Skip to content
Part 12 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Kaso mai yawa na farincikin Khamis yana tafiya ne tare da farincikin Aisha, sai dai tsananin kishin da ke damun ta ya hana ta lura da hakan.

Murnar da take yi a dalilin fita unguwar da za ta yi ce ta sa shi jin sawai a zuciyarshi, don ba ƙaramin ƙunci yake samun kansa a ciki ba idan ya ga tana fushi.

Duban ta ya yi a lokacin suna zaune a falo, dukkan su a kan kujera two seater, fuskarsa a sake ya ce,

“Aisha ina ma fuskarki za ta kasance haka a koyaushe.”

‘Yar dariya ta yi, saboda ita kanta ta san cikin annashuwa take, tambayar shi ta yi,

“To da ya fuskata take?”

Amsa ya bata da,

“Ba walwala a cikinta ko kaɗan, kuma ganin ki a wannan yanayin ba ƙaramin sosa mini zuciya yake ba?”

Murmushi ta yi ta ce,

“In Sha Allahu za ta ci gaba da kasancewa haka, amma sai ka taya ni da addu’ar Allah ya rage mini zafin kishi.”

Saboda bayan shi ba ta da wani ciwo a zuciyarta wanda zai hana ta sakin fuska ga mijinta, bare har ya ji daɗin rayuwa da ita.

Cewa ya yi,

“Ai kuwa in dai wannan ne zai yaye duk wani ƙuncin da ke ranki, na miki alƙwarin zan taya ki da addu’a.”

Ɗan rausaya kai ta yi sannan ta ce, “To Allah ya ba ka iko.”

“Amin.”

Ya ce. Daga nan suka ci gaba da tattaunawar su ta mata da miji. Nan yake faɗa mata cikin Maryam watansa uku daidai, baki ta ɗan taɓe sannan ta ce,

“Lallai kun sha miya.”

Yana ‘yar dariya ya ce,

“A hakan?”

Ta ce,

“Eh mana.”

Dariya kawai ya yi, cikin ransa kuma yana tunanin ko Maryam ta farka daga baccin da ya baro ta tana yi?.

Tashi daga kan kujerar ya yi, idanunsa na kan Aisha ya ce,

“Bari ma in ga idan ta farka, ko za ki je?”

Miƙewa ta yi ta ce,

“Ok to mu je na ganta.”

Zaune suka samu Maryam a gefen gado tana ta maida numfashi, sakamakon aman da ta gama yi yanzu, cike da tausayin ta Khamis ya zauna a gefenta, lokaci ɗaya kuma ya ce,

“Sannu Mairo, aman ne ko?”

Kai ta ɗaga tare da duban Aisha da ke tsaye agabansu.

“Sannu.”

Wadda iyakar ta baki Aisha ta yi mata, saboda wata irin tsanar Maryam da ke cike da ranta, musamman yadda Khamis yake rikicewa kamar shi ke ciwon. Yanzu haka zaman da yake a gefen Maryam ɗin ji take kamar ta fizgo shi don har ya kwanto da ita jikinsa, haka kuma yake ririta ta in dai suna tare, kuma ko a gaban waye.

Duban ta Khamis ya yi ya ce,

“Ki zauna mana.”

‘yar ajiyar zuciya ta yi tare da faɗin,

“To.”

Lokaci ɗaya kuma ta zauna a kan stool.

Hira Khamis ya ja ta da ita, inda ya ce,

“Kema fa haka kika sha wahala a cikin Haneef da Haneefa ko?”

Ba tare da walwala a fuskarta ba ta ce,

“Uhm, ai ni nawa ya fi wannan ma Abban Haneef, ka manta sai an kwantar sai an tayar?”

Tabbas laulayinta ya fi na Maryam, amma ta faɗi haka ne duk don ta nuna ma Maryam ba komai take yi a laulayi ba.

Kai Khamis ya jinjina ya ce, “Gaskiya ne, kema kin ji jiki.”

Ta ce,

“Ai ba kaɗan ba ma, ciki da laulayi ba daɗi.”

Khamis ya ce,

“Wallahi dai kam.”

Maryam kuwa duk tana jin su, sai dai azabar da take ji a ƙirjinta kaɗai ta ishe ta, saboda wani aman ne ke shirin taso mata.

Ɗan zame jikinta ta yi daga na Khamis, cike da kulawa ya tambaye ta,

“Ya aka yi?”

Bannun da ya ga ta toshe baki da shi ne ya ba shi amsar tambayarshi.

