Kamar daga sama Aisha ta ji muryar Khamis ya ce,
“Wane cikin ne ki ke cewa sai dai wani ba shi ba?”
Cikin muguwar kiɗima ta dube shi lokacin yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji, sai dai tsananin tashin hankalin da ta shiga ya hana ta lura da tashin hankalin da shi ma ya shiga, domin ba abin da jikinsa ke yi sai karkarwa.
“An yanka ta tashi.”
Ta faɗa a ranta, lokaci ɗaya kuma idanunta da ke ɗauke da zallar rashin gaskiya na ci gaba da kallon sa.
Khamis da akan idonsa ta aiwatar da komai ya daka mata wata irin tsawa,
“Na ce cikin wa za ki ɓarar?”
Jikinta na ɓari ta ce,
“Kai Abban Haneef, wace irin tambaya ce Wannan?”
Ba tare da ta sani ba kuma jug ɗin kunun ayar ya ɗan karkace ya fara zuba ƙasa.
Ganin Khamis ya tako ya zo gabanta ne ya ƙara ɗimauta ta, musamman da ya ce,
“Amsa kawai nake so saboda na ga komai.”
Gani take kamar barazana ce yake mata, amma ba abin da ya gani, domin tabbatar da gaskiyar maganarsa ne ta tambaye shi.
“To me ka gani?”
Lokaci ɗaya kuma tana kallon idanunsa da suka rine zuwa launin ja.
Cikakkiyar amsar abin da ya gani ya faɗa mata, inda ya ce,
“Na ga kin ɓalli magani kin saka a jug, sannan kin maida sauran a zani kin ƙulle.”
Ɗorawa da tambayar ta ya yi ya ce,
“Maganin me ye kika saka wanda har kike cika bakin sai dai wani cikin?”
Wata irin ajiyar zuciya Aisha ta sauke tare da lumshe idanunta da suka fara ƙafewa saboda tsananin masifa da tashin hankali. Idan akwai ranar tonon asiri a wurin Aisha to wannan ce, domin bata da hujjar da za ta ce bai ganta ba, ‘To yaushe ma ya shigo?’
Ta tambayi kanta, ba ta da amsa, amma ta san dai lokacin da take ƙoƙarin saka maganin ba ta ji kuma ba ta gani, to a wannan lokacin ne ya zo ya ga komai.
Ji ta yi ya dafa kafaɗunta ya fara magana cikin murya mai ɗauke da tsantsar baƙinciki. Baƙincikin da bai taɓa tsammanin zai haɗu da irinsa ba, saboda ya yarda da ita ɗari bisa ɗari.
“Aisha me Maryam ta tsare miki ne da ba kya son ta, me miskinin cikin Maryam ya yi miki ne da kike son ganin bayansa?”
Samun kanta ta yi cikin naɗe tabarmar kunya da hauka, buɗe idanunta yi, sannan ta yi magana a ɗan fusace ta ce,
“Ni na faɗa maka bana sonta ne?” Ya ce,
“Eh mana ga shaida nan a cikin jug, yaushe ki ka zama muguwa ne, yaushe kishi ya raba ki da imani da kuma tsoron Allah?” Waɗannan tambayoyi da yake mata ba ƙaramar azaba suke gana mata a zuciya ba, ba ta san sa’adda ta saki jug ɗin da ta gaji da riƙo a ƙasa ba.
Ko kusa Khamis bai damu da yadda kunun ayar ya zubo masa a ƙafafu ba, saboda baƙincikin ganin matarsa kuma uwar ‘ya’yansa ta sauya, sauyawar da ta haifar mishi da gagarumin tsoro a zuciya, don Allah kaɗai ya san mugun abin da take da niyyar aikatawa a nan gaba ma, take ya ji tsanarta ta fara ratsa dukkan jikinsa, wanda kuma wannan tsanar ita ce ta farko a wurinsa.
Kamar zai yi kuka ya ce,
“Aisha me na tauye ki da shi, me ye laifina da za ki jefa ni a baƙinciki? Aure! Na san ita ce amsarki, toh ƙarin auren haramun ne? Yinsa ya sa na rage ki da wani abu? To me ya sa Aisha ki ka zaɓi ki cutar da ni, don duk abin da ki ka yi ma Maryam ni ki ka yi ma wa, saboda amanarta na hannuna ne.
