Skip to content
Part 1 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

JAN HANKALI

Wannan littafi ƙirƙirarre ne, ban rubuta shi don cin zarafin wani gari ba. Asali ma littafin na ‘yan kowane gari ne, idan kina Kano ne, to ki ɗauke shi a matsayin KISHIYAR KANO, na sa jihata ne don ni ‘yar Katsina ce, ke ma ki kalli labarin da sunan jiharki, ta haka ne za ki fahimce shi.

Durƙushe take a gaban mijinta mai suna Khamis, wanda ke zaune a gefen gado yana ƙare mata kallo. Idanunta cike da ƙwalla ta dube shi tare da yin magana cikin raunin murya ta ce, “Ni fa ban ce zan hana ka ƙara aure ba, kawai dai ‘yar Katsinar ce bana so.”

Ɗago kafaɗunta ya yi tare da faɗin “Tashi ki zauna.” A ƙasan ransa kuma yana mamakin sauyawarta na lokaci ɗaya, don tun da ya fara zancen ƙara aure take ƙoƙarin danne kishinta, amma da jin ‘yar Katsina ce zai aura sai rauninta ya rinjayi ƙarfinta.

Bayan ta zauna a gefenshi ne ya jefo mata tambaya cikin taushin murya, “Meye aibun matan Katsina da ba kya son in ƙara aure da su?”

Ƙara raunana murya ta yi sannan ta ce, “Kowa ya shaida Katsinawa mugun asiri gare su yanzu kana auro ta sai ta raba mu da kai, ni kuma shi ne bana so.”

Ko da jin hujjar da ta bayar sai ya gane ‘yan zuga ne kawai ke son rikita mata lissafi, saboda ba inda ta san Katsinawa bare ta yi musu wannan muguwar shaidar. Cewa ya yi, “Kin taɓa ganin wanda suka yi ma asiri?”

Shiru ta yi saboda ba ta taɓa gani ba. Ya numfasa sannan ya ce, “To Aisha ki dena kula ‘yan zuga, don ba inda za su jefa ki sai cikin ruɗani.”

“Wallahi ba wani batun ‘yan zuga a nan.” ta faɗa tare da sake fashewa da kuka, saboda ta fahimci ƙorafinta bai karɓu ba.

Yadda take kukan ne ya ba shi tausayi, lallashinta ya shiga yi da maganganu masu tausasa zuciya. Ya ce, “Aisha ki kwantar da hankalinki, bana jin ƙarin aurena zai rage ko da ƙwayar zarra na son da nake maki, kuma yarinyar da zan aura kowa ya shaida bata da matsala, don haka nake da yaƙinin ba zata taɓa zama matsala a gare ki ba.”

Ido ta lumshe tare da

haɗe gululun baƙincikin da ya tokare mata zuciya, a ɓangare ɗaya kuma tana ganin tunda har zai mata kishiya alhalin haihuwarta biyu, to ba wani sauran sonta a ransa, kawai dai yana faɗin haka ne don ya kare kansa. Ba za ta iya fitowa kai tsaye ta ƙaryata shi ba, sai dai ta yi mishi hannunka mai sanda. Don haka sai ta ce, “Ba zan yi maka musun so ba, amma ba sai ka ɓata lokacinka wurin faɗa ba.” Rufe bakinta ya yi daidai da fitar siraran hawaye a idanunta, bayan hannu ta sa ta cigaba da gogewa.

Kai kawai ya girgiza, don ya san kishi ne ke ta ɗawainiya da ita. Bai fasa lallashinta ba, don ba zai so ta ce ya wulaƙanta ta saboda ƙarin aure ba. Jin shi kawai itama take yi, mafarin yana fita kenan ta kira aminiyarta da ake ma laƙabi da Zuzee a waya, labarta mata yadda suka yi da Khamis ta yi, saboda ita dama ke tsara mata komai. Tsaki Zuzee ta ja tare da faɗin, “Ke rabu da shi, ƙaryar so yake miki, kuma don yana son yarinyar ne yake wani kare ta, amma waye bai san mugun halin Katsinawa ba.”

Tsoro bayyane a fuskar Aisha ta ce, “To Zuzee ni yaya zan yi da shi, wallahi tsoron asiri nake yi.”

“Ki kwantar da hankalinki, muma ai mun iya irin namu shige-shigen.” Zuze ta ba ta amsa.

