Yana kaiwa ƙarshen maganar ya zuge glass ɗin motar ya jata aguje ya bar wajan, bayan ya baɗeta da ƙura sunkuyawa tai ta ɗau katin sai taji hawaye na bin fuskar ta kanta ya kulle ta nemi natsuwa ta rasa, so take tayi dunani amma hakan ya gaza samuwa, sai tarasa inda zata nufa tsakanin bin bayansa da kuma zuwa Asibiti don ganin halin da ake ciki, sai kawai ta fashe da kuka mai sauti azuciyata take faɗin shin kasantuwata mai kyau laifine da kowa zai dinga bibiyata anason ɓataman rayuwa, ko talauci ne ya jaman, miyasa ƙaddara. . .