Skip to content
Part 19 of 21 in the Series Kishiyar Katsina by Hadiza Isyaku

Kallo mai cike da nutsuwa Ameer ya yi ma Khamis, kasantuwar sa Police sai ga shi ya fahimci lallai Khamis na da matsaloli ma ba matsala ba. Gyara zamansa ya yi sannan ya tambaye shi,

“Matsalar me?”

A hankali Khamis ya buɗe idanunsa da ke a lumshe saboda faɗuwar da gabansa ke yi.

“Ina son ka yi mini kallon tsaf, sai ka faɗa mini kalar canjin da ka gani a tare da ni.”

Ameer ya ce,

“Yi maka kallon tsaf kamar maida aiki baya ne, saboda tunda ka ambaci matsala na kalle ka, kuma na ganta, sai dai bana iya tantance wace kala ce sai ka faɗa.”

Jinjina kai Khamis ya yi sannan ya ce,

“Da kyau Ɗansanda.”

Shiru na wasu ‘yan daƙiƙu ya yi, yana kuma son tuna abubuwan da suka sa shi a matsala, Ameer kuwa ya zaƙu, don burinshi bai wuce jin idan akwai inda zai iya bada gudunmuwa a matsayinsa na Police ba.

Gaba ɗaya damuwar Khamis a kan Maryam take, zullumin tuna ta da kuma jimamin rashin sake neman ta ne jigon damuwarshi, idanunsa cikin na Ameer ya ambaci sunan shi.

“SP Ameer.”

Bayan Ameer ya ce,

“Ina sauraron ka.”

Sai Khamis ya ci gaba da faɗin, “Ban san wane hali Maryam take ciki ba.”

Cike da mamaki SP Ameer ya ce, “Kamar ya ba ka san halin da Maryam ke ciki ba, ina ce matarka ce, kuma ba ta da lafiya?”

Khamis ya ce,

“Duk da haka dai ban sani ba Ameer.”

Ameer ya ce,

“To me ya hana ka sani?”

Irin amsar farko Khamis ya sake ba shi,

“Shi ma ban sani ba.”

Ameer na cikin jerin mutanen da suka shaida son da Khamis ke yi ma Maryam, kasantuwarsa cikin jerin abokan da Khamis ya fi ji da su, kuma a wani ɓangare matar Ameer ‘yar Katsina ce, tare shi da Khamis suke koɗa matan Katsina, don shi ma ta shi gwana ce a wurin iya kula da miji, shi ya sa ma tasu ta zo ɗaya da Maryam, ga su ‘yan jaha ɗaya, bugu da ƙari ga su gwanayen mata. Maryam ta kan ƙyanƙyasa ma matar Ameer irin son da Khamis ke yi mata, ita ma tana faɗa ma Maryam irin son da Ameer ke mata. To kuma duk wadda ta keɓe da mijinta sai ta ba shi labari, a irin haka ne Ameer ya ƙara sanin ba ƙaramin so Khamis ke yi ma Maryam ba. Kuma a hakan ne Khamis zai ce bai san halin da take ciki ba? Bayan da idonshi ya ga yana sharar hawaye a asibiti duk a kan Maryam ɗin. Lallai akwai wani abu a ƙasa.

A zahiri kuma Ameer ya ce,

“To kana da matsala.”

Khamis ya ce,

“Na yarda ina da ita, sai dai fatan Allah ya magance mini ita.”

Rufe bakinsa ya yi daidai da kai hannu ya dafe kansa da ke mishi wani irin sarawa, sai da ya sake kashe wasu daƙiƙun sannan ya janye hannun tare da buɗe idanunsa da suka ƙanƙance.

“Ameer.”

Ya faɗa, wanda ya yi sanadiyyar tattaruwar nutsuwar Ameer a wuri ɗaya.

“Ina son Maryam har a cikin raina, amma ban san me ya sa firgici baya barina tunaninta ba, sannan bai bari na kalli ko hotunan ta, balle kuma na samu damar zuwa inda take duk da mawuyacin halin da take ciki, anya SP wani abu bai shafe ni ba nima?”

A yadda ya ƙarashe maganar kana ji za ka fahimci zuciyarshi a cunkushe take.

Ameer Police ne ƙwararre, a cikin Ɗansandan tunaninsa ya ce, “Akwai abin da ya same ka, ko dai ka daina son Maryam, ko kuma an yi maka sihiri don ka daina son ta.”

Faɗar Khamis ya daina son Maryam ma labari ne, don a yanzu haka jin kwararar madarar son ta yake a ƙoƙon zuciyarsa, ya fi gamsuwa dai da sihirin, sai dai wa zai yi? Ameer ya ce,

“Wanda bai son tarayyarka da Maryam mana.”

Tunanin wanda ya san bai son tarayyarsa da Maryam ya shiga yi, sai dai bai samu kowa ba sai Aisha, ita kuma yana tababar ba ta iya zuwa gidan boka.

“Ni dai Aisha ce kaɗai na san kishi na damunta a kan Maryam, kuma ba na jin za ta iya cutar da ni irin haka.”