Aisha kin sauya, sauyawar da ta tafi da kaso mai yawa na matsayinki a wurina, don haka dole na ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kanki.”
Kamar saukar Aradu ta ji kalmar ‘Dole na ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kanki’ take ta ji zuciyarta ta fara ƙeƙashewa don akan ta yi yinƙurin cutar da Maryam ne ya ce haka.
“Akan waccan matsafiyar za ka ɗauki mataki a kaina? Ita ka san irin cutarwar da ta yi mana ni da kai?”
Aisha ta faɗa tana zare mishi idanu. Cewa ya yi,
“Maryam ɗin ce matsafiya?”
Ta ce,
“Eh.”
Ya ce,
“To in dai tsafi halinta ne, wata rana zan kama ta kamar yadda na kama ki a yanzu.”
Tsuru Aisha ta yi da idanu, cikin ranta kuma tana jin ina ma ba’a haife ta a duniya ba bare har ta ga ranar tonuwar asirinta, wasu hawaye ne masu zafin gaske suka gangaro mata a kumci, kasa goge su ta yi don ta san aiki ne za ta ɗora ma kanta don ba za su tsaya ba. Ji ta yi Khamis ya ce,
“Ki bani maganin da kika ɓoye a zaninki, shi kaɗai zai sassauta hukuncin da zan yi miki a gidan nan.”
“Ni ba wani magani da na ɓoye, kawai sharri kake son ja mini, kuma ka je kai da Allah.”
Murmushin da ya fi kuka ciwo Khamis ya yi, a ƙasan ransa kuma yana mamakin ƙarfin halinta na barinsa ga Allah, duk da ta san ba ta da gaskiya. Hannu ya kai zai ɓalle mata zani, aikuwa cikin masifa ta ce,
“Kada ka sake taɓa ni!”
Ɓangare ɗaya kuma tana riƙe da hannun.
Ya san riƙon da ta yi mishi bai isa ya hana shi yin abin da ya ga dama ba, saboda ƙarfinsu ba ɗaya ba ne, sai dai kuma baya son su yi hayaniyar da Maryam za ta jiyo su.
Sassauta murya ya yi ya ce, “Aisha bana son taurin kai, don ba zai jiyar da ke daɗi ba. Ki sake mini hannu, sannan ki bani maganin, idan ba haka ba wallahi da mahaifanki zan haɗa ki su karɓi maganin a wurinki, idan kuwa ki ka bani to abin zai tsaya daga ni sai ke.”
Idan akwai abin da Aisha ta tsana shi ne a kai ƙararta a wurin mahaifanta, kuma a yadda ya yi maganar ba wasa zai aikata, don haka ba ta san sa’adda ta kwance maganin ta miƙa mishi ba.
Kasa karɓa ya yi, sai ma ya kafe ta da idanun da ke ɗauke da yanayin tafarfarsar da ke cikin zuciyarshi. Aisha baiwar Allah, mai nagartaccen hali, ita ce kishi da ƙawaye suka canja mishi ita, anya zai iya yafe ma kansa, don ƙila da bai ƙara aure ba hakan ba za ta faru ba. Zuciya ce ta ce mishi,
“Ba wani laifin ƙarin aurenka a nan, kawai ta sa kanta ne, ƙawaye kuma ba ka san tun yaushe suke tare ba.”
Jiki a mace ya karɓi maganin tare da rumtse shi gam a hannu, cikin ƙunar rai ya ce,
“Aisha kin zama sakarar banza da wofi, kin manta Allah, kin kuma kama ƙawaye, waɗanda idan sun kai ki baro ki za su yi. Don haka a shirye nake da gano ko su waye kuma in ɗauki mugun mataki a kansu.”
Yana faɗin haka ya juya a fusace ya fita daga kitchen ɗin.
Ɗakinsa ya nufa ya watsa ruwa tare da canja kaya saboda ɓacin da na jikinsa suka yi. Daga nan kuma ɗakin Maryam ya nufa, sai dai kafin ya shiga ya zura maganin da ya fito da shi a aljihu.