Bayanta suka bi shi da Aisha a lokacin da ta tashi daga kan gadon ta nufi banɗaki.

Zuciyar Khamis cike da tausayin ta ya riƙe ta lokacin da take sheƙa aman.

“Sannu Maryam.”

Kawai yake faɗi, cikin ransa kuma yana ta addu’ar Allah ya tsaida mata wannan amai ta huta, don shi kaɗai ke wahalar da ita, duk da magunguna da alluran da take sha, amma har yanzu bai tsaya ba sai Allah ya nufa.

Da kanshi ya wanke mata baki da fuska, sannan ya riƙo hannunta suka fito, Aisha da ke bakin ƙofar banɗakin ta ce,

“Gaskiya kina jin jiki, ciki mai sa amai bai da daɗi”

Sannan ta bi bayansu.

Taimaka mata ya yi ta kwanta, sannan ya rufa mata bargo bayan ya zauna a gefen gadon.

Duƙowa ya yi sosai saitin fuskarta ya ce,

“Sannu Maryam.”

Kai ta ɗan ɗaga alamar,

“Yauwa.”

Tambayar ta ya yi,

“Me za ki ci?”

Murya can ciki ta ce,

“Ba komai.”

Saboda ruwa ne kaɗai idan ta sha baya sanya ta amai.

Khamis ya san dama haka za ta ce, sake tambayar ta ya yi,

“Ko za ki sha black tea?”

Girgiza kai ta yi “A’a na ƙoshi.”

Cike da damuwar rashin cin komai da take yi ya ce,

“A’a Maryam, rayuwa ai bata yiwuwa babu abinci, ki faɗi duk abin da ki ke iya ci sai Aisha ta girka miki.”

Aisha na jin ya ce haka ta yi magana a ranta,

‘Tunda Uwata ce ba.’

Ita dai Maryam shiru ta yi, cikin ranta kuma tana tunanin me za ta ci wanda zai iya tsaya mata, duk abin da ta tunano sai ma ta ji amai na shirin taso mata.

Katse mata tunani Khamis ya yi, in da ya ce,

“Ko za ki ci tuwo?”

Kai ta ɗaga,

“Eh zan ci.”

Khamis kuwa ya ji daɗi, don rabon da ta ce za ta ci wani abinci an daɗe.

Duban Aisha da ke zaune kan stool ya yi.

“Aisha tuwo take so, kin ga sai ki yi mana shi baki ɗaya”.

Idan akwai girkin da Aysha ta tsana to tuwo ne, kuma ba ci ne bata yi ba, aikinsa ne kawai ba ta so, ba yabo ba fallasa ta ce,

“To an gama, sai dai tuwon me?”

Cewa ya yi,

“Na semo, kuma miyar kuka, idan kuma na masara za ki yi sai na karɓo gari.”

Fuska kicin-kicin ta ce “A’a bar ni da semon.”

“Ok, to ki hanzarta, kin ga har fita za ki yi anjima.”.

Ko bai ce ta tashi ba dama dole ta tashi tunda ya ɗora mata jidalin aiki, wanda saura ƙiris ta ce ta gaji duk da halin da ta ga Maryam a ciki.

Tashi ta yi ta fice ba tare da ta sake kallon inda Maryam take ba, don ji take kamar ta maƙare ta.

Maryam ɗin ma bata san da fitarta ba saboda baccin da ya ɗauke ta.

Ƙuri Khamis ya yi ma fuskar Maryam da ta rame, cikin ransa yana jin son ta da tausayin ta na ci gaba da mamaye filin zuciyarshi.

Samun kansa ya yi cikin son kwanciya a gefenta, a hankali ya kwanta tare da shigar da ita jikinshi, hakan ne ya ba Maryam ɗin damar yin bacci mai cike da nutsuwa.

Bai jima da kwanciya ba kuwa sai ga Aisha ta shigo ɗakin da nufin kawo mishi wayarshi da ya manto a ɗakinta.

Ganinshi kwance a gaban Maryam ne ya harzuƙa mata zuciya, ba ta san lokacin da ta yi magana cikin ɗaga murya ba ta ce, “Abban Haneef wai ba fita za ka yi ba? Ka zo nan ka wani kwanta.”

A can cikin baccin da ya ɗan fizgi Khamis ya ji muryarta a saman kansa. Da sauri ya buɗe idanu don bai son yana bacci a yi mashi magana a saman kai, hakan na sa shi falkawa da faɗuwar gaba.