So da yawa ana sa ran wuta a maƙera, amma sai a ga ta bayyana a masaƙa, Ameer ya ji a jikinshi Aisha ce don yana jin labarin takun saƙar da suke da Maryam a bakin matarshi, sai dai tunda mijinta bai zarginta to shi ma ba zai bayyana zarginsa a kanta ba, cewa ya yi,

“Gaskiya ba lallai ne ya zama ita ba, amma yana da kyau ka sanya mata idanu sosai.”

Maganar Ameer ta sanya Khamis jin son sanya ma Aisha ido, saboda tunawar da ya yi da lokacin da ya kama ta red handed za ta sanya ma Maryam maganin zubar da ciki.

‘To wanda ya iya ɓarar da ciki zai iya asiri?’

Tambayar da ya yi ma kansa. Lallai duk da halin damuwar da yake ciki dole ya sanya mata idanu domin samun amsar tambayar shi, musamman da ya san ta da bin zugar ƙawaye.

A cikin ɗan lokaci Ameer ya fahimci an yi ma Khamis farraƙu ne shi da Maryam, don ko da yake Police to kuma masanin ilimin addini ne. Shawara ya ba Khamis akan ya bi a hankali wurin sanya idanun, don idan ba ka iya kama ɓarawo ba shi sai ya kama ka. Sannan ya ba shi shawarar fara neman maganin sihiri don ko shakka babu shi ne a jikinsa

Khamis ya ce,

“In Sha Allah kuwa, in dai na gane mai son raba ni da farincikina da kai zan haɗa shi ka gyara mishi zama.”

Dariya kawai Ameer ya yi tare da yi mishi maganar motar da yake son canja ma matarshi.

Khamis na ‘yar dariya ya ce,

“Kana ji da matar nan taka.” Ameer ya ce,

“Ai dole Khamis, yarinyar ta iya kula da miji.”

Khamis ya ce,

“Ai ga alamu nan a jikinka, ka san jikin mutum na nunawa idan yana samun kula a wurin abokin zamansa.”

Ameer ya ce,

“Gaskiya ne.”

A cikin ransa kuma yana ganin hada rashin kular da Khamis ke samu ne ya ƙara canja shi.

Khamis ya ce,

“‘Yar Katsina ce ko?”

Ameer ya ce,

“Ƙwarai.”

Khamis ya ce,

“Wai miye sirrin matan Katsina ne, Maryam ma fa haka take da iya kula da namiji, ni sai da na ji da ita ce ta farko ba zan sake wani aure ba.”

Ameer na dariya ya ce,

“Uhm, a haka kuma ka manta da ita.”

Khamis ya ce,

“Kai ka san lafiya ba za ta sa in manta da Maryam ba.”

Ameer ya ce,

“Haƙƙun, Allah ya yaye”

Khamis ya ce,

“Amin.”

Wannan ‘yar maganar ta Maryam da Khamis ya yi ba ƙaramin daɗi ta yi mishi ba, don bai ji faɗuwar gaban da yake ji idan ya tuna ta ko ya ambaci sunanta ba. Hakan ya ba shi damar ci gaba da maganarta jefe-jefi.

Maganar wani mai maganin Islamic Ameer ya yi mishi. Khamis kuma ya yi na’am da zuwa wurin mai maganin, domin Ameer ya faɗa mishi abokinshi ne.

Lambar Malam Muhammad Ameer ya yi dialing, yana ɗagawa ya ce,

“Ya Shaikh.”

Daga can ɓangaren Malam Muhammad ya ce,

“Ɗansanda abokin kowa.”

Ameer na dariya suka gaisa, tambayar shi ya yi,

“Kana gida?”

Malam Muhammad ya ce,

“Eh yanzu nake shirin fita, ka san Weekend ranarmu ce.”

Ameer ya ce,

“Haka ne, to bari mu zo office ɗinka.”

Malam Muhammad ya ce,

“Kai da waye ne?”

Faɗa mishi ya yi tare da Khamis suke, kuma zai ba Khamis ɗin magani ne, da yake ya gane Khamis ɗin ya ce,

“A’a bari na jira ku a gidan.” Sallama suka yi da Muhammad. Ba tare da ɓata lokaci ba suka miƙe. Sai da Khamis ya kira yaronsa Lawal ya faɗa mishi zasu je wani wuri, fatan zuwa lafiya Lawal ya yi musu.

Motar Ameer suka shiga. A hanya Khamis ke faɗa mishi labarin yanayin da kullum yake samun kansa, ya ce,

“Ameer ji nake kamar an ɗora mini kaya masu nauyi a saman kai, banda zazzaɓi da faɗuwar gaban da ke hanani walwala, ga rashin cin abinci, har ulcer ta fara damuna.”

Murmushi mai ɗauke da tausayinsa Ameer ya yi, ya kuma ce,

“In Sha Allah komai zai zo ƙarshe tunda har ka fahimci kana da damuwa, matsalar a ce mutum na da damuwa amma bai san yana da ita ba, ka ga ba zancen ɗaukar mataki kenan.”

