Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Kirkira by Bala Anas Babinlata

Godiya

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ina godiya ga Allah Subhanahu wata’ala da ya bani ikon kammala wannan ɗan ƙaramin littafi mai suna Ƙirƙira. Na samar da littafin ne domin ya taimakawa duk mai sha’awar ya zama ma’abucin ƙirƙira ta hanyar taimakawa mutum don ya kaifafa ko ya farfaɗo da ƙirƙirarsa. A cikin wannan ɗan littafin zamu feɗe yadda ƙirƙira take aiki, da ma yadda ake gane manazarta na haƙiƙa. Da yadda ake iya amfana da sharhin manazarta don inganta ƙirƙira. Wannan littafi zai taimakawa duk wani mai sha’awar ƙirƙira ta hanyar sanin yadda zai iya faɗaɗa ƙirƙirar sa. Ina fatan zaku fa’idantu da wannan ɗan littafi.

Na gode.

Bala Anas Babinlata

ƘIRƘIRA

Ƙirƙira na nufin samar da wani abu sabo ta hanyar amfani da basira da tunani. Ƙirƙira na iya kasancewa, samar da wani abu na zahiri, irin mota ko gini ko littafi ko fim da makamantansu,
za kuma ta iya kasancewa, zayyanannen aiki kamar zane, waƙa, kiɗa, ko samar da labari.

Ƙirƙira babban sinadari ne da ake buƙata a kowane fanni na rayuwa, kamar kasuwanci, ko kimiyya, ko fasaha. Ƙirƙira bata tsaya kawai iya fito da tunani ba: ƙirƙira ta haɗa da ganowa da tankaɗewa da rairaye tunanin domin mayar da shi mai mamora.

Wani shahararren masani mai suna S. Weisburd, yana cewa:

1. Ma’abuta Ƙirƙira mutane ne da shauƙi kan ja su wajen samar da kyawawan, tsararrun abubuwa, haka nan sun gwanance wajen jurewa saɓanin fahimta tsakaninsu da manazarta. Jurewa saɓanin fahimta na nufin duk abin da manazarci zai ce game da aikinka kada ka ji haushi. Kuma kada ka ƙaddara a ranka cewa manazarcin maƙiyinka ne.

2. Shauƙin ƙirƙira ya fi jan hankalin (Ma’abuta Ƙirƙira) fiye da kuɗin da zasu samu. Ma’ana idan harkar ƙirƙira ta zame wa mutum jiki zai ji yana yinta ba don kuɗin da zai samu ba.

3. A ko da yaushe suna maraba da sababbin matsaloli da ba a taɓa cin karo da irinsu ba. Ita matsala, idan ta afku, ita ke sanya ma’abuta ƙirƙira su zage don samo hanyar warware matsala. A ƙarshe kuma wannan warware matsalar sai ya ƙara buɗe musu ƙwaƙwalwa ya kuma gogar da su.

4. Ma’abuta ƙirƙira mutane ne masu bin hanyoyin ba-zato domin warware matsala.

5. Gwanayen kasada ne, a yayin aikinsu su kan ketare iyaka domin neman sakamako.

Lallai gwanaye ne wajen kasada, amma ai ko jirgin sama ai da gwaji ya tashi.

Anan Idan ana maganar ƙirƙira, ba Ilimi ake nufi ba, sai dai fa ma’abuta ƙirƙira na da kaifin basira. Kawai dai ilimi yana ɗaya daga cikin sinadarai dake taimakon ƙirƙira. Haka nan hankali ma baya cikin abubuwan bukata. Haka nan ƙwarewa ma, akwai buƙatar ƙwaƙwalwa ta ɗan yi sako-sako kafin ta iya samar da tunanin ƙirƙira mai kyau.

Shin ana iya farfaɗo da ƙirƙira? Ko kuma idan mutum ba ma’abucin ƙirƙira ba ne zai iya koya?

Idan mutum na da ƙarancin kaifin basira a fannin kirkira, kada ya damu! Ƙirƙira halitta ce a jikin Ɗan Adam, kowa yana da ƙirƙira daidai gwargwado a ƙwaƙwalwar sa. Yana daga cikin abin da ke taimakon yara su koyi abu cikin sauri a zamanin kuruciyarsu kafin su girma. Yawancin mu mukan rasa baiwar yin irin wannan tunanin yayin da muka girma, sai dai akwai hanyoyin da ake bi domin sake farfaɗo da ita.

Ƙirƙira wata baiwa ce ta halitta, don haka kowa yana da damar ya farfaɗo da tasa. Waɗanda suka fi wasu kwarewa a ƙirƙira daga cikin mutane, sun fi su ne kawai saboda suna cikin tsarin, ko da kuwa sun sani ko basu sani ba. Wadanda ke kasa fito da zalaƙar su ta ƙirƙira, suna kasa fito da ita ne saboda, ko dai ba su da nasaba da tsarin, ko sun yi nisa da tsarin.

Farfaɗo da ƙirƙira na farawa ne daga lokacin da ka fahimci yaya tsarin ke aiki. Sanin haka zai taimaka maka ka tunkari ƙirƙira ka farfaɗo da ita, kuma ya baka damar farfaɗo da baiwarka ta ƙirƙira cikin dan lokaci.

