Rayuwa ta wani irin canzawa iyalin Baba Bello rana daya, fiyeda sanda yake aikin gwamnati a jami’ar Katsina.
Wani abu da zai burgeka ya kuma baka mamaki da Zayyan Bello Rafindadi shine, ko sau daya arzikin mahaifinsa na yanzu bai taba canza tsarin rayuwarsa daga wadda yakeyi a baya ba, kamar yadda ta kannensa mata ta canza. Yana nan a yadda yake. Zayyan mijin Nana Safiyyah. Don hatta Zahra da Zaitoon yanzu motar kansu suke ja mulmulalla, kalar da kowaccensu ta zaba Baba ya sai mata.
Shi kam har lokacin yana nan a yadda yake rayuwarsa tun fil azal. . .