Khamis ya ce,

“Gaskiya ne.”

‘Yar doguwar tafiya suka yi sannan suka isa gidan Malam Muhammad. Da fara’arsa ya tarbe su tare da miƙa ma kowannen su hannu suka gaisa. Malam Muhammad ya ce ma अमीर,

“SP ya Jama’a?”

Ameer ya ce,

“Alhamdulillah.”

Ko da Malam Muhammad ya kalli Khamis sai ya fahimci akwai sihiri a tare da shi. Kai ya ɗan girgiza don Khamis yayi kalar tausayi. Sitting room ɗinsa suka shiga. A kan kujera kowannen su ya zauna sannan suka ƙara gaisawa, Tambayar Khamis ya yi,

“Malam ya rayuwa?”

Khamis ya ce,

“Alhamdulillah, amma ina buƙatar taimako irin naku.”

Malam Muhammad ya ce,

“Allah ya bamu ikon taimakawa, amma ba zan ɓoye maka ba akwai alamun sihiri a tare da kai.”

Duk da aikin Malam Muhammad akan Alƙur’ani da Hadith yake yinsa, amma yau da gobe ta sa yana fahimtar idan mutum na da sihiri a jikinsa.

Tambayoyi ya yi ma Khamis a kan abubuwan da yake ji, Khamis ya ce,

“Malam ina jin komai ma, sai dai abin da ya fi damuna shi ne ciwon kai da kuma fargaba, sannan ba na iya taɓuka komai sai yadda aka yi da ni, musamman a gida.”

Malam Muhammad ya ce,

“Toh ciwon kan shi ne alamar farko da ke nuna sihiri na tare da kai, don haka zan maka karatu kuma in ba ka wasu magunguna.”

Alwalla su duka suka yi a tsaftataccen banɗakinsa.

Sannan suka zauna a kan carpet suna fuskantar juna, Ameer kuma na daga gefensu a kan kujera.

Karatu Malam Muhammad ya shiga rerawa, aikuwa kan ka ce me jikin Khamis ya ɗauki karkarwa. Zufar tashin hankali ce ta shiga karyo ma Khamis, ji yake kamar ya gudu, sai dai kuma ba dama.

Malam Muhammad na lura da yanayin Khamis ya ƙara ƙaimi wurin karatun, duk wasu ayoyi da kuma addu’o’in karya sihiri da korar shaiɗanu sai da Malam Muhammad ya karanto su.

Ameer kuwa ba ƙaramin tausayin Khamis ya ji ba. Shi kuwa Khamis a hankali ya riƙa jin kamar ana rage mishi nauyin da ke kansa.

Lokacin da aka gama kuwa sai jin kansa ya yi sawai, godiya yayi ma Malam Muhammad, sannan ya dubi Ameer,

“Ka ji yadda kaina ya yi kuwa.” Ameer na dariya ya ce,

“Yo an kore albatsutsan da suka danne kan.”

Sosai maganar Ameer ta ba su dariya. Wani magani ne Malam Muhammad ya haɗa da zuma ya miƙa ma Khamis cup ɗin,

“Gashi ka shanye yanzu.”

Karɓa Khamis ya yi lokaci ɗaya kuma ya yi bismilla tare da shanye maganin da ƙyar, saboda maganin bai da daɗin sha.

Ruwa ya miƙa ma Khamis, yana sha kuwa sai ya ji amai ya taso mishi.

Banɗaki Malam Muhammad ya nuna ma Khamis, da sauri ya faɗa ciki ya dunga sheƙa wani irin baƙin amai mai sirkin jini.

Kiran Ameer Malam Muhammad ya yi, Ameer na zuwa ya ce, “Subhanallah, Malam ya haka?” Malam Muhammad ya ce,

“Gubar da ya sha ce Allah ya taimake shi yake fitarwa.” Nannauyar ajiyar zuciya Ameer ya sauke, sai da ya ƙara kallon aman sannan ya ce,

“Wai ina mutane za su ne Malam? Zukata sun ƙeƙashe, ba tsoron Allah a tare da su, yanzu wannan gubar da yake fitarwa ina imani ga wanda ya bashi ita?”

Malam Muhammad ya ce, “Wallahi SP babu, Allah dai ya sa mu fi ƙarfin zukatanmu.”

Ameer ya ce,

“Amin.”

Sannu suka riƙa yi ma Khamis don kamar zai amayar da cikinsa. Bayan ya gama ne ya wanke bakinsa da fuska, Ameer kuma ya wanke banɗakin, duk da Khamis ya so ya bar shi ya wanke, amma ya ce,

“Kai hutu fa kake buƙata.”

Malam Muhammad ya ce,

“Lallai kam.”

Komawa suka yi falon suka zauna. Khamis kuwa ji yake kamar zai faɗi, jingina bayansa ya yi da kujera ya lumshe idanu. Sannu suka riƙa yi mishi, bayan ya ɗan dawo daidai ne suka yi magana da Malam Muhammad, nan yake faɗa mishi matakan kariyar da zai ɗauka saboda gaba.