Ruwan rubutu ta kawo ma Aisha ta ce su riƙa sha ita da yaranta har da Khamis, wai duk kariya ce daga asirin Katsinawa, tunda dai maganar aure tana nan daram.

Da yamma liƙis Khamis na zaune a falo ta kawo mishi ruwan rubutun a kofi, ɗan yamutsa fuska ya yi tare da tambayar ta, “Mene ne wannan haka?”

“Ruwan addu’a ne,” ta bashi amsa, sai da ya ƙara kallon kofin da kyau sannan ya ce, “Kuma shi ne baƙi haka?”

Aisha ta ce, “Eh, ka daure ka sha.” Bayani ta yi mishi wai na kariyar jiki ne. Ba tare da ya tambaye ta inda aka same shi ba ya ɗan kurɓi kaɗan, saboda ya san ƙawayenta ‘yan zuga ne suka kawo mata, kuma da sannu zai raba ta da su, don ba zai so su rikita mishi ita ba.

“Ka shanye mana Abban Haneef.” ta faɗa tare da maraicewa.

“Ba na jin ƙishirwa yanzu, amma ki kai shi ɗakina a fridge, anjima zan sha.”

Karɓar kofin ta yi tare da yin abin da ya ce. Aikuwa yana komawa ɗakin ya juye ruwan a flowers ɗin dake bayan windown ɗakinsa, don ba zai iya sha ba. A saman fridge ya aje kofin, sannan ya shiga banɗaki ya yi alwalar Magariba, yana fitowa ya sanya baƙar jallabiyarsa. Kofin ya ɗauka ya kai mata kitchen, sannan ya kama hannun Haneef suka tafi masallaci.

Ganin kofin ya tabbatar mata da ya shanye, aikuwa kusan kullum sai ta kawo mishi, bai taɓa musun karɓa ba, kamar yadda bai taɓa sha ba, saboda yana cewa a’a rigima za ta tashi. A zihiri kam Aisha ta samu nutsuwa, amma a baɗini cikin tashin hankali take, kullum gani take kamar ƙarshen farincikinta ne ya zo. Khamis kuwa ya fahimci ba ta da nutsuwa a zuciya, mafarin ya ƙara ƙaimi wurin faranta mata rai kenan, duk sa’adda ya ga ta yi jugum, to sai ya san abin da zai mata wanda zai sa ta dariya.

A lokacin da Auren ya gabato ne ya ɗauke ta suka nufi wani katafaren kanti, kayan ɗaki na gani na faɗa ya siya mata. A ɓangaren lefe ma duk abin da ke cikin akwatin amarya itama akwai shi a nata, yaranta 2 ma sai da ya haɗa musu nasu lefen, daga ƙarshe kuma ya damƙa mata kuɗi masu yawa ya ce “Idan zan dawo aza room in ji canji.”

Butulu ne kaɗai ba zai iya gode ma Khamis ba a kan Alkhairin da ya yi ma Aisha. Sosai itama ta gode mishi, sai dai maimakon ta fara gyaran jiki da kuɗin, sai ta ɗibi kaso mai yawa ta ba Zuzee, wai za’a yi mata addu’ar dangana, saboda tana ji kamar itama za ta iya cutar da amaryar idan ta shigo. ‘yan kuɗin da suka rage kuma ta yi gyaran jiki da su.

A daren ɗaurin auren kuwa kasa bacci ta yi, Khamis da shi ma baccin ya ƙaurace ma Idanunsa saboda farinciki ya tashi zaune, tsam ya ɗago ta tare da yi mata lafiyayyar runguma.

Tambayarta ya yi cikin raɗa, “Aisha har yanzu ba ki yi bacci ba?” Saboda ya lura tunda ta kwanta take ta juye-juye.

Sai da ta matse ƙwallan tausayin kanta sannan ta yi magana cikin muryar kuka da cewa, “Ta yaya zan yi bacci a daren da mijina zai damƙa rabin soyayyar da yake mini a hannun wata?”

Ido Khamis ya lumshe, cikin ransa yana jin wani irin tausayin ta da ya fara zame masa jiki.

“Aisha ban san da wane baki zan tabbatar miki da son da nake miki yana nan daram ba, amma ina so ki ɗauki wannan auren a matsayin wata ƙaddara, wadda muke fatan ta zama mai kyau a garemu baki ɗaya.”