Tsakanin hankali da ƙirƙira

Akwai ɓangarori biyu na tunani dake ba da gudummawa ga ƙirƙira:

Ɓangarorin dama da na hagu na ƙwaƙwalwa.

Wani mai bincike Roger Sperry ya gano cewa tsagi na bangaren hagu da dama na ƙwaƙwalwa na da wata baiwa ta musamman. Sakamakon bincikensa ya nuna cewa yankin hagu na ƙwaƙwalwa yana haifar da tsari kuma shike da alhakin tunani mai ma’ana. Sabanin yankin bangaren dama na ƙwaƙwalwa wanda ke da ‘yanci, ɓangaren hagu ne ke da alhakin tunanin da ya danganci ƙirƙira. Sperry ya sami kyautar Nobel da wannan binciken nasa.

Ƙwaƙwalwar Hagu: na da nasaba da:

  • Tsari
  • Ma’ana
  • Nazari

Ƙwaƙwalwar Dama: na da nasaba da:

  • Gudanar tunani
  • Gaba-gaɗi
  • Ƙirƙira

A Nazarin rinjayen kwakwalwa (brain dominance) wanda Ned Herrmann ya yi, ya inganta da ɗorawa akan binciken rabe-raben-kwakwalwar da Sperry ya gabatar a baya. Binciken Hermann ya gano cewa mutane su kan fifita ɓangaren ƙwaƙwalwa ɗaya bisa ɗaya. Misali, mutane masu dogaro da bayanai, kamar Akantoci (Accountants), suna amfani da bangaren hagu na kwakwalwar su ne, yayin da masu fasaha kan yi amfani da bangaren dama na ƙwaƙwalwar su. Ba wai mutum yana zaɓar ɓangaren da yafi so ya ƙarfafa ba ne a ƙashin kansa, sai dai mutum na iya sarrafa zaɓin.

Mafi kyawun hanyar warware matsala shi ne ta hanyar yin amfani da duka ɓangarorin na ƙwaƙwalwa guda biyu: gefen dama ya samar da ƙirƙira, gefen hagu ya tabbatar da abin da aka ƙirƙiro. Sai dai kuma abin takaicin shi ne, yawancin mutane zance kawai suka iya, wanda shi ke sanya wa su gaza wajen aiwatar da aiyukansu.

Kwanshos (Conscious) da Sabkwanshos (Subconscious)

1. Masanin ilimin Taɓin-hankali Sigmund Freud yana cewa zuciya tana aiki ne a bisa matakan tunani biyu, waɗanda ake kira Kwanshos da Sabkwanshos. Wato tunanin zahiri da kuma tunanin ilhama. A matakin Kwanshos, (zahiri) muna da cikakkiyar masaniya game da abin da ke faruwa yayin da zuciyoyinmu ke karɓar bayanai. A matakin Sabkwanshos, (ilhama) ba ma sanin ta yaya bayanan suke zuwar mana. Duk da haka, yawancin tunaninmu ya fi ta’allaka ga abin da zuciyoyinmu ke raya mana wato (sabkwanshos) . Akan kwatanta zuciya da ɗabi’ar kankara, wato kashi goma 10% a sama, shi ne ke wakiltar (Kwanshos) wato zahiri, misali shi ne abin da muke yi muna sane. Yayin da kashi casa’in 90% na ƙanƙarar yake a can ƙasa (Sabkwanshos), wato ilhama.

Misali a nan shi ne 10% na tunanin da ƙwaƙwalwarmu ke yi shi ne wanda take yi tana sane. Yayin da 90% ƙwaƙwalwarmu tana yinsa ne ba tare da tana sane da yadda tunanin ke zubowa ba. Idan marubuci ya zauna yana ƙirƙirar labari, baka isa ka ce ga takamaiman daga in da Aidiyar take kwararowa a gare shi ba, saboda Aidiyar tana zubowa ne ta hanyar ilhama. Amma idan labari ya kasance true story ne, babu ƙirƙira a cikinsa, abin nufi babu wata ilhama a cikin sa. Ana rubuta abin da ya faru ne kawai a zahiri.

Saboda haka kwanshiyos (Conscious) na da nasaba da bangaren ƙwaƙwalwar hagu. Sabkwanshos kuwa (Subconscious) da ɓangaren ƙwaƙwalwar dama yake da nasaba. Sabkwanshos, wato ilhama, na da sarkakiya wajen bayani. Ko da yake akwai nazarce-nazarce da dama game da yadda yanayin ilhama yake. Wanda hakan ke nuna akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin kwanshos da sabkwanshos, sabkwanshos ce ke lalube, kwanshos galibi a lokutan da mutum ke bacci. Wanda sakamakon daga ƙarshe kan dawo ya shafi tunanin kwanshos. Mutane kan dangantaka sabkwanshos da emotion, sai dai kuma an haƙƙaƙe cewa, ba kwanshos ce kaɗai ke sarrafa bayanan ilimi ba, sabkwanshos ma na iya sarrafa bayanan da suka shafi ilimi. Wannan ne dalilin da yasa sabkwanshos (ilhama), ta kan iya shafar mu ta ko wace hanya.