“Haba Aisha me ya sa za ki ɗaga mini hankali, alhali kin san bana son irin haka?”

Bayan ya tashi zaune ne ya yi mata wannan tambaya.

Baki ta turo tana yi ma Maryam da ta yi nisa cikin bacci mugun kallo, a ƙasan ranta kuma tana jin zuciyarta na tafarfarsa.

Tambayar ta Khamis ya yi,

“Ya aka yi?”

A taƙaice ta bashi amsa “Wayarka.”

Tare da miƙa mishi.

Karɓa ya yi, sannan ya bata amsar maganar da ta yi mishi a saman kai,

“To yau ba zan fita ba sai da yamma.”

Lokacin da ya rufe bakinsa ma har ta juya tana ta huci. Da idanu ya raka ta, cikin ransa kuma yana ƙara nema mata sauƙin wannan azababben kishin da ke damunta, ta san yau a ɗakin Maryam yake, amma duk da haka sai da kishinta ya fito fili.

Kira ne ya sake shigowa wayarsa, yana dubawa ya ga Sani ne, da hanzari ya ɗauki kiran domin jin me ke gudana.

Aisha kuwa da baƙinciki cike da ranta ta gama aikin, don so take ta fita da wuri. Tana gamawa ta nufi ɗakinta da nufin shiryawa.

Khamis da ya fito zai ɗauko yara a school ya leƙa kitchen, ganin bata nan sai ya tafi ɗakinta.

A gaban dressing mirror ya hange ta tana make-up.

Daga bakin ƙofar da yake tsaye ya tambaye ta,

“Ba dai har kin gama girkin ba?”

Ta ce,

“Aikuwa na gama, sai shirin fita ma.”

Fuskar wayarsa ya kalla ya ga duka sha biyun rana, kai ya jinjina ya ce,

“Sannu da ƙoƙari, dama haka kike kullum.”

Saboda nawar girki sanannen halinta ne.

Ba ta bashi amsa ba, sai dai ta ce, “Da na shirya fa tafiya zan yi.” Cewa ya yi,

“Ki bari na kai ki mana.”

Ta ce,

“A’a ni dai gara in tafi.”

Ya ce,

“To a dawo lafiya, ki gaida su Mommy, kuma yamma na yi ki dawo.”

Yana gama faɗin haka ya juya ya tafi.

Ba tare da ɓata lokaci ba ita ma ta shirya cikin riga da zani na atamfa, sannan ta ɗauko mayafinta orange ta yafa saboda akwai kalar a jikin atamfar.

Tarkacen waya da key ta ɗauka sannan ta jawo ɗakinta, ba ta wani yi ma Maryam bankwana ba ta tafi, don dama ba ita ke gabanta ba.

Kai tsaye gidansu ta nufa, inda ta taras da ƙanwarta mai suna Nabila da kuma matar Yayansu Abdul sun zo, duk suna zaune a ƙasan carpet.

Tun kafin ta zauna a falon ta ce musu,

“Hala kun ji zan zo shi ne ku ma kuka zo”, zuciyarta cike da farincikin ganinsu ta ƙarashe maganar.

Fatima matar Abdul na dariya ta ce,

“A’a zuwanki daban, namu ma daban.”

Sai da ta karɓi yaron Fatima da suke kira da Sultan sannan ta zauna a kan kujera, gaisawa suka yi da juna, Nabila ta ce,

“Ina yaran?”

Aisha ta ce,

“Suna school.”

Fatima ce ta tsokane ta da cewa, “Uwargida Sarautar mata, ina Amarya?”

Sai da Aisha ta taɓe baki sannan ta ce,

“Tana gida tana laulayi.”

Idanu su duka suka zaro, Nabila na dariya ta ce,

“Hegiya Amarya ta kwasa.” Fatima ta ce,

“Ai ba laifi ta sha miya, sun kusa shekara fa, duk da dai ban san cikin ko wata nawa ne ba.”

Idanun Aisha a kan Mommynsu da ta sauko daga kan steps ta ce, “Wata uku ne in ji mai cikin.”

Sosai maganar Aisha ta sa su dariya, Nabila ta ce,

“Wai mai cikin.”

Fatima ta ce,

“To mai cikin mana.”

Mommynsu na ƙarasowa ta ce, “Dariyar me ake?”

Basu ba ta amsa ba sai dai suka ci gaba da dariya, ko da jin haka ta san gulma ce suke yi.

