Farkon Fari.
Garin Dandume gari ne da Allah yayiwa albarkar noma da yalwar lafiyar kiwon dabbobi. Galiban al’ummar Dandume manoma ne da ‘yan kasuwar gona, sannan da makiyaya, Dandume tsohon gari ne dake cike da tubarrakin manyan malamai na addinin musulunci kamar dai mahaifin su Safiyyah.
Safiyyah ta taba bashi labarin cewa ita FGGC Bakori tayi, kuma ta yi nasarar lashe jarrabawar JAMB da tayi a boye bada sanin mahaifinta ba, saboda ya sha alwashin shi aure yakeso zai yi mata da zarar ta gama karatun sakandire in dai miji ya bayyana, saboda shi Malami ne na kwarai, bazai. . .