Tunda ta shiga unguwar ta sheda ta baro yankin talakawa ta shiga layin masu hannu da shuni, saboda wata irin sanyayyar iska da ta ziyarceta sakamakon manya -manyan shukokin dake zagaye da kowane gida, masu ƙamshi da kyau gwanin birgewa, kowane gida fayau da haske kamar ba dareba, domin kuwa duhu yayi sosai wani waje anngama sallar issha'i wani wajan kuma yanzu akeyi.
Unguwar shiru tayi tsit babu kowa kuma kowane gida akulle yake gam, haka kawai sai taji ƙirjinta yana bugawa Dam! Dam!! Da ƙarfi kuma da sauri, amma sai ta aro jarumta ta yafama kainta ta soma. . .