Ya zamana Zayyan na taimaka mata sosai a harkar karatunta, a matsayinsa na gaba da ita a shekaru da matakin karatu a lokacin.
To shi dai Zayyan daga karshe bai tsaya batawa kansa lokaci ba, ko yaudarar kansa na tsayin lokaci, kamar yadda Safiyyah ke yaudarar kanta da cewa abokantaka ce ta karatu a tsakaninsu, ya tara hankalinsa waje daya ya gayawa kansa gaskiyar cewa ainahin son Safiyyah Dandume zuciyarsa ke yi, so tsantsa kuma na zallar soyayyar Da namiji ga ‘ya macen data dace da duka burikansa, babu wani friendship ko makamancinsa a zuciyarsa gameda Safiyyah, bayan So. . .