Duk yadda ya so ɓoye damuwarshi ga Maryam sai da ya kasa, Maryam na ganin ya zauna jagwab a kan sofa tare da dafe kai da hannaye ta fahimci a kwai wani abu. Tasowa ta yi daga kan gadon tare da zama a gefensa
“Wa ya taɓa mini Ogana?”
Ta faɗa tare da janye hannayen daga kansa a hankali.
Shi ba zafin da yake ji a ransa ne damuwar shi ba, tsoron kada wani abu ya samu cikin Maryam ne damuwar shi, dubanta ya yi, ya ce, “Kada ki damu da damuwata Mairo, cikinki na ke son jin idan yana lafiya?”
Da ɗan mamaki ta dube shi, cewa ta yi,
“Damuwarka ai damuwata ce mijina.”
Ya ce,
“Haka ne, amma ba kya jin wani sauyin yanayi a tare da ke?”
Don zuciya na ta ruwaita mishi cewar Aisha ta daɗe tana ɗura ma Maryam maganin zubar da ciki.
Har yanzu mamaki bai rabu da Maryam ba, saboda tambayar yau a kan cikinta ta sha banban da ta kullum, hannayenta cikin nashi ta ce,
“Gaskiya ba na jin wani ciwo a tare da ni, amma me ya sa ka ke ta jero mini waɗannan tambayoyi?”
Shiru ya yi, don ba zai iya faɗa mata ba, saboda gudun fitina, sai dai ya ce,
“Ba komai, kawai ina son sanin lafiyar babyna ne.”
Murmushi ta yi tare da kwantowa jikinsa. Shiru ne ya ratsa a tsakaninsu, kowa da abin da yake tunani.
Khamis da ya ji bai gamsu da lafiyar Maryam ba ya ce,
“Mu je dai asibiti Mairo.”
Janye jikinta ta yi ta ce,
“Wallahi lafiya lau nake ji na.” Cewa ya yi,
“Na san da haka ai, kawai dai yana da kyau ki riƙa ganin doctor akai-akai, saboda wahalar da ki ka sha a baya.”
‘Yar ajiyar zuciya ta yi, sannan ta ce,
“To bari na sha kunun ayar.”
Kai ya girgiza,
“A’a, idan mun je can na siya miki wani.”
Lambar Dr. Dini ya kira ya shaida mishi gasu nan zuwa wurinsa. Kaya Maryam ta canja ta kuma zura hijabi da takalma. A parking space ta iske shi suka nufi asibiti.
Aisha na jin fitar Khamis ta ɗan ji dama-dama a ranta, lambar Zuzee ta kira, aikuwa tana ɗagawa Aisha ta ce,
“Ke allura fa ta tono garma, Abban Haneef ya kama ni ina sanya ma wannan tsinanniyar maganin da Anty Jamsy ta bani!”
Daga can Zuzee ta dafe ƙirji tare da zaro idanu ta ce,
“Ke don Allah!”
Aisha ta ce,
“Wallahi kuwa Zuzee, ba ki ji tashin hankalin da nake ciki ba yanzu, tsorona kada ya faɗa ma mahaifana in shiga uku”
Zuzee da itama tsoron kada a ce ita ta yi hanyar samuwar maganin ya kamata ta ce,
“Kema Aisha ya aka yi ki ka bari ya gani? Ko da yake ma ya tambaye ki ina ki ka samu maganin?”
Aisha ta ce,
“A’a.”
Daga can Zuzee ta ce,
“To don Allah ko da ya tambaye ki kada ki saka mu, kema ɗin idan ya kai ƙarar ki ko za’a kashe ki kada ki ce a hannunki ya same shi, idan ya so ma ki liƙa ma Maryam ɗin, ki ce da kanta ta baki ta ce ki jiƙa mata don ba ta iya shan magani a haka, ke kuma baki san ko maganin miye ba.”
Sosai Zuzee ta yi ma Aisha karatun ko za’a kaɗa ta dambu da taliya kada ta amsa laifinta a gaban iyayenta. Aisha kuwa a gaggauce ta hau kan shawar Zuzee ta zauna, har ma ta riƙa jin kamar abin da Zuzee ta faɗa mata shi ne gaskiya.
