Kafin Al'khalin yayi magana Baristar Aminatu ta amshe zance da cewa “ bawai ina ƙoƙarin ɗaura mata laifi bane ina son tabbatar da gaskiya ne ni Lauyace ina da ilimi da gogewar da zan iya gane mai laifi ko da kuwa da kallo da Ido ne ka duba kaga yadda jikinta yake rawa, duk wani mai hankali yasan cewa tsoro da fargaba na marar gaskiyane ”.
Ihimmm Alƙalin yayi gyaran murya kafin yace “ ƙorafi ya ƙarbu akiyaye harshe Baristar Aminatu nan kotuce ba Office ɗin ƴan sandaba bazamu iya gane mai laifi ta hanyar kallo saba sai dai zamu. . .