Tun bayan da suka yi sallar asubah Daddy ya juya yace mata ta sameshi a dakinshi.
Don haka daga nan falo kai tsaye can ta wuce, Hajiya Hadiza tana binta a baya.
Ta sameshi zaune akan kujera, don haka ta zube a kasan carpet, kanta a kasa, zuciya na bugu da duka a kirjinta kamar zata fito waje. A lokacin ne wani irin taraddadi ya ziyarceta, taji wani tsoro yana shigarta da ratsa mata sassan jiki. Tunda take, bata taba barin gida ta fi wata daya ba, amma gashi a yau, a yanzu, zata bar gidan na lokacin da bata san adadinshi ba. Babu kuma yiwuwar komawa cikinshi. Kewar gidan dama mutanen gidan ta lullubeta.
Bayan Hajiya Hadiza itama ta zauna, sai Anty Aisha ta shiga dakin itama ta zauna a kujera.
Daddy ya fara magana, ya fara budewa da addu’a kafin nasihohi da wa’azi masu shiga jiki su biyo baya, duk akan zaman aure da tasirin hakkin miji akan matarshi. Bayan ya gama, itama Hajiya Hadiza ta dora da nata. Kafin wannan lokacin tuni fuskarta ta gama jikewa da ruwan hawaye. Kuka take na zuci, saboda ji tayi abubuwan sunyi mata goma da ashirin, har ta rasa yadda zata yi.
Anty Aisha kam koda aka bata fili ta fadi abinda zata fada, cewa tayi, “sai hakuri, kuyi ta hakuri da juna Kauthar, wannan ne kadai abinda zaku yi ku ceci rayuwar aurenku anan gaba. Allah kuma Ya baku zaman lafiya da zuriyyah dayyiba!”
Daddy da Hajiya Hadiza sune masu gyada kai tare da bin kalamanta da kalmomin “ameen” da “wannan haka yake!”
Kauthar kam takaici da kukan dake cinta ma yasa ta kasa aikata komi duk da yadda kalaman nata suka tunzurata. Wai suyi ta hakuri da juna! Yo an fada musu dama zaman aure ko na hakuri da juna ne zai kaita?! Tayi kuta a kasan ranta.
Hajiya Hadiza ta mikawa Daddy takardu, ya amsa ya sanya hannu akai, kafin ta kara amsa ta mikawa Kauthar. Cikin rawar hannu ta amshesu, kamar yadda tayi tsammani, kadarorine da hannun jari da kuma ajiyayyun kudi a asusun banki wadanda suka tasamma miliyoyi.
Hajiya Hadiza tace, “to Alhamdulillah! Yau dai amanar da aka damka min ta fita a hannuna lami-lafiya. Abubakar, idan da sauran abinda zaka fada mata sai ka fada mata, saboda mu fara shirye-shiryen tafiya da ita kuma, nasan masu kaita ma suna can suna jira.”
Daddy yace, “Alhamdulillah, duk wani abu daya kamata in fada mata na fada Umma. Sai dai kuma in ce Allah Ya kiyaye musu hanya. Allah Yayi mata albarka kuma!”
Anan sai taji wani sabon kuka yana kokarin barke mata, kalmar sanya albarka abune da bata taba jin ya fita daga bakin Daddynta zuwa kunnenta ba. A kullum maganganune masu cike da umarni kawai, babu tausasawa babu gardi.
A haka tana ji tana gani Hajiya Hadiza ta tattagota daga dakin zuwa falo inda sauran mutanen biki wadanda yawancinsu daga bangaren su Anty Aisha suke, suka yi dandazo.
Duba da kaya da yan aikin gidan suke fita dasu a hannu, Kauthar tasan kayan da Anty Aisha ta shirya matane ake fita dasu.
Bayan sun gama gaisawa da mutanen, masu Allah sanya alkhairi sunyi, nan suka hau kan dinning domin su karya. Kauthar kam bata iya cin wani abin arziki ba duk da lallashin da Hajiya Hadiza ta dinga mata.