Ya faɗa mishi ya riƙa yawaita azkar da karatun Alƙur’ani, ya kuma ba shi ruwan addu’ar karya sihiri da wasu magunguna, faɗa mishi yadda zai riƙa amfani da su ya yi, akwai na sha da shafawa, sai kuma hayaƙi.

Duk wannan ƙoƙari da Malam Muhammad ya yi ma Khamis kyauta ne, saboda akwai alaƙa mai kyau a tsakaninsa da Ameer. Sai dai ya ce idan magungunan sun ƙare sai ya siya, don zai yi wata huɗu yana sha.

Kunun gyaɗa mai daɗi Malam Muhammad ya karɓo ma Khamis a wurin matarsa, saboda yunwar da ta taso mishi. Sosai ya sha kunun don dama masoyinsa ne, bayan kunun ya faɗa suka tashi, saboda Ameer da ake ta nema a Police headquater.

Godiya mai yawa da fatan Alkhairi suka yi ma Malam Muhammad sannan suka tafi.

Bayan sun ɗauki hanya ne Ameer ya ce ma Khamis,

“Gida zan kaika ko?”

Saboda alamu sun nuna Khamis na son hutu. Lokaci ɗaya Khamis ya ji ya tsani gidansa, kuma bai san dalilin wannan tsana ba,

“A’a kai ni gidanmu wurin Ummana.”

Ɗan duban shi Ameer ya yi, “Okay.”

Sannan ya maida hankalinsa ga tuƙi.

Sosai Khamis ke jin kaso mai yawa na damuwarsa ta tafi, duban Ameer ya yi.

“Gaskiya Alƙur’ani waraka ne.” Ameer ya ce,

“Ai duk wanda ya yi watsi da shi ya yi asara.”

Khamis ya ce,

“Lallai kam.”

Wayar Khamis ɗin ce ta katse musu maganar, Aydah ya gani a screen ɗin. Dogon tsaki ya ja sannan ya ɗaga kiran, gaisawa suka yi, yana jin za ta fara yi mishi surutu ya ce,

“Zan kira ki.”

Daga can ta shagwaɓe,

“Uhm yaushe?”

Ya ce,

“Anjima.”

Bai tsaya saurarar abin da take cewa ba ya katse kiran, saboda wata irin tsanarta da yake ji a ransa wadda ta yanzu ta zarta ta kullum.

Ameer dai yana ta jin ikon Allah, tambayar kansa ya yi ‘Ko an yi sabuwa ne?’

Labarin da Khamis ya bashi ne amsar tambayar shi, inda ya faɗa mishi asalin haɗuwarsu da Aydah ta waya ne. Ya kuma faɗa mishi irin zaƙewarta wadda ke ƙona mishi rai, Ameer ya ce,

“Mace mai kauɗi da rawar kai ba ta yi ba, irin su sai su ga kamar suna birge mutane, ba su san tsana da tsangwama suke siyo ma kansu ba.”

Khamis ya ce,

“Wallahi kuwa, ni dai na tsani wannan yarinya, kawai dai ina son mu rabu lafiya ne don kada ta ce na wulaƙanta ta.”

Birki Ameer ya taka sakamakon umurnin stop da traffic light ya ba su. Duban Khamis ya yi yana dariya don ya ga tsanar ta a tare da Khamis,

“A’a ka daina tsanar ta, ba ka sani ba ko ta zama ta uku.”

Saurin tarbar maganar shi Khamis ya yi,

“Allah ya kyauta, biyun ma sun wadatar.”

Dariya suka yi sosai, sannan Ameer ya tambaye shi sunanta, Khamis ya ce,

“Wai Aydah.”

Ameer da ya san hanoyin cutarwa na da yawa ya ce,

“Wanda ta faɗa maka ba.”

Khamis ya ce,

“Nima ina zargin Aydah sunan ƙarya ne, tana da wani.”

Tafiya Ameer ya yi saboda hanyar da aka ba su, lokaci ɗaya kuma ya ankarar da Khamis inda ya ce “Kai da ke fama da lalura, kuma ka ke neman ƙarin wata lalurar.” Khamis ya ce,

“Kamar ya?”

“Wannan zamani, wa ya faɗa maka ana yarda da irin wannan, haka kawai ba ka san manufarta a kanka ba, za ka sake mata.”

Khamis shi ma ya yi mamakin yadda har ya iya sake ma wata macen da shi ya san ba aurenta zai yi ba, koda yake a lokacin bai da lafiya, amma yanzu tunda ya fara jin daidai dole ya san abin yi.

Lambarta aya ba Ameer cewar ya gwada ta, idan ma muguwa ce can ta haɗu da wanda zai yi maganinta, don Ameer jajirtaccen Police ne.

Unguwarsu Khamis suka shiga, tafiya kaɗan suka ƙara motar ta tsaya a bakin gate ɗin gidan.

Godiya Khamis ya yi mishi, sannan ya fito a motar tare da shiga gidan, shi kuma Ameer ya ja motarsa.