Zama ta yi akan kujera, cikin ladabi Aisha ta gaishe da ita

Cike da kulawa ta amsa tare da ɗorawa da,

“Ina Maryam da jiki?”

Saboda sun haɗu a asibiti lokacin da Khamis ya kai Maryam ɗin.

Aisha ta ce,

“Da sauƙi, amma har yanzu dai a kwance take.”

Mommynsu da bata ɗauki duniya a bakin komai ba ta ce,

“Kuma kika fito?”

Gaba ɗaya suka kalle ta, Nabila ta ce,

“To Mommy idan ta zauna a gidan me za ta yi mata?”

Mommy ta ce,

“Jiyyar ta mana Nabila.”

‘Yar dariya su duka suka yi, Fatima ta ce,

“Ai ƙila mijin na gida.”

Aisha ta ce,

“Ko bai nan ba abin da zan zauna in yi mata, wanda na yi Allah ya bada lada, sauran kuma ya nemi mai kula mishi da ita, don wallahi na gaji.”

Kallon Mamaki Mommy ta yi mata.

“Kamar ya kin gaji?”

Aisha ta ce,

“Mommy tunda ta samu cikin nan ni nake mata girki, amma kuma da dare ya yi sai in nemi Abban Haneef in rasa, a ranar girkina ma kusan can yake kwana, wai bata da lafiya sosai.”

Wannan doguwar maganar Aisha ta ɗauka za ta samu goyon bayan Mommy.

Sai ji ta yi ta ce,

“Gashi da kanki kin ce ba ta da lafiya, kuma duk abin da kika yi mata kema lokaci zai zo da za ta yi miki, don haka kada ki sake cewa ma kin gaji.”

Ɗan haɗe rai Aisha ta yi, wanda alamu ke nuna ba lallai ne maganar mahaifiyarta ta yi mata tasiri ba.

Tsegumin kishiya suka shiga yi su uku, wani su samu saka bakin Mommy, wani kuma ta yi musu shiru, can Fatima ta ce,

“Ni dai na gode ma Allah da ya sa Abban Zarah miskilin mutum ne, ko kallon mata baya yi.”

Dariya su duka suka yi, Nabila ta ce,

“Wa ya faɗa miki bai kallon mata, to irin miskilan mazan nan sun fi tsula tsiya, don haka ma kiyi ta addu’a.”

Aisha kuwa da ta san Zuzee na son Abdul, kuma tana goyon bayan Zuzee ta same shi sai bata sa baki ba. Dawowar yaran gidan daga makaranta ne ya sa su Aisha komawa upstairs, saboda hayaniyar yaran ba ta bari su yi magana.

Zamansu a bedroom ɗin Mommy ke da wuya wayar Aosha ta shiga ruri, duba ta kai ga fuskar wayar, tana ganin Zuzee ta ji gabanta ya ɗan faɗi. Bayan ta ɗaga kiran suka gaisa, nan Aisha ta yi suɓul da bakar faɗa ma Zuzze tana gidansu, aikuwa Zuzee ta ce,

“Toh bari in zo sai mu gaida Inlaw a tare.”.

Aisha ba ta da damar ce ma Zuzee kada ta zo, sai dai kuma cikin ranta cike da tsoron yadda za’a tarbe ta saboda ba mai son Zuzee a gidan.

Nabila da Fatima sun ji lokacin da Zuzee ta ce za ta zo, sai dai ba su yi ma Aisha magana ba sai da ta ce musu,

“Wai Zuzee ce za ta zo, gashi Mommy bata son ganin ta.”

Fatima da ta rasa dalilin tsanar Zuzee a ranta ta ce,

“Kema Aisha meye haɗinki da wannan figaggiyar yarinyar, ni wallahi ko me aka bani ba zan iya ƙawance da ita ba.”

Shiru kawai Aisha ta yi, cikin ranta kuma tana ƙulla yadda za ta hana Zuzee zuwa. Sai dai kafin ta samu nasara har Zuzee ta sake kiran ta, ta ce gata nan fa mai Napep ya aje ta.

Mommynsu Aysha na zaune a falo ita da wasu baƙi da ta yi sai ga Zuzee ta shigo. Take fara’ar da ke fuskarta ta ɗauke saboda a duniya ba wanda ta tsana kamar Zuzee, kuma muguwar rawar kan Zuzee ɗin ce ta ja mata.

Ita kuwa Zuzee sai wani washe baki take ta zauna a ƙasan carpet, cike da son cusa kai ta gaishe da Mommy.

