Aidiya (Idea)
Nazari ya nuna cewa aidiya galibi tana afkuwa ne ta hanyar mafarke-mafarke, da haɗuwar ba-zata (accidental connection) da nuni cikin surori ko alamomi (symbolic cues). Wannan yana nuna cewa tushen aidiyoyi na da nasaba da tunanin sabkwanshos, da fahimta, wato (insights) da kalmomi da hotuna dake kai-kawo tsakanin kwanshiyos da sabkwanshos in da suke sake haɗuwa don ƙara ƙirƙirar sabbin fahimta, kalmomi da hotuna.
Ga ma’abuta kirkira, kwararar bayanai tsakanin kwanshiyos da sabkwanshos na haddasa aidiyoyi su bijiro a kowane lokaci. Da zarar hakan ta faru, kwararar bayanan na iya zama tamkar atisayen sojoji. Yadda zaka ji an ruɗe da harbe-harbe ɗin nan a lokaci ɗaya. Yayin da ka zauna kana kallon ma’abuta ƙirƙira na ɓarin aidiyoyi ta irin wannan hanyar zasu yi matuƙar baka sha’awa. Irin wannan zuzzurfan matakin ƙirƙirar yana kama da na ƙananan yara. Maganar gaskiya ma dai ana ɗauko shi ne tun daga ƙuruciya. Zaku iya sake farfaɗo da basirarku ta ƙirƙira ta hanyar amfani da dabarun da zamu tattauna a nan gaba. Dabarun da zamu tattauna a yanzu, suna bayani ne a kan yadda ake zaƙulo bayanan da sukan ingiza ƙirƙira ta hanyar tilasta sabkwanshos har sai ta bayyana kanta. A wani ƙaulin kuma, sukan kurɗa cikin sabkwanshos in da kalmomi da hotuna suka a laɓe don samar da abin da zai fito da ƙirƙirar fili.
Zafafa tunani (Brainstorming)
Zafafa tunani (brainstorming) shi ne makami ko hanya mafi ƙarfi da ake amfani da ita wajen ƙirƙirar sabbin dabaru da warware matsalolinsu, musamman yayin ƙirƙirar aidiyar labari. Hanya ce dake sanya sabkwanshos zaƙulo bayanai da adana su a rubuce. Masana halayyar dan adam na kiran wannan dabarar da Free Association.
Ana fara zafafa tunani ne (brainstorm) ta hanyar rubuta aidiyar farko da ta fara zuwa a zuci, sannan sai a cigaba da rubuta duk aidiyar da ta faɗo a rai babu ƙaƙƙautawa, har sai an ƙarar da iya abin da aka iya tunanowa na kalmomi da hotuna a lokacin. Ba a so mutum ya tsaya ƙalƙalewa a wannan gaɓar, saboda yin hakan zai iya datse ɓuɓɓugar tunanin.
Bayan marubuci ya ƙarar da duk aidiyoyin da zai iya tunawa, sai ya koma ya dubi abin da ya rubuta, ya fara ƙoƙarin alaƙanta su da juna.
Akwai hanyoyi daban-daban da ake bi don zafafa tunani. Na farko shi ne taswirar zuciya, wato mind mapping.
Bayan mutum ya ƙirƙiro aidiyar da ya gamsu da nagartarta to akwai hanyoyin da ake bi don faɗaɗa aidiyar. Ita ake kira zafafa tunani wato brainstorming. Shi brainstorming akwai hanyoyi da dama na yinsa. Ga hanyoyi daban-daban da ake bi don zafafa tunani:
Taswirar zuciya (Mind mapping)
Tony Buzan ne ya fara samar da Taswirar Zuci a bisa dogaro da tsohuwar hanyar Zafafa Tunani da aka saba da ita a al’ada. A kan fara ne da rubuta aidiyar farko a tsakiyar sabon shafi. Sannan, sai a yi ta rubuta duk abin da ya faɗo a zuci game da wannan aidiyar. Ana farawa ne da rubutu kalma ɗaya ko kalmomi biyu don kada rubutun ya cunkushe ya kasa cigaba da ɓuɓɓuga. Za a iya rubuta aidiya a kusa da aidiyar da ta haifar da ita. Yin hakan zai taimaka wajen kusantar da kalmomin dake da alaƙa da juna. Za iya amfani da kowace kalma daga cikin kalmomin da aka samar a matsayin jagorar kalma wato (starting idea).
