*****
A Ranar, abinda ya faru bayan ya dawo daga Dandume shine, ya dawo gida da farin cikin amincewar iznin neman auren Safiyya da mahaifinta Mallam Usman ya bashi, kai tsaye bai tsaya ko’ina ba sai falon Mamanshi Haj. Fatu.
Yana saka kafa a falon Mama, bakinsa dauke da sallama cikin doki da kaikayin baki, da kafafun Hatoon ya fara cin uban karo a bakin kofa, suka tadiye shi har suka kusa fadar dashi a kasa.
Haushi ya kama shi. Ya juya ya kalleta da manyan idanunsa, tayi shame-shame a bakin kofa wai ita tana azumin ramuwa, lokacin ana. . .