Ba yabo ba fallasa Mommy ta amsa, gaishe da sauran matan biyu Zuzee ta yi, sannan ta maida dubanta ga Mommy.

“Mommy Aisha na sama ne?”.

“Umm tana can.”

Mommy ta ba ta amsa. Ai kuwa Zuzee ta miƙe ta nufi sama kamar dama gidansu ne.

Da idanu su duka suka bi ta, sai da ta ɗan yi nisa sannan ɗaya daga cikin matan ta kalli Mommy “Wannan kuma fa Hajiya Habiba?”

Mommy ta ce,

“Tarkacen Aisha ne” matar ta ce “Okay”, cikin ranta tana jin kamar ta taɓa ganin Zuzee a gidan wani Malami, don ɗabi’ar matar ce shiga lungu da saƙon gidan Malamai.

Kai tsaye ɗakin Mommy Zuzee ta shiga, aikuwa tana ganin Fatima gabanta ya faɗi.

Gefen gadon da Aisha ke zaune ita ma nan ta zauna.

Lokaci ɗaya kuwa duk suka ɗaure fuska har da Aisha, Nabila ma saboda tsanar Zuzee sai dai ta fito daga ɗakin.

Ita kuwa da yake ba ta da lura, sai ta buɗe baki tana ta surutu, ko da Mommy ta shigo ba ta fasa ba.

Aikuwa Mommy ta ce,

“Don Allah Sallah zan yi, a ɗan saurara mini.”

Zuzee ta ce,

“Muma dai bari mu tashi mu yi sallar.”

Fitowa suka yi daga ɗakin suka shiga ɗakin Sumayya da Hauwa, waɗanda suma ƙannen Aishar ne, sai dai suna makaranta.

Nan suka gabatar da Sallah. Aikuwa Aisha na gama Sallah saƙon kiran Mommy ya zo mata.

Jiki a mace Aisha ta shiga ɗakin Mommy,

Mommy da ke zaune kan abin salla ta ce,

“Aisha yanzu za ki bar mini gida tunda ke ba kya jin magana, na raba ki da yarinyar can amma kin ƙi ji ko?”

Kamar Aisha za ta yi kuka ta ce, “Don Allah Mommy ki yi haƙuri, ita ɗin ce ta maƙale mini wallahi.” Mommy ta ce,

“Ta maƙale miki ɗin su wa, wallahi idan kina son kan ki da arziƙi ki rabu da ita, idan ba haka ba duk abin da ya biyo baya ke kika siya da kuɗinki.”

Faɗa sosai ta yi mata akan ta kiyayi Zuzee, ta kuma nuna mata ta san ita ke zuga ta, don tun sa’adda suka haɗu ɗabi’un Aishar suka canja.

Daga ƙarshe kuma ta ce,

“Ana yin la’asar ki kama gabanki wallahi.”

Marairaice fuska Aisha ta yi,

“To Mommy Alhajin fa?”

Saboda yau mahaifinsu zai dawo daga tafiyar da ya yi.

Mommy ta ce,

“Ai saboda shi ɗin na ce ku tafi, don kin san ya fi ni tsanar ta, idan har ita ya gani bai ga jikokinsa ba kin shiga uku.”

Wannan zuwa na Zuzze bai ma Aisha daɗi ba, musamman da Zuzee ta ci gaba da ɓarin baki tana nuna ma su Fatima kamar ta fi su sanin halin da Aisha ke ciki.

Ana maganar kishiya shi ne take cewa,

“Ai duk laifinki ne Aisha, sai ki wani shige ɗaki ki ƙumshe.” Fatima ta ce,

“Wane irin shigewa ɗaki ana zaman lafiya?”

Zuzzee ta ce,

“Wallahi kuwa, ko da yake wannan munafukar kishiyar ta Aisha ai dole take shigewa ɗaki.”

Kai kawai Fatima ta jinjina, cikin ranta kuma tana ta mamakin Aisha, bata ma dai sake magana ba.

Ana yin La’asar kuma Mommy ta ce ma Aisha ta zo ta kama gabanta tunda ta baro marar lafiya, ba don ta so ba ta haɗa kayanta ita da Zuzee.

Suna fita Aisha ta dubi Zuzee ta ce, “Ni fa ban yi niyyar komawa gida yanzu ba, ko mu je gidanku, anjima gab da Magariba sai in tafi.”

Ɗan shiru Zuzee ta yi don ita ma ba son komawa gidansu take son yi ba, cema Aisha ta yi,

“A’a gidan wata ƙawata za ki raka ni.”