Khamis da Maryam sun yi sa’a ba kowa a office ɗin Dr. Dini lokacin da suka shiga. Da fara’a Dr. Dini da ke sanye da farin glass a idanu ya tarbe su tare da nuna musu kujeru biyun da ke gaban table ɗinsa ya ce su zauna.
Gaishe shi Maryam ta yi. Khamis kuma ya miƙa mishi hannu suka gaisa. Tambayar Khamis ya yi,
“Ya madam da jikin?”
Khamis ya ce,
“Da sauƙi sosai.”
Ci gaba da faɗa ma Dini ya yi akan yana son a yi ma Maryam da cikinta checkup. Dini bai wani tambayi dalili ba don buƙatarsu ce dama irin haka.
Tambayoyi Dini ya yi ma Maryam, ta kuma bashi amsa daidai gwargwado. Bayan ya gama jin ta bakinta ne ya kira wata nurse a waya, tana zuwa ya haɗa ta da Maryam ya ce su je ayi mata scanning.
Bayan fitarsu Maryam ne Khamis ya fiddo maganin da ke aljihunsa ya miƙa ma doctor Dini.
“Wannan maganin na mene ne?”
Dini na karɓa ya zaro idanu, saboda maganin na abortion ne.
Duban Khamis ya yi ya ce, “Wannan maganin ai masifa ne, babu mai cikin da za ta sha shi kuma cikin ya zauna a jikinta.”
Sallallami Khamis ya ci gaba da yi, wanda har Dini ya ce,
“A ina a ka same shi?”
Don ya fahimci saboda maganin ne Khamis ke sallallami.
Khamis da wani irin zafi ya turnuƙe ma zuciya ya ce,
“Na kama ne za’a sanya ma Maryam shi ta sha ba tare da ta sani ba.”
Jinjina kai Dini ya yi tare da faɗin, “To Allah ya kyauta, yana da kyau kam ka sanya kula a kanta.” Maganganu suka yi sosai da Dr. Dini akan cikin Maryam. Nan Dini ya yi ta bashi shawarwarin da za su kula da cikin ta yadda wani abu ba zai same shi ba da ikon Allah.
Bayan wannan kuma suka dasa hira, saboda kusan aminan juna ne, sun san juna ne adalilin mahaifansu da suke manyan abokai.
Shigowar Maryam ne ta katse musu hirar. Result ɗin da ke hannunta ta miƙa ma Dini, daga ita har Khamis kuma suka yi ma Deeni zuru suna jiran ya faɗa musu sakamako.
Iska mai ɗan zafi Dini ya furzas wanda ya yi sanadiyyar faɗuwar gaban Khamis, tun kafin Dini ya yi magana Khamis ya ce,
“Ya dai?”
Murmushi Dini ya yi sannan ya aje result ɗin a gabansa,
“Madam da baby suna cikin ƙoshin lafiya.”
Cewar Dini yana duban Khamis.
Khamis ya yi farinciki da jin haka, godiya ya yi ma Allah akan hana Aisha cutar da Maryam da ya yi.
Shwarwari suka ƙara karɓa daga wurin Dini, sannan suka yi bankwana da shi suka fito.
Babban shagon da ke asibitin Khamis ya biya tare da siya mata kunun aya mai sanyi, sannan suka tafi.
A hanya Maryam ta ce,
“Na so ka raka ni scan ɗin, da ka ga babynmu.”
Idanu Khamis ya ɗan zaro ya ce, “Ke don Allah, ke kin ganshi?”
Kai ta ɗaga mishi tana dariya.
Ba ta ankare ba sai gani ta yi ya riƙe sitiyarin motar da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya dafa mata ciki da shi, ai kuwa kamar babyn jira yake ya fara motsi.
Da sauri ya janye hannun yana dariya, idanunsa a daidai gate ɗin makarantar su Haneef ya ce,
“Ka ji baby ɗan albarka, ina taɓa shi ya fara motsi.”
Parking motar ya yi a gefe, suka ci gaba da hirarsu, ɓangare ɗaya kuma tana shan kunun ayarta. Ba su fi minti goma da zuwa ba aka tashi su Haneefa. Daga nan gidansu Khamis suka nufa.
