Skip to content
Part 9 of 26 in the Series Kauthar by Hauwau Shafiu (Jeeddah)

Tana nan tsaye a inda ya barta tana sharar hawaye har da fyace majina, yaje ya dawo cikin yan mintunan da basu wuce biyar ba.

Ya tsaya yana kallonta kamar zai ce wani abu, ita kuma ganin haka sai ta kara volume din kukan har da hadawa da ‘wayyo Allah na!’

Gogan sai kawai ya kada kai yayi wani dan corridor daga gefen dakinta kadan. Takaici da gululu suka hade mata a rai, cikin rishin kuka tace, “shikenan ni yanzu rayuwata ta gama lalacewa, dama nasan babu wanda yake sona a duniya daya rage! Allah sarki Anty Ummy, Allah Yayi miki rahama! Dama ke kadai ke sona!!”

Cak! Ya tsaya da jin haka.
Suddenly, taga ya juya ya nufi inda take gadan-gadan. Tayi tsit tana kallonshi a gigice kafin ta fara kokarin ja da baya, amma tuni ya cimmata. Ya tsaya a gabanta hannu harde a kirji yana kallonta da wadannan idanun nashi masu nuna alamun no-nensense.

Sun dauki akalla minti daya a haka, shi yana aikin kallonta, ita kuma tana kallon yatsun kafarta don kuwa ta kasa hada idanu da shi ko kadan.
Gyaran murya ya yi, yace mata, “kin ci abinci?”
Tayi shiru bata amsa ba.
Ya sake cewa, “kin yi sallah?”
Nan ma shiru.

Shima shiru yayi yana kallonta na wani lokaci, kafin ya gyada kai a hankali, “ki samu ki ci abinci kiyi sallah kuma kafin ki kwanta. Akwai abinci da duk abinda zaki bukata a kicin…” ya fada yana yi mata nuni da hanyar kicin din, “…idan kuma wani abu kike bukata na daban, zaki iya kirana ta waya!”

Daga haka ya juya ya fara tafiya, sai kuma ya sake waiwayawa, “nasan ma ba lallai kina da lambata a halin yanzu ba! Amma zaki iya buga min kofar daki gashi can,” ya mata nuni da dan corridor dinnan.” Sai a samo miki. Sai da safe!”

Daga haka bai sake cewa komi ba ya sake juyawa.
Kasa ko motsi tayi sai aikin binshi da kallo da take, har ya wuce. Sai da taji alamun karar budewa da rufe kofa sannan ta saki numfashin da bata ma san ta rike ba. Wai sai kuma ta hau hararar hanyar da yabi har da gunguni.

Ta wuce zuwa dakinta fuuu kamar guguwa, ta shiga tare da maida kofar a zuciye ta buga garamm kamar itace mai laifin. Ta zauna a gefen gado tana kumbure-kumbure.

A hankali taji zuciyarta tana dan lafawa, ta mike a nutse taje tayi alwala. Sallar isha’i tayi ta dora da shafa’i da wutiri.
Daki guda aka ware mata na kayan sanyawa kawai. Tsabar gajiya data yi ce ta hanata tsayawa kalle-kalle da ba idanunta abinci. Ta zaro riga da wando 3-quarter na barci ta sanya, ta fesa turaruka masu sanyin kamshi, daga nan ta bi lafiyar gado ta kwanta.

Sake-sake ta fara yi akan shakulatin-bangaro da taga AbdulMalik yana nuna mata. Tasan idan tace zasu tafi a haka lallai za a sha da ita. Ba irin zaman da taso suyi ba kenan, so take yi suyi ta rigima da sa-in-sa har yace ya gaji daga karshe ya sallameta.
Don haka ba zata yi kasa a gwiwa ba, she’ll keep pushing his buttons har sai ya tanka mata, ya kuma yi mata abinda take so.
Da wadannan tunanikan ta samu barci ya warceta a haka. Bata kara sanin inda kanta yake ba sai da alamun taba filon da kanta yake kai sau uku a jere ya shiga kunnenta cikin daddadan barcin da take yi.

Ta bude idanunta, blinking cikin duhun dakin, tana kokarin daidaita kanta.
Aka sake bubbuga filon, wannan karon da dan karfi. Ta juya kanta gefen da ake tana kallon mai wannan aikin.
Tayi face-to-face da shi, saye da jallabiya fara kar, duk da dakin babu wadataccen haske, hakan bai hanata kasa ganin wadannan idanun nashi ba, hard and unyielding.

Tayi baka-baka ta daure fuska tana laluben aids dinta dake kan bed side drawer ta manna a kunnenta, ganin haka sai shima yaci mur din.
“Ki tashi lokacin sallah yayi!”
Abinda yace mata kenan, ya juya ya fita.
Ta bi bayanshi da kallo, kamshin daddadan turarenshi na kara surnanawa cikin hancinta.