Misali idan aka fara da kalmar:
“Marainiya”
Sai kuma a rubuta:
“Hatsarin mota”.
Sai kuma kalma irin su:
“Mutuwar iyaye”
“rasa dangi”
“gidan marayu”
Haka nan dai mutum zai ta jero duk abin da ya faɗo masa a rai, kalma ɗaya ko biyu da zata taimakawa aidiyar ta cigaba da ɓulɓulowa.
Haka nan za iya rubuta kalmar da ke da alaƙa a ƙasan aidiya. Misali:
“hatsarin mota”
Sai a je ƙarƙashi a rubuta. Kamar:
“Zuwan ‘yansanda”
Ko wani abu makamancin hakan. Wannan kan taimaka a gane kalmomin dake da alaƙa da juna.
Baya ga faɗaɗa aidiyoyi, ana iya amfani da taswirar zuci don warware matsaloli. Maimakon farawa da (starting idea) aidiyar share-fage, sai a fara da matsalar da ake ƙoƙarin warwarewa.
Lotus blossom
Lotus blossom wata irin fulawa ce mai kunnuwa da yawa a gewaye da ita.
Wannan salo na zafafa tunani ya yi yanayi da kunnuwan fulawar lotus blossom, shi ya sa ake misali da ita.
Michael Michalko ne ya ɗabbaƙa wannan hanya ta zafafa tunani mai suna. Lotus blossom na kama da taswirar zuci, sai dai ita an tsara ta ne da nufin ta gaggauta samar da sakamako. Ga yadda lotus blossom take:
1. Ana raba shafi ne zuwa sassa 9 ta hanyar zana da’irori gida tara.
2. Sai a rubuta aidiyar farko a tsakiyar shafi.
3. Sai kuma rubuta sabbin aidiyoyi a cikin sassa 8 da ke kewaye; Waɗannan su ne “feda” ga Lotus Blossom.
4. Haka nan za a cigaba da maimaita tsarin a kowace feda
5. Sai a yi ta maimaita tsarin har sai an gamsu da sakamakon, ko kuma a sauya ta hanyar bin wata fedar dabam.
Yawan aidiyoyin yakan ƙaru zuwa kashi 8 a duk lokacin da aka maimaita fitar da sauran aidiyoyin. Don haka yana da muhimmanci mu bibiyi aidiyoyin da kaɗai suke kusantar da mu ya zuwa ga aidiyar mu ko matsalar da muke so mu warware.
Tambayau (Questions Question)
Wannan wani salo ne na taswirar zuci da ke amfani da salon tambayoyi maimakon jimilla. Akan fara shi ne da sigar neman ƙarin bayani, sannan sai a bi shi da ƙarin wasu tambayoyin da suka zo a zuci. Wannan salon ya fi amfani a fagen bincike, wato (research). Haka nan za’a iya amfani dashi kafin a fara (Mind Mapping) taswirar zuci don haɓaka sabuwar aidiya.
Free writing
Ana yin Free writing ne da rubutun zube maimakon jimilla. Marubuta sun fi amfani da Free writing, sai dai ana iya amfani da shi a kowane fanni tun da yana iya ɓuɓɓugo da aidiyoyi. Free writing yana iya ɗaukar kwanaki kafin a samar da isassun bayanan da ake buƙata. Babu shakka, wannan hanyar, hanya ce mai cin lokaci, amma yawanci marubuta suna son ta saboda suna sha’awar su yi ta rubutu.
Kwatanta taswirar zuciya (mind mapping) da free writing
Ana amfani da Taswirar zuci da Free Writing ta hanyar matsar sabkwanshos domin samar da sabbin aidiyoyi. Akan sarrafa aidiyoyi, da kalmomi da hotuna ta hanyar yamutsa su, har sai sun fitar da surar sabkwanshos.
Akan fara ne da rubuta jimilla game da matsalar da ake so a warware, sannan sai a wasa ƙwaƙwalwa, a yi ta rubutu, a yi ta rubutu. Bayan nan, sai kuna a dawo a daidaita jeruwar aidiyoyin da aka rubuta. Wasu sukan ajiye rubutun ya yi ‘yan kwanaki ko makwanni kafin su sake ɗaukowa su duba.