Sabkwanshos kai tsaye na bayyana wane ne kai a matsayin ka na mutum, duk da cewa ba mu da cikakkiyar masaniyar yaya aikin sabkwanshos ke wakana. Sabkwanshos na da wuyar fahimta da wuyar sarrafawa. Sai dai ana iya amfani da ƙarfin ƙirƙirarta cikin sauƙi. Tun da bamu san ainihin yadda take aiki ba, zamu iya cewa kamar a zura matsala ne ta wani bangare na na’ura, sannan a samar da mafita ta ɗaya bangaren na’urar.

Manufar wannan darasin ita ce mu nuna muku yadda za ku inganta tunanin ku don samar da kyakkyawar ƙirƙira. Tsarin yana da matakai biyu waɗanda suka haɗa da samar da ƙirƙira ta hanyar yin amfani da sabkwanshos, sannan kuma a yi amfani da duka ɓangarorin biyu, (hagu da dama na ƙwaƙwalwa) don samar da haɗakar ayyukan da ɓangarorin biyu suka saba yi.

Tsarin yana buƙatar nutsuwa, don haka zai ɗauki lokaci ana gwaji. Misali, mutumin da ya saba aikin lissafi da nazarin kudi, ko koyarwa a Aji duk tsawon rayuwarsa ya kasance yana aiki ne da bangaren hagu na ƙwaƙwalwarsa. Zai ɗauki lokaci kafin ya iya amfani da ɓangaren dama na ƙwaƙwalwarsa kasancewar ɓangarorin biyu suna aiki ne mabanbanta da juna.

Tsarin ƙirƙira

Tsarin ƙirƙira na da matakai daban-daban, kamar yadda ya zo a jerin da ke ƙasa. Lokacin da tsarin ya zama jiki a gare ka, zaka iya gane a wane matakin kake. Wannan zai iya zame maka dabi’a mai ƙarfi da zata rinƙa motsa maka sha’awar aiki.

Matakan ƙirƙira su ne;

  • Samar da Aidiya
  • Nazari
  • Ƙirƙirar tunani
  • Ra’ayin Manazarta
  • Bita

Matakan ba lallai ne sai sun kasance a jere ba kamar yadda aka rubuta su a sama. Misali zaka iya farawa da samar da aidiya, maimakon ka shiga nazari da bincike a kan aidiya ɗin sai ka yanke shawarar kawai bari ka tsallake kawai ka shiga ƙirƙirar tunanin, wato rubuta shi. A ƙarshe dai abin da ake so shi ne ya kasancewa an samar da farko da kuma ƙarshe. Kasancewarsa tsari ne na fikira, yana da muhimmanci ya zama an bar kafar tsokaci da shawarwari.

Ba za a takura kai sai an bi shi daki-daki ba. Babban abin la’akari a nan shi ne ya kamata a san lokacin da ya dace a bi shi kwabo da kwabo da kuma lokacin da ya dace a kauce don zaɓen hanyar da ta fi dacewa.

Yin amanna da tsarin

Ma’abota nasara na amfani da ƙwarewar su ta ƙirƙira wajen samarwa da warware matsaloli da zartarwa. wasun su na yin hakan ne ta hanyar ilhama, yayin da wasun su ke yi suna sane da abin da suke yi. Duk da haka yawancin mutane suna yin aiyukan su na ƙirƙira ne da ka. Ma’ana ba su da alaƙa da tsarin a yayin yin aiyukan su na ƙirƙira.

Abin taƙaicin shi ne, za ka iya kasancewa mai hazaka ko baiwa, amma daga ƙarshe baiwar ta tashi a banza muddin baiwar taka ba ta motsa ba.

Ba yin amfani da tsarin ne cikas ga baiwarka ta ƙirƙira ba, rashin amincewa tsarin yana aiki shi ne babban cikas ɗin. Sau tari mutane kan yiwa tsarin duban wani abu maras tushe da makoma ballantana har su yarda zai iya zamowa mai mamora.

Tsarin ƙirƙira yana da ƙarfi matuƙa. Ayyukan sabkwanshos da na ɓangarorin ƙwaƙwalwa sun ta’allaƙa ne kacokan, a bisa binciken kimiyya na ma’abuta kirkira. Duk da wannan ingancin, yawancin mutane suna cikin shakku. Na san da yawa daga cikinku zasu karanta waɗannan bayanan ne suna kallonsu a matsayin ƙanzon kurege!

Saboda haka, mataki na farko na cimma nasara game da harkar ƙirƙirarka shi ne ka koyi amincewa da tsarin. Me yasa? Domin tsarin na aiki! Wanda shi ne in da yawancin mutane suka gaza. Hakika tsarin yana buƙatar aiki tuƙuru.

Gano basirar ka a fagen ƙirƙira bai da wahala, abu mafi wahala shi ne koyar da kanka amincewa da tsarin ƙirƙira.

Kirkira 2 >>

1 thought on “Kirkira 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×