Bai taras da kowa a falon ba, don haka ya miƙe ƙafa kan kujera three seater, saboda baccin da yake ji.

Ummansa da ba ta daɗe da dawowa gidan ba ce ta fito falon, ganin Khamis a kwance ya ba ta tsoro, wani ɓangaren kuma ya mata daɗi, don kullum addu’ar ta kenan Allah ya karkato hankalin ɗanta ya dawo gare ta.

Tsaye ta yi a gabansa tana ƙare ma fuskarsa da ta faɗa kallo, sosai ta fahimci bai da cikakkiyar lafiya, kamar za ta yi kuka ta koma kan kujera ta zauna, lokaci ɗaya kuma tana kallon yadda yake bacci mai cike da aminci.

Shigowar yara ce ta tada shi. Gani yayi kowa na mishi kallon da ke nuna a kwai magana. Basarwa ya yi tare da yi musu magana. Gaishe shi suka yi, bayan ya amsa ne Umma ta yi musu umarnin su je su yi wasa.

Suna tafiya ta dube shi,

“Khamis yau kai ne a gidan?” Wannan magana ta sanya shi tambayar kansa ‘Na daɗe ban zo ba kenan?’ A zahiri kuwa kasa magana ya yi sai dai kallon mahaifiyarsa da ta yi jugum.

A hankali ya ce,

“Umma na shiga yanayin da ban san me ke faruwa da ni ba. Amma yau Allah ya fitar da ni.”

Ummansa ta daɗe da sanin akwai abin da ya faru da shi, don har gida Mamansu Haupha ta iske ta tare ta tambayarta ko Khamis ya saki Maryam ne don su san abin yi? Da ta nemi ba’asi Mamansu Haupha ta faɗa mata rabon shi da neman su wata uku kenan. Daga nan ne Umman Khamis ta gane dalilin da ya sa ‘yan gidansu Maryam suka daina ɗaukar wayarsu. Jiran zuwan shi ta yi, sai dai tunda ya ɗauke ƙafa ba ta sake ganinsa ba. Faɗa mata aka yi an ga Aysha a gidan wani ƙasurgumin boka, aikuwa ba ta sake neman shi ba, sai dai ta shiga addu’ar Allah ya kuɓutar mata da ɗa. Har gida ta samu Mamansu Haupha ta ba ta hakuri, ta kuma ce su ci gaba da addu’a kawai, domin akwai wani ɓoyayyen al’amari, wanda suke fatan Allah ya bayyana shi.

Ce mishi ta yi,

“Alhamdulillah Khamis, na daɗe da sanin ɗauke mana ƙafa ba yin kanka bane. Ni dai tunda Allah ya ba ka lafiya shikenan, duk wanda ya cutar mini da kai na bar shi da Allah.”

Shiru suka ɗan yi, kowa da abin da yake saƙawa a zuci, daga bisani maganar da Ummansu Khamis ke yi a zuci ta fito.

“Me na yi ma mutane da za su hana ni zaman lafiya ni da zuri’a ta?”

Kamar za ta yi kuka ta ƙarasa maganar.

Hankali tashe ya ce,

“Umma ba wanda ya isa ya yi mana abin da Allah bai yi mana ba.”

Lallashin mahaifiyarshi ya yi, bayan ta sauko ya ba ta labarin mawuyacin halin da ya samu kansa a ciki.

Ta ce,

“Ai tunda na daina ganinka na san ba lafiya ba, Hajiya Rabi ta zo har nan ta faɗa mini ka fita batun su da Maryam, faɗa mishi ta yi mahaifan Maryam sun fusata, har sun daina ɗaga kiransu.

Cikin wani tashin hankalin ya ce, “Umma ina zaton raba mu aka yi saboda ba na son ko tuna Maryam, nan gidan ma da na daina zuwa don kada ku yi mini maganarta ne. Kuma ko waye ya yi mana wannan ina fatan tonuwar asirinsa.”

Ummansu ta fara zargin Aisha, don banda gidan boka da aka ga fitowarta kuma su Hafsat sun je gidan ta yi watsi da su saboda ta yi baƙi, kuma a cikin baƙin ne wata ke yi ma Aishar maganar gidan Malamin da suka je, sai dai ganin su Hafsat ya sa Aishar basar da maganar.

Ɓoye ma Khamis zarginta ga Aisha ta yi, sai dai ta yi fatan duk inda gaskiya take Allah ya bayyana ta.

Maganar magani ta yi mishi don ta ga alamar yana buƙatar shi, faɗa mata daga wurin mai magani yake ai, har ma ya tuna ya bar magungunansa a motar Ameer.

Ummansa ta ji daɗi, fatan Allah ya kiyaye gaba ta yi mashi. Sallar Azuhur ya fita ya yi, yana dawowa ya ci abinci ya ƙoshi, tsarawa suka yi sai ya ƙara samun lafiya sannan za a je Katsina. Shirin tafiya ya yi, Ummansa ta ce mashi,

“Ka sa ido tare da taka tsantsan da gidanka, kuma ka riƙe addu’a.”

