Skip to content
Part 10 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Lokaci mai ɗan tsayi Khamis da Maryam suka ɗauka ba tare da rabuwa daga jikin juna ba. Faɗin irin farincikin da kowannen su ya samu kansa a ciki ma ɓarnar baki ne, musamman Maryam da idan kewar sa ta motsa mata sai dai ta rungumi pillow, shi kuwa yana da wata matar da yake ɗebe kewa da ita.

A hankali Khamis ya buɗe idanunsa da suka fara ƙanƙancewa saboda shauƙin da raɓar jikinta ya saka shi, ɗan janye jikinsa ya yi tare da dafa kafaɗunta duk a lokaci guda.

Hakan ne ya yi sanadiyyar buɗewar fararen idanun Maryam gami da sauke su a kan fuskarsa da ke ɗauke da mayalwaciyar fara’a. Sosai suka ga ƙaruwar kyawun junansu fiye da can baya.

Kallon fuskar Maryam kaɗai bai wadatar da Khamis ba, hannunsa ya ɗauke daga kafaɗunta ya maida su saman kanta tare da yaye mayafin da ta lulluɓa da shi ya ajiye shi a kan kujerar da ke gefensu.

Take cikakkiyar surarta ta bayyana a cikin riga da skirt na red ɗin sweez less.

“Ma sha Allah!”

Ya furta a fili, cikin ransa kuma yana jin ƙaruwar shauƙin sonta yana ɗibar shi.

Ita ma irin abin da yake ji a zuciyarshi ne take ji a tata zuciyar lokacin da ganinta ya haɗu da nashi.

A hankali ta lumshe idanu tare da buɗe su lokacin da ya tallabi kumatunta ya ce,

“Haka kika ƙara kyau?”.

Murmushi mai sauti ta yi tare da faɗin,

“Kai ma ai ka ƙara kyau.”

Ɗan rau ya yi da idanu tare da faɗin,

“Da gaske na ƙara kyau?”

Ta ce,

“Allah kuwa.”

Murmushin jin daɗi ya yi sannan ya ce,

“Ba zan miki musu ba, amma na san soyayyarki ce ta sa na ƙara kyau Mairo.

Ni kaina na san tunaninki shi ne lafiyayyen abinci ga ruhina, shi ya sa na ɗauke shi abin yi a dukkan dare da rana. Don haka ina ƙara tabbatar miki da ina son ki, son da ake kira so.”

Hannayensa a kan kafaɗarta ya ƙarashe maganar, lokaci ɗaya kuma ya sumbaci ɗan ƙaramin bakinta da farinciki ya hana ta rufe shi.

Maryam ta rasa sirrin da ke cikin lafuzzan Khamis, saboda duk lokacin da ya furta mata su sai ta ji kamar ta fi sauran mata sa’a a rayuwa, cikin murya mai jan hankalin mai sauraro ta ce,

“Na fahimci kasancewa da kai shi ne mafi farincikin lokaci a wurina, don haka nima ina sonka mijina.”

Sake maida ta ya yi jikinsa, kalmomi masu nuna soyayyarta a gare shi ya cigaba da raɗa mata a kunne. Sun ɗan ɗauki lokaci a haka sannan suka rabu da juna. A ƙasan carpet suka zauna, abincin da Maryam ta kawo mishi ne ta yi serving ɗinshi, sinasir ne da miya, ɓangare ɗaya kuma ga pepper chicken nan sai tashin ƙamshi yake.

Sosai ƙamshin girkin ya tafi da Khamis, ce mata ya yi,

“Hala ke kika yi girkin nan?”

Kai ta girgiza,

“A’a Hajiyarmu ce, ta ce ba wanda zai ma surukinta girki sai ita.”

Khamis na dariyar samun matsayi a wurin Hajiyarmu ya ce,

“Wow! Sai ni ɗan gatan Hajiyarmu.”

Maryam na dariya itama ta ce,

“Ai tana ji da kai.”

Ya ji daɗin samun wannan matsayi a wurin Hajiyarmu, ya san ba ita kaɗai ba kowa na gidan ma yana son shi, duba da irin farincikin da ahalin gidan suka yi lokacin da ya zo. Tabbatar mata da tashi soyayyar shi ga family ɗinta ya yi.

Farinciki fal a zuciyarta ta gutsuri sinasir tare da sanya miya ta ce, “Buɗa bakin na ciyar da kai bebina.”

Cike da soyayyarta ya buɗe bakin. Kamar ƙaramin yaro ta riƙa saka mishi sinasir da naman yana karɓa, sai da ya cika cikinsa sannan ya tsotse mata yatsu tas.