Da fara’a Ummansu Khamis ta tarbi Maryam da jikokinta, bayan sun zauna ne suka gaisa, nan Umman Khamis ta tambaye Maryam ina Aisha, Maryam ta ce, “Tana gida.”
Haneef da Haneefa kuwa tuni sun shige cikin ɗakunan gidan wurin su Salma.
Nan Khamis ya bar su Maryam da nufin anjima zai zo ya ɗauke su.
Jagwab Khamis ya yi a cikin motarsa yana tunanin hukuncin da zai yi ma Aisha na yunƙurin zubar masa da gudan jini. Tambayar kansa ya shiga yi.
“Ina ma Aisha ta samu wannan maganin?”
Haka kawai ya ji zuciya ta bashi amsa da,
‘Ranar da ta fita ne.’
Don tana dawowa abubuwa suka canja, hakan ya nuna a can ta samo maganin.
Da tunanin irin hukuncin da zai yi mata ya tada motarsa ya nufi gida. Kai tsaye ɗakin Aisha ya nufa, aikuwa a bakin ƙofa ya jiyo muryarta tana magana a waya inda ta ce,
“To ba dole na bashi ba tunda ya gani.”
Bai son ya jiyo abin da zai ƙara mishi tsanarta, don haka ya kutsa kai cikin ɗakin. Firgitar da ta yi ce ta sa shi faɗin,
“Ɗayar munafukar ce kuke waya halan, da sannu sai mugun abun ku ya koma muku.”
Ita dai kasa magana ta yi, tana ta mazurai.
Dab da ita ya je ya tsaya, sannan ya sassauta murya ya ce,
“Kin bani mamaki wallahi, kin kuma fusata ni, don haka ki shirya ki tafi gidanku zan zo idan na huce.”
“Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un!”
Aisha ta furta a fili, saboda in dai maganar nan ta je gidansu to ta shiga uku, kuka ta fashe da shi. “Wayyo Abban Haneef, yanzu har abin ya kai haka?”
Tare da ruƙo mishi hannu.”
Fizge hannunshi ya yi ya ce,
“Ya wuce haka ma, saboda ban san me kika shirya ba, kin ga gwara a yi ma tufkar hanci.”
Yana faɗin haka ya juya, sai da ya kai bakin ƙofa sannan ya ce, “Wallahi kada na dawo na taras da ke a ɗakin nan.”
Don wani irin kuka take yi, wanda ke nuna zallar nadama, sai dai ko kusa bai taɓa mishi zuciya ba, don zai iya zama na munafurci.
Da idanu Aisha ta raka shi har ya fice daga ɗakin, cikin ranta kuma tana jin tashin hankalin da bai misaltuwa.
Wayarta ce ta yi ƙara, kuma Zuzee ce da itama tana can cikin tashin hankalin da bai misaltuwa.
Aysha na ɗaga wayar Zuzee ta ce, “Aisha to ya ake ciki?”
Aisha na kuka ta ce,
“Ya ce na tafi gida, tashin hankalina mahaifana su sani.” Daga can Zuzee ta ce,
“Mun shiga uku ni Zuhura, Aisha ko da an tambaye ki waye ya baki don girman Allah kada ki sa sunana.”
Aisha ta ce,
“Hmm, ta kanki kike ko?”
“A’a wallahi kema ina yin taki Aisha, mu yi mahaɗa idan kin fito sai mu tsara ƙaryar da za ki yi idan kin je gida.”
Da wannan suka yi sallama, Hijabi da jaka Aisha ta ɗauka. A falo ta taras da Khamis kwance a kan kujera yana fuskantar sama, yadda ya dafe kansa da hannu ne ya tabbatar mata da shi ma yana cikin damuwa. Raɓawa ta yi ta wuce shi a nan.
Zaune Khamis ya tashi tare da raka ta da idanu, wani irin tausayin kansa da Aisha gami da yaransa ne ya mamaye shi, bai so Aisha ta zama haka ba, don har ga Allah yana matuƙar sonta.
Aisha kuwa tuni sun yi mahaɗa da Zuzee. Nan Zuzee ta shirya mata sharrin da za ta ja ma Khamis, sannan batun magani ta ƙara jaddada mata kada ta yarda a hannunta aka ganshi duk yadda kuwa za’a yi. Da wannan shawara ta Zuzee ta isa gidansu.