Cikin sigar lallashi ya ci gaba da faɗa mata maganganu masu tausasa zuciya. Ba su suka kwanta ba sai da Khamis ya ga ta samu ‘yar nutsuwa tukunna.

Da ƙarfe huɗun Asuba suka tashi, wanka suka gabatar da ‘yan nafilfili, bayan gamawarsu kowa ya roƙi Allah buƙatarsa, shi dai Khamis fatansa shi ne Allah ya sa su je ɗaurin aure lafiya kuma su dawo lafiya. Aisha kuma roƙonta Allah ya sassauta mata wannan azababben kishin da ke addabar zuciyarta.

Da sanyin safiya kuma Khamis da Haneef suka fara shirin tafiya ɗaurin aure. A ɗan lokaci kowannen su ya fito cikin farar getzna da aka ƙawata aikin babbbar rigar da blue ɗin zare, hular da suka sa ma ta dace da aikin rigar. Haneefa na ganin su ta kama kuka, wai sai an tafi da ita, dabara Khamis ya yi mata ya ce “Je ki ce ma Anty Hafsat ta yi maki wanka.”

kasantuwar a gidan ƙannensa mata suka kwana, da gudu kuwa ta ruga a ɗakin da su Hafsat ɗin suke.

“Abba mu tafi kafin ta dawo.” Cikin zaƙuwa Haneef ya faɗi, don ya san wayau ne aka yi mata.

Sai da Khamis ya ɗauke dubansa akan Aisha da itama ta kafe shi da idanu sannan ya ce ma Haneef, “Bari Mommy ta fesa mana turare.”

Murmushin yaƙe Aisha ta yi sannan ta ɗauki ƙayataccen turaren da ke kan dressing mirror ta shiga fesa musu, cikin zolaya kuma ta riƙa faɗin,

“Ango ka sha ƙamshi.”

Dariya kawai Khamis ya yi, sannan ya tura Haneef waje.

Jawo ta ya yi dai-dai lokacin da take faɗin,

“Ka yi kyau mijina, Allah ya sa ku je lafiya, kuma ku dawo lafiya.”

“Amin Habibty, godiya mai yawa.” ya faɗa tare da sumbatar ta a goshi. Irin wannan kulawar ce Aisha ta tsani wata mace ta same ta a wurin Khamis, kasantuwar sa mutumin da ya ƙware a wurin cire ma mace damuwa.

“Aisha ki iya control ɗin damuwarki kin ji, kada ki bari a taron da za a yi a gane kina da damuwa, kaɗan za ki yi kuskure mutane su samu abin faɗi.”

Ɗaga kanta ta yi alamar ‘zan kula’ lokaci ɗaya kuma ta maida kan ƙirjinsa. Sun ɗan ɗauki lokaci ba tare da ɗayansu ya yi magana ba, daga bisani suka fito falo.

Sosai ƙannensa suka yaba kyawun da ya yi, fatan dawowa lafiya suka yi mishi, Haneefa kuwa tana can cikin towel, wai sai ta tsane sannan za a shirya ta.

Falo Aisha ta zauna suka cigaba da hira ita da ƙannen Khamis, a zahiri ba za ka taɓa cewa tana da damuwa ba, a baɗini kuwa ji take kamar zuciyarta za ta buga.

Washegari ran walima ne takamaiman abin da take ta ƙoƙorin ɓoyewa a zuciyarya ya fito fili. A wurin buɗar kai ana damƙa mata amanar Amarya ta ce, “Amana wuya gare ta, don haka ban karɓa ba.” Wannan magana da ta yi duk shawarar Zuzee ce, domin sun daɗe a jiya suna ƙullawa da kwancewa. Sosai ta ba kowa mamaki, musamman danginta da na Khamis, saboda basu taɓa tsammanin haka daga gare ta ba.

“To ba damuwa, In sha Allahu mu ‘yarmu za ta riƙe ki da amana, saura kuma ya rage naki.” In ji Gwaggon Amarya.

Jiki ba ƙwari ta miƙe tare da kama hannun Amarya da ke ta mazurai a cikin lifaya ta ce, “Mu je Maryam.”

Kishiyar Katsina 2 >>

2 thoughts on “Kishiyar Katsina 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×