Ruwa da lemu ya sha, ya na gyatsewa ya ce,

“Alhamdulillah, Allah ka ƙara ma Annabi S.A.W daraja, sannan ka albarkaci Katsinawan Dikko, saboda komai na su na daban ne.”

Dariya Maryam ta yi sannan ta ce, “Amin ya Allah.”

Kimtsa komai ta yi a gefe, sannan ta dawo daf da shi suka cigaba da hirar mun yi kewar juna. Tun tana zaune a gefensa sai gashi ta dawo saman cinyarsa.

Ganin yadda duk ta rikice a jikinsa ne ya sa shi cewa,

“Haka kika yi kewa ta?”

A shagwaɓe ta bashi amsa,

“Kai ɗin na daban ne ai.”

Dariya su duka suka yi.

Gaba ɗaya Maryam ta manta a gidansu take, shi ma Khamis ya manta a gidan surukansa yake, soyayya mai faranta rai suka ci gaba da nuna ma juna.

Sai da aka fara kiran La’asar sannan Maryam ta tashi za ta fita, ce mata ya yi,

“Da an yi sallah ki dawo mu dasa daga inda muka tsaya.”

Gira ya ɗaga mata yana ‘yar dariya.

Maƙe kafaɗa ta yi don idan ta biye mishi to fa za a tafka abin kunya a gidan surukai.

A cikin ɗakin akwai ƙofar da za’a shiga cikin gidan.Ta wannan ƙofa Maryam ta shiga gida, shi kuma ya faɗa banɗakin da ke cikin ɗakin ya yi alwalla, da nufin idan ya fito zai tafi masallacin da ke a layin gidansu Maryam.

A tsakar gida Maryam ta haɗu da Asma’u, cikin tsokana Asma’u ta ce,

“Su Maryam an shige wurin miji an yi bulunbuƙui.”

Dariya kawai Maryam ta yi ta wuce.

Da idanu Asma’u ta bi ta har ta shige ɗakin Mamansu.

“Allah ka ci da mu.”

Asma’u ta yi wannan fata a ranta, don yadda ta ga farinciki kwance a fuskar Maryam ya tabbatar mata da kulawar da ta samu a wurin mijinta ce.

Khamis kuwa a Masallaci suka haɗu da Baban su Maryam, sahu ɗaya suka yi sallah. A tare kuma suka fito lokacin da aka gama sallar, nan Khamis ya gaisa da wasu abokan Baban su Maryam da tun yana neman aurenta ya san su.

Jerowa suka yi suna hira, da suka zo ƙofar gidansu Maryam ne suka zauna a kan wani benci shi da Alhajin.

Hira mai cike da alhinin matsalar tsaron da ke ta afkuwa a arewacin ƙasar nan suka dasa, inda har suka taɓo sace-sacen ‘yan makaranta da ‘yan ta’adda suka tsira.

Cike da damuwa Baban su Maryam ya ce,

“Abin dai sai addu’a kawai, yanzu an ce kuma an sace ɗalibai mata har ɗari uku da wani abu a Jihar Zamfara.”

Doguwar ajiyar zuciya Khamis ya sauke tare da ɗan girgiza kai saboda yana jin ciwon rashin tsaron yankin Arewa

“Wallahi kuwa Baba, ai an sako yaran ma.”

Babansu Maryam ya ce,

“Na Jangebe fa.”

Khamis ya ce,

“Eh su ɗin, ɗazu nake gani a news.”

Babansu Maryam da

ke ji kamar har da ‘yarshi a cikin ‘yan matan ya ce,

“Kai Alhamdulillah, Allah ka tsayar kansu.”

Khamis ya ce,

“Amin ya Allah.”

Cike da rashin jin daɗi suka ci gaba da hirar. Daga bisani Babansu Maryam ya shiga cikin gida, Khamis kuma ya bi ta ƙofar waje ya shige ɗakin da ya sauka.

Ya yi niyyar idan ya gama sallah ya sake kiran Maryam ɗakin, sai dai jimamin matsalar tsaron da ta mamaye yankunan Arewa ta sa jikinsa ya yi sanyi, gaba ɗaya sha’awar komai ma ta fice mishi a rai, saboda idan ba shawo kan matsalar aka yi ba, to Allah kaɗai ya san inda matsalar Arewa za ta tsaya.

“Allah ka dubi raunin mutanen Arewa, ka kawo mana ɗauki daga matsalar tsaron nan da duk wata matsala ma.”

A fili ya yi wannan addu’ar tare da jingina kansa da bayan kujera ya lumshe idanu.

A cikin ransa ya ci gaba da neman tsarin Allah daga wannan bala’i, sai da ya ji firgicin da ya cika mishi zuciya ya yi sauƙi ne ya buɗe idanun, wayarsa da ke gefensa ya ɗauka.