Zuciyarsa riƙe da wannan nasiha ta mahaifiyarsa ya nufi gidansa. A farfajiyar gidan ya ga an faka wata danƙareriyar mota, tambayar mai gadi ya yi,

“Wannan motar fa?”

Mai gadi ya ce,

“Wata Hajiya ce ta zo da ita.” Khamis ya ce,

“Ka taɓa ganin ta a gidannan?”

Don ya fara shirin sanya ido a gidansa, tuni ya kamata ya yi haka, amma tsananin kyautata zatonshi ga Aisha ya sa shi yin watsi da abin.

Maigadi ya ce,

“Eh Alhaji.”

Khamis ya ce,

“Ok.”

Sannan ya nufi ciki.

Shewar su ya ji suna kwasar dariya, muryar Jamsy ya ji tana faɗin,

“Ai ke Aisha kin kama ƙasa, yanzu juyinki ki ke son ranki.”

Aisha ta ce,

“To me ya fi raina, cin tsiren mata.”

Khamis bai iya laɓe ba, don haka ya kutsa kai cikin falon.

Aisha ta san Khamis ya zama mijin ta ce, don haka ba ta damu ba don ya ji maganarsu. Shi kuwa sai da ganin Jamsy ya kada mishi da gaba, don bai taɓa ganinta ba sai yau, haka kawai ya ji bai yarda da ita ba.

Gaishe da shi ta yi, a mutunce ya amsa sannan ya wuce ɗakinsa.

Sai da Aisha ta yi kusan minti biyar kafin ta same shi a ɗakin.

Wannan ne canjin farko da ya gani.

Na biyu kuwa bayan ta shigo ne yake tambayar ta,

“Waccan fa?”

Ta ce,

“Ƙawata ce.”

Ya ce,

“Ƙawa fa, ina za ki kai waccan giwar matar?”

Don Jamsy ta girme ta ba kaɗan ba.

“To ita abota ina ruwanta da shekaru?”

Ya ce,

“Babu.”

Ta ce,

“To ba ruwanka da ita, kada ka sake batun wata ƙawa tawa ma.” Aisha na da sarar yaɓa mishi magana, amma yadda ta yi saurin dakatar da shi a kan ƙawarta ya nuna akwai wani abu.

Da idanu ya bi ta lokacin da ta wuce. Har takai bakin ƙofa ya ce, “Me kika girka?”

Ta ce,

“Yau ba ka ci a waje ba?”

Ta yi wucewarta.

Yadda take mishi magana a gadarance ne ya ba shi mamaki.

Wanka tare da canja kaya ya yi, yana fitowa da nufin tafiya ta ce, “Sai ina Haji Khamis?”

Dakatawa ya yi don maganar ta mishi girma, wani irin kallo ya yi mata wanda ta kasa fahimtar manufarsa, ce mata ya yi,

“Waje ranki ya daɗe.”

Tare da sa kai ya tafi.

Aysha ta ce,

“To wallahi kada ka daɗe.”

Bai bata amsa ba ya fice falon, “Wai yaushe iskancin Aisha ya ƙaru ne?”

Da wannan tambaya ya isa gaban mai gadi.

“Sule, sau nawa ka taɓa ganin waccan matar?”

Sule ya ce,

“Sau biyu kenan.”

Khamis ya ce,

“To bayan ita fa su wa ke yawan zuwa a gidannan?”

Zuzee ce kaɗai ya san kusan kullum sai ta zo, Khamis ya ce,

“Ka ci gaba da sanya mini idanu don Allah.”

Jamsy kuwa hannunka mai sanda ta yi ma Aisha, inda ta ce,

“Sai ana yawan kai ma Malam ziyara fa, saboda asiri na karyewa.”

Don ta lura da kallon mamakin da Khamis ke yi ma Aisha.

Aisha ta ce,

“Gwara da kika tuna mini.”

Don so take ta dauwama tana mulka gida. Kuma ba zai yiwu ba. Rana suka fidda wadda za su koma wurin Malami.

Khamis kuwa yana fita ya kira SP Ameer, ce mishi ya yi,

“Ameer na fara zargin gidana.” Yadda suka yi da Aisha ya faɗa mishi.

Ameer ya ce,

“To ka yi irin yadda Al-ameen ya yi.”

Khamis ya ce,

“Wane Al-ameen kuma?”

Ameer ya ce,

“Na littafin Mai Awara mana, kasan shi ma haka matarshi ta so sabauta shi, asirin na karyewa ya ci gaba da pritending, aikuwa sai ga shi ya gano abubuwa da yawa.”

Shawarar Ameer kuwa ya bi, tamkar sakarai ya koma ma Aisha, mulki ta riƙa yi mishi a cikin gida, waya kowace iri ce sai ta yi ta a gabanshi.

A ranar da suka shirya za su haɗu da Jamsy ne ta ce mishi,

“Anjima zan fita fa, don kada ka taras da bani nan ka yi ta ƙorafi.” Cewa ya yi,

“To madam, ina za ki je?”

