Aisha kuwa kamar ta haɗiye zuciya.
“Bari mu fita.”
Ta faɗa tana duban shi, ɗago kan ya yi ya ce.
“Ok, gida dai sai anjima idan zan koma ko?”
Kai ta ɗaga sannan ta ja yaranta suka fice daga ɗakin.
Yana shirin sake duƙar da kansa ya ga Maryam ta yi motsi. Cike da fargabar kada ta tsorata da shi ya dube ta lokacin da ta buɗe idanu.
Yadda yake tsammanin za ta tsorata da shi ba haka ba. Sai dai kuma kamar ba ta gane shi ba ma, saboda irin kallon da take mishi.
Shigowa ɗakin Dini ya yi don yana da tabbacin farkawarta a wannan lokacin. Yunƙurin tashi ta so yi, Dini ya ce,
“No, ki yi kwanciyarki.”
Ba musu ta kwanta, amma sai ta ce,
“Su waye ku?”
Ras gabansu ya faɗi, cikin kiɗima Khamis ya ce,
“Maryam ni ne Mijinki Khamis.” Daga kwancen ta girgiza kai tare da ƙyalƙyalar dariya.
“Miji? Ni bani da wani miji.”
A tare Dini da Khamis suka dubi juna. Wata sabuwa, in ji ‘yan caca. Maryam ta samu taɓin hankali.
Su Umma na ji suka shiga sabon tashin hankali. Babu wanda bai yi kuka ba. Ummansu Khamis ta ce, “Maryam idan Allah ne ya ɗora miki mun karɓa, idan kuma halittarsa ce ta zalunce ki mun barta da Allah.”
Me kaza a aljihu baya jimirin as! Aisha ji ta yi kamar da ita Umma take. Wata kulawar Maryam ta samu, daga nan kuma aka sake maida ita bacci.
Har ƙarfe sha ɗaya su Aisha ba su tafi gida ba. Sai Sha ɗaya da rabi Khamis ya ɗauko su suka dawo gida. Zamansu Falo ke da wuya sai wayar Khamis ta fara ruri. Lamba ce, ɗagawa yayi da sallama a bakinsa. Muryar mace ya ji ta gaishe shi.
“Abban Haneef ina wuni.”
Idanunsa kan Aisha da ta ke mishi kallon tuhuma ya amsa.
Daga can ta tambaye shi,
“Ya jikin Maryam da baby?”, Khamis ya ce,
“Alhamdulillah, amma da wa nake magana?”
“Zuhura ce.”
Ta ba shi amsa, ya ce,
“Ayya Zuhura, ai ban gane ba da farko.”
Daga can ta ce,
“To ai don ba ma waya ne. Dama na kira in ji lafiyar Maryam ne. Aisha na kira ta ban samu ba.” Godiya Khamis ya yi mata sannan ya miƙa ma Aksha wayar don ta gane Zuzee ce.
Ce mata Aisha ta yi,
“Ke shegiya har kinsa na fara zargin mijina.”
Wata irin dariya Zuzee ta yi ta ce, “Haba don Allah.”
Aisha ta ce,
“Ai kin san ni dai akan mijina.”
‘Yan maganganu suka yi sannan suka yi sallama. Ɗaki Aisha ta bi Khamis ta bashi wayar. Tea kaɗai ya iya sha. Wanka da sallar neman lafiyar Maryam ya dasa. Sai can wurin ukun dare ya kwanta, shi ma yadda ya ga rana haka ya ga wannan daren.
Preemie da ke killace a NICU kuwa tun da asuba Allah ya karɓi abinsa, domin ya rasu, kuma likitoci ba su san me ye ajalinsa ba don ya samu sauƙi sosai.
Da asubar aka sanar da Khamis. Daga Masallaci ya wuce asibitin.
Tuni an fito da yaron daga NICU. Khamis na rungume da shi acikin towel ya shiga room ɗin da Maryam take. Fuskarta da ke bacci ya kalla, wasu irin hawayen tausayinta ne suka zubo mishi.
Ba ƙaramin tanadi suka yi ma wannan baby ba idan Allah ya sa ya zo duniya. Sai dai suna nasu tsarin, tuni Allah kuma ya gama nashi.
