WANENE ZAYYAN?
Tunaninsa ya mika ya tafi ga ainahin asalinsa, tushensa da tarihin iyayensa.
Iyayensa duka Katsinawan Dikko ne na asali, gidan mahaifinsa babban gida ne ginin zamani, yana nan daga farkon shigarka shiyyar Rafindadi, wanda a yanzu ya zama ‘landmark’ na kwatancen kowanne gida a unguwar, misali da ka ce “layin gidan Bello Rafindadi” ko yaro karami zai nuna maka.
Mahaifinsa Arch. Bello dan asalin shiyyar Rafindadi ne, gabansa da bayansa can aka haifeshi, iyayensu da kakanninsu sune tushen kafa/assasa Rafindadi a Charanchi.
Gidan Bello Rafindadi ya fita dabam ne a unguwar kasancewar yafi duk wani gida a. . .