Lambar Aisha ya lalubo, cikin ransa kuma yana ta tunanin yadda aka yi bata kira ta ji ko ya sauka lafiya ba. Danna mata kira ya yi, sai da ya fara cire tsammanin za ta ɗaga kiran ya ga kuma ta ɗaga.

Shi ya fara magana ya ce,

“Da kyau Indon birni, ko kuma in ce Indon ƙauye, ace na yi tafiya amma ki kasa kira na ki ji na sauka lafiya, ko don yana garinsu kishiya ne kika yi mini haka?”

Cikin yanayin damuwa da faɗa-faɗa ta ce,

“Haba Abban Haneef, ka san dalilin rashin kiran?”

Girgiza kai ya yi kamar tana ganin shi,

“A’a, ki faɗa mani dalilin”, shiru ya ji ta yi, da alamun tunanin wani abu take.

Cewa ya yi,

“Kin yi shiru Madam.”

Daga can ta ce,

“Bana jin daɗi ne fa.”

Cike da damuwa ya tambaye ta abin da ke damun ta,

“Zazzaɓi.” ta bashi amsa.

Tsokanar da ya saba yi mata ce ya fara,

“Ai na faɗa miki an samu ɗan ƙanen Haneefa, amma kin ce A’a.”

‘Yar dariya ta yi sannan ta ce,

“Ni ba wani ƙanen Haneefa.” Tambayar ya sauka lafiya ta yi mishi, ya faɗa mata gashi nan ma zaune cikin aminci.

Maryam kuwa zaman jiran kiransa ta yi, sai dai har aka kira Isha’i bai neme ta ba, ita ma ɗin ba ta neme shi ba, don yaran gidansu da suka dawo Islamiyya gab da Magarib sun faɗa mata sun ganshi a waje yana hira da su Yaya Auwal.

Sosai zukatansu ita da shi ke tunanin juna, sai dai har aka kira Isha’i text ne kaɗai ya shiga tsakaninsu, shima ɗin ita ce ta tura mishi, bai kuma yi mata reply ba.

Cikin ɗan lokaci ta shiga ‘yar damuwa, sai dai ta yi ƙoƙari sosai ta yadda ba za a gane ba.

Zaune suke a bedroom ɗin Mamansu ita da Zahra’u, maganar saƙon da za ta ba Maryam ta kai ma Haupha ta yi mata, sai dai gaba ɗaya Maryam ɗin kamar ba ita take saurare ba.

Kiran da Hajiyarmu ta yi ma Maryam ɗin ne ya sa ta dawowa hayyacinta.

A kitchen ta same ta tare da faɗin, “Gani Hajiyarmu”

Tuwon Semo da miyar busassar kuɓewa Hajiyarmu ta ba ta.

“Ki kai ma mijinki, Alhaji ya ce ya dawo daga masallaci.”

Da hanzari ta ce,

“To Hajiyarmu.”

Ɗaki ta koma ta kimtsa, sannan ta ɗauki tuwon da kuma damammiyar fura a jug ta kai ma Khamis. Zaune ta same shi a ƙasan carpet kamar dama jiran ta yake.

Aje tuwon ta yi tare da zama ta ce, “Na yi fushi ai.”

Saboda ta lura da wani irin kallo da yake mata.

Hannunta ya ruƙo,

“Sorry, bana son zaƙewa ne a gidan surukai.”

Murmushi ta yi ta ce,

“Uhm.”

Da hannunsa ya maida tuwon gefe, tambayar shi ta yi,

“Ba yanzu za ka ci ba?”

Amsa ya bata da,

“Sai zan tafi tukunna.”

Hannu ya ware mata, bata wani ɓata lokaci ba ta dawo a jikinsa ta zauna.

Zare Hijabin jikinta ya yi, sai ya ga kwalliyar yanzu ta daban ce, riga da skirt ne na english wears a jikinta.

Kansa ya cusa a wuyanta tare da yin magana cikin kasalalliyar murya,

“Gobe sai gida ko?”

Girgiza kai ta yi.

“Sai mun ƙara sati.”

Da ‘yar dariya a bakinta.

Ɗago da jajayen idanunsa ya yi,

“Fa kuwa an yi abin kunya.”

Dariya ta yi.

“Kamar ya abin kunya?”

Bakinsa ya sa a kunnenta ya yi maganar da ita kaɗai ta ji me ya ce, dariya su duka suka yi.

Saukowa Maryam ta yi daga jikinsa ta sa musu tuwon, sosai Khamis ya cika cikinsa har ya kasa shan furar. ‘Yar hira suka taɓa, daga bisani ta koma cikin gida, shi kuma ya tafi hotel ɗin da zai kwana.