Zama yayi a kan kujera don jiri ke ɗibarshi. Hajiyarsu Haupha kuwa sai magana take bashi, tana nuna mishi kowa da kalar ƙaddararsa. Fata dai Allah ya ba Maryam lafiya.
Fita Hajiyarsu Haupha ta yi, don ta lura kamar yana son kaɗaicewa da iyalinsa.
Gaban Maryam ya aje yaron, tsaf zakae ce bacci yake, saƙalo mata da hannu yayi a jikin yaron kamar ta rungume shi. Photos masu kyau ya yi musu ita da yaron. Gadon bai isa ya kwanta ba shima, amma sai ya yi dubara ya ɗauke su wasu photos ɗin da vedios. Cikin ransa ya yi tanadin aje ma Maryam su idan ta samu lafiya.
Gari na ƙarasa wayeya aka nufi gida domin shirya jana’izar yaron. Aisha na ganin ya shiga da gawar ɗakinsa ta bi shi.
“Ni sai wani nan-nan kake da gawa, ko ƙyama ba ka yi.”
Ita dai baƙin kishinta ke zaftarar da darajarta a wurin Khamis. Wani mugun kallo yayi mata.
“Na san gawar don ba ta ɗanki ce ba shi ya sa kika ce haka.”
Ɗaukar gawar ya sake yi ya rungume tsam a ƙirjinsa.
“Allah dai ya nufa ba za ka rayu ba my NICU baby, Allah ya sa can ta fiye maka nan, Allah kuma ya ba Mom ɗinka lafiya.”
Tuni Aisha ta fice, kuma dama don ta bashi wuri ya yi mata haka.
Da ‘yan dubaru aka yi ma babyn wanka aka kuma shirya shi cikin linkafani. Duk da jariri ne, kuma preemie ma, amma an samu mutane a wurin jana’izar, saboda akwai kyakkwar alaƙa tsakanin Khamis da mutane.
Sai dai zaman ta’aziyya ne Khamis bai yi ba. Duk masu son jajanta mishi sai dai su kira shi a waya ko kuma su iske shi asibiti, don ya koma can da zama.
Jama’ar Katsina kuwa tuni sun hau hanyar zuwan wurin ɗiyarsu.
*****
Lalurar taɓin hankalin da Maryam ke fama da ita ba ta yi ƙamarin da za’a ce tana hauka tuburan ba, saboda abin yana lafawa har a yi hira da ita, sai dai mutum na jin hirar zai fahimci ba ta mai hankali ba ce. Idan kuma abin ya tashi duk wanda ke wurin sai ya matuƙar tausaya mata, saboda burinta bai wuce ta ruga a guje ba. Ga kuma ciwo a jikinta wanda bai son gajaniya, don ma Allah ya taimaka ba ta da ƙanjiki, kuma tana samun kyakkyawar kulawa a wurin duk wani mai haƙƙin kula da ita.
Sosai kuma wannan lalura ta Maryam ta jefa mutane a cikin ruɗani. Wasu na ganin haihuwa ce sanadi. Wasu kuma sun yarda iska ne suka shafe ta. Kuma waɗanda suka yadda iskan ne suka fi rinjaye. Sai dai kuma tambayar da suka kasa samun amsarta ita ce, ‘Yaushe iskan ya sami Maryam?’ Saboda duk waɗanda suka san ta, basu san tana da lalurar iska ba. Allah mafi sanin komai suka bar ma lamarin, saboda shi ke da ikon ɗora ma bawansa lalura ba tare da ya yi shawara da kowa ba.
Aisha kuwa tuni ta daina nadamar yi ma Maryam asiri, sai ma daɗin da take ji akan mutuwar ɗan Maryam, da kuma lalurar da take fama da ita. Tuni ta so kiran Jamsy domin shaida mata aiki fa ya ci, ba ta samu dama ba, saboda mutanen da ke ta shigowa jefi-jefi yi musu jajen mutuwar babyn Maryam. Can wurin sha biyun rana ne mutane suka ɗauke ƙafa. Curry ta sanya ga miyar da take yi a kitchen, sannan ta koma ɗakinta. Duk wanda ya ga yadda take ta annuri dole ya fahimci akwai wani abu da ke faranta mata rai.
