Skip to content

Kauthar | Babi Na Uku

2
(3)

<< Previous

Unguwar tasu a wannan lokaci, babu hayaniya balle giccin mutane. Ta kara daga kafa tana sauri don ma kada wani ya ganta idon sani ya nemi bata mata shiri.

Sai da tayi tafiya mai tsayi sosai, Allah ma Ya taimaketa Yasa takalmin data sanya flat ne.

Cikin ikon Allah tana fita can bakin titi, taci karo da taxi. Da sauri ta tare ta fada ciki.

Matukiyar, -Kauthar tayi mamakin ganin mace na aikin tuka motar haya, don kuwa bata taba ganin haka ba- ta juya ta kalleta, cikin karyayyen turanci take tambayarta, “madam, to where?”

Tayi duru-duru, don kuwa bata da wajen zuwa. Bata da inda zata je a ciki da wajen garin Abuja.

Idan ma a wajen Abujar ne wa zata nema? Dangin mahaifiyarta dake can a garin Naija wadanda bata sani ba, suka kuma nuna baro-baro basu sonta? Ko kuwa dangin mahaifinta da tasan tana dira kafa ta shiga gidan kamar a gaban Daddy ne ta shiga gidan? Ko kuwa dubunnan abokan da bata dasu?!

Dama can abokan Anty Ummy sune nata, dangin Anty Ummy ne nata. To yanzu kuwa ina ita ina zuwa wajensu?!

Ta juya tana kallon direba din, “kaini tashar mota!”

Direbar tace, “which dey?”

Nan ma wani duru-duru din ta sake yi, “kowacce ma!”

A ganinta ai duniyar nan mai fadi ce, duk inda ta shiga ba zata rasa wajen zama ba.
Da jin haka direba taja mota suka dauki hanya.

Tafiya suke suna ratsa wajaje da anguwanni, direba din tana yi tana satar kallonta.

Basu yi nisa ba taji wayarta tana kara, ta duba sunan mai kira. Adda Fatima, wata tsohuwar yar aikin gidansu ce wadda tayi aure da dadewa. Da yake suna mutunci da ita tun a wancan lokacin, sun ci gaba da zumunci har a zuwa yanzu. Anan cikin Abuja din take aure don haka suna gaisawa lokaci zuwa lokaci har takan je gidan ko su suje mata ita da Anty Ummy.

Tayi kamar ba zata daga kiran ba, sai kuma ta daga ta kara wayar a kunnenta.
Fatima tace, “hello Kauthar, yau kuna gidane zamu zo muku yini ni da su Ilham?”

Tayi jim na dan wani lokaci kafin tace, “wallahi yanzu haka bana gida Adda Fatima”
Tace, “ayya, zaki dade ne, ko kuwa mu zo sai mu jiraki?”

Wata shawara ta darsu a ranta, tace, “bari kawai in zo yanzu ina cikin mota yanzu haka.”
Mamakinta ya gaza boyuwa lokacin data amsa mata da, “to, Allah Ya kawoki lafiya.”

Tafi-tafiya har suka isa Gauraka junction. Inda take can ciki yake saboda ko mota bata iya shiga, ita kuma bata iya hawa acaba ba balle tace zata hau ya kaita. Haka ta dinga hawan duwatsu tana sauka, tana bi kwararo da kwararo har Allah Yasa ta karasa dan kangon da Adda Fatima take kira gida.

Gidane da ko a cikin irin kaskantattun unguwannin nan, babu wanda ya kaishi muni.

Yayansu uku da mijinta, Kauthar tana mamakin dalilin da yasa Fatima ta iya jurewa zama a kaskantacciyar rayuwa kamar wannan a cikin rayuwarta, bayan iyayenta suna da rufin asirinsu daidai gwargwado duk da cewa a can cikin Kaduna suke.

Filin gidane tangameme, haya ce suke yi anan. Baka hangen komi sai wasu kananun dakuna guda biyu da idan aka sanya mutane goma ciki ba zai daukesu ba. Bandaki ma sai zagayeshi aka yi da itace da kwano. Daga nan kuma baka ganin komi sai filin gidan kawai.
Yayanta suna tsakar gidan suna wasa duk sunyi futu-futu da kura da dauda kai kace shekara da shekaru suka dauka wani abu mai kama da ruwa bai ga jikinsu ba.

Ita kanta Babar tasu sai taga duk ta kara munance mata, tayi karo-karo cikin wasu yagaggun riga da zani na atamfa da suka sha ruwa suka yi fari tas har ba ka iya gane ainihin kalarsu. Ko kuwa don ta jima rabonta da gidanne? Kodayake ko dama can Fatima din ita tafi ziyararsu, sau daya Kauthar ta taba zuwa gidan da suke a yanzu, wancan gidan da suka tashi da yake a Gwagwalada tafi zuwa.