A ɗakin Hajiyarmu Maryam ta kwana, aikuwa cikin dare Maryam ta sha karatu wurinta, musamman akan sirrin zama da kishiya. Washe-gari da misalin ƙarfe goma ne suka fito cikin shirin tafiya.

Nasiha ce tuni kowa ya yi wa Maryam, hatta Asama’u da ke ƙanwarta sai da ta ba ta shawara akan zamantakewa.

Maryam na kukan barin gidansu ta shiga motar Khamis, inda yayyenta da ƙannenta suka ci gaba da ɗaga mata hannu har suka fice daga layin gidan.

Hawan su titi ke da wuya Khamis ya dube ta.

“Bakya son tafiya ko?”.

Gidan iyaye daban ne, haka gidan miji shi ma daban ne, duk wanda ka shiga sai ka ji ba ka son fitowa. Ɗan girgiza kai ta yi.

“A’a.”

Ya ce,

“To kukan na meye?”

Shiru ta yi ba ta ba shi amsa ba, cikin ranta kuma tana jin kewar ‘yan gidandsu. Wani ɓangaren kuma tana zullumin takun saƙar da za su dasa ita da Aisha idan ta koma. Ita bata ƙi su zauna kamar Yaya da ƙanwa ita da Aisha ba, sai dai ta lura Aishar dole sai an biyo mata ta bayan gida sannan za a zauna lafiya da ita.

Dariya kawai Khamis ya yi lokacin da ta ƙi ba shi amsa, sannan ya maida hankalinsa ga tuƙi, cikin ransa kuma yana ta fatan sauka lafiya.

*****

A wurin Aisha kuwa, ruɗanin da ta shiga bisa ga ganin ƙaho a ɗakin Maryam ya hana ta saƙat.

Ga Zuzee kuma ta dame ta da akwai wani malami, wai ɗan’uwansu ne da za ta haɗa su, ita kuma har yanzu babu maganar zuwa wurin Malami a ranta.

Tunda ta sallami su Haneef suka tafi makaranta take zaune a falo, kiran Zuzze da ya shigo wayarta ne ya yi sanadiyyar janye tagumin da ta yi.

“Aisha wai me kika yanke ne, kin ga yarinyar nan tana hanya, kuma Allah kaɗai ya san abin da za ta ƙullo ta dawo da shi.”

Abin da Zuzee ta faɗa ma Aisha kenan bayan ta ɗaga kiran.

Aisha ta daɗe da sanin manufar Zuzee, ce mata ta yi.

“Zuzee ni fa ba zan kai kaina ga halaka ba, idan akwai wata mafita ki faɗa mini, amma ba zuwa wurin wani Malami ba.”

Ɗan shiru Zuzee ta yi, daga bisani ta ce,

“Bari in ƙara nazari to.”

Aje wayar Aisha ta yi lokacin da suka gama wayar, ƙahon da layun ne ta ɗauko, sai ta ji wani irin tsoro ya kama ta. Hanyar mafitar da take nema ce ta faɗo mata a rai, ‘Mahaifiyata, ai uwa ita ce maganin komai’ a cikin ranta ta yi wannan maganar.

Shirin tafiya gidansu ta yi, dama Haneef da Haneefa ne damuwarta, kuma basu nan, don haka tafiyar ba za ta ta yi mata wahala ba.

Dogon hijabi ta zura, sannan ta ɗaura Face Mask a fuska yadda ba za a gane ta ba, achaɓa ta hau sai gidan su.

Zaune ta samu mahaifiyarta da kuma Yayansu Abdul a falo.

Sosai suka lura da yanayinta na damuwa, zama ta yi suka gaisa, daga bisani mahaifiyarta ta ce, “Aisha lafiya dai ko?”

Aisha ta ce,

“To da sauƙi dai Mommy?”

Shiru ta yi tana son faɗin damuwarta, tana kuma tsoron Yaya Abdul da ba annuri ko kaɗan a fuskarsa, shi haka yake dama, kafin ka ga dariyarsa sai an daɗe, ba kuma mutane ne bai so ba, kawai dai raini ne baya so.

Tashi Abdul ya yi.

“Mommy bari in dawo.”

Tunda shima kukan kansa ne ya kawo mata, yadda ba zai so wani ya ji damuwarsa ba haka shi ma ba zai so jin ta wani ba.

Bayan fitarsa ne Mahaifyar Aysha ta dube ta.

“Aisha mi ye matsalar?”

Kamar Aisha za ta yi kuka ta ce, “Mommy yanayin zaman mu da Maryam ne ke bani tsoro.”

Cike da damuwa Mommy ta ce,

“Kamar ya yake baki tsoro Aisha?”