Bayan sun gama, aka fara haramar tafiya.
Dakinta suka koma aka shiryata cikin wata farar gown da aka yiwa ado da bakin leshi da net, tabi jikinta dam kamar don ita aka kera. Aka nada mata head navy blue, sai aka yafa mata mayafi a saman kanta fari. Duk da ba wata kwalliya aka yi mata ba, amma fadar irin kyan da tayi ma bata baki ne. Tubarkallah, Masha Allah!’ kawai kake ji ana fada. Aka bi jikinta da turare aka fesa mata, kafin Anty Aisha ta kama hannunta suka koma falon kasa.
Nan fa sabon kuka da koke-koke ya tashi. Daga Hajiya Hadiza sai daya daga cikin kawayen Anty Aisha, Aunt Halima za a tafi, mazauniyar Lagos din ce.
Ita Anty Aisha sai an kwana biyu sannan zasu je ita da su Lukman.
A karon farko na rayuwarta, sai ga Kauthar ta rungume Anty Aisha tana kuka da idanunta. Itama nata idanun cike da kwalla ta kama hannunta har zuwa gaban galleliyar jar limousine da aka faka a bakin kofa tana jiranta. Su Lukman suna daga musu hannu tare da sauran mutane, abokan rakiyarta suka shiga mota aka ja aka tafi.
Bata yi mamakin ganin filin jirgi aka nufa ba, sai ganin cewa su kadai ne a cikin jirgin wanda madaidaici ne mai wani irin interior design mai tsananin kyau da daukar hankali. Gabadayan mazaunan ciki bai fi su dauki mutane ashirin da hudu ba, watakila private jet ne. Kodayake Anty Ummy ma ai kusan a yadda aka kaita kenan, don haka ba abin mamaki bane.
Tunanin Anty Ummy da tayi duk sai taji ranta ya kara jagulewa waje daya, tunda ta zauna har jirgi ya gama daidaita bata motsa ba tun bayan seat belt data daura, taja gyalen da aka yafa mata ya zamana har idanu ya rufe mata, ta cigaba da zancen zuci tana tsiyayar da ruwan hawaye cikin tausayin kanta.
*****
Wata lafiyayyar limousine ce ta sake komawa daukarsu, dark maroon sai daukar idanu take Yi a rana.
Bayan an gama loda kayansu a wata Hillux, suka dauki hanyar gidanta na aure.
Aunt Halima da sauran kawayen Anty Aisha da yan’uwanta su suka dinga shigi da ficin duba kayan gado da sauransu. Tun farko da aka tambayi opinion dinta cewa tayi kawai suyi abinda ya dace, don haka Anty Aisha bata sake bi ta kanta ba suka cigaba da gudanar da al’amuransu.
Ita dai sai dai taji ana ta santin gidan da kayan, amma bata taba tambaya ba ko tace a nuna mata.
Again, wani mamakin ya sake kasheta da taga an nufi wata unguwa daban ba wadda aka fara kai Anty Ummy ba.
Duk da cewa wancan dinma tana da kyau da tsari, kuma bata da hayaniya, amma wannan tafi tsari, ko yanayin gidajen a matukar tsare suke kamar estate.
Aka tsaya da motar a gaban wani tangamemen gate ruwan gold mai wasu irin intricate zane masu ratsin ja. Da maigadin gidan ya bude aka shiga, sai taji gabadaya numfashinta yana kokarin daukewa saboda kidima.
Saboda duk wani mafarki nata da buri data dinga ci a kan gidan da zata zauna wanda ita da kudinta zata gina shi, shine suka taka suka shiga. Yadda kasan daga ainihin mafarkin nata aka daukoshi kuwa saboda yadda komi yake in sync with her dreams and imaginations.
Can a kasan ranta take tuna wani lokaci…
Yaya Abdul, tunda kai Architect ne, kazo ka zana mun dream house dina!