Sai bayan daya fita kafin taja wayarta, ta duba taga biyar ce da yan mintuna.
Ta sauka daga kan gadon, taji dadin yadda taji jikinta sawai alamun ta samu wadataccen barci. Taje tayi alwala, ta dora zani akan kayan barcinta ta sanya hijabi ta fara da nafila har zuwa lokacin da taji an tayar da sallah, tayi.

Bayan ta gama sallar, ta zauna tana azkar. Tana jiyo motsi a falo, da alama AbdulMalik ne ya dawo daga masallaci. Tayi tunanin ko zai leka inda take, har da kara yin kini-kini da fuska, sai taji ya wuce ta kofar dakinta yayi gaba abinshi. Ta gyada kai kamar tsohuwar kadangaruwa a ranta tana mita da fada ita kadai.

Kasa komawa barcin tayi, ta dinga juyi akan gado har gari yayi haske, duk sai taji ta rasa ma abinda zata yi.
Kewar gidansu ta cikata, watakila da yanzu war haka ta dawo daga gaishe da Daddy, ko kuma kila tana kicin tana taya Anty Aisha hada abin kari kamar yadda take yi a wasu ranakun, watakila kuma da tana kwance a dakinta, akan gadonta, tayi dai-daya tana kwasar barcinta mai dadi.

Ganin tunanika sun addabeta suna neman su mata yawa, sai ta dauki wayarta ta shiga cikin jerin contacts dinta. Ta ma rasa wa zata kira, sai kawai ta kira layin su Lukman. Ta shiga tayi ya kara ba a daga ba. Sai data kira har sau wajen hudu ba a yi picking ba, sannan ta hakura.

Tana ta sake-saken zuci, daga karshe dai kawai sai ta kira Anty Aisha. Tayi mamaki data daga a ringing din farko, da taji muryarta tana sallama, sai duk ta dabarbarce, ta rasa me zata ce mata.
Sai data sake yin sallamar, ta kara da ambatar sunanta, sannan ne ta dawo cikin hayyacinta.
Ta gaidata cikin sanyin murya, ta amsa, ta kara da jefa mata tambayar tana lafiya? Ya suka tashi ita da maigidan? Duk tace lafiya lau.

Tace, “Anty ko su Mahmoud suna kusa dake? Nayi ta kiran wayarsu amma basa dauka.”
Ta ce, “yanzu dai suka fita daga nan babu jimawa, amma bari in kai musu wayar”
Tace, “to!”

Su dukansu babu wanda ya kara yin magana har ta kaiwa yaran wayar. Suka amsa da dokinsu da murnarsu har sai da taji kwalla ta cika mata idanu. Tana jin Anty Aisha na musu warning din suyi behaving, daga karshe dai ta sa musu wayar a hands-free ta fita.

Nan kuwa aka bude babin hira ita da yaran, duk wani abu daya faru tun bayan tafiyarta har kaiwa safiyar ranar, sai da aka wassafa mata.
Sun jima suna hira sosai, sai da Anty Aisha ta koma da kanta ta amshe wayar, sannan suka yi sallama.
Data kashe wayar sai taji ranta har ya dan yi mata sanyi.

Ta duba taga karfe bakwai da rabi, don haka ta kira Hajiya Hadiza. Already tana filin jirgi sun kusa tashi, don haka ta mata fatan Allah kiyaye da fatan su sauka lafiya, suka yi sallama.

Bayan sun gama wayar, wanka ta shiga. Ta fito ta sanya wata doguwar riga ta yadi mai taushi da kyau. Bata tsaya yin wata kwalliya ba, mai kawai ta shafa sai turare data fesa mai kamshi.

Tana tsaye a gaban gado tana tunanin abinda zata yi, sai taji alamun ana taba kofa, ta juya fuska a cune sanin wanda zai shigo.
Kamar kuwa yadda tayi tunani, shi dinne ya shiga a shiryenshi tsaf cikin yadi ja, ya dora hular zanna baka a kanshi.
Fuska babu yabo babu fallasa yake kallonta, “yauwa, tunda kin tashi ki fito kiyi kari!”

Baki ta turo cikin alamun tunzura, “Bana jin yunwa!”
Ta fada dai-dai lokacin daya kama handle din kofa zai bude. Ya juya yana kallonta, “Ba kya jin yunwa? Well too bad, haka nan zaki fito ki ci. Abu na farko da ba zanyi tolerating ba shine rashin cin abinci a cikin gidana, kin gane? Don wasu kananun rigingimunki da fada, duk bai dameni ba Kauthar!”