A tsakar gida Fatima ta shimfida musu tabarma suka zauna don dakin nata baya shiguwa. Hargitse yake da tarkacen kaya, ga wani irin wari da yake fita.

Da kyar Kauthar ta iya daurewa ta sha ruwan data kai mata a wata yar tasa da tayi yagale-yagale.

Fatima ta watsa mata yagalallun hakoranta da suka gama dafewa da rashin gyara, tace, “Anty Kauthar muna kokarin zuwa mu gaidaku kuma sai ga ki a gidan namu!”

Dan murmushin yake tayi, “ai da yake akan hanya nake a lokacin, shi yasa kawai nace bari in karaso.”

Tace, “gaskiya ba karamin dadi ba naji kuwa. Allah dai Yasa zaki kai mana har yamma kafin ki juya, nasan sam baki son rabuwa da gida kamar wata kifin rijiya!”

Tayi wani murmushi mai ciwo, “ai Adda Fatima na ma bar gida kwata-kwata, ba zan kara komawa ba!”

Wata irin zabura tayi, idanu waje ta dafe kirjinta, tace, “me kike fada ne haka Anty Kauthar?!

Kamar ya ba zaki koma gida ba? Kaura zaku yi ne daga can ko me?!!”

Ta girgiza kai a hankali, “ko kadan. Ni ce dai nayi ra’ayin hakan!”

Fatima ta gyara zama, “akan wane dalili?!”

Kauthar bata da niyar fayyacewa wani dalilin da yasa take kokarin aikata abinda zata yi, amma data hanga da kyau sai taga cewa ai bata da wata mafita wadda tafi hakan. Saboda a lokacin babu abinda tafi bukata irin ta fadi abinda ke ranta ko Allah zai sa taji dan sauki ai cikin ranta.

Tace, “kin tuna AbdulMalik Kwangila?”

Tace, “ina kuwa zan manta dashi Kauthar? A rayuwa yana daya daga cikin mutanen da ba zan taba mantawa dasu ba!”

Ta jinjina kai, kwalla har ta fara taruwa a cikin idanunta, “shine fa… Shine fa… wai… Daddy yace zai aura min shi nan da sati biyu!”. Kuka ya nemi ya kwace mata, ta rufe bakinta da tafin hannu don kada sautin ya fita.

Ga mamakinta sai taga Fatima na fara’a, tace, “shine ma abin kuka? Lallai Kauthar! Ina ganinki a yadda kike dinnan, ashe dai sai a hankali?”

Ta daga baki da mamaki, “AbdulMalik fa nace miki? Mijin Anty Ummy idan baki manta ba!!”

Tace, “na sani ai sarai! To menene a ciki? Haram zaki aikata ne? A duniya ba zaki taba dacen miji kamar AbdulMalik ba wallahi Kauthar, idan kika rasa shi har abada ba zaki sake samun tamkarsa ba!”

Ta tabe baki, “sai me? Abu daya na sani shine ba zan taba aurenshi ba ko zamu rage daga ni sai shi a duniyar nan! Shi yasa ma na shirya shiga duniya kawai! Sai in ga wadda zasu aura mishi kuma!!”.

Fatima ta dora hannu aka kamar zata kurma ihu, sai kuma ta hau tafa hannuwa, tace, “ban taba sanin baki da wayo ba sai yau Kauthar! Wannan ai sakarci ne, akan aure kawai kike fadin wai zaki shiga duniya? Anya kanki daya kuwa?!”

Ta kawar da kanta gefe tana guna-guni.

Fatima tace, “to wallahi tun wuri ma ki canza shawara, ki nemi abinda zai fissheki don kuwa guduwa ba ita ce mafita ba. Kina da tabbacin idan kin shiga duniyar zaki tsira ne? Kauthar, ni nan ni ce shaidar kin bin umarnin iyaye da gujewa hukuncinsu. Don kuwa nima auren dole aka shirya yi mun na bijirewa iyayena, na gudu can wajen dangin Babana suka daura min aure da wanda nake so ba tare da sanin iyayena. Abin ya musu zafi har suka ce sun yafeni haihata-haihata, babu ni babu su. A lokacin ban damu ba don ina cikin giyar so.

Amma sakayyar Allah tasa ba a dade ba duk wannan soyayya da kaunar suka bi iska. Ki kalli rayuwar da nake ciki ta kaskanci da talauci Kauthar. Kin ganni nan sai in kwashe fiye da wata ban sanya mijina a idanuna ba.

