Shawarar Bilkisun hajiyar ta bi domin a gabanta mahaifinta ya rasu don haka zata iya gane duk wanda ya rasu, sai tai saurin kamo hannun Ameerah tana danna jijiyoyin ta takai ɗayan hannun a saitin hsncinta amma babu sauyi sai ta kwantar da kunnuwanta a dai dai saitin bugun zuciyar Ameerah, amma babu wani sauyi sakamakon ɗaya ne Ameerah ta bar duniya ta amsa kiran mahalicci, da wani irin ruɗani da firgici shinfiɗe a fuskar hajiya farida take kallon Bilkisu kafin ta hau faɗin “taya kikai haka ta mutu bata lumfashi ”.
Wani irin kuka ta fashe da. . .