Aisha ta ce,

“Duk ta bi ta rikita Abban Haneef, in dai a kanta ne za ki ga ya manta da komai.”

Wani irin kallo Mommy ta yi mata, “Sakacinki ne to, yanzu ke ba kya jin kunyar faɗin haka ma?”

Aisha da ta ga laifin na neman dawowa kanta ta ce,

“Mommy yarinyar nan asiri gare su, ‘yar Katsina ce fa.”

Baki ta taɓe,

“Aisha akwai inda ba a asiri? Kin manta mu irin ƙazafin da aka yi mana, an ce muna da zafin kishi, har kashe kishiya muke yi. Ko da yake gaki nan za ki ja ƙazafin da ake mana ya tabbata gaskiya.”

Jaka Aisha ta buɗe ta ɗauko abin da suka gani a ɗakin Maryam, “Mommy kin gani fa, a ɗakinta muka ɗauko shi”.

Wata irin faɗuwa gaban Mommyn su Aisha ya yi.

“Subhanallahi, meye wannan?”

“Mommy laya ce.”

Aisha ta bata amsa.

Sake tambayar Aysha ta yi.

“Ina aka same ta?”

Aisha ta ce,

“A ɗakinta muka ɗauko ta?”

“Ke da wa?”

Nan fa Aisha ta yi shiru.

“Ko ke da Khamis ɗin?”

Aisha ta girgiza kai, shan jinin jikinta da ta yi ne ya sa mahaifiyarta ta fahimci wani abu.

Faɗa ta yi mata akan buɗe ɗakin Maryam da ta yi, sannan ta ce, “Laya ai kala-kala ce, wata ta neman lafiya ce.”

Ko kusa bata goyi bayan Aisha ba akan maganar asiri, layun ma ce mata ta yi ta ƙone su can, ta kuma ci gaba da Addu’a, idan ma Maryam na asiri toh kanta ta cutar ba kowa ba, tunda ba a duniya za a tabbatar ba.

Jikin Aisha a mace ta dawo gida. Kitchen ta shiga ta haɗa girkin tarbar su Khamis. Da misalin ƙarfe biyar na yamma Khamis da Maryam suka iso gida.

Tun kafin su fito a mota Haneef da Haneefa suka ruga tarbarsu.

Suna fitowa kuwa su duka suka maƙalƙale Maryam suna,

“Oyoyo Anty.”

Itama rungume su ta yi ta ce, “Oyoyo Yarana.”

Murna sosai suka yi da dawowarsu, Khamis kuwa ya ji daɗin yadda suke Murnar ganin Maryam, hakan ya nuna akwai kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu.

“Ni ba za a yi mini oyoyon ba.” Khamis ya faɗa yana dariya.

Haneef ne ya ce,

“Sorry Daddy, ai kai kwana biyu kaɗai ne ba ka nan.”

Haneefa kuwa maƙalƙale shi ta yi tana murna. Maryam ce ta riƙe hannun Haneefa, Khamis kuma ya riƙe hannun Haneef suka nufi falo.

A daidai ƙofa suka ci karo da Aisha ta fito, faɗuwar gaban lokaci ɗaya ce ta riski kowaccensu, take Aisha ta ji kamar ta ga dodanniya, murmushin yaƙe ta yi ta ce, “Oyoyo ‘yan tafiya.”

Cikin falon suka ƙarasa, anan Aisha ta yi musu sannu da zuwa, Ita ma Maryam gaishe da ita suka yi. Sosai Khamis da ke kan kujera ɗaya da Maryam ya lura da rashin walwalar Aisha.

“Har yanzu zazzaɓin?”

Ya tambaye ta.

“Eh to da sauƙi dai.”

Ta faɗa tana duban shi.

Sai a lokacin Maryam ta san bata jin daɗi, fatan samun lafiya ta yi ma Aisha.

Tashi Khamis ya yi ya nufi ɗakinsa, key ɗin ɗakin Maryam ya ɗauko, inda ya ba Maryam ɗin ta buɗe, shi kuma ya tafi kwaso kaya a mota shi da yara.

Ras Aisha ta ji gabanta ya faɗi, take ta Tambayi kanta.

‘Anya mun maida komai a muhallinsa?’

Tana tuna yadda suka baro ɗakin a firgice hankalinta ya soma tashi.

Maryam kuwa tana shiga ɗakinta ta ga ba yadda ta barshi ba, zanen gado gashi nan a ɗage. Pillows ɗin kuwa a warwatse a ƙasa.

Abin da ranta ya ba ta kawai Khamis ne ke shigowa ɗakin.

Tunawa da Jakarta da ta bari a falo ta yi, ta zo fitowa Khamis kuma zai shiga.

“Ina za ki je?”