Gabaki daya dawainiyar gidannan ni nake daukarta Kauthar, wallahi kafin ya kawo naira biyar yace ta amfanin gidace har na manta. Ga wulakanci da kaskanci da nake fuskanta daga gareshi, wasu lokutan haka yake dawowa gidannan a make ya sha giya ya bugu, ni da ‘ya’yana babu wanda ya bari, hakan zai samemu ni da su ya mana dukan tsiya da kyar makota suke iya kwatarmu.

Amma duk da hakan, dole in shanye komi don bani da wanda zai tsaye min a wannan bangaren. Wadanda suka tsaya min na sabawa iyayena yanzu su suke zagina da cewa ni butulu ce marar tarbiya, sun juya min baya sun kasa kwatar min yancina. Yanzu kuwa ko ni ce shugabar marasa kunya kina ganin zan iya zuwa in kalli iyayena in zayyana musu kalar rayuwar da nake ciki?!

Shi yasa nake zaune a cikin wannan ukubar da zaman rashin yanci, don bani da yadda zanyi. Don haka Kauthar, ina shawartarki da kiyi hakuri kada ki tafi ki bar gida. Idan kin gwada yiwa Daddy bayani bai fahimceki ba, sai kiyi hakuri ki rungumi kaddararki. Watakila alkhairin rayuwarki ne a tattare da AbdulMalik din.”

Kauthar ta kai babban dan yatsanta ta share hawaye a fuskarta, gabadaya sai taji jikinta yayi sanyi. Tausayin Fatima ya cika mata zuciya, ji take kamar ta dargwaje mata da kuka.

Fatima tayi dan murmushi mai ciwo, tace, “kada kiyi mun kuka Kauthar, ban cancanci jin tausayin kowa ba saboda ni na jawa kaina. Ki tayani da addu’a kawai.”

Ta kasa cewa komi sai kanta data iya daga mata.

Wayarta tayi kara alamun shigar sako daga cikin jakarta, tana dubawa sai taga Audullahi ne yake tambayarta tana gida zai je ya sameta? Ta mayar mishi da amsar cewa bata gidan amma idan ta koma zata kirashi.

Yini guda ta yiwa Fatima har sai da aka kira la’asar sannan ta fara haramar barin gidan. Da rana dambun gero ta musu suka ci, duk da cewa ba cimarta bace, taji dadinshi kuma taci sosai.

Da zata tafi ta zuge jakar hannunta, tarin kudaden dake ciki wadanda ita kanta bata san adadinsu ba ta dauko ta mikawa Fatima, tace mata ta kama sana’a tana juayawa, kuma ta bata shawarar ta dage ta nemi yafiyar iyayenta tayi sulhu dasu.

Kafin ta tafi ta kira Abdullahi tace yaje ya dauketa, acan bakin titi suka hadu dashi.

Ta bude motarshi Matrix ja ta shiga gidan gaba, kyakkyawan matashin da kana ganinshi bashi da maraba da Anty Ummy da su Aunty Aisha, ya juya yana kallonta ta cikin gilashin daya saye idanunshi dasu, “ke kuma me kike yi anan wajajen?”

Dan tsaki ta saki kasa-kasa, “to tambayau, wadanda basu gani su kyale, ina ruwanka ne?!”

Motar ya tasa yayi gaba yana gaggaba dariya, “Allah Ya baki hakuri baiwar Allah! Ba ni na kar zomon ba…!”

Bata ce mishi komi ba ta kawar da kanta gefe, don gabadaya bata cikin yanayin yin wasa da hira a lokacin.

Tayi shiru tana kalle-kalle da sake-sake a cikin ranta. Duk zaren data kamo ta kitsa sai taga ya warware kafin ma ta kai ga yin nisa. Abdullahi yana ta janta da hira da magana, tayi banza dashi. Shi kanshi haka nan ya gaji ya kyaleta.

Suna shiga gida yayi parking, taji dadi da taga har lokacin Daddy bai dawo ba. Ta juya tana kallonshi, “to saura kuma wani yaji inda kaje ka daukoni, don nasan bakinka bashi da birki!”

Ya jefa mata hararar wasa, “wai me kika daukeni ne Kauthar? Kamar wani wanda bai iya rike sirri ba?”

Bata ce mishi komi ba ta juya ta cigaba da tafiya. Ya bi bayanta da yar sassarfa, “so nake muje ki tayani rokon Aunty Aisha don Allah, wallahi aljihuna a kone yake, so nake a min refill”

Ta juya tana dan harararshi, “ai dama tunda naji ka kirani nasan da wata a kasa. Kaje can kaji da ita, ni babu ruwana”

Suka shiga falon gidan yana mata magiya da lallashi, ta kyaleshi.

Kamshi take jiyowa yana fitowa daga kicin, tana ji tasan cewa Aunty Aisha ce a ciki, watakila abinci take yi ko kuma abubuwan marmari data saba hadawa idan tana da lokaci.