Wayarta da ke kan mirror ta ɗauka tare da zama a gefen gado, missed call ɗin Zuzee ta gani, sai dai ba ita ta fara kira ba. Lambar Jamsy ta danna, bugu biyu ta ɗaga. Cike da zumuɗin son sanar da Jamsy ta ce,
“Antyna ta kaina.”
Daga can Jamsy ta ce,
“Ya dai ƙanwata?”
Aisha ta ce,
“Sai na zo yi ma Malam godiya.”, shewa Jamsy ta yi,
“Ke ƙanwata, bani in sha.”
Aisha na dariyar jin daɗi ta ce, “Mairo na can hauka tuburan, gashi an ciro babyn jikinta, kwana ɗaya shi ma ya ce ga garinku nan.” Sai da Jamsy ta gama dariyar cikar burinsu na kai Aisha su baro sannan ta ce,
“Ai wannan yaron dama dole aljanu su kashe shi.”
Aisha ba ta san mutuwar yaron Maryam na da nasaba da asirin da ta yi ba sai yanzu, idanu ta ɗan zaro,
“Yanzu ba mutuwar Allah da Annabi ya yi ba?”
Ta faɗa bayan ta tashi tsaye.
Domin Jamsy ta ƙara tabbatar mata ne ta ce,
“Ko uwar idan kina son ta yi mugunyar mutuwa sai Malam ya sa a kauda miki ‘yar banza.”
Kasa ci gaba da magana da Jamsy ta yi saboda Khamis da ya kunno kai cikin ɗakin.
Cikin faɗuwar gaba ta samu kanta, tsammaninta ya ji wayar da take, don haka ta katse kiran ba tare da ta yi sallama da Jamsy ba. Cike da son gane idan Khamis ya ji wayar da take ta wayance. Ƙarasawa ta yi gefansa a kan sofa ta zauna.
“Yanzu ka shigo kenan.”
Ta faɗa tana dariyar yaƙe. Khamis ta kanshi yake, bai wani lura da yadda take ta kama kanta ba, ko ma ya lura ba ita ce a gabanshi ba, cewa ya yi,
“Umm shigowata kenan, ina ta sallama ba ki ji ba.”
Ƙara matse mishi ta yi.
“Waya nake a lokacin.”
Ya ce,
“Na gani ai da na shigo.”
Yadda yake mata maganar cikin sanyin murya ne ya tabbatar mata da bai ji ba.
Tambayar shi ta yi,
“Ya jikin Maryam ɗin?”
Cike da damuwa ya ce,
“To da sauƙi za’a ce, amma tana buƙatar addu’a saboda gaba ɗaya ciwonta ya tashi daga na asibiti ya koma na gida.”
Aisha ta san in dai aka dawo gida da magani to akwai yiwuwar tonuwar asirinta, don tsaf masu magani za su iya cewa asiri ne.
“Uhmm, to me zai hana a kai ta psychiatric hospital tunda kamar kanta ne ya taɓu.”
A yadda ta ƙarashe maganar kai ka ce har cikin ranta tausayin Maryam take yi.
Shiru ya yi don duk yadda ta so ɓoye dafin da ke cikin maganarta amma sai da ya ji raɗaɗin shi a zuciya. Maganar abinci yayi mata wanda zai tafi musu da shi a asibitin.
Tashi ta yi ta koma kitchen. Shi kuma ya kishingiɗa kan sofar bayan ya ɗauke wayarta da ta manta a nan. Sosai ya yi nisa cikin tunanin Maryam wanda yake sa shi kukan zuci, musamman idan ya tuna da rasa ɗanta da ta yi, ga kuma ciwon da suke roƙon Allah ya yaye mata.
“Allah ya ba Maryam lafiya.”
Ya faɗa a ransa, tare da lumshe idanu, saboda wata irin suka yake ji a cikin zuciyarsa.
Wayar Aisha da ke kan jikinsa ce ta shiga ruri, a hankali ya buɗe idanu tare ɗaukar wayar ya duba. ‘Anty Jamsy’ ya gani a lambar. Shi dai ya san kusan duk contacts ɗin Aisha, daga family sai friends, idan aka kira ta bata kusa lokuta da dama yana ɗaga kiran.