Aisha ta ce,

“Ba nisa dai ko?”

Zuzee ta ce,

“Eh ba nisa.”

Motar Aisha suka shiga, kai tsaye sai gidan ƙawar Zuzee mai suna Jamsy.

A babban falon gidan suka haɗu da Jamsy lokacin da ta sauko daga kan benen gidan, Aisha na ta mamakin inda Zuzee ta san Jamsy domin duk in da ƙasaitacciyar mace ta kai to ita ma ta kai.

Da fara’a Jamsy ta tarbe su, bayan sun zauna a falo suka gaisa, Jamsy ta dubi Zuzee ta ce,

“Wallahi Zuzee ba ki da kirki, wato kin yi sabuwar ƙawa shi ne kika manta da ni.”

Idanunta na kallon Aisha ta ƙarashe maganar.

Zuzee na dariyar ta ce,

“A’a ni ban manta da ke ba, Aisha kuma mun daɗe tare da ita ai.”

Aisha ta ce,

“Ke dai Zuzee faɗa mata kin rage zumunci, kin ga nima da ta manta ni sai da na fara bada cigiyarta.”

Jamsy ta ce,

“Aha! Ni fa na san hali.”

‘Yar hira suka ɗan taɓa, daga bisani Jamsy ta ƙwala kira, “Hannah.”

Ba a fi minti ɗaya ba sai ga Hannah ta fito daga kitchen, a yadda ta ƙasƙantar da kai a gaban Jamsy za ka yi tunanin ‘yar aikinta ce, sai dai kyawu da kuma nagartacciyar suturar da ke jikinta ne za su sa maka shakku.

A yatsine Jamsy ta dubi Hannah “Ki gaishe da baƙina, sannan ki kawo musu ruwa da lemu.”

Cikin girmamawa Hannah ta dubi su Aisha da ke a kan kujera three seater ita da Zuzee ta gaishe su.

Mamaki cike da ran Aisha ta amsa da,

“Lafiya lau.”

Zuzee kuwa da yake ta san ko wacece Hannah sai ta kama ‘yar dariyar mugunta bayan ta amsa.

Hannah na tafiya Zuzee ta dubi Aisha da ta bi Hannar da idanu ta ce,

“Kishiya ce fa ba ‘yar aiki ba.”

Baki da idanu Aisha ta buɗe duk a lokaci ɗaya.

“Kishiya fa ki ka ce?”

Zuzee ta ce,

“Tambayi uwar gayyar ki ji.”, Aisha na duban Jamsy ta ce,

“Da gaske kishiya ce ke maki wannan ladabin?”

Jamsy da ke jin kanta ya cika fam ta ce,

“Wallahi kishiya ce, ai kaɗan ma ki ka gani a ladabi.”

Haɓa Aisha ta riƙe, cikin ranta tana jin ina ma ita ce ke juya Maryam haka.

Dafa tan da Zuzee ta yi ne ya sa ta sakin haɓar lokacin da Zuzeen ta ce,

“Kin ga irin abin da ake so kishiyarki ta riƙa yi miki, amma kin kasa ganewa.”

Jamsy ce ta riga Aisha magana inda ta ce,

“Kamar ya ta ƙi ganewa?”

Zuzee ta ce,

“To kamar tsoron kishiyar take, ko da yake kishiyarta murucin kan dutse ce, ba ta fito ba sai da ta shirya.”

Jamsy ta ce,

“‘Yar ina ce?”

Zuzee ta ce,

“Katsina.”

Sai da Jamsy ta jinjina kai sannan ta ce,

“Gandun asiri kenan.”

Nan ta shiga basu labarin Katsinawan da ta sani masu mugun asiri, wasu ma ƙawayenta ne, tare suke bin gidajen bokaye da malamai duk don su mallake miji da kishiya.

Ita dai Aisha baki ta buɗe tana mamakin yadda Jamsy ke bada labarin, kai ka ce babu laifi dangane da zuwa gidan Malaman.

Zuzee kuwa daɗi ne cike da ranta, don ta samu wadda za su taru su kai Aisha ga mahallaka.

Hannah ce ta kawo musu ruwa da lemu, ɗan daɗewar da ta yi ne ya ja mata zazzaga wurin Jamsy, jikinta na ɓari ta ce ma Jamsy,

“Ki yi haƙuri Anty.”

“Toh ɓace min da gani.”

