Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Kisan Boko by Faisal Haruna

Duniya gidan kashe ahu, duniya mai yayi ta ɗauka ta ajiye duk inda take so a kuma loƙacin da take so. Duk da na daɗe da haddace wannan kirarin da ake yi wa duniya hakan bai zama linzamin jan ragamar tunanina zuwa ga nemo fassarar su ba; har zuwa loƙacin da kwale-kwalen rayuwata ya yi karo da ƙaton dutse a loƙacin da yake tsaka da sheƙa gudu a tsakiyar teku.

Iya ruwa fidda kai, sai dai a wannan gaɓar fitar da kaina daga cikin kwale-kwalen da nake ciki ya zamo mini jidali, domin tuni manejin gudun shi ya ƙare har sai da ya dangana da ni tashar da na sani. Rayuwar ta zame mini gaba ƙura baya siyaƙi. Fitilar da take hasko mini irin taɓargazar da na gabza a loƙacin da nake kan sharafina, loƙacin da ludayina yake kan dawo tuni hasken ta ya fara dusashewa kamar yadda kyawun jiki da fuskata suka fara yi mini sallamar bankwana.

“Yaushe za ki yi Aure?” Tambayar da har yanzu da na gama ƙure malejin tunanina na kasa lalubo amsar ta. Duk yadda zuciya ta kai da buga tsere, tawa zuciyar tsayawa take yi cak a duk loƙacin da aka yi mini wannan tambayar. Duk da ƙudurin auren duk wanda ya zo gare ni da kalmar so sai dai kuma na san na makara domin an bar kari tun ran tubani.

Na ƙara sakankancewa da lamarin duniya a loƙacin da na tsinci Talatata a Laraba. Addu’a da kai kukana ga Allah su suka zama makamin da yake rage raɗaɗin rashin auren da ke damu na. Kyawun jiki da na fuskar da nake tutiya da shi tuni ya fara zama tarihi kamar yadda samarin da suke shige da fice a ƙofar gidanmu tuni sun watse tamkar tantabarun da aka jefa da sanda a loƙacin da suke tsakiyar kiwo.

Na yi ɓatan ɓaka tantan mutuwar almuru, ba ni ga tsuntsu ba ni ga tarko. Karatun bokon da na ɗora burina gabaɗaya a kan shi tuni na kammala digiri na biyu har na tsunduma dumu-dumu cikin cin gajiyar shi, sai dai rashin aure ya zama cikas wajen sharɓar romon karatuna. 

A duk loƙacin da rana za ta hudo ba ni da abincin karya kumallo sai tunanin rashin aure na tare da neman dalilin da ya sa na koma tamkar jaɓa a wajen samarin da suke bi na ina korar su. Halin da nake ciki ya mayar da ni tamkar kazar da aka tsoma a ruwan sanyi. Shiga cikin ƙawayena kuwa tuni na assasa ƙaton shinge a tsakani, domin kariya daga tuggun shaiɗan da ka iya miƙa mini goron gayyata har hassada ta samu matsuguni a zuciyata. Domin kafatanin su daga mai yara biyar sai mai bakwai, waɗanda aka yi musu aure kafin mu kammmala sakandire kuwa ba kowa ke iya bambance uwar da yarinyar ba; ga waɗanda suka haifi yara mata a farko. Sannan da yawan su auren bai hana su ci gaba da karatu ba kamar yadda na yi wa kaina huɗubar ba a haɗa gudu da susar katara.

Na ƙara shiga ɗimuwa ne a loƙacin da zaren ƙaddara ya nannaɗo ni zuwa ga ofishin tsohuwar ƙawata wadda tuni na ɗebe tsammanin ƙara ɗora kwayar idona akan nata. Yanayin yadda ta ambaci sunana ya ƙara tabbatarwa da zuciyata gaskiyar abin da idanu ke gani.

Cikin nutsuwa zuciyata ta tafi gudanar da aikinta wanda cikin daƙiƙun da ba su haura uku ba ta harba saƙo mai gamsarwa zuwa ga ƙwaƙwalwa.

“Aisha Yusuf!” Na ambaci sunan da ƙarfin gwiwata ina ƙare wa hamshaƙiyar matar da take zaune da farin tabarau a fuskarta kallo.

“Ikon Allah! Ashe rai kan ga rai wai ɗan koli yaga fura? Ai ban yi tsammanin zan iya shaida fuskar ‘yarbokonmu ba”

Ta ajiye maganar cikin sigar zolaya ne, sai dai ta ɓangare na ambatar kalmar ‘ƴarboko’ da ta yi, ya zame mini tamkar harbin kibiya mai dafi a ƙahon zuciyata ne. Domin, tamkar yaɗuwar wutar daji haka sunan ya gama karaɗe kafatanin zuri’armu da zama cikin su tuni ya yi mini ƙamshin ɗan goma.

“Dakta Sa’a zan ce ko Farfesa Sa’a; domin na san tuni an taka wannan matakin a karatun boko?”

Na mujiya na zuba mata tare da tilasta wa kwakwalwata son gano manufarta ta jifa na da waɗannan kalaman masu zafi.

Murmushin yaƙe na ƙirƙiro na shimfiɗa shi a dandamalin fuskata da ta daɗe da yin adabo da ganin hoda.