A falo ta taras da mahaifiyarta da kuma ƙannenta. Kallon farko suka fahimci tana cikin tashin hankali, mahaifiyarta na faɗin,
“Aisha lafiya?”
Sai ta fashe da kuka.
Hankali a tashe ta ce,
“Ke me ke faruwa ne?”
Kasa magana Aisha ta yi, sai ma ta ci gaba da kukan.
Duk wanda ya ga yadda Aisha ta narke tana irin wannan kuka ya san ba lafiya ba. Hannunta Mommy ta kama suka koma sama, nan Aishar ke shaida ma Mommysu akan amaryarshi ne ya ce ta ta bar mishi gida. Ɗa da uwa sai Allah, Aisha na karanta ma mahaifiyarta ƙarya da gaskiya sai ta yarda, faɗa Mommy ta shiga yi tana faɗin,
“Wato ya ci moriyar ganga dole ya jifar da kwabrenta.”
Alhajinsu Aisha na dawowa Mommy ta same shi a katafaren ɗakinshi, sai da ta tabbatar ya ci abinci sannan ta ce,
“Aysha na nan fa.”
Tambayar ta ya yi,
“Kamar ya tana nan?”
Cewa ta yi,
“Khamis ya ce ta dawo gida zai zo.”
Ya ce,
“Shi Khamis ɗin?”
Ta ce,
“Eh”
Ya ce,
“To sai ya zo.”
Ci gaba da maganar dalilin dawowar suka yi, da Alhajin ya ji dalilin don ba ta yi ma amaryarsa girki da wuri ba, sai ya ji bai gamsu ba, cewa ya yi,
“A bari ya zo ɗin kawai.”
Aisha kuwa a wannan dare kasa rumtsawa ta yi, ba komai kuma ya hana ta bacci ba sai kewar yaranta da kuma tsoron kada Khamis ya faɗa ma mahaifanta laifin da ta yi mishi, don ta na da yaƙinin ba za su raga mata ba, saboda su ba ƙananun mutane bane. Zaune ta tashi a kan gadon da take kwance tare da zabga tagumi, zuciya ce ta fara ruwaita mata ko ta kira Khamis ta roƙe shi kada ya faɗa ma mahaifanta, sai dai tuna shawarar Zuzee na ko da ya faɗa ɗin ta murje idanu ta ce ba ta san an yi ba, sai ta ɗan samu nutsuwa, da kuma wannan gurguwar shawarar ta kwanta.
Shima ɗin rutsum bai runtsa ba, har yanzu baƙincikin samun Aisha da son zubar masa da gudan jini ya hana shi saƙat, tunda ya kwanta yake juye-juye a kan gado. Maryam na lura ta tashi zaune, hakan ne ya yi sanadiyyar tashinsa zaune shi ma.
Ɗan kwantowa ta yi a jikinsa tare da magana ƙasa-ƙasa ta ce,
“Kasan tafiyarta za ta hana ka bacci, kuma shi ne ka barta ta tafi?”
Don ya faɗa mata Aisha na gidansu, amma bai faɗa mata dalilin tafiyar ba. Kuma a zatonta kewar Aishar ce ta hana shi bacci.
Jawo ta ya yi sosai a jikinsa tare da cusa kansa a wuyanta yana shaƙar ƙamshin da ke fitowa a gaɓoɓin jikin ta.
“Ba wannan ne damuwata ba Mairo, dalilin tafiyar ne ke damuna, tsoro na ci gaba da mamayar zuciyata, don ban san me zai faru a gaba ba.”
Duk da Maryam ba ta san abin da ya faru ba, da kuma tsoron da yake ba, amma ta taka muhimmiyar rawa wurin kwantar mishi da hankali, inda ta ce,
“Ba abin da zai faru sai alkhairi mijina, kuma a ganina bai kamata ka ce Umman Haneef ta tafi ba.” Cewa ya yi,
“Ko?”
Ta ce,
“Eh.”
Ya ce,
“Me ce ce hujjarki?”
Ta ce,
“Kun zama ɗaya ai, duk girman laifinta a nawa ganin za ka iya hukunta ta ba tare da kowa ya sani ba ma, bare har ta tafi.”
