“Baba!”
Yadda ‘ya’yansa ke kiransa, bashida zafi ko kadan amma yau ya sille Mama tas da soso da sabulu, sannan yace tasa a ranta auren diyar Alaramma an yi an gama ma, sai idan su suka ce bazasu baiwa dan sa Zayyan ‘yar su ba, ko yarinya tace bata sonsa.
Yace “kuma auren ma na gata zan yi masa, ba sai na jira samun aikinsa ba, zan masa komai a matsayinsa na Da namiji daya tilo da na mallaka a rayuwata”.
Baba bai bata lokaci ba, sati daya da wancan zuwan na Zayyan gidansu Safiyyah yasa Zayyan din a. . .