Malam ya baiwa Ammi kudi masu yawa kasancewar yana noma yana fidda amfanin gona duk shekara, sannan yana kiwo, ga gudunmuwar da Sheikh ya aiko musamman don auren kanwarsa Safifi. To kacokam abinda Malam ya fidda wannan shekarar a kan kayan dakin Safiyya ya karar dashi.
Ya hana Ammi sayar da filinta, yace ta ajiyewa kannenta suma ba jimawa zasu yi ba a gaban su, tunda duk suna sakandire yanzu.
Ammi ta cigaba da shirye shiryen tarewar Safiyyah a hankali, ta sayi wannan ta sayi wancan ta adana, yayinda Safiyyah nata dokin ga tarewar kullum raguwa yake yi. Bata san. . .