Tabbas da Maryam ta san laifin da Aisha ta yi wanda akanta ne da ba ta ce haka ba, baya son kuma gwasale Maryam ɗin, sai dai ya ce, “Gaskiya ne, nima ban so haka ba, amma In Sha Allahu komai zai wuce.”
Fatan haka Maryam ta yi.
Kwantawa ta yi. Inda shi kuma ya tafi wurin yaransa da suke ɗakin Aisha. Haneef da ke kwance a kan katifa ya kai banɗaki ya yi fitsari, sannan ya maidoshi ya yi mishi addu’a.
Wurin Haneefa da ke kan gado ya koma, tada ta ita ma ya yi, tana buɗe idanu ta tambaye shi, “Mommy ta dawo?”
Kai ya girgiza mata,
“A’a.”
Baki ta buɗe za ta yi kuka, lallashinta ya yi sannan ita ma ya kaita ta yi fitsarin.
Addu’a ita ma ya yi mata, daga nan ya koma kan sofa ya zauna, addu’a ya ƙara tofe ɗakin da shi, sannan ya bar ma Allah sauran. Ɗakin Maryam ya koma ya kwanta, amma yadda ya ga rana haka shi ma wannan dare ya ganshi.
Washe gari da kansa ya haɗa musu breakfast, Tea ne sai ƙwai kaɗai suka ci, sannan suka shirya baki ɗaya suka fita shi da yaran.
Yana aje yaran ya biya gidansu, a ɗaki ya samu Ummansa, bayan sun gaisa ne ya buƙaci girkin rana daga gare su.
“Ina Aishar ne?”
Saboda Umma ta san ragamar girki ta koma a hannunta.
Khamis bai ɓoye mata ba, cewa ya yi,
“Tana gidansu tun jiya Umma.” Ranta a ɗan ɓace ta ce kamar ya. “Tun jiya tana gida, Khamis bana son irin haka fa.”
Cikin ladabi ya ce,
“Umma Aisha ce ba ta ji ko kaɗan.”
Ta ce,
“Yanzu ka san da haka?”
Faɗa ta yi mishi, har sai da ya ji dama bai faɗa mata ba, sai dai ya mata uzuri don ita ma bata san laifin Aishar ba.
Aisha da mahaifanta kuwa sun zuba idanu suna jiran Khamis, sai dai har kwana huɗu kenan bai zo ba. Tuni kewar yaranta ta fara damunta, don ko da take da kyarar yara, to kuma tana da sarkafar su a ranta. Gaba ɗaya ta daina shakkar zuwan Khamis saboda ta shirya ƙaryata shi.
Ganin har an kai kwana biyar ne Mommy ta matsa ma Alhaji akan ya kira Khamis fa don a ji matsayar aurensa da Aisha, saboda ganin Aishar ba ƙaramin ɗaga mata hankali yake ba, don babu uwar da za ta so ganin ‘yarta ta koma bazawara.
Da farko kam ya cije, don ransa ya fara ɓaci shi ma, gani yake Khamis ya gama cin fuskarsa. Lallaɓashin da Mommy ta yi ne ya sa sai ya amince zai kira shi.
Da yamma Khamis na zaune a falo yana rarrashin Haneefa da ke ta kukan ya kai ta wurin Mommy, wayarsa ya ji ta fara ruri, yana dubawa ya ga ‘Alhajinmu’ ras gabanshi ya faɗi don haka ya sanya ma babansu Aisha.
Ɗaga kiran ya yi, cikin ladabi ya gaishe da Alhajin. bayan Alhajin ya amsa ya kuma ɗora da,
“Bayan magarib ina son ganinka.”
Cikin ladabi Khamis ya ce,
“To In sha Allahu.”
Sannan suka yi sallama.
Haneefa da ta san da wanda yake waya ta ce,
“Daddy nima zan je.”
Wayau Khamis ya yi mata ya ce, “To In Sha Allahu zan je da ke.”
Lallaɓata ya yi, sannan ya tura ta wurin Haneef da ke ta ball shi kaɗai a farfajiyar gidan.