A lokacin dariya yayi, yace, “banda abinki Kauthar, me zaki yi da zanen gida a yanzu?!”_*
Tace, “idan na girma zan gina in shaa Allah, in sanya Mamana da kannena a ciki, mu zauna tare dasu!
Tayi saurin kwabar kanta a lokacin. To shine me don yaje ya gina irin gidan da take so? Wannan fa ba shi zai sanya ta zama maci amana ba, kuma ba zai sa ta manta da cin amanar da shima ya yiwa Anty Ummy ba.
Sai taja tsuka acan kasan ranta.
Suna shiga gidan shuke-shuken fulawowi da itatuwa suka fara cin karo dasu kamar a kwari ko lambu. Tafiya kadan suka tarar da garejin motoci amma babu ko daya a lokacin. Daga karshe dai suka dangana da main building na gidan.
Ta yarda kam AbdulMalik karshe ne ba wasa, domin kuwa gida yayi sosai da sosai ba karya a ciki.
Tasan kuma Daddy shima yayi kokari, kallon kayan da aka yi mata jere dasu ma kadai abin kallone balle kuma gidan da aka shirya kayan a ciki.
Suka ratsa latsa-latsan kujeru masu kyau, suka shiga daki daya cikin jerin dakunan dake gidan, aka zaunar da ita a gefen gado dan Italia mai rumfa.
Daga nan kuma kowa watsewa yayi ya hau aiki. Hajiya Hadiza ta shiga adjoined bathroom zata hada mata ruwan da zata yi wanka, Aunt Halima ta fita tana kulawa da masu shigar da kayan da suka je dasu, ta fara shiga dakin dasu tana lodewa, da alama dai wannan ne dakinta.
Tana zaune har Hajiya Hadiza ta fita tace mata taje tayi wanka, Aunt Halima tace, “Yauwa, maza kiyi wankan bari in fitar miki da kayan da zaki sanya. Munyi waya da angon yanzu yace karfe hudu za a gudanar da walima anan gidan ta abokanshi kawai!”
Tun ma kafin Aunt Halima ta gama maganar taji ranta yana mata wani irin tsalle cike da taraddadi. Tayi tunanin ta shirya, apparently bata shirya ba ashe. To ta yaya ma zata hadu da AbdulMalik a haka, bayan ambatar sunanshi ma kadai yana jefata cikin irin wannan halin?
Ta dai yi ta maza ta mike, data shiga bayin sai da taja tunga tayi turus! Wajen wankan shower daban, ga wata irin jacuzzi da ita duk leke-lekenta bata taba ganin irinta ba. Hade take da wajen wanke kafa da wankin kai kamar a wani spa parlour. Kan mirror kuwa ta bandakin shake yake da mayukan wanka, turarukan ruwa na wanka, shampoo, abubuwan dai sai wanda ka gani.
Ta tube ta shiga cikin bahon da ruwa mai dumi yana ta tashin wani irin kamshi mai dadi.
Data gama wankan sai ta daura alwala saboda taga har karfe biyu na rana tana shirin yi.
Bayan tayi yan shafe-shafen mayuka, ta dauki towel babba mai taushi ruwan bula ta yane jikinta.
Data fita Aunt Halima kadai ta gani ta fito daga wata kofa da taga ana zugewa, da kaya a hannunta. Ta fada mata Hajiya Hadiza din tana sallah ne a dakin baki.
Ita kuma ta nuna mata inda ta shimfida mata abin sallah da jallabiya ja da hijabi, don haka ta zura ta a jikinta ta tayar da ikama.
Kafin ta gama Aunt Halima ta shigar mata da tray babba shake da abinci.
Tana sallame sallah ta tura mata plate din jallop din shinkafa da taji busasshen kifi da naman kaza da kayan ganye, kyawun da tayi kawai a idanu yasa bata tsaya gardama ba ta ja farantin gabanta ta fara ci. Abincin yayi dadi fiye da tunaninta, watakila dalili kenan da yasa ta samu ta ci abincin sosai. Data gama ta kora da lemun kwakwa da abarba.