Tayi hanyar kicin din, Abdullahi yana binta a baya. Aunty Aisha tana tare da daya daga cikin yan aikin gidan suna ta yanka kayan vegetables, ga abu akan wuta yana dahuwa.

Ta juya ta kallesu a kaikaice, cikin halin ko-in-kula tace, “wai dama baki a gidan?”

Wani kududun takaici ya tokare mata wuya, koda yake dama tasan za a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Bata ce komi ba ta wuce, firjin ta bude ta dauki lemun 5 alive mai sanyi ta juya ta fita daga kicin din.

Tana jin lokacin da Aunty Aisha din suka bi bayanta ita da Abdullahi yana zuba mata hira, ta haye sama ta shige dakinta ta rufe. Bata san lokacin da Abdullahi ya tafi ba, daya kirata a waya tana bayi bata daga ba.

*****

Ta gama shirin kwanciya barci kenan, har ta kashe wuta ta rufa da bargo, taji ana kwankwasa kofa.

Ta tashi ta zauna ta kunna bedside lamp, abin jinta ta dauka ta makala a kunne tare da bada izinin a shiga.

Ga mamakinta sai taga Aunty Aisha cikin shigar kayan barcin itama, doguwar riga mai hannun lace, sai ta dora karamar himar wadda ta tsaya mata a kirji.

Tasan ko menene ba karamin abu bane zai sanyata zuwa dakinta da daren nan ba, don haka ta gyara zamanta sosai tana kallonta.

A hankali, kuma cikin taku na natsuwa da kasaita -abinda Kauthar din ta tsana kuma take so a lokaci guda- ta taka har zuwa bakin gadon, kujera fara taja ta zauna daidai fuskar Kauthar.

Kauthar wadda taji kamar duniyar is closing on her, ta dan muskuta tana kallonta fuska a cune. Ta rasa dalilin da yasa, duk yadda ta kai ga son ta tsani matar, ta mata rashin kunya da tsaurin ido, take kasawa.

Itama Aunty Aisha din fuskartata a cunen take, kodayake a kodayaushe dama haka take, musamman a gareta.

Ba tare da wani bilayi ba tace, “auren dolen da za ayi miki ne ya sanyaki neman guduwa daga gida?!”

Zuciyarta tayi wani irin daka a kirjinta, da mamaki take kallonta cikin zare ido. Lamarin na matar ya daina daure mata kai, ya fara bata tsoro kuma. Mata kamar wata mai aiki da yayan aljanu?!

Wani malalacin murmushi ta saki, “kina mamaki ko? Sai dai zuwa yanzu Kauthar, ina ga ai yakamata ki daina mamakina. Rayuwarki gabadaya a tafin hannuna take Kauthar, and like it or not, ni nake juyata. Wannan dalili yasa nasan dalilinki na kin aure, har ma shirinki na barin gidannan da zarar kin kammala karatunki!”

Kauthar kai ta hau jinjinawa kawai, mamaki ya sankarar da ita a zaune har ta kasa yin motsin kirki.

Rankwafawa tayi kusa da Kauthar din, let’s cut a deal Kauthar! Ki yarda da auren AbdulMalik, ayi auren ba tare da wata matsala ba, ni kuma na miki alkawarin damka miki duk wasu bayanai akan mahaifiyarki da kike nema!”

Bata ma tsaya tambaya da mamakin yadda aka yi duk tasan wadannan abubuwa da daga ita sai Allahn da Ya halicceta suka sani.

Da kyar ta iya daga baki tace, “me yasa? Me aurena da AbdulMalik zai tsinana miki?”

Kai ta girgiza, “bai shafeki ba a halin yanzu. We don’t have much time, don haka zan baki kwanaki uku. Ina kuma son ki sani, idan har kika kuskura kika kara fita daga gidan nan da sunan guduwa, ba zan tura a dawo dake cikin ruwan sanyi ba, katti zan sa su dauko min ke a ka! Kina jina?!”

Kauthar tsabar mamaki da takaici da bacin rai, kasa magana tayi sai kallo da take binta dashi.

Ta shafa gefen fuskarta tana wani murmushin tura haushi, “be a good girl!!”

Daga haka ta juya ta bar dakin.

Ta bi bayanta da harara, ranta yana mata wata irin suya. Tsananin bacin rai yasa jikinta har rawa yake yi, ruwan hawaye suka fara bulbula daga cikin idanunta.

Wannan matar ta shigar mata hanci da kudundune.

Ta gama saninta ciki da bai, shi yasa take mata dabaibayi yadda ta ga dama.

Gashi yanzu tana nema ta mayar mata da rayuwa kamar ba tata ba!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “Kauthar | Babi Na Uku”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×