Ko da ya isa gidan shiru kamar babu mutane a cikin sa yana gama faking ɗin motarsa ya fito ya tunkari ƙofar falon gidan, yana shiga ya sami hajiya Farida zaune a kan one siter tana kallon TV a tasharar TRT, hannun ta ɗauke da robar Icecrem tana sha a hankali.
cike da tsananin tsanarta mai tarin yawa ya fara tako ɗaya bayan ɗaya har ya iso gabanta.
Dam! Gabanta ya daɗi domin bataji sallamar sa ba kuma bataji takonsa ba sai dai kawai ta ganshi a gabanta, hakan kuma ba ƙaramin tsoratata yayi ba.
Sai da ta ɗaure fuska. . .