Ta ce,

“Ina ruwanka?”

Shiru ya yi, cikin ransa yana jin wani irin takaici, Aisha ta zama me kenan?

Tafiyarsa ya yi, amma hankalinsa ya ƙi kwanciya da sauyin yanayin matarsa. Kewar Maryam ke damunsa saboda ‘yan gidansu sun ƙi ɗaga wayarsa, ga kuma duk wani picture nata Aisha ta goge daga wayarshi.

Sai dai kuma tsoron halin da yake ganin Aisha na shirin faɗawa ya danne kewarsa ga Maryam, saboda zai iya shawo kan duk wani mai alaƙa da Maryam, amma Aisha idan ta lalace bai san yadda zai gyara ta ba. Uwar ‘ya’yansa ce, kuma ko ba su haihu ba yana son ta, son da a dalilin shi ne ya zauna da ita bayan ya kama ta za ta zubar ma Maryam da ciki. Tabbas ya tsane ta a lokacin, amma ƙaunarshi gare ta ce ta yi tasiri har son da yake mata ya dawo.

Kasa komai ya yi bayan ya fita, don haka bai jima a wajen ba ya dawo gida. Taraswa ya yi har ta shirya, kuma da yaranta saboda an yi hutun Islamiyya.

A gadarance ta ce,

“Har ka dawo?”

Ya ce,

“Eh madam, ba ki tafi ba?”

Ta ce,

“yanzu zan fita.”

Wayarta da ke kusa da shi aka kira, sai da ya duba sunan Anty Jamsy sannan ya ba ta waya. Yanzu kam ya san wacece Jamsy tunda har ta zo gidanshi.

Ɗaga wayar Aisha ta yi.

“Yanzu za mu fito Anty, har da yaran ma.”

Daga can Jamsy ta ce,

“Ina za mu je da yara?”

Aisha ta ce,

“A nan gidanki za mu bar su ai.”

Wani mugun kallo Khamis ya ci gaba da yi mata, sai da ya ga za ta juyo sannan ya yi saurin ɗauke kansa.

Tattara yaranta ta yi, Haneefa ta ce,

“Daddy ka taso mu tafi.”

Kai Khamis ya girgiza.

“A’a ni bana zuwa.”

Haneef kuwa tuni ya yi gaba don an ce gidan Jamsy za a je.

Aisha na fita, Khamis ya tari Ɗan Acaɓa suka bi bayanta don hankalinsa ya kasa kwanciya. Duk hanyar da Aisha ta bi, sai shi ma Mai Acaɓa ya bi, har suka isa gidan Jamsy, fitowa ta yi ta shiga, ba a jima ba suka fito suna kwasar dariya.

Gani ya yi sun shiga motar, shi ma acaɓan ya hau suka bi su har gidan Malam.

Mai a caɓa ya tambayi Khamis “Malam idan ba za ka damu ba, ya kuke da waccan da kake bi?”

Khamis ya ce,

“Matata ce.”

Kai Mai Acaɓa ya girgiza ya ce, “To gaskiya matarka ba matar arziƙi ba ce, duk wadda ta shiga wancan gidan to a yi mata addu’a kawai, saboda gidan ƙasurgumin boka ne.”

Ƙirji Khamis ya dafe,

“Boka?”

Shi a tsammaninsa hidima ake a gidan, don ya ga mata jefi-jefi suna shiga. Mai Acaɓa ya ce,

“Wallahi kuwa boka, Na sha kawo mata ai nan.”

Wutar Khamis ce ta ɗauke ɗif, sai da ya ji dama bai biyo Aksha ba bare ya ga wannan bala’in.

Tuni ya naɗi Vedion ta lokacin da suka shiga gidan. Aljihu ya maida wayar tare da duƙar da kansa a kan mashin ɗin.

Mai Acaɓa ya ce,

“Alhaji ka yi hakuri kawai, kuma ka bi ta da addu’a.”

Kasa magana Khamis ya yi, faɗin ruɗun da ya shiga bai misaltuwa. ‘Aisha ce ta haukata Maryam?’ tambayar bazatan da ta zo mishi a rai kenan.

Kasa amsa tambayar ya yi, sai ma ya riƙa ƙoƙarin yakice tambayar don kada amsarta ta ɗaga mishi hankali.

Wannan tsayuwar ba ta da amfani, don haka ya hau mashin ɗin suka tafi. Dubu ɗaya ya ba mai Acaɓan, ai kuwa ya yi ta godiya.

Cikin gida ya shiga, mai gadi na mishi sannu da zuwa, amma tashin hankali ya hana shi amsawa. Jagwab ya zauna a falo, dafe kai ya yi saboda ji yake kamar zai rabe biyu.

“Me na ragi Aisha da shi da ta zaɓi wargaza farincikina, meye laifina don na ƙara aure?”

A fili ya riƙa yin wannan maganar.