Ya tambaye ta, amsa ta bashi da, “Jakata zan ɗauko.”

Wucewa ta yi, inda shi kuma ya kutsa kai a cikin ɗakin.

Raba idanu ya riƙa yi cikin ɗakin saboda ba haka ya barshi ba, don ko ranar da zai fita sai da ya shigo ya ganshi tsaf.

“To ya haka?”

Ya tambayi kansa, ko shakka babu an shigo ɗakin nan kuma alamu sun nuna an yi bincike a ciki.

Musamman da ya ga katifar gadon ba a daidai take ba.

Yana cikin wannan mamakin ne Maryam ta shigo. Tambayar da ta fara yi mishi ita ce,

“Nan ɗakin kake kwana ashe?”

Shiru ya yi, don idan ya ce mata a’a, kamar ya bata damar tuhumar mai shigo mata ɗaki ne.

Jikinsa ne ya yi sanyi, filon da ke ƙasa ya duƙa ya ɗauke tare da maida su a kan gadon, daidai inda katifar ta ɗago kuma ya zauna a wurin don bai son Maryam ta lura.

Gefensa Maryam ta zauna tare da ɗan kwantowa jikinsa, ce mata ya yi,

“Kin gaji ko?”

Ta ce,

“Uhm.”

“To mu yi wanka da sallah. Da mun ci abinci sai mu kwanta mu huta.”

Tashi suka yi, ɗakinsa ya tafi da tunani kala-kala, gaba ɗaya ya ɗaura zarginsa a kan Aisha saboda makullan duka gidan suna ɗakinsa.

Maryam kuwa sallallami ta shiga yi lokacin da ta buɗe wadrobe ta ga kayanta gaba ɗaya a hargitse.

“Kai ya haka kuma?”

A nan ma Khamis ne ta ɗaura ma wannan alhakin, sai dai mamakin yadda ya yamutse mata kaya ne bai gushe a ranta ba, zuciya ce ta ce ‘ƙila wani abu yake nema’ wani sashe kuma ya ce,

“To miye abin.”

Saboda sai da ya karɓi duk wata ajiya da ya bata kafin ta tafi.

Rufe wardrobe ɗin ta yi ta shiga banɗaki, ko kusa bata son ta yarda da cewar shigo mata ɗaki aka yi saboda gani take kamar ba zai yiwu ba.

Wanka ta yi ta fito, sallar Azuhur da La’asar ta gabatar, sannan ta fito falo, ta lura da yadda Aisha ke ta wani cin magani, sai dai ta bar shi a don bata da lafiya ne kawai.

Abinci suka ci har da yaran, sannan Maryam ta gabatar ma kowa da tsarabarshi, ai kuwa yaran duk sun yi murna.

Sauran kayan girki irin su daudawa, kuka da kuɓewa da ta zo dasu, sai ta kai su can store ɗinsu. Aisha kuwa ta ɗaukar ma ranta ba za ta yi amfani da su ba, don bata san me aka sa musu ba.

Ɗaki Maryam ta koma da nufin gyarawa, bayanta Khamis ya biyo ya taras tana maida zanen gadon, taya ta ya yi ta kimtsa ɗakin. Cikin ran kowannensu kuma da magana.

Da daddare Khamis na shirin tafiya ɗakin Maryam, Tsaida shi Aisha ta yi.

“Wai da kake ta wani azarɓaɓi, ina za ka je?”

Ya fahimci manufarta, cewa ya yi “Haba Aisha kwana nawa na yi a wurinki?”.

Aikuwa ita Allah kashe ta kwananta ne, gudun fitina ya ce, “To ba damuwa, amma ai zan iya jewa na ce mata ta rufe ɗaki ko?”

Baki kawai ta taɓe ta bi shi da idanu. Zaune ya samu Maryam da su Haneefa a ƙasan carpet. Tura yaran ya yi waje sannan ya zauna a gefen gado.

A jikinsa Maryam ta zauna tare da kwantawa a ƙirjinsa, shiru ce ta ɗan ratsa su, daga bisani ya kira sunanta.

“Maryam.”

Ɗan ɗagowa ta yi suna kallon juna. “Yau ba nan zan kwana ba.”

Wani irin kallo Maryam ta yi mishi, damuwa bayyane a fuskarta ta ce,

“Kamar ya ba nan zaka kwana ba?”

Bai faɗi mata dalili ba, sai dai ya ci gaba da bata haƙuri.

Ta lura da shi kanshi bai son tafiya ya barta, hakurin da ya ba ta shi ɗin ta yi.

Ce mata ya yi.

“Bari na turo miki Haneefa.”

Kai ta girgiza.

“A’a, bana so.”

Ya ce,

“Saboda me?”