Wannan kuwa da bai san ta a contacts ɗin Aysha ba ƙin ɗagawa ya yi. Sake kira aka yi bayan wayar ta tsinke.
Daga kwance da yake ya ɗaga muryarsa da bata fita sosai saboda damuwa ya kira Aysha. Sa’ar da aka yi tana kusa.
Da sauri ta karɓi wayar tare da ɗagawa ta ce,
“Zan kira ki Anty.”
A can baya kusan duk wayar da aka kira Aisha a gabansa take ɗagawa, wannan kuwa da ba gaskiya sai ta ƙi yin doguwar magana. Shi kuma da yake ba mai zargi bane sai bai damu ba.
Su Haneefa ne suka dawo daga school. Duk da suna yara amma basu matsa mishi ba don sun fahimci yana hutawa, saboda a kyawawan halayen Maryam ta koya musu kada su dami mahaifinsu in dai sun lura da hutawa yake yi.
Cire uniform suka yi tare da canja wasu kayan. Komatsansu na school suka ɗauka suka koma falo domin yin home work.
Khamis kuwa bai tashi ba sai da ya ji ana ta kiran sallar Azuhur. Ɗakinsa ya koma ya yi wanka gami da canja kaya, lokacin da ya fito har Aisha ta shirya mishi abincin da zai tafi da shi asibiti. Yara ne suka taya shi kai manyan food flasks ɗin mota. Sannan suka dawo cikin gida, basu wani matsa mishi akan za su bi shi ba don sun san anjima Aisha za ta tafi da su.
Ko da tafiyar Khamis sai Aisha ta koma ɗaki, kiran Zuzee ta yi don hankalinta ya kasa kwanciya a kan cewar aljanu suka kashe babyn Maryam.
Zuzee na ɗagawa ta ce,
“Ni fa na kasa sukuni.”
Daga can Zuzee ta ce,
“Da me kuma ya faru?”
Aisha ta ce,
“Ɗazu na faɗa ma Anty Jamsy baby ya mutu, sai ta ce ai dama dole aljanu su kashe shi.”
Zuzee ta fahimci Aisha tsoro take ji, don ta cire mata wannan tsoro sai ta ce,
“To miye na damuwa tunda ba ke kika kashe shi ba.”
Aisha ta ce,
“Ai ni na sanya.”
Zuzee ta ce,
“A’a, ba ki da hannu a nan, don haka ki kwantar da hankalin ki.”
Aisha so take ta kuɓuta daga zargin kanta, don haka sai ta yi gaugawar ɗaukar maganar Zuzee.
Asibiti kuwa, tuni Khamis ya kai musu abinci, kuma a gidansu ma an kawo. Daga gidansu Haupha ma sai da aka kawo, Rahama kuma ta yo musu coslow mai yawa don abincin ya yi musu daɗin ci. Ruwa da lemu kuwa tuni jama’ar Khamis sun aiko musu su da su.
Abincin da ke wurin ya musu yawa, ga asibitin private ce, duk kusan waɗanda ke wurin suna da abinci. Rufewa aka yi saboda baƙin da ke zuwa.
Maryam ma cikin ikon Allah ta ci abinci. Umman Khamis ce da kanta ta riƙa ba ta a baki, tana gamawa kuma ta koma bacci, don yanzu shi ne aikinta.
Tun bayan Azuhur visitors suka fara zuwa, kusan dangin Khamis ne saboda shi ɗan gari ne, sai kuma abokansa da matansu. Haupha ma ita da ƙawayenta duk sun zo, sai kuma wasu daga ahalinsu na mahaifi.
Duk wanda ya samu zuwa sai da ya tausaya ma Maryam, wasu ma har kuka suka yi saboda a gabansu Maryam ta yi ta fizge-fizge. Addu’a ce suka yi ta tofa mata a ruwa ana bata. A nan aka kawo shawarar a jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya. A nan tana karɓar magani wurin Doctors, sannan ga na islamic ana yi mata, haka ɗin aka yi a take, inda dama Khamis ya siyo Habbatu Ssauda tun jiya. Causin brother ɗinsa mai suna Adam ne ya karɓa ya yi addu’a a ciki, sannan ya ba da a riƙa shafa mata. Sannan yayi wasu addu’oi a ruwan da zata riƙa sha.