Aunt Halima cewa tayi ta kara hutawa zuwa lokacin da za a zo a shiryata, don haka ta bi lallausan carpet din dakin ta kwanta. Ita kuma Aunt Halima ta fita taci gaba da gudanar da wasu ayyukan.
Barci har ya fara daukarta taji alamun hayaniya a falo sama-sama. Sai kuma taji an bude kofar dakin an shiga, ta juya tana kallon Aunt Halima suna shiga dakin tare da wasu yanmata. Sai da suka matsa kusa da ita sannan ta fahimci ashe Na’ima da Umaimah ne, kannen AbdulMalik.
Ta tashi da sauri tana kallonsu, duk sai taji nauyinsu ya kamata. Ko a matsayin me zasu dauketa?
Su kuwa sai taga kamar ma ko a jikinsu, faram-faram suka gaisa dasu har suna hadawa da tsokanarta.
Da Aunt Halima ta gama yi mata bayanin cewa Umaimah ce zata yi mata kwalliya, ta kuma fadawa Umaimah din simple din kwalliya zata yi mata ba heavy ba, sai ta kara fita ta barsu.
Nan da nan Umaimah ta kama aikinta. A hankali-a hankali suna hira su biyun suna kokarin sanyata ciki, sai taji ta dan fara sakewa dasu. Wayayun yarane da suka san inda yake yi musu ciwo, akwai kusanci a tsakaninsu sosai. Na’imah itace babba, ta ba Umaimah shekaru biyu a shekarunta na ashirin da uku. Kaninsu kuma Hashim, shekarunshi sha tara, yana makarantar koyon aikin jirgi a Washington a halin yanzu.
Nan da nan aka gama kwalliyar kuwa. Kayan da Aunt Halima ta fitar suka bude ta sanya bayan tayi sallar la’asar. Wata doguwar rigar shadda sky-blue, taci surfani da stones. Data sanya rigar, Umaimah ta nada mata dankwalin, sai tayi wani irin sharr kamar ka dauketa ka zura da gudu. Aka bata takalmi mai tsayi fari da karamar pouch mai lullube da stones itama fara, suka dora farin net a saman dankwalinta aka danne da kananun pins saboda fita. Subhanallahi! Malam zo kaga kyau. Tayi kyau har ta gaji, su kansu sai da suka yi santinta har suka gaji.
Suka sakata a tsakiya suka fita falo, sai a lokacin taga ashe mutane tuni sun fara taruwa. Yawancinsu matan abokan AbdulMalik dinne, sai kadan daga makota a cewar Na’imah.
Bayan sun gaggaisa sama-sama, suka fita wajen walimar. Anan lambun gidan aka shirya fararen kujeru a karkashen sunshades manya.
Tana tsakanin Na’imah da Umaimah. Tun daga nesa ta hangoshi cikin zugar abokanshi, suna zazzaune akan kujeru suna hira.
Sai da taji kafafunta suna hardewa, numfashinta ta dauka yayi sama, taji kanta yana wani juyawa. Tayi gaggawar kawar da kanta zuwa wani gefen.
Bata kara kuskuren hada idanu dashi ba har su Umaimah suka zaunar da ita akan kujera. Ba karamin jindadi tayi ba data gane cewa ba tare da AbdulMalik zasu zauna ba. Don haka ta fara sakin jikinta.
Ashe jindadinta na dan lokacine. Babu jimawa taga an fitar da kujera mai cin mutum biyu tsakiyar wajen. Ya taso daga cikin abokan nashi inda suke hirarrakinsu, cikin taku na kasaita da ginshira, sai taji abokan sun sanya tafi da shewa. Ya taka a nutse, wasu abokan nashi suna binshi a baya. Daya zauna, sai taga abokan nashi suna zuwa daya bayan daya, wasu su fesa mishi turare, wasu su bude bakin aljihun babbar rigarshi -da sai a lokacin ta fahimci cewa anko suka yi dashi- su dunkule kudi su zuba, wasu kuma zasu ajiye kyauta zagaye a cikin gift paper a kusa dashi, a haka har suka gama.
