Zayyan wanda a lokacin duk ta kara rikita shi da wannan salon shagwabar da bai taba gani a tare da Safiyyah ba, har dasu shura kafa irin na rigimammun yara, ba shiri yace ya hakura, domin ta tabo wani irin feeling da bai taba ji ba a kasan ransa, ya daga mata hanauwansa sama cikin saddaqarwa da bada kai, yana dariya yana cewa “nayi saranda Sophie! Na yarda ni Zayyan mijin Ustaziyyah ne, to yaya zanyi da ustaziyya ta? Daina borin haka kinji! Na hakura na bar miki abinki, ince ko shikenan zance ya kare?".
Ita kanta Safiyyah sai da. . .