guda a jibge, yan aiki zasu je a dan yiwa gidan kwaskwarimar da za a iya, kafin a sama musu wani gidan a wata unguwar, abinda Kauthar din ta kudurta kenan. Gida kawai zata canza musu don tasan hankalinta ba zai taba kwanciya ba idan tasan suna rayuwa a wannan unguwar.
Lallai fa aka ce wani aiki sai mai shi! Adidat zubewa tayi akan gwiwoyinta tana godiya fuska faca-faca da hawaye, har ma sai data rasa irin kalmar da zata yi amfani da ita wajen godiyar.
Makota suka fara zaryar shiga suma su ganewa idanuwansu wannan kayan arziki. Kwalayen sabulun wanka aka fasa duk wanda ya shiga gidan wannan sai ya fita da sinki guda a hannunshi. Nan fa waje ya kaure fa iface-ifacen godiya.
Zuwa jimawa bayan an gama wannan, Zainab ta shirya itama suka tafi yawon gaida dangi na kusa dana nesa. Taji dadin fitar wannan sosai, mutanene su masu karamci da girmama bako. Irin rungumar da wadansu suke bata idan sun je sai taji har hawaye take yi. Wani wajen kuma idan suka je haka za a cika musu gabansu da abubuwan ci da sha, idan kuma sun tashi tafiya a hada su da wani abun da zasu rike.
Don haka koda suka tashi juyawa gida, Hannuwansu niki-niki da ledoji haka suka dawo.
A can bakin titi keke napep ta ajiyesu bayan da suka je can gidan wata Yayar Mamansu a wata unguwa.
Yamma ce mai cike da sanyi da dadi, iska mai dadi da sanya natsuwa take kadawa. Ta dan lumshe idanunta a hankali tana kara shakar iskar, wani irin sansanyan kamshi daya sanya taji jikinta ya dauki rawa cikin wani yanayi ya shiga cikin hancinta, sai data ji shi har cikin kokon kanta, ya shige cikin makoshinta kamar wani guguwa, taji yarrr! tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin kafarta.
A hankali ta bude idanun, ta juya zuwa inda ta jiyo kamshin. Duk duniya, mutum daya ta sani da wannan masculine kamshin, wanda a kowane yanayi da hali take ciki, ba zata taba mantawa dashi ba.
Jingine a jikin farar motar Kia 12G, jikinshi saye da bakin yadin voile wanda aka yiwa dinkin Sanata, bai sanya hula ba, sai sumar kanshi daya kwantar ya kuma taje sajenshi yana ta sheki, ya rabbe hannuwa a kirji yana kallonta. Ita kadai.
AbdulMalik Nuhu Kwangila da kanshi ba dan aike ba. Mijinta!