“Aisha kenan, kina nan ba za ki sauya ba ke dai…”

Maganata ta tsinke a loƙacin da ganina ya sauka a kan tamfatsetsen hoton da ya samu gurbi a bangon Arewa na ofis ɗin, igiyar sadar da saƙonni na ta fara aikin ta domin da gani babu tambaya, haka ido ba mudu ba ya san ƙima. Murmushin da yake shimfiɗe a fuskokinsu kaɗai ya isa ya fallasa nishaɗin da suke ciki. Cikin azama na fara yaƙi da tsokar da take maƙale a ƙirjina. Wannan hoton ya tsinka duk wani hange da hasashe da nake yi. Ya tabbatar mini hangen Dala ba shi ne shiga birni ba. Burina na nemo inda Iro yake, take na gabatar da jana’izar shi.

Tsam! na miƙe ina ƙoƙarin daidaita natsuwata yadda zan ji ƙarfin jan kasalallun ƙafafuwana da ke ƙoƙarin tilasta mini komawa na zauna. Ban san gidan rina na kawo kaina ba sai yanzu. Igiyar nadama ta yi dirar mikiya wajen yi mini ɗaurin huhun goro.

Ban saurari kiran sunana da Aisha take yi ba na zarga wa karena igiya kafin na kai ga zama nama a da’irar da na faɗo domin farauta.

Kaico! Na yaudari kaina; na biye wa ruɗin duniya na ɗauki huɗubar ƙawaye da kullum zancensu bai wuce ba a haɗa taura biyu a baki ba. Aure da karatu ba sa haɗuwa a inuwa ɗaya. Busar sarewarsu ta yi zaƙin da ya ba ni damar taka rawa, amma kuma tsalle-tsallen da na yi ya gurɓata rawar. Da a ce rayuwa kamar hannun agogo take da tuni na dawo da tawa baya domin gyara kuskuren da na aikata.

‘Aisha Yusuf idan kin ji haushi ki aure shi mana. Ai ban hana ki ba. Ki dubi zubi da tsarin halittata ai kin san ruwa ba sa’an kwando ba ne. Sama ta yi wa yaro nisa wallahi kamar yadda kika sani bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne.’

Irin waɗannan kalaman su ne suka zama ruwan da nake shayar da Aisha a duk loƙacin da ta same ni da ƙoƙarin kafa gwamnatin Iro.

Kalmar ‘Ki je ki aure shi’ kuwa da a ce tana tsiro da tuni ta daɗe da game jikin Aisha. Wannan ya sa ban yi mamaki ba a loƙacin da labarin auren Aisha da Iro ya riske ni. Sai ma shige wa gaba da na yi aka yi hidimar komai tare da ni. Hidimar karatuna kuwa da ita nake fakewa wajen ƙin halartar duk wani taro da ya danganci ƙawayena na sakandire hakan ya sa duk suka fita sabgata, ni a wajena ruwa ta sha.

A daddafe na iya kai kaina gida. Ga gida ga aiki ga kwalin digiri har guda biyu amma sun gaza wajen cike babban giɓin da ke watangaririya da rayuwata. Gaban madubi na yada zango bayan idanuwana sun sauka a kan hotona da yake maƙale a bangon ɗakin, na ɗauki hoton a loƙacin da duniya take yi mini huɗuba , loƙacin da kyawun jiki da na fuska tare da burin karatun boko ke yawo da ni a sararin samaniya. Tsayuwata gaban madubi ya sa na tabbatar lallai ruwa ya ƙare wa ɗan kada.

Jibril shi ne sunan da ke rubuce ɓaro-ɓaro a jikin kamfafacen hoton nawa da na kasa ɗauke magainana a kansa, tabbas Jibril ya kai ya amsa sunan masoyi a duniyar soyayya. Amma, a wancan loƙacin bai yi sa’ar dasa soyayyarsa a lambun da ya dace ba, duk da kwarewar shi da naci wajen ganin yabanyarsa ta yi yaɗon da zai iya amfana da ita. Na wahalar da Jibril fiye da yadda tunanin mai hankali zai ɗauka, a yau ga shi Jibril ya yi mini fintinkau domin na san a yanzu ruwa ba sa an kwando bane. Ƙarar wayata da ta karaɗe ɗakin shi ya tilasta yankewar igiyar tunanina. Da kakkausar murya mahaifiyata take jaddada saƙon nema na a gidanta cikin gaggawa, ɗamarar da na ɗaura na ƙin bijire wa mahaifiyata a karo na biyu kamar yadda na yi watsi da nasiharta a baya su suka ja ragamata a loƙacin da ta titsiye ni da batun ta gaji da zamana a haka dangi suna yi mata shaguɓe domin uwar ‘yarboko tuni ta yi sabo da wannan sunan.

Da a ce za a duba gudun jinina ba makawa za a tabbatar da cewa ya yi tashin gwauron zabi. A loƙacin da na ke tsakiyar tunanin yadda duniya ta yi mini gwatson kuliya. Allah ya jefo mini Alhaji Sale shugaban direbobin ma’aikatarmu, ban tsaya duba yawan iyalansa ba ballantana girman matsayin da na fi shi na bayar da kai bori ya hau. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×