Yadda ya yi maganar cikin daurewar fuska da nuna alamun rashin wasa don ma kada taga fuskar musa mishi, sai duk ta sha jinin jikinta. Musamman da ya ki matsawa daga inda yake bayan ya bude kofar, ya zuba mata idanun nan nashi da a lokacin suke kokarin sanyata ta zube a kasa saboda yadda suke kallonta tun daga sama har kasa, in appreciation? Ko kuwa me? Oho!
Ya ce mata, “after you!”

Babu musu ta kwashi kafafunta, tsabar kidima ko silifas din data ware mai taushi bata tuna dashi ba, tayi gaba salalaf-salalaf kamar wadda aka kama ta nannagawa sarkin garinsu karya.

Falon tas-tas a share kal, ko’ina yana tashin kamshin freshner mai dadi. Kan dinning dinsu inda yake a can gefe wata yar kwana, an yiwa wajen kwalliya mai burgewa yayinda dinning table din mai cin mutane shida yake overlooking bayan gidan inda take hango swimming pool da su basketball. Duk taji doki da marari ya kamata don bata samu ta karewa wajen kallo sosai a jiya ba.

Taja kujera daya ta zauna, an cike kan dinning din da warmers na abinci masu kyau da plates da jugs da kofuna.
Bata jima da zama ba, AbdulMalik ya biyo bayanta shima. Bata iya daga kai ta kalleshi ba, taci gaba da kallon kasa. Sai da taji alamun dukawarshi a kusa da ita, ta dan juya ta kalleshi daidai lokacin yana ajiye mata silifas dinta data baro a daki, ya daga kai suka hada idanu.

Ya Allah! Wai menene a tattare da idanun mutumin wannan ne dake kada mata ‘ya’yan hanji? Suna sanyata jin wani abu a game dashi wanda karamar kwalwarta da ranta basa fahimta? Meye a tattare da kallonshi da idan yayi mata ya kan sa ta zubar da duk masu makaman yaki da take tanada, ya dinga warware mata duk wani zaren hadda data kama daya bayan daya?

Bata san kallonshi take yi tun karfinta ba, sai da taga ya mike tsaye, duk da bai yi magana ba amma tasan ya gama ramfota. Ko ba don komi ba, don wannan stupid -yet kyakkyawan- murmushi da yake saki na gefen baki.
Takaici da kunya suka mata rubdugu, ji take yi kamar ta kama kanta tayi ta bugu. Maimakon bugun, sai dan tsaki data saki tana hararar takalman daya ajiye mata.

Wani sashe na zuciyarta yake watsa mata zagi iri-iri, akan bai kamata taji wani abu mai kama da dadi ba wai don kawai ya dauko mata takalmi. Ta kara sakin wani tsakin.

Bai bi ta kanta ba shi kuwa, yaja kujera wadda take gefenta na hagu, ta tsakiyarsu kuwa empty, ya ja plate yana daga warmers yana zuba abinci.

Tuni kamshi ya cika mata hanci ta kowane bangare, miyanta har wani gudana yake yi yana taruwa. Ta tabbata idan ta cigaba da cin wannan abincin, cikin lokaci kankani sai ta kanainaye ta yi kiba. Abinda ba shi ya kawota nan ba kenan.

Tunda ya fara har ya gama, bata daga kai ta kalleshi ba. Sai daya gama, ya tura mata bowl na faten dankalin turawa, ya sha vegetables da yankakkiyar hanta da fatar sa, ga soyayyen agada da kwai, ga kuma hadin shayi mai kauri.
Dama can shayi mai hadi bai dameta ba, ita yaushe rabon data sha ma wani shayi da madara? Ta ja bowl din da faranti a gabanta, maimakon tace mishi wani abu, sai ta dauki wani cup din ta bude flask ta tsiyaya ruwan shayi daya sha kayan kamshi, ta dauki lipton din Victoria ta Minthe ta saka, ta zuba sugar ta koma ta zauna.
Kallonta kawai yake yi bai ce komi ba.

Taja fuska, ta fara cin abincin. Kunnenta har wani motsi yake, amma tsabar miskilanci taki nuna hakan a fuskarta.
Shima ci kawai yake yi yana gudanar da harkokin gabanshi. Wanda yawanci amsa wayane da kuma mayar da sako.

Bata san me yasa ba, sai taji hakan ya tuno mata da lokutan baya. Lokutan da yake zuwa gidansu.
Haka suke kasancewa su biyun ko uku, suna cin abubuwan motsa baki, suna hirarrakinsu masu cike da nishadi da ban dariya.

Gabadaya sai taji ranta ma ya sosu, duk dadin abincin da take ji sai ya fita a kanta.
Ta ture kwanon gefe guda, ta fara kokarin tashi.
Kallonta ya yi, “Ina zaki je?”
Kafada ta daga, “Na koshi ne!”