Cikas
Babbar matsalar da mutane ke fuskanta lokacin da suke Zafafa Tunani shi ne sukan soki duk aidiyar da ta bijiro musu. Ƙalubalantar aidiya a lokacin zafafa tunani kan yanke kwararar tunani! Ya kamata mu sani, Bita da Nazari wasu matakai ne masu zaman kansu, saboda haka a daure a jira har sai an zo matakin tukuna. A lokacin da ake zafafa tunani, ya kamata a rubuta duk aidiyoyin da suka faɗo. Ba a son gyara ko waskwarima a wannan gaɓar.
Amfani da taswirar zuci ko lotus blossom ana yinsa ne kamar haka:
A lokacin da aidiya ta faɗo wa marubuci a kan labarin wata marainiya da ta tashi bata san kowa nata ba a gidan marayu, amma ta samu labari hatsari iyayenta suka yi suka mutu aka kawo ta gidan marayu. Yawwa, idan mutum ya tashi zai zafafa tunani akan wannan labarin zai ɗauki farar takarda ne a tsakiyar takarda ya rubuta.
Aidiyar farko bari mu ce
MARAINIYA
To, me ke da nasaba da wannan kalmar ta marainiya a labarin?
Daga cikin abubuwan da ke da nasaba da kalmar akwai
“Hatsari”
Saboda iyayenta sun yi hatsari. Ita kadai ta tsira iyayen duk suka mutu. Saboda haka
“Mutuwar iyaye”
Zai iya zama point na gaba. Mai yiwuwa bayan mutuwar iyayen yarinyar
“ Zuwan Yansanda”
Zai iya zama point na gaba. Bayan sun dauke ta sun tafi da ita zuwa
“Police station”
Shi ma wani point ne.
Haka nan
“Rubuta rahoto”
Point ne. Yadda su Miƙa ta ga hannun
“Gidan Marayu”
Shi ma point ne.
Abin da ake nufi da wadannan points ɗin shi ne, marubuci idan ya zauna yana brainstorming points na abubuwan da zai faru a cikin labarinsa duk da point ɗin nan yake fitar da su. Saboda haka wannan shi ne daya daga cikin salon brainstorming da na yi bayani. Idan akwai wani abu da ba a gane ba to a ƙara tambaya.
Lateral thinking (Tunani a kaikaice)
Lateral thinking wata hanya ce mai ƙarfi ta samar da ƙirƙira. Edward de Bono ne ya samar da wannan hanyar, wadda ta ƙunshi bin murɗaɗɗun hanyoyi don samar da tunani da warware matsaloli. Ma’ana, maimakon a tunkari matsala kai tsaye, sai a tunkare ta a kaikaice. Akwai hanyoyi da yawa na yin hakan, mashahurai daga ciki su ne:
“IS NOT”
Wata hanya ce mai ban sha’awa ta samar da sabbin aidiyoyi ta hanyar ƙwaƙulo mene ne kishiyar aidiyar ka. Wato mene ne abin da aidiyar ka ba ta ƙunsa ba. Misali, yayin da kake ƙoƙarin ƙirƙirar wani abu, zai taimaka ƙwarai idan ka baje abin da nufin ka gano waɗanne abubuwa ne aidiyar ka bata ƙunshe dasu.
Wanda hakan zai ƙara armashin aidiyar da ka ƙirƙira ya kuma fito da gundarin abubuwan da baka sanya ba.
Sauya mahanga (Change perspective)
Sauya mahangar aidiya ko matsala, wata hanya ce dake taimaka wa kwararar aidiyoyi. Akwai hanyoyi da dama na yin haka: canza wuri; canza lokaci ko canza zamani, canza sakamako (watau kamar mutum ya juya nasara zuwa rashin nasara). Akwai buƙatar ware lokaci na musamman don zafafa tunani (brainstorm) domin zaƙulo yadda za a iya sauya wa aidiya mahanga.
“Me zai faru idan?” “What if?”