Cike da ƙunci ta ce,

“Baccin zai fi yi mini daɗi a haka.” Ranta a ɓace ta ƙarasa maganar.

Lallashinta ya shiga yi, ya ce,

“Ki yi hakuri Mairo.”

Ce mishi ta yi,

“Ni fa ba wani abu.”

Fita yayi daga ɗakin, ita kuma ta sa key. Kan gado ta zauna tana jin wani irin baƙinciki na taso mata, “Ina amfanin auren mijin wata, lokacin da kake buƙatarshi lokacin ne zai tafi wurin wata.”

Da wannan baƙinciki ta kwanta.

Shi kuwa falo ya zauna shi da yaransa suna kallo, duk don ya ɗauke hankalin Haneefa kada ta tambaye shi ina za ta kwana.

Sai da suka yi bacci sannan ya ɗauke su ya maida ta ɗakin Aisha su duka. Ko kusa bai yi niyyar tuhumar Aisha ba tunda ya lura Maryam bata damu ba, sai daga baya zuciya ta ruwaita mishi yin shirun zai haifar da matsala a nan gaba.

Bayan sun yi shirin kwanciya ne ya ce mata,

“Aksha me aka ɗauko a ɗakin Maryam ne na ganshi a hargitse?”

Wata irin faɗuwa gabanta ya yi “Kamar ya me aka ɗauko a ɗakin, ka bani key ne?”

Ta faɗa tana ta ƙyafta idanu.

Zaman shekara takwas da suka yi ya sa ya san halinta, idan tana da gaskiya yana kallonta zai gane, haka idan bata da ita.

To a yanzu kam ko shakka babu bata da gaskiya. Dubanta ya yi, “Aisha ban san ki da wani hali na daban ba, don ko ni da ke mijinki ɗakina bai sha miki kai ba, don haka ki kawar da idonki ga ɗakin Maryam.”

Wani irin ba daɗi ta ji a ranta da ta ji yayi wannan maganar. Masifar ƙarya ta shiga yi

“Wai miye haka Abban Haneef, me zan tsinta a ɗakin waccan da za ka tuhume ni?”

Ya ce,

“Ke kin san abin da kika tsinto a can.”

Abu kamar wasa sai ya zama gaske, kuka ta kama yi wai ya liƙa mata ta shiga ɗakin Maryam.

Ya ce,

“Ni ba na liƙa miki ba ne, ina dai gargaɗinki, kuma tunda kin ce ba ke bace, zan tambayi mai gadi ya faɗa mini daga jiya zuwa yau su wa suka zo, to a cikinsu ƙila wani ne ya shiga.”

Ta san zai aika, kuma sanin Zuzee kaɗai ta zo ta ce,

“Shi mai gadi ina ruwansa, mutum nawa ne ya zo?”

“Hmm.”

Kaɗai ya ce tare da ci gaba da ja mata kunne, haka gaba ɗaya suka yi bacci ba da wani daɗin rai ba.

Washe-gari da Asuba ɗakin Maryam ya zarce, gani ya yi ta watso kayanta duka a kan gado za ta sake maida su.

“Kayan da ke tsaf me kuma suka yi, ko da zan tafi Katsina fa na buɗe na gan su.”

Dubanshi Maryam ta yi, tana tunanin ko bata ji daidai ba, sai da ya ce.

“Muddin kaya na jere ki daina sauko su ƙasa.”

Gabanta na faɗuwa ta ce,

‘Kai wallahi an shigo ɗakin nan.’

A ranta ta yi wannan maganar, gabanta ne ya ci gaba da faɗuwa, ‘To wa ya shigo?’ ta tambayi kanta, zuciya ta ce,

“Ba dai ɓarawo ne ba.” don ba a ɗaukar mata ko zobe ba duk da gold da kuma kuɗaɗen da ke ɗakin.

Wani irin ruɗani ta samu kanta a ciki wanda har ya lura, sosai jikinshi ya bashi wadrobe ɗin ma an buɗe ta, kuma Maryam ta gane don bata bashi amsa ba. Jikin kowannensu a mace suka gyara ɗakin.

Aisha kuwa da Asubar fari ta aje ma Zuzee saƙo a WhatsApp.

‘Zuzee Abban Haneef fa ya gane an shiga ɗakin.’

Zuzee na gama Sallah ta shiga WhatsApp, tana cin karo da saƙon Aisha ta yi reply da,

“Mun shige su, to ya ya ce?”

“Aisha ta ce,

“Ya yi faɗa, amma dai maganar bata yi wani tsayi ba.”

Hankali Zuzee ne ya kwanta, nan Aisha ke bata labarin yadda ta hana Khamis kwana a ɗakin Maryam, Zuzee ta ce,

“Kin mini daidai, ai idan kina haka za ta san kema gwana ce.”