Fitowa duk wani namiji dake wurin yayi don a samu damar shafe mata jiki, sai Khamis kaɗai da ya tsaya.
Hajiyarsu Haupha na tsiyaya man a hannu Maryam ta dube shi tare da yamutse fuka.
“Miye wannan me hawan kai?” Hajiyarsu Haupha ta ce,
“Mai ne.”
“Wa za’a shafa mawa?”
Cewar Maryam tana toshe hanci.
“Ke za’a shafa ma wa.”
A tsiwace Maryam ta ce,
“Kai ba dai ni ba, ba wanda zan yadda ya shafa mini wannan mugun abun a jiki ya hana ni zaman lafiya.”
Shi dai Khamis da Ummansu ido ne kaɗai nasu, sai kuma tausayin Maryam ɗin da ya zame musu jiki.
Hajiyarsu Haupha na nufar Maryam da wannan Habbatu ssauda za ta shafa mata ta riƙe mata hannu gam tare da zare idanu.
“Na rantse da Allah ba za ki shafa mini shi ba, ke ɗin ma wacece?” Maryam yarinya mai sassauta murya ga manya, amma ita ce lalura ta sa take jayayya da su.
Ciwon da ke jikin Maryam ne kaɗai ya hana a shafa mata shi. Hajiyarsu Haupha na dariyar da kuka zai iya biyo bayanta ta ce, “Kin ci arziƙin ciwon da ke jikinki, amma da sai na shafa miki shi.” Hararar ta Maryam ta yi tare da kauda kai, ta kuma yi ma wuri ɗaya ƙuri.
Turo ƙofar aka yi, dangin Aisha ne da ita kanta Aishar suka shigo. Mommy ce da Alhaji Usman, sai kuma ƙannen Aishar mata.
Cike da mutunta juna suka gaisa, kuma suka nuna tsantsar tausayinsu ga Maryam, musamman Mommy da ta ji ciwon ya koma na iska.
Cike da damuwa ta ce,
“A maida ta gida mana, nan asibiti me za su yi ma Iska.”
Alhaji Usman ya ce,
“Ba ki ga aiki a jikinta ba, a bari ta ƙara samun sauƙi tukunna.”
Kai Mommy ta jinjina. Nan Khamis ya shaida musu nan da two days ma za a sallame ta In Sha Allah.
Fitowa suka yi, inda suka nufi baranda da duk wanda ya zo yake zama. Hira suke ta yi, shi kuwa Khamis hankalinsa na wurin matarsa.
Sanin akwai visitors ɗin da suke shiga gano ta ne sai ya je office ɗin Dini. Sosai yake son keɓancewa da matarshi, duk da keɓancewar ba ta ƙara mishi komai sai damuwa, amma ya gwammaci ɗaukar damuwar kusantar ta, a kan nisa dai ita.
Ce ma Dini ya yi,
“Ni fa son zuwa wurin matata nake, ga kuma mutane sun hana ni.”
Cike da tausayinsa Dini ya ce,
“Mu je na fidda maka su.”
Tashi ya yi suka tafi.
Ɗakin cike yake da mutane maza da mata. Kuma nutsuwar Maryam ɗin ce ta basu ikon zama a wurin.
Hannu Khamis ya miƙa ma ƴan’uwansa suka gaisa. Cousin ɗinsa mai suna Sagir ya ce,
“Haba Khamis, ka rage damuwa don Allah.”
Sauran danginsa suka sa baki. Kalmomi masu tausasa zuciya suka riƙa faɗa mishi.
Godiya ya yi musu, sannan suka fita bisa ga umarnin Dini.
Zama ya yi a gefen gadon, tare da riƙo hannunta,
“Maryam, ya jikin?”
A hankali ta ce,
“Da sauƙi.”
Lokaci ɗaya kuma ta zame hannunta, a ganinta bai kamata wani namiji ya taɓa ta ba.
“Kin gane ni?”
Kai ta girgiza “A’a.”
Cike da damuwa ya ce,
“Mijinki ne.”
Baya ta fara yunƙurin ja ta ce, “Shi ma fa wannan mugun da nake gani ce mini yake mijina ne, kuma a haka yake zalunta ta, shi ya sa na tsani jin sunan miji tunda mugu ne.”
