Dariya take yi sosai, ta shagaltu da dariyar shima ta shagaltar dashi cikin kallonta da shaukinta, tace “wannan kuma “C” ce Malam, don ka san bazan iya waka bane kake mun ba’a”.
Da rana ma tare suka yi girkinsu inda sukayi lunch mai saukin girkawa, jollof din shinkafa tayi musu da taji daddawa da naman saniya. Tun anan Zayyan ya fara gane kwarewar Safiyyah a girkin hausawa ne, ba girkin turawa ba, tunda har tasa daudawa a jollof. Sai ya bashi wani irin aroma da dandano, da bai saba ji ba, kuma ya masa dadi, Ammi ta musu wannan. . .