Wanka Khamis ya yi tare da canja kaya, faɗa ma Maryam inda zai je ya yi. Kawai sai ji ta yi gabanta ya faɗi, a zahiri tana son Aisha ta dawo, amma a baɗini ɗan kishi na sa ta jin ina ma kada ta dawo, don bata san gidan zai fi yi mata daɗi ita kaɗai ba sai da Aishar ba ta nan.
Fatan dawowa lafiya ta yi mishi, sannan ta rako shi har parking space, Allah ya kiyaye suka yi mishi har ya fice, da zummar zai dawo ya tafi da yaran.
Unguwarsu Aisha ya nufa, a lokacin kuma ana ta kiraye-kirayen sallar Magriba, a masallacin gidansu Aishar ya gabatar da sallolinsa na Magrib da Isha’i, daga nan kuma suka yi tsinke shi da Alhajinsu Aisha a falon gidan.
A tsarin shari’a in dai adalci ake son yi a tsakanin ma’aurata, to a haɗa su domin jin ta bakin kowa.
Haka aka yi kuwa, a falo aka zauna, inda Aisha da Khamis suke zaune a kan lallausan carpet ɗin da ke shimfiɗe a ƙasa, Mommy da Alhaji Usman kuma na zaune a kan kujera three seater suna fuskantar su.
Wata irin faɗuwar gaba ce ke ci gaba da tafiya da Aisha, duk da ƙaryar da take shirin shirgawa, sai dai zuciya na faɗa mata idan mahaifanta sun yarda da maganarta saboda rashin sani, to shi kuma fa? Ya san gaskiya, kuma ko da ta koma ɗakinta to fa daraja da ƙimarta sun zube, don haka dole soyayyar da ke tsakaninsu ta samu naƙasu, ita kuma ba ta fatan haka, musamman da tsawon kwana bakwai ita kaɗai ta san irin azabar da rashin ganinsa da kuma ‘ya’yanta ta haifar mata.
Khamis kuwa tuni ya yanke hukuncin da yake gani shi ne daidai, don haka iznin magana kawai yake jira.
Jin Muryar Alhaji Usman inda ya ce “Khamis” ne ya ba shi damar dubanshi tare da amsawa da “Na’am.” Yadda ya ga fuskar Alhaji Usman a murtuke ne ya ɗan sa shi faɗuwar gaba.
Nutsuwa ya yi tare da ci gaba da saurarensa inda yake cewa, “Tsawon mako ɗaya kenan da dawowar matarka gida, me ke faruwa ne?”.
‘Allah ka rufa mini asiri, ka sa Abban Haneef ya rufa mini asiri.’ Aisha ta faɗa tare da gyara zamanta, zuru ta yi ma Khamis don jin me zai ce, lokaci ɗaya kuma ƙirjinta na ci gaba da dukan uku-uku.
Ɗan shiru Khamis ya yi, daga bisani ya ce,
“Alhaji ni ban san ta ina zan fara ba, saboda Aisha ta wani irin canja, halin da ta tsira a yanzu idan ba cewa na yi ta dawo gida ba zan iya cutar da ita nima, kamar yadda ita ma take yunƙurin cutar da ni.”
“Wa ce irin cutarwa?”
Mommynsu Aisha ta tambaye shi.
Yaufa ake yinta, cikin Aisha ne ya ɗauki rugugi, sai dai lokacin da Khamis ya ce,
“Mommy Aisha uwar yarana ce, laifin da ta yi mini tsakanin ni da ita ne.” sanyi ne ya ratsa zuciyar Aisha.
Alhaji ya ce,
“Ka san tsakanin ku biyu ne kuma ka turo ta gida?”
Khamis ya ce,
“Cewa ta dawo gidan ne kaɗai mafita a gare ni.”
Shiru wurin ya yi, daga bisani Alhaji Usman ya maida dubansa ga Aisha,
“Ke kuma me za ki ce?”
Shiru Aisha ta yi don bata da abin cewa a yanzu.
Juyawa Alhaji Usman ya yi ga Khamis da kansa ke ƙasa,
“To Khamis, shirun da Aisha ta yi ya nuna ba ta da gaskiya, don haka za mu iya ci gaba da zama da ita mu yi mata faɗa, ko kuma ka gama aurenta ne tunda ta sauya?
Interesting