Sai kuma taga su Umaimah sun sake zuwa sun tayar da ita, and to her horror, suka nufi wajen da yake zaune da ita.
Ji take Yi kamar ta kwace daga hannunsu ko kuma ta juya, ta dai hakura cikin tsananin dauriya, ta taka kafafunta da suke rawa, har zuwa inda yake. Da suka je shi kuma sai ya tashi tsaye, sai da aka zaunar da ita sannan shima ya koma ya zauna.
Daya bayan daya suma matan wajen haka suka yi mata wannan. Hankalinta sam tuni ya jima da barin wajen, idan bayan fitinannen kamshin turarenshi da duk turarukan da aka dinga fesa mishi basu dusasheshi ba, babu abinda take fahimta. Sai kuwa kusancinsu dashi. Taji yayi kane-kane a wajen, ilhamarshi da kwarjininshi sun cika wajen har da kyar take iya shakar numfashi mai dadi.
Shi kuwa yadda kasan bata wajen, ko kallonta bai sake yi ba tun bayan zaman da tayi.
Ya cigaba da gaisawa da abokanshi da matayensu wadanda suke zuwa suna yi musu murna da fatan alheri, bayan an gama yi mata karin itama.
Bayan nan kuma sai daya daga cikin abokanshi ya amshi lasifika ya bude taro da addu’ah, daga nan yayi musu nasiha da wa’azi game da rayuwar aure. Bayan nan ya kara da basu shawarwari. Yana gamawa kuma aka fara fita da take away da souvenirs -Memo da mug da jaka- duk da sunansu a rubuce a jiki, ana rabawa mutane da abubuwan sha. Zuwa karfe shida taro ya gama watsewa.
Su Na’imah ma daga nan suka mata sallama, saboda a ranar ma zasu bi jirgi su koma Abuja.
Bata kara sanya angon a cikin idanunta ba sai bayan isha’.
Shima da alama Aunt Halima ce ta kirashi, suka dukufa a gabanta da Hajiya Hadiza ita da shi. Suma dai nasiha da wa’azin suka musu. Suna gamawa kuwa taga dukansu sun fara alamun mikewa.
Ta zabura ta mike tsaye tana kallonsu, fuska dagaja-dagaja da hawaye.
Tace, “Aunty ina zaku tafi kuma?”
Hajiya Hadiza tace, “ina kuwa zamu tafi wanda ya wuce masauki Kauthar? Tunda mun riga mun gama abinda ya kawomu, zaman me zamu yi kuma?!”
Kamar kuwa mai jira, sai ta bare baki ta hau kuka. Hajiya Hadiza ta kalleta cikin mamaki har tana kama baki, tace, “lallai Kauthar, rayuwar dadi ta miki da alama. Kin ganni nan gobe jirgin farko zan bi in koma Saudiyya, Halima kuma tana da iyalanta da suma suke jiranta, to me zamu zauna mu miki kuma?”
Amma Kauthar kuka yaki karewa. Hajiya Hadiza da taga dai duk lallashin da suke yi taki yin shiru. Sai ta tusa keyar Aunt Halima a gaba, suka musu sallama suka yi gaba.
Shi kuwa gogan ya bisu a baya.
Suka barta ita kadai a tsakiyar falo wani sabon kuka yana kara barke mata.
AURE YAKIN MATA, KAUTHAR!
Oh boy! This page was sweet sosai gsky. To Kauthar an shiga sahun ma’aurata, Allah dai Ya bada zaman lafiya
Hummn! Wannan kauna ta Kauthar da AbdulMalik za fa su bada citta idan Kauthar ta bada kai bori ya hau 😂
Masha Allah littafi Yana bada citta
Can’t wait to read soyayya Kauthar da Abdulmalik. Thank you
Ki bari kawai sis, nasan wannan shi zai zama bakandamiyar duk labaran jiddu gaskiya idan ka dauke ni da abokin babana that is