Cak suka tsaya daga ita har mai gadin dake ta yimata surutai na jan kunne
Wani irin abune yasoki zuciyar sireenah take jikinta ya fara kyarma da mazari tamkar an joganamata shoking na wutar lantarki, wani irin abu ya fara yawo ajikinta tundaga ƙarƙashin ƙafarta har zuwa cikin kwakwalwarta, zufa ta fara tsatssafomata a kowacce gaɓa ta jikinta, kanta ya ɗau wani irin turiri tamkar garwashin da yake karɓar zuga acikin ramin maƙera, tashin hankali wanda ba asamasa rana.
Kafin tayi wani ƙwaƙƙwaran motsi sai ga Alhaji a gabanta yayima hannunta wata irin cafka yajata. . .