Jamsy ta faɗa tare da nuna mata hanya. A tsorace ta raɓa ta wuce, su kuma suka raka ta da idanu.

Bayan ta shige kitchen ne Jamsy ta dubi Aisha ta ce,

“Baiwar Allah ki zo mu sa ki a hanya, daga miji har kishiya sai kin yi yadda kika ga dama da su.”

Zuzee ta ce,

“Yauwa Antyna.”

Lokaci ɗaya kuma tana dariyar jin daɗi.

Aisha kuwa yanzu ba juya miji ko kishiya ne gabanta ba, juna biyun Maryam da take ganin zai iya zama barazana ga sauran farincikinta shi ne damuwarta, don tun kafin a haifi ɗan tana ganin yadda Khamis ke ji da cikin, to ina ga kuma an haife shi. Wannan fargaba ta Aisha ce ta fara ƙeƙasar mata da zuciya, har take jin ina ma cikin Maryam ya ɓare.

Tattaro dukkan nutsuwarta ta yi ta maida ta ga Jamsy,

“‘Yar’uwa ni yanzu ba wannan ne a gabana ba..”

Zuzee na jin Aisha ta faɗi haka ta ɗan ɓata rai.

“Ai fa, yanzu za ki fara kawo wani ƙalubalen banza.”

Aisha ta ce mata,

“Kin ji ƙarshen maganata ne da za ki ce haka?”

Jamsy da take ganin cimma manufa a tare da Aisha ta ce ma Zuzee,

“Rabu da ita ta yi magana.”

Ɗorawa Aisha ta yi da magana, “Cikin da ke jikin yarinyar ne bana so wallahi, jikina na bani tana haihuwa za ta ida raba ni da Abban Haneef.”

Jamsy ta ce,

“Ciki, toh ya aka yi ma kika bari ta ɗauki cikin?”

Zuzee kuwa sai da ta sauke numfashi sannan ta ce,

“Tambayar mana ita dai Anty, ai wallahi idan ni ce ma ba zan bari ta ɗauki ciki ba bare har ta haihu, idan kuwa ta same shi sai na zubda ɗan banza.”

A yadda Zuzee da Jamsy suka yi maganar cikin kai ka ce ikon ɗaukar ciki na hannunsu, sun manta da ba mai bada ciki ko hana samuwar shi sai Allah, duk wani ƙulunboto da mutum zai yi bai isa ya yi abinda Allah bai yi ba.

Aisha na ‘yar dariya ta ɗan bugi Zuzee.

“Ke kam ba ki da dama Zuzee, nima fa a yanzu fata nake cikin ya zube wallahi, ke ban ƙi ba ma ta mutu, don ita ce matsalata a duniyar nan.”

Zuzee ta ce,

“Ai tsaf za ki iya ɓarar da ɗan banza.”

Ɗan zaro ido Aisha ta yi.

“Kamar ya?”

Don duk wata hanyar makirci ba ta san ta ba.

Sai da Zuzee ta ɗan dafa Aisha sannan ta ce,

“Ba ke kike girki ba yanzu?”, Aysha ta ce,

“Eh ni ce.”

Zuzee ta ce,

“To tsaf za ki maka ma shegiya ƙwaya a ruwa ko lemu ki bata, tana sha za ki ga ikon Allah.”

Karon farko da Aisha ta ji bata ji shakka ba a shawarar Zuzee, saboda kishi ya fara busar mata da zuciya, komai ma yanzu za ta iya yi.

Da yake Aisha ba ta san kalar maganin ba, tambayar Zuzee ta yi, “Toh ina zan samu maganin?”

Zuzee ta nuna Jamsy da ke ta jinjina kai ta ce,

“Wannan Hajiyar za ki tambaya.” Da yake cikin makircin Jamsy sau uku tana ɓarar ma Hannah ciki, daga ƙarshe ma sai ta yi asirin da mijin zai daina kusantar Hannah bare har ta samu cikin.

Kalar maganin Jamsy ta ba Aisha, don tana da saura, ta kuma ce kafin ta sanya ma Maryam maganin sai ta jawo ta a jikinta, yadda ba za’a gane ita ta ɓarar mata da ciki ba. Mugun karatu Aisha ta sha shi a wurin Jamsy, nan ta ƙara yi ma Aisha huɗubar yadda za ta yi ta tsula tsiyarta ba tare da wani ya ankare da ita ce ba.