Bai kara cewa komi ba, itama bata sake bi ta kanshi ba, ta koma kan luntsuma-luntsuman kujerun falon ta zauna.
Dama can ita ba ma’abociyar kallace-kallace bace, don haka zama tayi tana karewa falon kallo da irin kayan alatun da aka zuba mata. Har ya gama cin nashi abincin.
Sai lokacin taga yar aiki taje ta kwashe kayan da suka yi amfani dasu.

Ya tashi tsaye hannu rike da kwalin lemun exotic daya gama sha, yana jefa mata wani kallo data kasa fahimta, yace, “zo muje inyi touring dinki a gidan.”

Da har zata ce mishi, ‘Meye abin gani a gidan da ba zama zanyi a cikinshi ba?’
Sai kuma ta kame bakinta ta tsuke, data fahimci kallonta yake gira a dage, daring her to say something, ta mike ta bi bayanshi.

Lungu da sako haka yabi da ita na gidan yana nuna mata. Sai lokacin ta fahimci ashe girman gidan ma ya wuce tunaninta. Bayan sun gama, ya gabatar mata da ma’aikatan gidan, Mai girki Amanda, mai goge-goge da share-sharen falo Blessing, sai kuma maza biyu, masu kula da farfajiyar gida da mai gadi.

Yana gama wannan da suka koma falo, ya juya ya fita ba tare daya ce mata uffan ba, itama bata tambayeshi inda zai je ba.
Ta koma dakinta ta dauki waya tana buga game har barci ya dauketa, ta kwanta.

Sai azzuhur ta tashi. Bayan tayi sallah, aka sanar da ita abinci ya sauka. Ta fita ta ci iyaka abinda zata iya, ta koma dakinta ta sake kwanciya.

Yini guda cur haka ta yini a daki, daga barci sai wasa da waya, sai kuwa jifa-jifa da za a kirata a waya ta daga, yawanci yan yi mata murnar aure ne.
Bata kara ganin AbdulMalik ba sai da dare, shima lokacin har ta gama cin abinci, tayi wanka ta sanya kayan barci. Tana zaune akan gado tana karanta addu’ar kwanciya barci, wajen karfe goma saura kenan.

Ya tura kofar ya shiga. Daga kai tayi a hankali ta kalleshi. Shiga dakin yayi, ya jingina da bangon dakin ba tare daya maida kofar ya rufe ba.
Kallonta yake yi kasa-kasa, ita kuma bata ce komi ba, kawai tsayawa tayi tana kallonshi.

Ya ce, “How was your day, Kauthar? Kin ci abinci?!”
Kwafa tayi tana harararshi kasa-kasa, can kasan makoshinta take cewa, “Wai wani ‘kin ci abinci!’ as if you care!!”

Ya ce, “Me ki ka ce Kauthar?”
Bata amsa shi ba.
Takawa ya fara yi cikin yar sassarfa, cikin dan lokaci ya karasa inda take. Ya dukufa yadda suke kallon juna ita dashi ido cikin ido. Ta fiddo idanu waje kuru-kuru, tana son ja da baya amma ta ma kasa motsi.

Murya kasa-kasa, kamshin Listerine daya wanke baki dashi yana bugun hancinta, kusancin da har dumin jikinshi tana ji yana bugun jikinta, “Tambayarki nake yi Kauthar, me ki ka ce?”

Kus! kake jinta kamar wadda ruwa ya cinye.
Wani dan murmushi ya saki, “Ga tsoro kamar farar kura, kuma ga jan magana. One of these days Kauthar, sai wannan bakin naki da ya iya tsiwa ya jawo na taune shi ko ya shiga hayyacinshi ya daina mun rashin kunya!”

Ta daga baki a matukar hargitse tana kallonshi, lebba na rawa.
Ganin haka yasa shi mikewa tsaye yana yar dariya, “Ki tabbata kinyi addu’a dai kafin ki kwanta. Sai da safe!”
Ba tare daya kara cewa komi ba ko shi ya bari tace wani abu, ya fita daga dakin.

Sai daya maida kofa ya rufe sannan ta iya sakin numfashin data rike. Ta dafe zuciyarta dake bugawa kamar ana gudun fanfalaki.

A karo na barkatai, ta sake tambayar kanta, anya kuwa duk abinda ta kullowa kanta daga gida zai tafi a yadda taso kuwa?
Don kuwa idan har aka cigaba da tafiya a haka, AbdulMalik tsaf zai sanyata ta zubar da makaman yakin data dauka ta ruwan sanyi, watakila ba ma tare da saninta ba.

Lallai-lallai tana bukatar ta sake sabon shiri kenan!!

TO! MU DAI JE ZUWA KAUTHAR… INJI MAHAUKACI DA YA HAU KURA!

<< Kauthar 8Kauthar 10 >>

8 thoughts on “Kauthar 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×