Wannan ma wata dabara ce da ‘yan wasan kwaikwayo ke amfani da ita don zaɓar hanyoyin da zasu bi yayin aiwatar da wasan kwaikwayo. Hanya ce mai burgewa da suke amfani da ita wajen haɓaka ƙirƙira. Da fari, sai an bayyana matsalar da ake ƙoƙarin warware wa, sannan a yi tunanin me zai faru idan aka sauya wasu abubuwan. Ga wasu ‘yan misalai:
- Mai daukar hoto zai iya tambaya “me zai faru idan” fitilar ta hasko daga wajen dakin maimakon daga cikin ɗakin?
- Marubucin labari zai tambayi “me zai faru idan” wanda ya yi kisan kan ya zama ɗan’uwan jarumin? Wato masoyinsa?
- Daraktan shirin zai iya tambayar “me zai faru idan” aka bar ɗan kallo ya san abin da jarumi bai sani ba?
Ajiye zato (Drop assumptions)
Kowace matsala tana da wani zato a ɗamfare da ita, wanda ba a faye baiwa zaton wani muhimmancin a-zo-a-gani ba. Ingantacciyar hanyar da ta dace a bi don ɓulɓulo da aidiyoyi ita ce, a sauke ko a ajiye zaton ɗaya bayan ɗaya, don ganin yadda sakamakon zai kasance. Warakar da ake nema na iya ɗamfaruwa da wani rarraunan zato ko ma gurɓatacce gaba ɗaya.
Maida matsala baya (Reverse the problem)
Yayin da wani abu ya ƙi yin aiki, hanya mafi sauƙi ta samar da mafita ita ce, a lissafe duk abubuwan da ke aiki. Misali, idan kana rubutu, sai wani scene (fitowa) ya ƙi samuwa daidai, sai ka jera duk abubuwan da suke daidai, ka tsame su gefe daya, yin haka zai baka damar ka gane abin da ke da matsala a ciki. Hanya ce ta tankaɗe da rairaya don gano tushen matsala.
Ƙarfa-Ƙarfa (Forced analogy)
Hanya ce ta kwatanta matsalar abu da wani abu can da basu da alaƙa da juna. Misali, kwatanta matsalar yin fim da matsalar aikin gini na iya bayyana wasu abubuwa masu kama da juna. Ko da yake su biyun na iya zama kamar ba su da alaƙa a zahiri, amma dukkansu sun haɗu a fannin tara ma’aikata daban-daban da buƙatar kala-kalar kayan aiki. Saboda haka za a iya ɗaukar dabarun da aka warware matsala a wancan fanni a yi amfani da shi don gyara ko inganta wannan fanni.
Murza tsohon tunani ya dawo baya
Wasu ƙwararru na bayar da shawarar yin amfani da dabarar nan ta ƙoƙarin gano abin da hankalin sauran mutane bai kai kai ba. A sauran sana’o’I wannan ba zai taɓa yiwu ba. Saboda basu yarda da shigege ba, suna yin komai ne yadda ya zo a ƙididdige. Hanyar da zaka iya tunkarar wannan ita ce ka juya wani tsohon tunani ta hanyar mayar da shi sabo.
Ga wasu sharhi nan daga wasu manazarta:
“Mawaƙin da bai goge ba sai dai ya yi kwaikwayo; Gogaggen Mawaƙi shi ke satar fasaha.”
-T. S. Eliot
“Me ake kira Sahihi? Satar Fasahar da ba a gano ba.”
– Dean William R. Inge
Jaridanci (Journaling)
Za a iya cewa kamar wani kundin adana bayanai ne, wato (diary). Kamar dai yadda Kaikaitaccen Tunani (literal thinking) yake, amma ba (literal thinking) ba ne kai tsaye. Hikimar ita ce ana iya yin bita lokaci zuwa lokaci don nemo jigogi, da hotuna da connection. Idan da fasahar journaling za ka yi amfani kana iya shigar da bayanai aƙalla sau ɗaya a rana. Babu wata ƙa’ida game da yawan bayanan da zaka iya shigarwa: bayanan zasu iya zama daga kalma daya zuwa shafuka masu yawa. Tun da wasu bayanan ba za a iya bayanin su cikin sauƙi ba, zaka iya zana ko da hotuna ne!