Ido Khamis ya lumshe tare da buɗewa,
“To na daina.”
Gani ya yi ta sa hannu a ɗinkin da ke cikinta ta ce,
“Wai miye nan aka liƙa mini.”
Dini da ke tsaye a gaban gado ne ya dakatar da ita.
“Kada ki taɓa, ciwo ne.”
Ido ta ɗan zaro.
“Ciwo, a jikina?”
Khamis ya ce,
“Eh.”
Ta ce,
“Yaushe na same shi?”
Suka ce,
“Haihuwa kika yi.”
Ɗan jan maganar ta yi ta ce, “Haihuwaaaa?!”
Tare da ɗan yin shiru kamar tana son tuna wani abu. A hankali ta riƙa hango rayuwarta ta baya kamar a mafarki.
Ta san mafarki ba gaskiya ba ne. Kai kawai ta gyaɗa.
“To ina ɗan?”
Khamis ya ce,
“Ya rasu.”
Nuna mata hoton babyn ya yi wanda suke ita da shi, taɓa kanta a screen ɗin wayar ta yi,
“Wannan kamar ni.”
Khamis ya ce,
“Ke ce, wannan kuma shi ne ɗan da kika haifa, amma tun jiya ya rasu.”
Inda za ka fahimci hankalinta ya yi rauni sai kawai ta ce,
“Wayyo.”
Cikin sigar tausayi, tare da yin shiru.
Fita Dini ya yi daga wajen ƙofar domin amsa kiran da aka yi mishi a waya.
Ita kuwa Maryam dube-dube ta riƙa yi a ɗakin, can kuma sai ta ƙyalƙyale da dariya.
Khamis da ya kasa share hawayen da ke fita a idanunsa ya tambaye ta,
“Dariyar me kike yi?”
Nuna mishi ƙofa ta yi.
“Wani ne, wani ne gashi can.” Kuma sai ta tuntsure da wata dariyar.
Ido Khamis ya lumshe, yana jin wani irin ƙunci a ransa. Wai Maryam ɗinsa ce ta haukace!
Ɗankwalinta ta shiga tauna kamar akuya, Dini na shigowa ya ce,
“Ki daina.”
Kallon sama da ƙasa ta yi mishi, “Miye naka ko duka kayan ɗakin nan na cinye?”
Shi dai Khamis kallon ikon Allah kawai yake.
Turo ƙofar da aka yi ne ya sa suka juya su duka har da Maryam. Safara’u ce, wadda kuma ƙanwa ce a wurinsa. Sai kuma Yayanta Lamis.
Gaisawa suka yi, tare da yi ma Maryam ya jiki. Sai dai Maryam ba ta yarda sun haɗa idanu da Safar’u ba. Itama Safara’un shiru ta yi tana jin kamar ana yamutsa mata kanta.
Safara’u na ganin komai zai iya faruwa a tsakaninta da Maryam ta ce ma Khamis,
“Bari na je wurinsu Hajiya.”
Tare suka fita ita da Lamis.
Aikuwa tana zuwa wurinsu Umman Khamis ta fara huci. Mamanta wadda suke Uba ɗaya da Ummansu Khamis ta ce,
“Ya dai Safara’u?”
Saboda ta san halin ‘yarta.
“Wallahi asiri aka yi ma Maryam.”
Safara’u ta faɗa cikin ɗaga murya.
“Asirin uwaki.”
In ji Lamis, don ya san sauran idan ba taka mata birki ya yi ba, tsaf za ta birkice musu, duk wani mai iska a nan ƙarshe shi ma ya birkice su yi ta bori.
Cikin Aisha ne ya murɗa saboda Safara’u na shirin tona mata asiri.
Ba Aisha ba, duk wanda a dalilin Maryam ya zo asibitin bai son Safara’u ta tada musu hankali. Gida aka ce Lamis ya maida ta, tana cijewa ba zata shiga mota ba ya daka mata tsawa, da yake tsoronsa take sai ta shige tana ta turo baki.
Bayan shi ma ya shiga ne ya ce, “Kina mini hauka zan bankaɗa ki waje mota ta murje ki ke da aljannun naki.”
