Alhaji Ummaru ya dakatar da hajiya farida dake ƙoƙarin kamo Ameerah, kafin yaci gaba da cewa “ ke ko baiwar Allah me ɗiyata tai maki da zaki rabata da ranta me ke tsakanin ki da ita ”. Ya kai ƙarshen maganar yana shirin zubda hawaye
“wallahi bani bace sharri ne suke so suyi man wallahi ban san wata Ameerah ba banma taɓa ganintaba me taiman da zan iya kasheta wallahi ban aikata ba, Hajiya ki faɗi gaskiya bakince Inkama maki akaita Asibiti ba kimasa bayani don ni ko kiyashi ban iya kashewa bare mutum ɗan Adam mai daraja. . .