Godiya Aisha ta yi ma Jamsy akan muguwar hanyar da ta ɗora ta, sai dai zafin kishi da son zuciya sun kasa nuna mata illar bin wannan hanya. Ita kuwa Jamsy sai ƙasaita take. Don ma ta ƙara nuna ma Aisha kishiya ba a bakin komai take ba sai ta ƙara kiran Hannah tare da sa ta wankin banɗaki.

Aysha na ganin yadda take isa ta ce,

“Lallai ke kike juya gida.”

Jamsy ta ce,

“Wallahi kuwa, ai ni ba ‘yar iskar da za ta zo ta yi yadda ta ga dama a gidana, daga mijin har ita sai in ci uban su.”

Zuzee ta karɓe da,

“Ai ke ba kya wasa, ita Aksha ana gwada mata hanya tana kaucewa, ko da yake alamu sun nuna ta fara gane gaskiya.”

Famfo suka ci gaba da yi ma Aisha a kan ta zo su kai ta wurin maganin da daga Khamis har Maryam sai sun raina kansu.

Aisha ta ce,

“Ku bari dai na fara zubar mata da cikin tukunna.”

Rufe bakinta kenan wayarta da ke hannunta ta shiga ruri, ganin Khamis ne sai hankalinta ya tashi, ɗaga wayar ke da wuya kuwa ya fara yi mata faɗan rashin dawowa da wuri don har shida saura, gashi da wuri ake Sallar Magariba.

Yadda ta ɗan tsorata da faɗan ne ya ba Jamsy mamaki, sai da Aisha ta gama wayar ta ce mata, “Namijin ne kike wani ɗaga hankalinki a kanshi, to wallahi sai mun fidda miki wannan tsoron.”

Aisha da ke shirin miƙewa ta ce, “Kada ki damu, ai kin zama Antyna nima.”.

Musayar lamba suka yi, daga bisani Aisha ta tafi, inda ta bar Zuzee kuma a nan gidan Jamsy.

Aisha na isa gida ta taras da Maryam ta tada kai da cinyar Khamis a nan falo. Ɗan haɗe rai ta yi, a zatonta Khamis zai mata faɗa, sai dai abin mamaki ta ji shiru.

Nan ta zauna suka yi ‘yar hira, duban Maryam ta yi tana washe baki.

“Mairo jiki ya yi sauƙi.”

Don so take tun yanzu ta fara jawo Maryam a jiki.

‘Yar dariya Maryam ta yi bayan ta tashi zaune, cewa ta yi,

“Ai kuwa da sauƙi sosai, tuwon da kika yi ma sosai na ci, kuma cikin ikon Allah ban yi amai ba.”

Khamis ne ya karɓe da,

“Irin shi za ki yi mata gobe.”

Ko kusa Aisha ba ta ɓata ranta ba don ta san me take shirin aikatawa.

Tun daga wannan rana Aisha ta shiga cusa kanta a wurin Maryam, har ɗakinta take shiga, ko kuma ta tsaya bakin ƙofa ta ce ta fito su yi hira. Girki kuwa tuni ta ɗauke ma Maryam ta ce sai ta haihu.

Khamis da Maryam kuwa sun yi mamaki tare da jin daɗin yadda Aisha ta sauya. Musamman Khamis da abin da yake fata kenan.

Maryam kuwa tuni itama ta fito da kyakkyawar manufarta a wurin Aisha, saboda burinta bai wuce su zauna lafiya ba, don ta lura abin da Khamis ya fi so kenan.

Tsawon mako ɗaya Aisha ta ɗauka kafin ta cimma burinta. Ita kuma Maryam sai wani ƙara shige mata take, duk wani abin kwaɗayi da take so sai ta langaɓe ta ce don Allah Aisha ta yi musu, saboda idan ita ta yi ba ta iya ci, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yake ma Aisha ba.

A ranar da ta ɗauri aniyar saka ma Maryam magani kuwa, kunun aya ta haɗa musu mai daɗi a kitchen, ƙaton Jug ta ɗauko ta zuba ma Maryam, sannan ta kwance maganin da ta ƙulle a zanenta.

Wani irin shu’umtaccen murmushi ta yi, sannan ta ɓalli maganin ta saka a cikin kunun ayar ta motse, a fili kuma ta ce,

“Yarinya sai dai wani cikin ba wannan ba.”

Don ta samu tabbacin maganin yana aiki sosai.

Cike da azarɓaɓi ta ƙulle sauran maganin, sannan ta ɗauki Jug ɗin da nufin kai ma Maryam.

<< Kishiyar Katsina 11Kishiyar Katsina 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×