A kan idon Khamis su Safara’u suka tafi, sai dai bai san dalilin tafiyarsu ba. Tambayar fushin me Safara’u ta ke ya yi, aka faɗa mishi iska take shirin tada musu.
“Allah ya kyauta.”
Ya faɗa, sannan ya shaida musu ‘yan gidan su Maryam na gab da shigowa asibitin.
Hajiyarsu Haupha ta ce,
“Wannan tafiya an daɗe ba’a zo ba.”
Khamis ya ce,
“Motarsu ce ta samu matsala a hanya.”
Hajiyarsu Haupha ta ce,
“Ko da na ji.”
Aisha ta gaza sukuni, gani take kuma kowa ya ga irin kyarmar da take tun da Safara’u ta so ɓalle liƙi. Jin zuwan dangin Maryam ma ya ƙara sa mata tsoro a zuciya.
Khamis na shirin tafiya bakin gate tarbo ‘yan gidan su Maryam ta ce mishi za ta tafi gida tunda Magariba ta doso, cewa ya yi,
“Ki bari mu tafi gidan tare.”
Bai tsayan jin me za ta ce ba ya yi tafiyarshi.
Mutum biyar ne suka zo daga Katsina, Hajiyarmu, Zahara’u, Ƙanwar babansu Maryam, da kuma babbar yayarsu Maryam mai suna Lubabatu, sai kuma Auwal da ya kawo su, shi ma yayan Maryam ɗin ne.
Tun farkon ganin su da Khamis suka fahimci Maryam na cikin wani hali, saboda ramar da ya yi.
Jikinsu a sanyaye suka ƙarasa wurin da su Ummansu Khamis suke. Sannu da zuwa sun sha ta a wurin duk wanda ke wurin. Aisha da ke ta noƙe kai kuwa basu wani damu da ita ba. Sai ma Hajiyarmu ta jawo Haneefa a jikinta saboda sun san juna a waya, kafin Aisha ta raba yaran da Maryam suna yin waya.
Ba wani dogon hutu suka yi a wurin ba, saboda sallar Magrib kaɗai suka gabatar.
Gaba ɗaya suka ɗunguma suka shiga wurin Maryam. Lokacin kuma abin na ka, saboda man Habbatussauda ɗin da Khamis ya shafa mata lokacin tana bacci.
Tamkar an watsa mata wuta a jiki take ji. Juye-juye ta riƙa yi saman gadon tana faɗin,
“Sai da na ce muku bana so, amma kuka shafa mini.”
“Wai miye aka shafa mata?” Hajiyarmu ta tambaya cikin faɗa-faɗa, don har cikin ranta take jin yanayin da Maryam ke ciki.
Mamansu Haupha ta ce,
“Magani ne fa, aljanun jikinta ne ba sa so, shi ne take haka.”
Matsanancin Kukan da Maryam ta fashe da shi ne ya karya musu zuciya. Ita dai Lubabatu sai dai fitowa ta yi daga ɗakin saboda bata iya ganin yadda ake riƙe Maryam. Faɗa Hajiyarmu ta kama yi akan kada wanda ya ƙara shafa mata magani, shi ma Dini bai san haka za ta kasance ba da bai bari aka shafa mata ba.
Wannan yanayi da ‘yan’uwan Maryam su ka ga ‘yar’uwarsu sai da suka ji ina ma ba ta zo ba. A gidan su Haupha suka kwana.
Hajiyarmu kuma ita ta kwana a wurin Maryam.
Akwai shaƙuwa a tsakanin Maryam da Hajiyarmu, don haka ba ta sake bari aka ɓata ran Maryam ba, bare har ta kama yi musu kururuwa.
Kwanansu biyu aka sallami Maryam, don ta ji sauƙi sosai.
Gidanta suka wuce aka haɗa mata kayanta, saboda dama da ita zasu koma.
A yadda Aisha ta kama kanta duk wanda ya gani zai fahimci ba ta da gaskiya, su kuma da yake manya ne sai suka nuna mata duk ba komai.
Ana gama kimtsa Maryam suka ɗauki ƴarsu sai Katsina. Inda Khamis da su Rahama kuma suka biyo bayansu a tasu motar.