Neman laifin da zai ɗora ma kansa ya shiga yi, don kafa ma Aisha hujja a kan halin da ta jefa kanta na bin malamai, sai dai bai samu kansa da laifin komai ba, don har ga Allah yana kwatanta adalci a tsakaninta da Maryam, kishi ne ke ta ɗawainiya da ita, gashi har ta jefa mutane cikin mawuyacin hali.

Jikinsa ba daɗi ya ɗauko magungunan da ya karɓo a wurin Malam Muhammad ya sha tare da shafawa.

Sallar la’asar ya yi, yana dawowa ya kwanta nan a falo.

Aisha kuwa sai da suka gama yawonsu sannan ta ɗauko yaranta suka dawo gida. Kwance suka samu Khamis, sai dai bai iya taɓuka komai saboda ciwon zuciya da kama shi farat ɗaya.

Ita kuka, yara ma kuka. Waya ta buga gida, sai ga ƙanensa Mukhtar wanda bai daɗe da dawowa daga Lagos ba ya zo ya ɗauke shi. Wani private hospital aka kai shi. Sosai likitoci suka bashi agajin gaugawa.

Mahaifiyarshi da ‘yan’uwansa kuwa sababi suka shiga yi, don an ce ciwon zuciya ne, kuma matarshi ce sila, Rahama ta ce, “Wallahi mun gaji da alaƙaƙai, dole a bar mana ɗan’uwa ya huta.” Aisha kuwa mirsisi ta yi kamar ba ta san me suke cewa ba, don yanzu tana da maganin kowa.

Khamis kuwa baya son ganinta ma don baƙinciki take ƙara mishi, don haka tana tambayar shi me za a girko mishi, ya ce ta bari, daga gidansu za a kawo mishi.

Tuni kuma mahaifyarshi ta san komai. Fatan samun lafiya ta yi mishi, daga ƙarshe kuma ta bashi iznin zuwa wurin Maryam.

Abin da ke ranshi kenan, gidansu Haupha ya je, Hajiyarsu Haupha ta ce,

“Haba Khamis, ba mu yi zaton haka daga gareka ba.”

Cikin damuwa ya ce,

“Ku gafarce ni Hajiya, wallahi nima Allah ne ya kuɓutar da ni.” Labarin halin da ya shiga ya bata. Sosai ta fahimce shi don Khamis mutumin kirki ne.

Aisha kuwa tana ganin magungunan da yake sha ta ce,

“Na miye?”

Ya ce,

“Na komai ma.”

Ɗauka ta yi ta kai hancinta, karɓewa ya yi,

“Bani nan.”

“To ka bari in haɗa maka.”

Ya ce,

“Bana so.”

Sosai ta fahimci wani canji daga Khamis, duk wannan ladabin ya daina yi mata, girkinta ma ya rage ci, ɗakinsa kuma ya kwashe key ɗin, ba mai shiga sai yana nan.

Kiran Jamsy ta yi ta faɗa mata Khamis fa ya canja, kuma yana shan wasu magunguna.

Jamsy ta ce,

“Yi gaugawar zubar da su, kada su tona maki asiri.”

Shammatar Khamis ta yi ta shiga ɗakin, sai dai bata samu sa’ar ganin magungunan ba. Shi kuma sa’ar da ya samu a kanta ita ce, ɗaukar lambar Malamin da suke zuwa wurin shi, da kuma lambar Jamsy lokacin da ta yi mata Text tana faɗa mata yadda za ta yi amfani da maganin da suka karɓo.

Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba. Tunawa yayi da baƙin aman da ya riƙa yi a gidan Malam Muhammad, wanda ya samu yaƙinin mugun abu ne Aisha ta bashi ya ci. Don yanzu ma Jamsy ta ce idan sun gama mu’amala, to ta wanke gabanta sai ta haɗa da ruwan magani ta bashi ya sha.

Adana lambobin ya yi, suna haɗuwar da Ameer ya bashi su, cewar za a yi bincike, lambobi uku kenan ya bashi.

Tuni ta fice mishi a rai, ya kuma ɗauki matakin da ya dace da ita, wanda sai Maryam ta warke zai yanke shi a gabanta.

Ranar da ya ce zai je Katsina kuwa ruɗewa Aisha ta yi,

“Wato sun murɗa nasu kambun asirin ba.”

Dariya kawai ya yi. Cikin ransa kuma yana mamakinta, ga ta dai ita ce muguwar, amma ta kasa ganewa.

Cewa ya yi,

“Zan je ne a yi ta ta ƙare, kin ga kema sai ki huta ko?”

A tsammaninta zai saki Maryam ne, don ya daina maganar ma a gabanta, bare ta ƙara yin wani mugun abun.

Ranar tafiya Katsina kuwa ita ce ta shirya mishi kayanshi, ta ce za ta yi mishi girki ya tafi da shi a hanya su ci, ya ce,

“Na hutar da ke.”

Gidansu ya nufa, inda ya ɗauki Ruƙayya da Hafsat, sai kuma Haupha da ita ma ta zo domin su yi mishi rakiya.

<< Kishiyar Katsina 18Kishiyar Katsina 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×