Sun sha hira duk a chat, suna gamawa Zuzee ta shiga tunanin yadda za ta kai Aisha ta baro.

Ita kam idan ta ce tana son Aisha ta yi ƙarya, ko da tana sonta, ma to Hassada ta danne wannan son, don haka dole ta auri yayan Aisha don ita ma ta samu daula, kuma sai ta nuna ma Aisha so ne za ta samu shiga a wurin danginta.

Hanyar da Aisha za ta gane tana sonta ita ce ƙyamatar abin da Aishar ba ta so, mafarin take son kai ta wurin Malamai don Aisha ta samu farincikin da za ta ce Zuzee ce sanadi.

Fita wurin Zuzee ba a bakin komai take ba, duk sa’adda ta ga dama sai ta fizgi mayafi ta fita, don ma Mahaifiyarta na kokartawa wurin taka mata birki.

To, yau ma tana gama breakfast ta fita, kai tsaye gidan malaminta ta nufa, a waje suka haɗu da shi.

Ai kuwa yana ganinta ya fara washe baki.

“Hajjaju Makkatun.”

Ya faɗa yana dariya, saboda da ya ganta ya ga samu.

Ɗakin zaure suka shiga, bayan sun gaisa ya ce,

“To ya mutuniyar taki?”

‘Yar ajiyar zuciya ta sauke.

“Wato Malam tana da taurin kai ne, ganin ƙahon nan da ka bani na saka bai sa ta sauko ba, wai ita ba za ta zo wurin malamai ba.”

Ƙasar da ke gabanshi ya zana, sannan ya m “Sha kuruminki za ta sauko,dai mijin ya shiga ɗakin amaryar.”

Leƙawa Zuzee ta yi cikin ƙasar duk da ta san ba abin da zata gani “Kai Malam wani abu zai faru kenan?”

Ya ce,

“Ƙwarai kuwa, ‘yar Katsinawa ta dawo da shiri ai.”

Abu biyu ne ya taso ma Zuzze, farincikin Aisha za ta karɓi ƙudurinta, saboda malamin duk abin da ya faɗa yana tabbata, kasantuwar sa ƙwararren ɗan duba.

Sai kuma baƙincikin Maryam, tamkar kishiyarta take jinta a rai, dole ne ta kai Aisha ta baro ko don ta hargitsa musu farinciki.

Mugun tsari suka shiga yi da malamin, inda suka tsara kashe mu raba ɗin da zasu riƙa yi idan har Aisha ta bi zugarta.

Ranar da Khamis zai koma ɗakin Maryam kuwa Aisha wani irin firgici ta samu kanta, jikinta ya bata Maryam ta dawo da wani asirin.

Don yadda yake ta azarɓaɓi ko a daren farko bai yi ba.

Tsaida shi ta yi lokacin da zai fito ɗakinta.

“Abban Haneef tun yanzu za ka fita?”

Wayarsa ya duba.

“Eh, ina jin bacci.”

Sanin ƙarfe takwas ta ce,

“Idan a ɗakinta ne baccinka ke zuwa da wuri, a ɗakina kuwa sai goman dare yake zuwa.”

Maganarta ba ƙaramar dakar mishi zuciya ta yi ba, ko kusa bai son makamanciyar irin wannan maganar saboda kamar zargin rashin adalci ne take mishi.

Juyowa ya yi gareta.

“Aisha kullum zargin rashin adalci kike mini, to ki je na gode, kuma tunda haka ne zan riƙa shigowa ɗakinki bakwai ba ma takwas ba, amma da sharaɗin sai kin rage ƙorafi idan na shigo, sannan ki riƙa kula mini da kanki.”.

Da tulin nauyi ya bar ta wanda ya hana ta magana har ya fice, tabbas tunda ya yi aure hirarsu ta canja salo, kullum ƙorafi ne, ga ƙarancin kular, don tuni ta yi watsi da shawarwarin Aisha, ‘yan kayan gyaran auren duk ta rage sha.

Ɗakin Maryam ya shiga tare da sanya key.

A yadda ta gyara ɗakin ya tabbatar mishi da ba ƙaramin farinciki zai samu ba.

Kwantawa ya yi a saman gadon, Maryam na fitowa daga wanka ta ganshi. Wani irin daɗi ne ya kama ta, a gurguje ta shirya cikin kayan bacci masu ɗaukar hankali.

Feshe jikinta da turaruka ta yi, sannan ta kashe musu fitilar ɗakin.

Cike da soyayyar juna suka shige

bargo mai taushi da kuma ƙamshin gaske.

<< Kishiyar Katsina 9Kishiyar Katsina 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×